Cikakken Bayanin Abubuwan Da Sai Dasu Aure Yake Zama Karɓaɓɓe

0
13
(1) Samuwar Amincewar Waɗanda za a Ɗaura wa Aure:

A shari’ance, aure baya zama zartacce, abin la akari da shi, sai idan an sami yardar ma’aurata da kuma amincewarsu.
Dalili kuwa faɗar Allah Madaukakin: “Ku auri abinda ya kwanta muku a rai daga matan (da suka halatta a gare ku), biyu-biyu ko uku-uku ko kuma hudu-hudu.
Da kuma hadisin da aka karɓo daga Ukbatu ɗan Amir (Allah ya yarda da shi) yace “Haƙiƙa Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) yace: “Da wani mutum (da zai ɗaurawa aure ) ka yarda in aura maka wance? Sai yace: eh (nayarda), sannan Annabi yace da matar: kin yarda in aura miki wane? Sai ta ce: eh (nayarda), Sai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ɗaura musu aure”. ( Baihaƙi da Hakim da wasunsu ne suka rawaito shi ).
Kuma Abdullahi ɗan Abbas ( Allah ya yarda da shi ) yace: “Haƙiƙa, wata budurwa tazo wajen Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) tace: Babanta ya ɗaura mata aure ( Da wani ) ba da sonta ba ( nan take) sai Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) ya bata zaɓin idan ta amince da wanda aka aura mata auren ya ɗauru, idan kuma bata son sa, to auren bai ɗauru ba”. ( Ahmad da Abu Dawud da wasunsu ne suka rawaito shi).
Sannan an karɓo daga khansa’u ‘yar khidan ( Allah ya yarda da ita ) Cewa: Babanta ya ɗaura mata aure da wani tana bazawara ba da sonta ba,sai taje ta shaidawa Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) sai yace :Auren bai ɗauru ba”. ( Bukhari ne ya rawaito shi ).

(2) Waliyyin Matar da za a Aura:

Waliyyi shi ne mutumin da alhakin aurar da mace yake wuyansu, kamar uba, ko madadinsa, ko shugaban musulmai.
Waliyyi ma sharadi ne daga sharuddan da sai dasu aure yake dauruwa a musulunce.
Saboda haka, bai halatta mace ta aurar da mace ba, kamar yadda bai halatta mace tayi gaban kanta ta aurar da kanta ga wani ba.
An karbo daga Abu Huraira ( Allah ya yarda da shi ) ya ce: “Manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) ya ce : “Mace bata aurar da mace, haka kuma mace bata aurar da kanta”. ( Ibn Majah ne ya rawaito shi ).
Kuma an karbo daga Ikrima da Abdullahi ɗan Abbas (Allah yayarda da su) sun ce: “Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yace:Babu aure saida waliyyi”.
Sannan kuma an karbo daga Aisha ( Allah ya yarda da ita ) tace: Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) yace: ” Duk matar da tayi aure bada izinin waliyyinta ba, auren ɓatacce ne,. Idan kuma wanda ya aure ta akan hakan, har ya sadu da ita to, ya bata sadakinta, saboda saduwar da yayi da ita. Idan kuwa mace da waliyyinta suka saɓa, to, shugaban musulmai shi ne waliyyin duk wacce ba ta da waliyyi”. ( Abu Dawuda da Ibn Majah ne suka rawaito shi).

(3) Shaidu:

Su kuwa shaidu su ne adalan mutanen da suke halartar gurin ɗaurin aure, su kuma kasance a gurin a lokacin daza a ɗaura auren.
A musulunce, mutane biyu sune mafi ƙarancin shidu game da ɗaurin aure. Saboda hadisin da aka karɓo daga Imran ɗan Husaini, da Aisha ( Allah ya yarda dasu ) cewa, Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) yace: Babu aure sai da waliyyi da kuma shidu biyu adalai”. ( Imam Ahmad ne ya rawaito shi ).

Amfanin Samarda Shidu a Aure:

Yana daga cikin amfanin da samar da shidu yake da shi:
1. Kawar da zargin zina, ko daduro tsakanin ma’aurata.
2. Hana a kira ‘ya’yan da mutum ya Haifa ‘ya’yan zina (shegu).

(4) Sadaki:

Sadaki shi ne dukiyar aure, wacce mace take cancantarsa daga wajen miji ta dalilin aure. Saboda faɗar Allah Maɗaukaki:
“kubawa mata sadakinsu cikin daɗin rai, idan kuma suka sayar muku da wani abu daga cikinsa da sonsu (don kansu), to, kuci shi (halak malak ) rai kwance”.
Da kuma faɗar Allah maɗaukaki:” To, waɗanda kuka ji daɗi da su daga cikinsu (mata) ku basu sadakinsu (cikakke) tilas”.
Sanan kuma Allah da hikimarsa da ya yi bayinsa bai yi su bai ɗaya ba, don haka ma, daya wajabta musu bayar da sadaki, sai ba iyakance musu shi ba. Saboda ya dace da mai hali da kuma mai ƙaramin ƙarfi. Kowanne gwargwadon halinsa.
Don haka, a musulunce ya halatta mutumin da yake da hali ya dunkule wasu maƙudan kuɗi ya bayar a matsayin sadakin matar da zai aura. Allah Madaukaki yace : ” Idan kuka yi nufin musanya wata mace a maimakon wata (da kuka saka) alhali kuwa da kun bawa dayarsu ( ta farkon ) dukiya mai ɗimbin yawa (a matsayin sadakinta ), to , kada ku karbi komai daga cikinsa, shin kwa karbe shi don zalunci da saɓo mabayyani”.
Sai dai kuma mafi falalar sadaki shi ne wanda bayayinsa ya zo kamar haka:
An karɓo daga Ukbatu ɗan Amir (Allah ya yarda da shi) yace: Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi) “ya aura wa wani mutum mace akan sadakin zobe na ƙarfe”. (Hakim ne yarawaito shi).
Bayan haka kuma, shi sadaki haƙƙi ne na matar da aka aura, kamar dai yadda bayani ya gabata. Saboda haka, bai halatta ba ga waninta yaci wani abu daga cikin sa, sai dai inda izininta.
To bayan kammalar bayanin waɗannan abubuwa da muka ji, anaso a lokacin daza a gudanar da ɗaurin aure a kwaikwayi Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) a rigayi ɗaurin auren da gabatar da wannan addu’ar kamar haka:
An karbo daga Abdullahi ɗan Mas’ud ( Allah yayarda dashi ) Yace: Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) ya koya mana yin ” Huɗubar Haja ” a lokacin ɗauren aure. Wato:
Innal hamdulillahi ta’ala, nahmadhu wanastagiynuhu, wanastagfiruhu, wa na’u’zu billahi min shuruwri anfusina wa min sayyi’a’ti a’a’malina, man yahdihil-llahu fala mudilla-lahu, waman yudlil fala hadiyaya lahu, wa’ashadu an lailahaillallahu wahdahu la shariyka lahu, wa’ashadu anna muhammadan abduhuwarasuluhu.
Ya ayyuhal lazina a’manuttaƙuwllaha haƙƙa tuƙatuhi wala tamutunna illa wa antum muslimun (Al-i-mran, aya ta (102)
Ya ayyuhannasu-ttaƙuw rabbakumullazhiy kalaƙakum min nafsin wahida wakalaƙa minha zaujaha wabassa minhuma rajalan kasiran wa nisa’a’wattaƙuwllahal lazhiy tasa’a’luna bihi wal’arhama innallaha kana alaikum raƙiyba (An nisa’i aya (1)
Ya ayyuhal-lazhina ‘a’manuttaƙuw-llaha wa ƙulu ƙaulan sadhidhan yuslih lakum a’a’malakum wa yagfir lakum zhunubakum waman yuɗi’illaha wa rasuluhu faƙad faza fauzan a’zhima (Al Ahzab aya,
Abu Dawud, da Nisa’i da wasunsu ne suka rawaito shi.
Sannan kuma ya halatta bayan gama daura aure, ranar akai amarya gidan miji, a buga dundufa domin sanar da aure da kuma faranta ran ango. Amma bai halatta ayi dauraba.

Ranar Haɗuwar Ango Da Amarya:

A musulunce ana so ranar da ango ya fara haɗuwa da amaryasa ko kuma ranar da aka kawowa ango matarsa gidansa, yayi ƙoƙarin yin waɗannan abubuwa masu zuwa kamar haka:
(1) Ango ya jagoranci matarsa suyi Sallah raka’a biyu- nafila don miƙa godiyarsa ga Allah daya cika musu burinsu kamar yadda Ibn Abi Shaiba ya rawaito.

(2) Ya ɗora hannunsa akan goshin matarsa, wato yakaanta ya riƙe, sannan kuma ya karanta wannan addu’a kamar haka:” Ya Allah ina roƙonka alherin wannan mata da alherin da ka halicceta akansa, kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin abin daka halicceta akansa”. ( Bukhari a cikin lianttafinsa da Abu Dawuda da Ibn Majah da wasunsu ne suka rawaito shi ).

(3) Gabatarwa da amarya wani ɗan abin kusa da baka, kamar yadda Annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) yayi wa matarsa Aisha (Allah ya yarda da ita ).

(4) Goge baki kafin kwantawa da amarya, domin kawar da wani hamami, ko wari da ka iya tashi daga cikin baki. Kamar yadda aka samu Muslim da Abu Awana sun rawaito Annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) ya yi haka.

(5) Yin addu’ar saduwa da mace, kafin fara saduwa da ita. Addu’ar kuwa itace: ” Ya Allah ka nesantani daga shaiɗan ka kuma nesanta shidan daga abin daka azurta ni da shi”.
Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) yace: Idan Allah ya hukunta wa miji da matarsa samun ɗa a saduwar da suka karanta wannan addu’ar, to, shaiɗan ba zai cutar da ɗan da suka samu ba har abada”. (Bukhari da Muslim da wasunsu ne suka rawaito shi ).

(6) Yin walima da abin da Allah ya hore, bayan tarewa da saduwa da amarya. Saboda aiwatarwar Annabi da kuma umarnin da yayi na ayi walima.
Sannan kuma idan za a kira jama’a walima, to ayi kokarin ganin an tara wadanda suke mabukata, saboda Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ) yana cewa: ” Mafi sharrin abinci walima, wanda ake kiran (ko gayyatar) mawadata a kyale mabukata “. ( wato a ki gayyatarsu ). ( Malik da Bukhari da Muslim da wasunsu ne suka rawaito shi ).
Daga lokacin da Allah ya hukunta wa Musulmi aurar wata mace, ko kuma ya hukuntawa Musulma auren wani Musulmi, to ya zamar musu lallai su san cewa, a musulunce akwai wasu nauye-nauye da suke tattare da rayuwar da zasu fuskanta ta zaman aure, wadanda suka sha bamban dana irin rayuwar da suka faro a baya ta zaman kaɗaici.

Domin karanta cikakken bayani akan Nauye- Nauyen Rayuwar Aure danna koren rubutun nan.

Wannan bayani anciro shi ne daga littafin Nagartacciyar Rayuwar Aure wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna koren rubutun nan.