Category: WikiHausa

Yadda ake amfani da WikiHausa

  • Baɗi Ba Rai Kashi Na Ɗaya

    Baɗi Ba Rai Kashi Na Ɗaya

    A short story by
    Sakina Yazid (Innar su Amal)

    Kamar duk lokacin da irin wannan abun ya faru yau ɗin ma haka ta shiga gidan cike da tashin hankali; duk da dai ta daina kukan ta share hawayenta. Hawayen iya na fuskarta ne kawai ta share amma tabbas ta san ba za ta iya daina kukan zuciya ba, ko za ta daina to ba ta san lokacin da za ta daina ɗin ba.

    Parlor ɗin shiru, da alama Umma da kuma su Maimuna suna ɗaki; wataƙila suna sallar la’asar domin lokacin sallar ne. Kai tsaye ta wuce ɗakin Umman ta tura ƙofar ta shiga da sallama.

    A kan dadduma ta hango Umman tana zaune tana azkar. Kallon da Umman ta yi mata ya sa duk wani karsashi da ta taho da shi ya zube kafin ta ƙarasa gabanta. Ta riga ta san amsar da Umman za ta ba ta guda ɗaya ce; wato wadda ta saba bata. Zuwa yanzu ma gani take yi gaba ɗaya kamar Umman nata ta ƙosa kuma ta gundura da jin matsalolinta.

    To amma idan ba wajen Umman ba ina za ta? Da wa za ta yi magana ta ji sanyi a ranta? Duk da dai yin maganar bai taɓa samar mata mafita ba. An riga an hane ta da yin ƙawaye tun lokacin da aka yi mata aure, don haka ta fita harkar ƙawayen har su ma suka rabu da ita. Mutum biyu ne a rayuwarta iyayenta da kuma mijinta Misbahu; su suka fi mata kowa muhimmanci a rayuwarta kuma su ne suke neman tura cikin halaka.

    Cikin sanyin jiki ta ƙarasa gaban Umman ta sauke goyon Adnan ta zaunar da shi; nan da nan kuwa ya rarrafa yana dariya ya haye jikin Umman wadda ta ɗauke shi tana dariya.‘Umma ina wuni.’ Ta faɗa cikin sanyin murya. Ta harareta sannan ta amsa ‘Lafiya ƙalau. Yanzu kuma me aka yi na ganki fuska duk a koɗe?’

    Ta sunkuyar da kai ta yunƙura ta haɗiye malolon da ya tokare mata ƙirji, ta buɗe baki da ƙyar tace ‘Umma duka na ya yi, kuma ya gaya min maganganu na wulaƙanci fiye da yanda ya saba gaya min. Ga neman mata Umma, a gabana zai yi waya da budurwa ya saka a loudspeaker wai na ko yi soyayya.’

    Cikin damuwa Umman ta sauke Adnan wanda ya kama rarrafe a tsakar ɗakin, ta dube ta cikin natsuwa kamar me nazari sannan tace ‘To in dai maganganu ne menene ba ki ji ba a bakin Misbahu? Ai tuntuni nace ki fita harkarsa ki mayar da hankali wajen wannan yaron da Allah ya ba ki. Kuma yau ya aka yi kika biye masa har ya kai miki duka?’

    Ta share hawayen da ya gangaro a kan fuskarta, ta yi ajiyar zuciya a karo na babu iyaka sannan tace ‘Hayaniyarsa ya gama yi ya shiga ɗaki ya kwanta shi ne na shiga maƙota dubiya. Shi ne ina dawowa ya hau zagina, kuma na ce ya yi haƙuri shi ne ya mammare ni yace wai zuwa na yi maƙota na kai gulmarsa.’

    Nan da nan ta sake fusata tace ‘To ke me ya kai ki maƙota kin riga kin san halin mutumin nan? Na riga na gaya miki ki fita harkarsa ki bar shi da mugun halinsa. Idan ba ya son shiga maƙota to ai sai ki bari. Umma bai taɓa hana ni shiga ba wallahi. Kuma na gaya miki idan ya tashi wulaƙancinsa bana ma sanin me na yi masa, tunda ko na saba yin abu wataran sai kawai ya hau zagina a kai.’

    ‘To ai sai ki kiyaye, tunda kin ga dai mahaifinki da kansa ya yi masa magana kuma yace ya daina. Ki je ki cigaba da lallaɓa shi ki mayar da hankali kan ɗanki. Bawa ba ya wuce ƙaddararsa, wata ƙila ke taki ƙaddarar kenan.’

    Suka yi shiru na ɗan lokaci; Farida tana ta faman share hawaye yayin da Ummanta take faman hidima da Adnan. Jimawa kaɗan tace ‘Umma na gaji da auren mutumin nan wallahi, son shi ya fice min daga rai. Bana son zaman gidansa; idan ina cikin gidan ji nake kamar an saka zuciyata a keji kuma an kunna wuta a cikin kejin. Wallahi Umma wulaƙancin da yake min ya ishe ni.’

    Ta kawar da kai tare da haɗe fuska sannan tace ‘Haƙuri za ki je ki yi, tunda dai mutumin nan babu abinda ya rage ki da shi; ci, sha sutura da sauransu. Ko muma nan kullum cikin hidima yake da mu. Kina kallo ga ƙannenki can a gidajensu amma ke kullum kina tafe kawo ƙara. Ni kaina da kika gani idan da ban yi haƙuri da ubanku ba da yanzu wani zancen ake ba wannan ba.

    Kuma ma idan dai maza ne na yanzu duk haka suke kowanne da tashi matsalar musamman neman matan; idan kin fito ba ki san gidan wanda za ki koma ba. Idan ma kin sami mijin kenan.’

    Haka dai Umma ta ƙare mata faɗa da nasiha sannan ta tursasata ta koma gidan; domin a faɗarta ba ta ma so a ɗaga maganar balle mahaifinta ya ji don ita ma sai ya yi mata faɗa. Don haka cikin matsananciyar damuwa ta goya Adnan suka kama hanya.

    Ƙwaƙwalwarta ta cushe gaba ɗaya; wace irin rayuwa ce wannan? Auren soyayya suka yi da Misbahu amma yanzu ba shi da aiki sai cuzguna mata; duk da dai ba wai kullum ba ne yake mata hakan. Sai suna zamansu lafiya kamar kowanne ma’aurata laifi kaɗan sai ya gaya mata maganganu masu zafi watarana ma ya mammare ta.

    Ga shi ba ta sanin wanne laifi ne za ta yi ya haifar da hakan don haka kullum a ɗari-ɗari take a gidan. In dai haka maza suke to idan ta samu ta rabu da Misbahu ma babu wani auren da za ta sake balle a ce ba a san wa za ta aura ba; tana ji a jikinta zawarci zai fi mata sauƙi da wannan rayuwar da take yi yanzu.

    Tana hango gidan bugun zuciyarta ya ƙara sauri, wata sabuwar fargaba ta shige ta. To amma idan ba nan ba ina za ta? Gidansu ne kawai ragowar gatanta kuma can ta je aka koro ta. Haka ta ƙarasa ta shiga gidan tana fatan idan dai har mutuwa ce za ta raba ta da Misbahu to tabbas ta shirya mutuwa don tana da yaƙinin Allah zai ji tausayin ta.

    Yana kashingiɗe a parlor ɗin a kan 3-seater ta tura ƙofar ta shiga; ƙasa-ƙasa ta yi sallama ta shige ba tare da ta saurari amsa ba. Tana jin ƙwayar idonsa yana bin ta da kallo na wulaƙanci irin wanda ya saba. Sai da ta kai tsakiyar parlor ɗin tana daf da shiga ɗakinta ya daka mata tsawa.

    ‘Daga ina kike? Akuya sarkin yawo.’ Ta ɗan diririce tana shirin komawa da gudu sannan ta dage ta lalubo nutsuwarta cikin in-ina tace ‘Gidanmu na je. Ya sake ƙare mata harara yana jan dogon tsaki ‘Mtsewww!’ Ta bi bango ta shige ɗakin ta turo ƙofar tana fatan kada ya zo yace zai doke ta.

    Haka ta lallaɓa ta yi sallar magriba sannan ta fito ta ɗora abincin dare tun kafin ya nema ya ɗaga mata hankali. Ya riga ya san babu abinda za ayi duk da kai ƙarar tasa da ta yi, don haka da ya fita ma bai dawo gidan ba sai da sha biyun dare ta gota; lokacin ta daɗe da yin bacci.

    A hankali suka ɗan shirya kamar yanda suka saba, sai dai ita duk a firgice take. Zama take na ɗari-ɗari a gidan saboda ba ta san me za ta yi ta tsokano shi ba. A bayan layinsu aka yi haihuwa, kuma da yake ya san maigidan tun jiya ya ba ta izinin zuwa suna da ake yi yau Asabar.

    Wajen 12pm maƙociyarta ta yi mata sallama a kan ta zo su je sunan don ita daga can za ta wuce cikin gari. Nan suka haɗu su uku maƙota suka wuce. Tun da suka shiga layin gabanta yake faɗuwa; akwai gidaje na ƴan jami’a a layin inda wasu ƴan mata ne suke zaman kansu wasu kuma samari.

    Akwai wata yarinya Shahida wadda Misbahu yake nema; ba ta taɓa ganin yarinyar ba amma an tabbatar mata a nan layin gidan yarinyar yake. Don matan layinsu ma sun sha gaya mata sun gan shi da yarinyar ya sauke ta nesa da unguwar. Sun yi magana sau babu iyaka har ma ta gaji; tunda yanzu ma a yanda ake ya gaya mata idan ta ƙara yi masa maganar wata daga cikin ƴan matansa sai ya kora ta gida ya kawo matan gidan ya ga idan akwai wanda ya isa ya hana shi.

    Haka dai ta dafe zuciyarta suka ƙarasa cikin gidan sunan; nan da nan kuma da suka haɗu da matan unguwa ta manta da komai aka ci gaba da hira cikin walwala. Sun kai kimanin awa ɗaya, ‘ƴan matan suka shigo gidan; da yake ba wani sosai aka cika tsakar gidan ba sai da suka tsallake suka zo kusa da Farida sannan suka zauna.

    Suka gaggaisa da mutane da alama wasu daga cikin matan da suke zaune a wajen sun san su. Ita ma Farida ta waiga ta gaisa da su. Suka tambayi maijego aka ce musu yanzu ta shiga canza kaya don haka suka zauna nan aka cigaba da hira.

    Jimawa kaɗan suka jiyo muryar maijego daga parlor tana magana da wasu matan. Ɗaya daga cikin ‘ƴan matan nan wadda take zaune kusa da Farida ta buɗe baki ta ƙwala mata kira bayan ta amsa tace ‘Da Allah ki zo ki nuna min matar masoyina na yi mata kallon ala tsine uwar mai ƙarya; ko da yake dai ya gaya min kalarta.’

    Ta fito daga parlor ɗin tana dariya ta nuna yarinyar tana cewa ‘Shahida ba fa na son wulaƙanci, duka nan babu sa’anki ƴar rainin hankali.’ Aka sheƙe da dariya gaba ɗaya wajen. Farida tana jin an ambaci Shahida ta sha jinin jikinta; ta juya ta kalle ta suka haɗa ido yayin da yarinyar ta tintsire da dariya. Maƙociyarta wadda suka zo tare ta taɓa ta tace ‘Tashi mu tafi Maman Adnan.’

    Suka miƙe a tare, ita ma Shahida ta miƙe tana dariya da kallon raini tana cewa ‘Ashe ma kusa dake na zauna, sannu fa. Mai jego tace ‘Ke Shahida ba fa na son raini… A a ku fa uwayen gidan nan haka kuke wallahi, ba ku iya kula da miji ba sai ikon tsiya. To komai baƙin cikinku sai mun shigo.’ Ta faɗa da shaƙiyanci tana dariya.

    Farida ta ja tsaki, ta raɓa ta gefenta ta wuce, maƙociyarta Anti Amina tana biye da ita. Ta ƙyalƙyale da dariya tace ‘A a fa kada ki bangaje ni idan ba haka ba wallahi na sa a baki red card a daren nan ki kwana gidan father ɗinki. Farida ta shammaci mutanen da suke wajen ta juya ta yi taku ɗaya ta ƙarasa gaban Shahida ta sauke mata mari a kumatunta.

    Nan take wajen ya yi tsit yayinda Shahida ta dafe kumatunta tana fitar da hawaye. Farida ta nuna ta da yatsa tana cewa ‘Idan ke ‘ƴar halak ce ki ba shi umarni kada ya bar ni na kwana a gidan yau.’ Ta sauke yatsan sannan ta cigaba ‘Ko da yake ba zan yi mamaki ba idan ke ɗin ba ‘ƴar halaka ba ce tunda ga shi nan kin mayar da kanki kamar public toilet.

    Kowa ya tashi juyen ƙazantarsa sai ya zo ya haye kanki. Ki bashi umarni yau kada ya bari na kwana a duniyar ba ma a gidansa ba. Ta juya ta fice ba tare da ta saurari kowa ba Anti Amina tana biye da ita. Nan ragowar matan da ke tsakar gidan suka haɗu da maijego suka fara ba wa Shahida haƙuri.

    Ta share hawayenta ta zauna, ta zari wayarta tana cewa ‘Wallahi sai ta gane kurenta, sai na saka ya ci ubanta tunda ta mare ni. Kuma wallahi ita da zaman lafiya da Misbahu har abada, sai na yi ajalin wannan auren nata.’

    Suka cigaba da ba ta haƙuri maijego tana cewa ‘Ki dai yi haƙuri ki bar maganar nan tunda kin ga kece ba ki da gaskiya, Please ki fita harkar ta.’ Ta goge fuskarta ta dubi matan tace ‘Ku yi shiru zan yi waya da Allah.’ Nan da nan suka yi shiru saboda son jin gulma.

    Ta lalubi lambar Misbahu ta danna masa kira; bugu ɗaya kuwa ya amsa yana cewa ‘Ƴan matana ya aka yi ne, har kin…’ Nan take ta rushe da kuka; abinda ya saka shi ya ruɗe ya shiga jero mata tambayoyi ‘Babe me ya faru? Kina ina ne? Ko accident kika yi ne?’
    Ta sassauta da kukan tace ‘Matarka ce ta mareni kuma ta zazzage ni a cikin mutane.’

    Cikin ƙosawa yace ‘Ban gane ba, Farida? A ina kuka haɗu? Ko gidan kika je? Ta sheƙe majina irin na me kuka tace ‘A gidan suna muka haɗu nan kusa da gidanmu, shi ne ƙawarta ta nuna mata ni suka haɗu suka yi min wulaƙanci a cikin mutane kuma ta mammare ni.

    Dole sai fitowa muka yi ni da Ikram saboda kunya. Wai ni take kira public toilet har da cewa ni ba ƴar halaka ba ce. ‘Ya isa, ki daina kukan mana. Kina ina ne na zo yanzu? Sai na ji yanda aka yi, kema kin san ba zan ƙyale ta ba.’ ‘Ni kada ka zo inda nake, ai duk kai ka janyo tunda kai ne kake zuwa kana ba ta labari na har ta sami damar yi min wulaƙanci.’

    Ta tsinke wayar ba tare da ta saurari amsar shi ba, ta mayar da wayar cikin jakarta ta kama hannun ƙawarta suka fice.

    Cike da damuwa Farida ta koma gida; ba ta nadamar marin da ta yi wa Shahida, amma dai tana fargabar haɗuwarta da Misbahu. Don ta san tabbas idan bai mammare ta ba to sai ya yi mata zagi na ƙasƙanci; idan ba ta yi wasa ba ma to sai ya ba ta red card kamar yanda budurwar tasa ta faɗa.

    Haka Anti Amina ta ɗauki lokaci tana ba ta haƙuri sannan ta bar ta ita ma ta wuce nata gidan. Ba ta jima da shiga gidan ba Maryam yarinyar da take mata aiki ta shigo; tunda dama tace mata ta zo bayan 2pm. Ta ji daɗin shigowar tata saboda ta san ko da Misbahu zai shigo yanzun to zai ƙyale ta a ƙalla zuwa lokacin da Maryam ɗin za ta tafi; kafin nan ta samu ta shirya yanda za ta ƙwaci kanta.

    A fusace ya shigo gidan wajen 2:30pm; tunda sai da ya tsaya a wajen Shahida ya lallaɓa ta yayin da ita kuma ta ƙara yi masa fanfo sannan ya huto gidan. A lokacin da ya shiga gidan Maryam tana kitchen tana aikinta yayin da ita kuma Farida take ɗaki tana kwantar da Adnan wanda ya yi barci.

    Ba ta rufe ƙofar ɗakin sosai ba don haka bai ma kula da mutum a kitchen ba ya shige ɗakin. Tana ƙoƙarin yi masa sannu da zuwa ya kama hannunta ya janyo ta daga ɗakin tana turjewa tana tambaya ‘Abban Adnan lafiya kake ja na haka? Ka bari na gyara masa kwanciya mana.’

    Bai saurare ta ba kuma bai fasa jan nata ba, har sai da suka fito ƙofar ɗakin sannan ta samu ta fincike hannunta. Cikin ƙarfin hali tace ‘Wai meye haka Misbahu, ya za ka kama ja na kamar wata yarinya.’

    Ya ɗan ja baya yana mata kallo na takaici da mamaki saboda bai taɓa zaton za ta iya yi masa magana haka ba. Ita kanta ba ta san ina ta samu ƙwarin gwiwar ba amma tabbas tana jin yau ba za ta saurara masa ba.

    Cikin huci yace ‘Ni za ki yi wa rashin kunya saboda ba ki da mutunci ko? Saboda kin haɗu da ƴan iskan ƙawayenki sun hure miki kunne ko?’ Ta sun kunyar da kai tana ja da baya saboda yanda yake nufo ta, sai dai kafin ta yi wani yunƙuri ya kwaɗa mata mari. Tana ƙoƙarin dafe kumatun ya sake kwaɗa mata a ɗayan sannan yace ‘Wace shegiyar ce tace ki mari Shahida? Kuma sannan ki zage ta?’

    Nan da nan hawaye ya wanke mata fuska, cikin ƙunan rai tace ‘Ita ba ta gaya maka abinda ta yi min ba kafin na mare tan, ko kuwa nice wadda ba ni da gata da za ka zo kana mari na saboda karuwa? Ya yi wata ‘ƴar dariyar mugunta sannan yace ‘An mare ki ɗin, ko akwai abinda za ki iya yi a kai? Shashasha kawai.’

    Cikin kuka tace ‘Babu abinda zan iya yi amma zan cigaba da kai ƙara wajen Allah. Duk wanda ya zalunce ni Allah ya isa ba zan taɓa yafewa ba.’

    A fusace ya fara ƙoƙarin kwance belt ɗinsa yana cewa ‘Lallai yau za ki gane kurenki, ni kike yi wa Allah ya isa saboda ba ki da mutunci? Jikinki zai gaya miki. Kafin ta yi wani yunƙuri ya zabga mata belt ɗin wanda ya bi ta wuyanta ya sauka a saman bayanta. Ta gantsare ta saki wata ƴar ƙara tana ƙoƙarin sosa wajen dukan; wanda tuni ya riga ya yi ja zur ya tashi.

    Ya sake ɗaga belt ɗin ya zabga mata. Ta ja baya kamar za ta faɗi bango ya tare ta; ƙoƙari take ta shiga ɗakinta ta turo ƙofa amma sai da ta wuce ƙofar sannan bangon ya tare ta. A nan ta sulale ta zube saboda zafin dukan da kuma gigicewa. Ya gyara belt ɗin ya riƙe ƙasan yanda ƙarfen belt ɗin zai sauka a jikinta; a daidai lokacin kuma Adnan wanda ya riga ya tashi daga bacci har ya sauko daga kan gadon ya rarrafo ya nufi jikin mamansa yana kuka.

    A lokacin Misbahu ya riga ya ɗaga belt ɗin zai zuba mata; tana ƙoƙarin ɗauke Adnan belt ɗin ya sauka a ƙeyarsa. Nan take jini ya wanke mata jiki yayin da Adnan ɗin ya yi wata gajeriyar ƙara ya faɗa ƙirjinta kamar wanda aka jefa.

    Ta jijjiga shi cikin matsananciyar firgita tana kiran sunansa; a dai-dai lokacin Misbahu ya saki belt ɗin ya nufo kanta yana ƙoƙarin karɓar Adnan ɗin yana cewa ‘Me kika yi masa? Inna lillahi wa Inna ilaihi raji’un!’

    Maryam wadda take tsaye a bakin ƙofar kitchen tana kallon su tana share hawaye ita ma ta zuba ihu ‘Inna lillahi wa Inna ilaihi raji’un!’ Kafin su yi wani yunƙuri ta zura da gudu ta yi waje ta ƙofar kitchen tana faman ihu tana kiran mutane.

    Nan da nan jikin Misbahu ya hau rawa suka miƙe tare da Farida wadda ita ma jikinta yake rawa tana ta wani gunji ta ƙanƙame Adnan saboda yanda hawayenta ya bushe ta kasa kuka. Kai tsaye waje Farida ta nufo rungume da Adnan yayin da shi kuma Misbahu ya juya kan center table inda ya ajiye mukullin motarsa yana cewa ‘Ki tsaya na fito mu kai shi asibiti.’

    Kusan a lokaci guda suka ƙaraso tsakar gidan inda suka ci karo da Maryam mutum uku sune biye da ita; maƙocinsu Dr. Abdul da wani mutum tare da shi sannan kuma da maigadin gidan. Dr. ya sha gaban Farida wadda ko ɗankwali babu a kanta yana cewa ‘Subhanallah! Me ya sami Adnan ɗin?’

    Cikin rawar baki tana waigawa tana kallon Misbahu tace ‘Ya fasa masa kai da belt, ya kashe min yaro. Maryam wadda take share hawaye ta tsomi baki tana cewa ‘Dukanta yake yi da belt ɗinsa wallahi yana ɗagawa ya kwaɗawa yaron, dukansa ya yi da belt ɗin. Shi ne baban nasa.’

    Dr ya ja su suka koma kan baranda sannan ya ba ta umarni ta kwantar da Adnan. Nan ta shimfiɗe shi ta janyo gefen rigar ta ta fara goge fuska ba tare da ta damu da jinin da yake jikinta ba. Ya dudduba shi sannan ya juya ya dubi mutumin da suka zo tare da shi yace ‘Inna lillahi wa Inna ilaihi raji’un! Wannan sai dai a yi haƙuri Allah ya karɓi kayansa.’

    Nan take Farida ta juya ta cakume Misbahu tana cewa ‘Ka kashe min yaro, sai ka kashe ni ni ma. Da ƙyar ya samu ya haɗa hannuwanta ya riƙe tana faman kuka. A hankali kuma kamar wadda aka zarewa laka ta sulale ta zauna kamar me zaman tahiya ta haɗa hannuwanta guda biyu ta rike tana fitar da numfashi a hankali.

    Maryam ta ƙaraso ta zauna a kusa da ita suka yi jugum suna bin mutane da kallo. Mutumin da suka shigo da Dr ya dube shi yace ‘Ai sai an kirawo police tunda ya zama case ɗin accident kenan. Ba tare da ɓata lokaci ba ya fidda wayarsa ya kirawo ‘ƴan sanda, a lokacin ne kuma Misbahu ya sami dama ya koma gefe ya kirawo mahaifiyarsa.

    Jimawa kaɗan ita ma Maryam ta miƙe ta koma cikin gidan ta ɗaukowa Farida hijab ta zo ta saka mata sannan ta kama hannunta ta dangwala a wayarta ta buɗe ta lalubo lambar Ummanta ta kirawo ta. Abinda kawai ta iya gayawa Umman Farida shi ne Adnan ya rasu, ta katse wayar ta riƙe a hannunta suka cigaba da kallon ikon Allah.

    Kusan a lokaci ɗaya ƴan sandan suka iso da mutanen gidan su Adnan, kafin wani lokaci kuma mutanen gidansu Farida suka iso. Mahaifin Adnan shi ya ja ƴan sandan ya sallame su, kusan ma babu wanda ya kula da lokacin da suka sulale suka fice.

    Tunda Umman Farida ta iso take fama da Farida a kan ta shiga cikin gidan su zauna amma ta ƙi, kuma ta ƙi yi wa kowa magana. Don haka suna nan tsaye aka yi wa Adnan sutura aka yi masa sallah yayin da Umma da Maman Adnan suke tsaye sun saka Farida a tsakiya suna lallashinta.

    Ana fita da gawar mata suka fara shigowa gidan domin ta’aziyya, sai dai har zuwa lokacin Farida ta ƙi shiga cikin gidan ga shi magriba ta fara kawo kai. Da yake maƙabartar babu nisa nan da nan aka kai shi aka dawo. Babu wanda ya kula da lokacin da Farida ta sulale ta fice daga gidan ta kama bin hanya.

    Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Ɗaya

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Ake Addu’ar Gamuwa Da Abokan Gaba Ko Wani Mai Iko 

    Yadda Ake Addu’ar Gamuwa Da Abokan Gaba Ko Wani Mai Iko 

    اللهُمَّ إِنَّا نَجْعَلُكَ فِي نُحُورِهِمْ وَنَعُوذُ بِكَ مِنْ شُرُورِهِمْ
    Allahumma ina naj’aluka fee nuhurihim wana’uzu bika min shururihim

    Ya Allah! Mu Muna sanya Ka a gabansu, kuma Muna neman tsarinka sharracensu.

    اللّهُمَّ أَنتَ عَضُدِي ، وَأَنْتَ نَصِيرِي، بِكَ أَحُولُ وَبكَ أَصُولُ وَبكَ أُقَاتِلُ

    Allahumma anta adudee, wa’anta naseeri, bika ahulu abika asulu wabika ukatilu

    Ya Allah! Kai ne Mai ƙarfafa ni, kuma Kai ne Mataimakina. Da ƙarfinka ne nake yin dabarun yaƙi, kuma da ƙarfinka ne nake kai hari, kuma da ƙarfinka ne nake yin yaƙi.

    حَمَّنَا اللهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ
    Hammanal lahu wani’’imal wakeelu

    Allah ne Mai isar mana, kuma madalla da Shi abin dogaro.

    Karanta Abin Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Mafarki Mara Kyau

    Edita@rumasau-kallamu

  • Mijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Ɗaya

    Mijin Marigayiya Babi Na Goma Sha Ɗaya

    Duk da bai ce mata zai zo yau ɗin ba amma dai haka kawai zuciyarta take gaya mata zai zo tunda an buɗe gari kuma tun wancan lokacin da aka buɗe gari ba su haɗu ba. Ta san dai yana jin haushinta daga yanda yake amsa wayarta amma ta nutsu a zuciyarta cewa zai zo ɗin.

    Tun wuri ta tashi ta yi wanka ta shirya don ya same ta a shirye; sai dai ga mamakinta har azahar tana zaune a parlor tana ta faman duba waya, duk wanda ya buga gate da hanzari take tashi ta buɗe tana saka rai Mustapha ne amma har la’asar bai zo ba.

    Dab da la’asar tana zaune a parlor tana ta faman latsa waya tana duba whatsapp ko ya buɗe saƙon da ta tura masa amma ga mamakinta har zuwa lokacin bai buɗe ba. Mommy ce ta fito daga ɗakinta; har ta kama hanyar kitchen sai kuma ta kula da Khadeeja a zaune a parlor ɗin.

    Ta dawo ta tsaya tace ‘Ya na ganki a nan, ina Nabila PA ɗin taki?’ Ta yi dariya tace ‘Tana can tana abinda ta saba wato bacci. Ta wuce kitchen ta bar ta a nan, jimawa kaɗan ta fito ta dawo parlor ɗin ta zauna a kan three seater daga bangareb da yafi kusa da single seater din ta Khadeeja take zaune.

    Ta ɗan yi gyaran murya tace ‘Uhm, ai na zata Mustapha zai zo yau ɗin, ko sai da yamma zai zo?’ Ta ɗan gyara zama tace ‘Umm! Ina jin dai sai da yamman, wataƙila gidansu ya wuce tunda shi da yara ne.’ ‘Um to bari mu gani. Amma dai kuna waya ko?’ ‘Eh, jiya da daddare ma mun yi magana.’

    ‘Ai shikenan bari mu gani. Suka yi shiru na ɗan lokaci; jimawa kaɗan tace ‘Mommy kina neman Mustaphan ne da naga kamar jiransa kike yi? Ta jijjiga kai tana murmushi ‘A a me zai yi min; kawai dai na san ya kamata a ce ya zo ya duba ki ko, ai ko gaisawa ne a yi duk da dai da an sallace za ki koma.’

    Ita ma dariyar ta yi sannan tace ‘Zai zo Mommy in sha Allahu.’ Abu kamar wasa har aka sha ruwa babu Mustapha babu labarinsa’ haka dai ta lallaɓa ta ci abincin ba tare da tana jin daɗinsa ba. Tana kula da yanda Mommy ta saka mata ido sosai tana kula da duk wani motsinta tun ɗazu da suka yi magana.

    Sai da aka tafi sallar isha’i lokacin ‘yan gidan duk sun tafi masallaci sannan Mommy ta kirawo ta; ta riga ta san kiran don haka cikin sanyi ta tashi ta wuce ɗakin Mommy ɗin. A zaune a kan dadduma ta same ta don haka ta zauna daga gefenta a kan kafet. Sai da Mommy ta ɗauki lokaci tana kallon fuskarta kamar mai karanta littafi sannan tace ‘Wai ya aka yi Mustaphan bai zo ba?

    Gashi kin san ba za a sake buɗe gari ba sai satin sallah. Ko wani abu ne ya tare shi?’ ‘Umm! Kin san sai sun je office da zarar an buɗe gari. Sai da aka fara kiran magariba sannan ya kirawoni yake gaya min a lokacin yake barin office ga shi yana so ya isa gida kafin a fara tare hanya.’ Ta sharo ƙarya.

    Ta sake kakkafe ta da ido na ɗan loakci sannan tace ‘Umm! Ko dai fushi yake don an ce ba za ki koma sai bayan sallah? Na ga fa bai sake zuwa ba tun wancan lokacin da ya zo ɗaukanki ba ki bi shi ba.’

    Ta sunkuyar da kai tana ‘yar dariya tace ‘Umm, ya ma gama fushin ai. Da farko ne ya fara fushin ya zata zan fasa zama har bayan sallar amma daga baya da ya ga ba zai sami yanda yake so ba ya hakura.’ ‘Umm! To ko shi yasa bai zo ba?’

    ‘A a fa Mommy, na gaya miki ya je aiki ne shi yasa ya makara bai zo ba. Idan aka sake buɗe gari ko kuma ranar sallah zai zo.’ ‘To Allah ya kai mu. Idan dai da akwai wata matsala gara ki faɗa tun kafin ki koma a san matakin da za a ɗauka don na kula kamar akwai abinda kike ɓoyewa.’

    Ta ɗan yi murmushi sannan tace ‘Babu wani abu fa Mommy, aiki ne kawai da raino; kin san harkar yara. Bana samun lokacin kaina kullum cikin hidimarsu nake. Shi yasa tunda Biba ta tafi ban sami natsuwa ba. Kin ga yanzu kin ce kafin sallah za a samo min yarinya sai mu koma tare, daga wannan babu wata matsalar.’

    Ta kalle ta da alamomin tambayoyi domin jikinta yana ba ta kamar akwai abinda Khadeejan take ɓoye mata, amma babu wani abu da za ta iya yi a kai tunda ba ta ma san menene matsalar ba. Tace ‘To kuma shi Mustaphan ba ya baki wata matsala? Ta yi dariya ‘Mommy kema dai kin san da da matsala da tuni na gaya miki fa, babu komai.’

    Dole Mommy ta haƙura ta ƙyale ta da tambayoyin nan ba don ta gamsu da amsoshin da ta bayar ba. Sai da ta yi da gaske sannan ta hana kanta kiran Mustapha a wannan daren; ta yi wa kanta alƙawarin daga yanzu ba za ta sake kiran shi ba har zuwa bayan sallah. Idan ya zo su koma, idan kuma bai zo ba ita dai to ba za ta neme shi ba. Haka ta kwana tana matse ƙwalla.

    Duk yanda ya so ya daure zuciyarsa daga sharewar da Khadeeja ta yi masa zuwa yanzu ya gaza; ya riga ya saba tana kiransa tana lallaɓa shi da ba shi haƙuri amma shiru. Yana kallon kiranta ranar Asabar ya ƙi ɗauka don ya san za ta ce ya zo gidansu ne; shi kuma ba zai je ba in dai ba ɗaukanta zai je yi ba. Don haka ya ƙi ɗaukan kiran yana sa ran idan dare ya yi ma za ta sake kira, a lokacin sai ya ba ta uzurin dare ya yi.

    Sai dai har ya kai yaran gidan Mama ya wuto gida ya gama duk abinda zai yi ba ta sake kira ba; lokacin da ya tashi sahur ma wayar ya fara dubawa ya ga ko ta kirawo yana bacci amma ga mamakinsa babu kiranta ko ɗaya. Haka ya yi sahur ya gama ibadarsa ya kwanta.

    Sai da gari ya waye zuwa azahar sanna ya tuna akwai messages ɗinta na whatsapp da ta turo bai buɗe ba don haka ya je ya lalubo saƙonnin ya buɗe. Ya bi su ɗaya bayan ɗaya ya tura mata amsa, wanda tambayarsa take yi ko zai zo sannan tana gaya masa kayan da zai ɗauko mata a ɗakinta ya taho mata da su.

    Har zuwa la’asar ba ta amsa saƙonninsa ba sai dai sun nuna alamar sun shiga; ya buɗa whatsapp sau babu iyaka amma har zuwa lokacin ba ta karanta saƙonninsa. Ba ta taɓa share shi haka ba; to ko dai ba ta da lafiya ne? kada fa ya je wani abu ne ya same ta don idan dai Khadeeja ce ya san za ta neme shi.

    Zuciyarsa tana gaya masa wulaƙanci ne kawai take so ta yi masa don haka ya rabu da ita duk da yanda ya kasa cire tunaninta daga ransa. Haka suka zauna ba sa waya kuma ga saƙonninsa nan ta gani amma ta ƙi ta ba shi amsa. Ranar jajiberin sallah ya kasa jurewa shiru ɗin don haka ya kirawo ta; wayar tana dab da tsinkewa sannan ta amsa.

    Murya ƙasa-ƙasa cikin halin ko in kula tace ‘Bana kusa da wayar ne. Kwana biyu na jiki shiru ne, kuna lafiya? Lafiya Alhamdulillahi. Ya yarana?’ Suna nan ƙalau, suna gidan Mama. Allah sarki, don Allah in ka je kace ina gaida su maman.’ Suka yi shiru na ɗan lokaci, jimawa kaɗan yace ‘Kin yi zamanki a gida gaba ɗaya kin manta da ni ko?’

    Ta yi ‘yar dariya tace ‘Ka dai manta da ni. Ko kayan sallarki ma ba ki tambaya ba. Uhm, akwai wasu ma a nan da Mommy ta ɗinka min. To ya kike? Lafiya dai kike ko?’ ‘Lafiya ƙalau. Suka ɗan taɓa hirar haka wadda duk gaba ɗaya kusan shi ne yake ta daddagewa don ita ma ta ji haushin abinda ya yi mata, daga baya yace ‘Gobe fa Sallah, yaushe zan zo mu taho gida?’

    ‘Umm, in dai ka cire jibi duk lokacin da ka shirya za ka iya zuwa mu tafi, tunda an riga an samo min mai aiki ga ta har ta koyi duk wani aiki da nake so. Uhm, dole dai sai kin sani cin tuwon sallah a gidan hajia ko? To ina laifi, idan ka ci ni ma ka yi min take away.’ Haka suka cigaba da hirararsu a hankali suna sakewa, daga baya suka yi sallama a kan ranar sallah zai zo ya ci tuwo kafin ya wuce gidan Hajia.

    Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Goma

    Edita@rumasau-kallamu

  • Mijin Marigayiya Babi Na Goma

    Mijin Marigayiya Babi Na Goma

    Karo na babu iyaka kenan da ta ɗauki wayarta ta buɗo whatsapp ta duba; har yanzu bai amsa messages ɗinta ba kuma bai biyo whatsapp call in da ta yi masa ba. To me yake faruwa ne? Allah dai yasa lafiya Mustapha yake da shi da yaran. Da farko da ta ga ta yi magana ta whatsapp bai kula ta ba kuma ta kirawo shi ta whatsapp ɗin bai ɗaga ba sai ta zata ko fushi ya yi, amma dai zuwa yau kwana uku abun ya fara ba ta tsoro kada ta je ko wani abu ne ya same shi.
    Ta riga ta san babu credit a wayar don haka ko balance ma ba ta duba ba; shi ɗin ba mutum ne mai son saka mata credit ba, idan ma ta yi magana sai yace wa za ta kirawo ko kuma me za ta yi da data ɗin. Idan aka yi albashi dai idan ta yi magana yana saka mata naira ɗari biyar, shi ne za ta samu ta raba ta sa data sauran ta ɗan yi waya.
    Don haka yanzun ma babu na wayar sai dai data ɗin da ta yi mata saura. Ta yi tsaki sannan ta sauka daga kan gadon Nabila inda take kwance ta wuce ɗakin Mommy.A parlor ta sami Mommy tana zaune tana kallon tafsiri a tashar Sunnah TV, ta zauna a kusa da ita bayan ta yi sallama ta amsa. Sai da suka ɗan yi jim kaɗan ta kula dai Mommy babu abinda za ta ce mata sannan tace ‘Mommy don Allah ki ɗan saka min 1k a waya mana.’
    Ta kalle ta tana dariya tace ‘1k kuma? Ina Mustaphan ko kuma yau ba nashi kike so ba tunda kina gidana nawa kike so?’ Ita ma dariyar ta yi ta ƙara langaɓe kai ‘A a Mommy, don Allah dai ki taimaka, wallahi ya saka min ƙararwa na yi kuma dai kin san ba ni da kuɗi. Ke kenan kullum ba ki da kuɗi?’
    ‘Mommy bari dai na fara aiki. Uhm, shi Mustaphan ko ɗan na kashewa ba ya yaga miki balle ga ki ‘yar makaranta?’ Ta ɗan marairaice ‘To ai kin ga yanzu an yi hutu Mommy, duk ‘yan sauran canjin ma na kashe. Shi yasa kike maula kuma? To ɗauko min wayata a ɗaki na saka miki a cikin wanda mijina ya ba ni.’
    Ta miƙe tana dariya tace ‘Mommy. Baffanta ba wai millionaire ba ne amma dai ta san yana da kyauta; duk da Mommy tana sayar da ‘yan kunnaye da sarƙoƙi amma duk wata sai ya tura mata kuɗin kashewa account ɗinta sai dai ko ya tura babu yawa amma fa sai ya tura.
    Kuma idan dai ta buƙaci wani abu bayan wannan to yana iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya yi mata sai dai ko idan babu hali. Ta yi zaton haka za ta je ta samu a wajen Mustapha, musamman da yake yana yawan yi mata kyaututtuka da saka credit a waya lokacin da yana neman aurenta.
    Sai dai bayan ta shiga gidan sai ta tarar ba haka ba ne; don wani lokacin a kan ya saka mata kati a waya ya gwammace ya ba ta aron wayarsa ta yi waya. Ko da ta koma makaranta ma ta yi zaton zai ɗan dinga ba ta kuɗin makaranta da kuɗin kashewa sai dai tun a ranar farko da gane ba zai jure ba.
    Domin da farko bayan ta gama shiryawa ta yi zaton zai kai ta ne, amma sai dai suna fitowa da aka zo inda zai ɗauke hanya ya wuce office ɗinsu sai yace ta sauka a nan ta hau motar haya. Da ta yi maganar kuɗin mota kuma sai yace mata wai ya zata tana da kuɗi; ta dai samu ya ba ta naira dubu kamar ba da son ranshi ba.
    Tun daga ranar ma sai ya zama ta daina damuwa ta yi sai ta shirya ta bi shi, yawanci sai ta jira idan ya fita sai ta kama hanya a motar haya. Kuɗin motar ma tana shirin ta tambayi Baffa ya dinga ba ta aka shiga lockdown; kuma har yanzu tana da niyyar kafin ta koma gida ta sanar da Baffanta kawai ya dinga tura mata kuɗin mota.
    Tana ta wannan tunanin ta je taɗdauko wayar ta kawo wa Momy; ba tare da ɓata lokaci ba ta tura mara katin naira dubu kamar yanda ta buƙata. Nan da nan ta koma ɗaki ta sake hayewa kan gadon Nabila sannan ta danna masa kira. Sai da wayar ta kusa tsinkewa sannan ya ɗauka, cike da isa yana magana da ƙyar ya amsa sallamarta, haka ma gaisuwarta kamar ba zai amsa ba.
    Wannan ya sa jikinta ya yi sanyi kuzarin da ta fara wayar da shi duk ya gushe. Cikin sanyi murya tace ‘Babe, ya na ji ka haka? Ko ba ka da lafiya ne?’ Sai da ya ɗan yi jinkiri sannan ya amsa ‘Umm, lafiyata ƙalau. Ke kin damu da lafiyata ne da kike wannan tambayar? Ba dole ki ji ni haka ba tunda kin zaɓi ki nesanta kanki da ni?’
    Nan ta fahimci inda zancen ya dosa, amma da yake so take ta waske sai tace ‘Haba Babe ya za a yi na guje ka? Tunda da kuka tafi daga nan nake ta yi maka message ta whatsapp, ba ka gani ba ne? Kuma wallahi wayar ma ka san ba ni da credit, yanzun ma da ƙyar na samu Mommy ta saka min ɗari biyu shine nake kiranka fa. Haba Babe ya za a yi kace ban damu da kai ba?’
    ‘To idan kin damu da ni ya za a yi na zo har gidanku ga azumi kin sani kuma ga shi ana lockdown? Amma kina kallonmu ni da yarana duk muna ta murna za ki dawo amma kika ce ba za ki dawo ba sai bayan sallah. To ai na gaya maka wannan ba ni na tsara haka ba, Mommy ce. Kuma ka san dai idan mace ta haihu dai ana yin gyara da sauransu, sallar nan fa kuma saura bai fi kwana goma sha shida ba.
    Haba Babe to meye na fushin?’ Shiru ya yi ba tare da yace mata komai ba suna sauraren numfashin juna. Ita ce ta gaji da sauraro tace ‘Ya na ji shiru ne? ina yara na?’ ‘Ai ba ki damu da su ba shi yasa suna ta cewa ki biyo su kika ƙi. ’Ta fara gajiya da wannan mitar tasa da duk abinda tace sai ya ce ba ta damu da su ba shi da ‘yayansa, to wai ita ba ta buƙatar a damu da ita ne ko me yake nufi?
    Shi ba zai iya kula da ita ba kuma ya bar ta ma cikin natsuwa a inda za a kula da ita ta ɗan sami natsuwa yana nema ya hana? Ta ɗan yi murmushi mai sauti ta danne fushinta sannan ta saita muryarta tace ‘To don Allah ka yi haƙuri ka daina cewa ban damu da ku ba, kai ka san na damu daku. Kamar yau ne za ka ga lokacin ya yi ai na dawo, ko ba shikenan ba.’
    ‘Umm, amma dai da za ki dawo yanzu ai da ya fi ko? Haka kawai ni ba gwauro ba kin saka ni azumi babu mata. Kawai idan an buɗe gari na zo na ɗauke ki mu tafi, shi ne kawai zan san kin damu da ni. Ta dan ɗaga murya tace ‘Ah, Babe to me zan cewa Mommy, ni daɗi miji zan bi mijina kenan ko me?’
    ‘Ba wani daɗi miji, ai aure ne kuma ita ma ta sani. To gaskiya dai ka bari sai bayan sallar kawai.’ Haka dai suka ɗauki lokaci suna waya ba tare da ta amince za ta dawo ɗin ba, maimaita masa kawai take sai bayan sallar. Don haka kusan a fusace ya katse wayar ba tare da sun yi wata sallamar kirki ba.
    Ta jefa wayar a kan gadon kusa da ita ta ja tsaki, sai kuma ta kifa kanta a kan pillow sai hawaye. Ta godewa Allah Nabila tana ɗakin Mommy tana bacci da sai ta gayawa Mommy tana kuka. Ta fara nadamar sakawa da ta yi Mommy tace ta zauna a gida har bayan sallah, yanzu gashi yana fushi da ita.
    Ita ba ta zata wannan abun zai sa ya yi fushi ba don da ta san zai yi fushi ma da ko gidan ba za ta taho ba za ta haƙura ya je ya ɗauko ta. Bata sani ba ko za ta iya jure jinsa a cikin damuwa har na tsawon sati biyu ko uku, amma dai za ta gwada. Don da kunya tace a barta sai bayan sallah sannan yanzu kuma ta zo tace za ta koma.
    Haka ta ƙarasa wunin ranar cike da damuwa da nadamar zaman da ta zaɓa za ta yi a gida. Haka ta cigaba da haƙuri tana buga masa waya wanda kullum idan ta buga gaisawa kawai suke yi babu wata magana mai daɗi, kamar ma shi dole take masa. Abun yana matuƙar damunta don haka ta fara rama wadda Mommy ta zata don ta cigaba da azumi ne tunda ta sami lafiya; idan ta yi zuru-zuru aka yi magana sai tace azumin ne da wahala.
    Tun da ya kai su gidan Hajia bai sake zuwa ba tunda garin a rufe yake ba a fita, sai yau Asabar a lokacin saura sati ɗaya sallah. Yana fita ya tsaya a shagon telansa ya karɓar musu ɗinkunan kayan sallansu wanda tun kafin a fara azumi ya kai; wanda har da na Khadeeja a ciki, ya tsaya aka ba shi leda ya ware nata waɗanda ba shi da niyyar kai mata gidansu.
    Ya dai yarda zai ajiye mata a ɗakinta duk lokacin da ta dawo ta gani. Yana karɓa kai tsaye ya wuce gidan Hajia cike da kewar yaransa. Tun daga nesa ya hango Habib a zaune a kofar gida tare da wani yaro, ba wasa suke yi ba a zaune suke kawai sun yi shiru kowa da abinda ya dame shi.
    Kafin ya ƙarasa tsayar da motar ya taso da fara’arsa; ya gyara tsayuwar motar ya buɗe kofa yana sake ƙarewa Habib din kallo wanda ya yi zuru-zuru kamar wanda ya kwana da yunwa. ‘Abba sannu da zuwa.’ Muryar Habib ta katse shi. ‘Yauwa Habib, ya naganka kamar kana jin yunwa ko azumi kake ya fara ba ka wahala tun da safe haka?’
    Idonsa ya ɗan yi rau-rau yace ‘Eh, azumi nake yi. To ba ka yi sahur ba ne?’ ‘Ba sosai ba, baƙin tuwo ne kuma ba na ci ga shi kuma babu wani abincin a gidan sai shi, na ɗan ci kaɗan dai. To ba sai ka fasa yin azumin ba? ɗa safe ka yi breakfast.’ ‘Hajia ma haka tace na fasa yin azumin amma ni nace zan yi, idan ma ban yi ba ba abinci zan samu ba sai an sha ruwa.
    Tunda muka zo ma sau ɗaya na sha azumi.’ Cike da tsananin mamaki yace ‘Ban gane ba abincin kake samu ba sai kace wani almajiri? Ba a ba ka abinci ne a gidan? Ina Baito? Ai Baito sai da rana take zuwa, kuma safiya tana yi Hajia take cewa mu tafi gidan Anti Jidda mu yi wanka a can mu ci abinci a can. Kuma idan mun je sai Anti Jiddan tace babu abinci sai dai kawai wata ran ta ba mu baƙin shayi da ragowar ƙosai ko doya.
    Idan kuma mutum ya dame ta sai ta yi masa faɗa, ita ma Shukra da Nasreen ragowar kunu ne kawai ko kuma idan an yi sa’a an rage abincin shan ruwa shi ne ake ba su.’ Mamakinsa ya ƙaru, yace ‘A a, ai na turowa Anti Jidda kuɗi a sayi indomie da cornflakes har da madara, ba a siya ba ko me ya faru da su.’
    Ya ɗan zaro ido ‘Tab, tunda muka zo ba mu taɓa cin indomie ba ko cornfalkes. In an sha ruwa dai da yake muna gidan Hajia shi ne aka haɗa mana shayi da madara har da ƙwai ma ake soya mana da kaza, amma dai da rana babu wanda yake ba mu abinci. A wajen Hajia ma muke shan ruwa tare da ita da Alhaji.
    Ya yi matuƙar mamaki kuma ya ji tausayin Habib; amma kuma yana matuƙar mamakin yanda za a yi a ce Yaya Jidda ta bar masa yara da yunwa. Ranar da ya kawo su bayan ya tafi ta kirawo shi tana tambayarsa kuɗi a sayi kayan shayi da indomie, kuma a take ya tura mata naira dubu goma don a siyo da wuri. To me ya faru da kuɗin da ake hora masa yara da yunwa?
    Tare suka jero da Habib ɗin suka nufi cikin gidan, suna daf da shiga suka ci karo da Afaf tare da Shukra da Nasreen kowacce sanye da hijabinta, nan da nan suka faɗa jikinsa suna murna ‘Abba, Abba. Bayan ya amsa gaisuwarsu yace ‘Ina za ku je?’ Afaf tace ‘Gidan Anti Jidda za su je su yi breakfast.’
    ‘Ke kina azumin ne?’ ‘Eh ina yi.’ ‘To ku zo mu wuce ciki ku yi breakfast ɗin a nan.’ Nasreen ta yi dariya tace ‘Tab ai babu abincin, da an gama shan ruwa Baito take juye duk wani ragowar abinci ta tafi da shi. Kuma Hajia cewa take mu je gidan Anti Jidda a dafa mana indomie amma idan mun je ba a dafa bana, baƙin shayi ake ba mu da ragowar ƙosai ko kunu.’
    Ya ɗauki shukra ya ja hannun Nasreen yana cewa ‘ku zo mu je. Bayan sun gaisa da Hajia tace ‘To ka bar su su je gidan Jidda ta dafa musu indomie ɗin su karya sai su dawo ko? Yunwa suke ji ga su nan.’ Nan suka yi wa Hajia bayanin abinda ake ba su idan suka je gidan yaya jidda; ita ma ta yi mamaki sosai. Tace ‘To me yasa ba ku taɓa faɗa ba?’
    Nasreen ta zumɓuro baki tace ‘Yaya Meena ce tace duk wanda ya faɗa sai ta ci ubansa ta karta masa rashin mutunci don ta san mu da tsinin baki.’ Daga Hajiyan har Mustaphan mamaki ne ya kama su, Meena ita ce babbar ‘yar Yaya Jidda. To amma me zai sa ta yi haka bayan Jiddan da kanta ta gayawa Hajia ya turo kuɗin indomie da kayan karin kumallon yaran?
    Tace ‘Lallai daga Aminan har Jiddan za su zo su same ni.’ Saboda tsabar takaici Mustapha kasa magana ya yi. A nan ya sake ba da kudi Habib ya fita kanti ya siyo musu indomie, yana kawowa Afaf ta dafa musu da ƙwai tunda dama da akwai ƙwai a gidan. Haka ya saka su a gaba duka sai da suka karya azumin suka ci suka ƙoshi.
    Nan ya zauna suka cigaba da hira wajen Hajia tunda shi ma Alhaji ya fice; sai dai har la’asar ta  kawo jiki Yaya Jidda bata zo gidan ba saboda yaronta Abdallah ya shigo gidan lokacin suna cin indomie shi ma ya zauna aka ci da shi kuma yana gamawa ya koma gida ya gayawa uwarsu Abban Afaf ya zo har ma ya sa an dafa musu indomie da ƙwai.
    Don haka tana sane ta ƙi zuwa saboda rashin gaskiya. Haka ya wuni a gidan ransa a ɓace yana tunanin mafita; tabbas duk Khadeeja ce ta janyo masa wannan wulaƙancin. To yanzu ya zai yi da yaran? Idan ya tafi da su ba za su bar shi ya zauna a nutse ba, kuma ma ya san Hajia ba za ta yarda ya tafi da su gida su zauna tare da shi ba.
    Sai dai kamar yanda ta riga ta faɗa ya je ya siyo abubuwan da suke buƙata ya kawo ita sai ta dinga dafa musu kafin Baito ta zo; domin ita ma Baito ɗin mijinta ne ba shi da lafiya take jinyarsa shi yasa ba za ta iya zuwa da safe ba. La’asar tana matsowa ranshi ya sake ɓaci, kuma har lokacin Yaya Jidda ba ta iso ba.
    Bayan ya idar da sallar la’asar yana zaune a kan dadduma yana tunanin mafita Habib ya shigo ya same shi. Bai daɗe da zama ba yace ‘Abba da ma ka kai mu gidan Mama, ka ga dama mun daɗe ba mu je ba tunda muka koma gida. Um, to ai da sallah za ku je ko? Ko ba kwa son zama a nan ɗin ne? Ai ka ga yanzu Hajia da kanta za ta dinga ba ku breakfast ɗin ko?’
    ‘Um, nan ɗin ma muna son zama amma can ɗin ma muna so, in ya so idan Anti Khadeeja ta dawo sai mu dawo.’ Nan sauran yaran suka shigo suka saka shi a gaba a kan su gidan Mama suke so su je; shi ɗin ma yana so ya kai su don ya san ba za a bar su da yunwa a can ba tunda ko babu mai aiki akwai ‘yan mata. To amma yanzu hakan yana nufin kenan ba za a iya riƙe masa yaransa a gidansu ba ko me?
    Ita kuma Yaya Jidda me take nufi? Gashi ta ƙi zuwa, shi kuma ba zai je gidanta ba don ya fi so ta zo su yi a gaban Hajia. Haka dai yaran nan suka saka shi a gaba dole ya amsa zai wuce da su. Ita ma Hajia da ya gaya mata zai kai su sai da ta nuna ɓacin ranta don gani take kamar fushi ya yi da yanda ya sami yaran, sai da Alhaji ya sa baki kuma suka ga Nasreen tana nema ta saka musu kuka sannan suka bari ya kwashi yaran suka wuce gidan Maman su Ma’u.
    Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Tara
    Edita@rumasau-kallamu
  • Abin Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Mafarki Mara Kyau

    Abin Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Mafarki Mara Kyau

    Wanda ya yi mafarki mara kyau ko ya ga abu mummuna a mafarki, to sai ya yi waɗannan abubuwan:

    -Ya yi tofi ta gefen hagunsa sau uku.

    -Ya nemi tsarin Allah daga Shaiɗan da kuma sharrin abin da ya gani, sau uku.

    -Kada ya gaya wa kowa wannan mafarkin.

    -Ya juya daga kwuiɓin da ya kasance yana kwance a kansa.

    -Idan ya so, ya iya tashi ya yi salla

    Karanta Addu;ar Sanya Sababbin Tufafi

    Edita@rumasau-kallamu

  • Mijin Marigayiya Babi Na Tara

    Mijin Marigayiya Babi Na Tara

    Kamar yanda aka sanar ranar Asabar aka buɗe gari, ba ƙaramin daɗi wannan buɗewar ta yi wa Mustapha ba. Tun waje ƙarfe takwas ya shirya sannan ya shirya yaran gaba ɗaya, sai dai da ya duba lokaci ya ga safiya ta yi da yawa ya bari zuwa wajen tara da rabi sai su fita; domin so yake su je su ɗauko Khadeeja sannan idan ya kawo ta gidan ya bar su ita da yaran ya wuce gidan hajia ya gaishe su.

    Sai wajen goma saura sannan suka kama hanya. Tun kafin ya gama tsayar da motar yaran suka ɓalle ƙofofi suka fice suka shiga gidan da gudu, bayan sun gaida Mommy wadda take zaune a parlor tace su shiga ɗakin Anti Nabila su taso Antin tasu inda take barci.

    Jin su kawai ta yi a kanta suna shewa, ba shiri ita ma ta miƙe. Nan take aka shiga ba ta labarin abubuwan da suke faruwa a gidan. Ita ma ta yi kewar yaran kuma ta ji daɗin ganinsu sosai. A farfajiyar gidan Mustapha ya tsaya sai da Mommy ta tura Nabila ta shigo da shi, ta buɗe parlor ɗin baƙi ta yi masa iso inda Baffa yake jiransa don shi ma fita zai yi jin isowarsu ya sa ya tsaya.

    Bayan sun gaisa Baffa ya tambaye shi wajen su Alhaji sai ya yi gyaran murya yace ‘Yauwa, ina ga za ka bar Khadeejan ta ɗan ƙara kwana biyu don mahaifiyarta tace akwai abubuwa suke yi na gyara wanda al’ada ta tanada. Don haka ina ga ka bar ta ta ɗan ƙara kwana biyu mu gani.’

    ‘Eh, kuma da zuwa muka yi mu tafi da ita Baffa.’ ‘Allah sarki, ina ga a ɗan ɗaga musu ƙafa su gama shirye-shiryensu, ba za su ɗauki lokaci ba su ma na sani in sha Allah.’ Babu yanda ya iya kwarjinin Baffa ya sa ba zai iya yi masa wani dogon musu ba, don haka sai kawai ya sunkuyar da kai.

    Baffa ya yi masa sallama ya fice ya bar shi a nan cike da taƙaici; yaya Baffa zai yi masa haka? Wannan ɗin shawarar Mommy ce ko kuwa dai Khadeejan ce ba ta son ta koma? Amma dai bari Khadeejan ta fito ya ji daga bakinta. Ya gyara zama ya haɗiye malolon da ya tokare masa maƙogoro ya daɗa saita fuskarsa da ya ji motsi ana taɓa ƙofar daga cikin gida, ya miƙe ya koma kan kujerar zaman mutum ɗaya ya zauna.

    Khadeeja ce ta shigo da sallama, bayan ya amsa ta nemi guri ta zauna a kan three seater ta gefen da ya fi kusa da shi, bayan sun gaisa tace ‘Ya kuke kai da yara? Sun ce min ku kaɗai ne a gida ko gidan Hajia ba ka kai su ba. To ina zan kai su gari yana kulle, dole haka muka zauna mu kaɗai; don ma dai Ummi tana taimakawa, jiya ne kawai da shekaranjiya aka ce ba ta da lafiya.’

    ‘Allah sarki ai iyayenta suna mana kirki gaskiya, Allah ne kawai zai biya su.’Suka yi shiru na ɗan lokaci; idan ma da yana da niyyar gaya mata wasu kalamai masu daɗi to Baffa ya goge masa haddarsu, yanzu haushin kowa ma yake ji. Sai dai fatansa ɗaya ya ga ko zai iya tsara Khadeejan ta canza wanna tsarin don yana jin idan tace tana son ta koma ba za a hanata komawa ba.

    Yace ‘Uhm, da ni fa zuwa na yi mu tafi amma na ji Baffa yace kamar za ki yi wanka ne ko gyara wai sai an kwana biyu za ki dawo.’ Ta ɗan gyara zama ‘Eh, Mommy tace a bar ni sai na yi wankan jego kuma dai da ‘yan gyare-gyare na ƙara hutawa sai na koma.’

    ‘Wai ba ki gayawa Mommy cikin bai ƙarasa wata uku ba ma, na zata haihuwa ake wa wankan jego. Ke dai idan akwai wani dalili ki gaya min sai mu ga yanda za a yi.’ Ta yi ‘yar dariya ‘Shi ne dai dalilin ga shi na gaya maka, don ka ga har yanzu ma ban gama jini ba kusan kwana biyar kenan.’

    ‘Uhm! To yanzu babu yanda za ayi mu koma yau, na san ai duk wani gyara ba zai gagare ki ba tunda kin sami lafiya ga laulayin ma yanzu babu. Gaskiya ka yi haƙuri kawai mu yi yanda Baffa ya faɗa, kwana nawa ne za ka ga ma na dawo gidan. Ya sunkuyar da kai; tabbas wannan tsarin na Khadeeja ne sai dai bai san laifin me ya yi mata ba take son ta yi purnishing ɗinsa haka.

    Muryarta ce ta katse masa tunani ‘Kada ka damu in sha Allahu zuwa bayan sallah zan dawo, ka ga kafin nan ma Mommy ta samo min mai aiki. Bayan sallah? Haba! Wajen sati uku fa kenan? Ai na zata duk inda aka kai nextweek kin gama hutawar. Kuma mai aiki ai Habi za ta dawo bayan sallah ko?’

    ‘Ban sani ba, wai dai don kada ta ba ni mamaki gara a samo min wata tunda ga aikin gida ga hidimar yara sannan ga makaranta zan koma idan an buɗe gari ka ga ina buƙatar taimakon mai aiki ko.’ Sai a lokacin ma sannan ya tuna ashe tana zuwa jami’a; amma dai shi har yanzu bai gane dalilin da yasa ba za ta koma yau ɗin ba har sai nan da sati biyu.

    Ya dai fahimci so take kawai tace aikin gida da na yara ya mata yawa, kuma shi bai ga wani wahala a ciki ba tunda Ma’u ma ko sau ɗaya ba ta taɓa ɗaukan mai aiki ba haka take komai da kanta. Kawai dai ya fahimci Mommyn Khadeeja tana da son zuciya da iko shi ne take son ta juya shi kamar yanda take juya Baffansu, kuma gaskiya shi ba zai ɗau wannan ba.

    Haka dai ya gama kwana-kwanarsa ya tashi ya kwashi yaransa suka wuce gidan Hajia cike da takaicin Mommy Khadeeja wadda duk ita ya ɗorawa laifi, gani yake kamar ita ce take juya Khadeeja da Baffan gaba ɗaya.Tuni Mommy ta ba da umarni a samo mata ‘yar aiki.

    Ransa a ɓace ya shiga gidan Hajia. Yana shiga ya tarar da Yaya Jidda a gidan ita da yaranta, suna zaune a parlor ɗin Hajia suna hira. A gaggauce yaran suka gaisa da Hajia da Yaya Jidda suka shige wajen Baffa da gudu inda yake zaune yana jiran Kamal ɗan autan gidan ya dawo daga shan mai ya kai shi unguwa.

    A nan Mustapha ya zauna wajen Hajia da yaya Jidda, bayan sun gaggaisaya dubi Yaya Jidda yace ‘Ke Yaya sai kace jira kike a buɗe gari ki taho, har ma kin riga ni zuwa.’ Ta yi dariya tace ‘Ni dama babu ni a lockdown in dai gidan nan ne kullum sai na zo, Alhaji ma ya gaji ya bar ni.’

    Hajia ta dube shi tace ‘Ya jikin Khadeejan?’ Ya ɗan karkata kai yace ‘Da sauƙi. Jiya ma mun yi waya da Mommyn tata ai, ta dawo gidan ko sai kun fita daga nan za ku ɗauko ta?’ ‘Mtseww!’ Ya ja gajeran tsaki sannan ya cigaba ‘Daga can muke, wai Mommyn tace ba ta gama hutawa ba kuma sai an mata wanka da gyara za a dawo da ita zuwa bayan sallah.’

    Hajia ta gyara zama ta kama haɓa ‘Ikon Allah, to kai kuma sai kace me?’ To Hajia ya zan yi da su; shi ma baban nata bayan tuni muka gama magana da shi yace nazo na ɗauke ta ina zuwa kuma ya canza zance; yace wai na bar ta. Ita ma kuma Khadeejan kamar haka ta zaɓa, kin ga kenan babu yanda zan yi da ita. Da a ce ma ta ba ni haɗin kai ne da za ta iya canzawa Mommyn ra’ayi don na kula kamar wannan shirin duka nata ne.’

    Kafin Hajia tace wani abu Yaya Jidda tace ‘Ai kuwa lallai shiri, ɓarin ne sai an yi wani wanka da gyara? Lallai matan nan, ni fa dama shi yasa yaran ‘yan bokon nan ba sa wani burge ni, ciki fal iyayin tsiya.’ Hajia tace ‘To me suke nufi? Wannan duk ranar da ta haihu ai sai ta shekara sun gyara sannan za su ba ka ita. To yanzu ya suke so ka yi da waɗannan ‘yayan, ko kuwa don ba ita ta haife su ba?

    Tunda ai da nata ne haɗawa za su yi da su ko kuma ita da kanta ma ba za ta yarda ta tafi ta bar su ba. Wannan ai ba tsari ba ne ba ma, sai dai da yake dama an bar gidan a hannun mace ai dole a ga son zuciya irin wannan.’ Ya gayara zama yace ‘Hmmm! Su suka sani kuma.’

    ‘To yanzu ya za ka yi da yaran? Ko kuwa haka za ku haƙura ku yi zamanku tunda dama babu fita?

    Ko kuma nan za ka bar mini su sai mu yi zamanmu, ka ga na sha allura a wajen Dr. Nasreen. Ya dubi Yaya Jidda sannan yace ‘Da tunani nake na bar su wajen Yaya Jidda sai na koma na ɗauko musu kayansu, in ya so sai a bar su iyayen Khadeejan mu ga lokacin da zasu dawo da ita.’

    Har hajia ta buɗe baki za ta yi magan Yaya Jidda ta tari numfashinta ‘Eh to kuma ka ga da sai mu yi zaman mu, sai dai ka san gidan namu ƙarami ne wajen kwanan zai iya yi musu kaɗan gaba ɗaya da nawa yaran. Ko nan ɗin ma ka bar su wajen Hajiyan ai duk muna tare tunda kullum ni nake zuwa na tsaya a kan hidimar gidan.’

    Suka yi shiru na ɗan lokaci kowa da abinda yake tunani, jiamwa kaɗan hajia tace ‘To hakan ma ai ya yi, ka bar min su a nan tunda ga Baito nan tana nan za ta iya duk wata hidimarsu. Tunda ka ga ai ba ma tsari a ce kana zaune a gida daga kai sai yaranka yaran ma mata.’

    ‘Ba damuwa, zan je na ɗauko kayansu kafin biyar ɗin ta yi. Ya tashi ya fice wajen Alhaji. Yaya Jidda ta bi bayansa da kallo; ya ba ta tausayi amma gaskiya ba za ta karɓi su Afaf ba, gara dai a nan ɗin. Can gidanta ita ma ga nata yaran waɗanda idan ta ga dama nan take turosu wajen Hajia su ci abinci su yi komai sannan kuma a ƙara mata wasu? Gaskiya ba za ta iya ba.

    Sai da la’asar ta kusa sannan ya fita yaje gidan ya haɗo musu kayansu ya kawo sannan ya koma ya bar su a nan

    Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Takwas

    Edita@rumasau-kallamu

  • Bayani A Kan Budurci Da Kuskuren Da Ake Yi A Kan Rashinsa

    Bayani A Kan Budurci Da Kuskuren Da Ake Yi A Kan Rashinsa

    A yawancin al’ummomi, musamman a cikin Hausawa, ana yawan ɗaukar cewa idan an auri budurwa, dole sai an ga jinin budurci a daren farko da aka sadu da ita kafin a tabbatar da cewa ba ta taɓa saduwa da namiji ba.

    Wannan tunanin ya samo asali ne daga tsohuwar fahimta marar tushe a ilimin likitanci da addini. A gaskiya, wannan ra’ayi kuskure ne.

    MA’ANAR BUDURCI

    A harshen Hausa, budurwa na nufin mace wadda ba ta taɓa yin aure ba balle ta yi saduwar aure ko jima’i ba. A addinin Musulunci da Kirista kuwa, budurci yana nufin kiyaye kai daga aikata zina ko duk wata hanya ta saduwa kafin aure.

    A mahangar likitanci, budurci yana nufin mace wadda ba a taɓa saduwa da ita ta farji ba, amma hakan ba ya nufin sai an ga jini domin ba kowace mace ba ce ke da yanar da ta rufe mata farji (hymen) mai yagewa ta fitar da jini a saduwar farko ba.

    YAYA JININ BUDURCI YAKE FARUWA ?

    Hymen wanda na yi bayaninsa a sama shi ne ake kira “yar hula” ko “farar fata” da ke gaban farji. Wata siririyar fata ce da ba kowace mace ke da ita ba. A wasu lokuta, tana iya yagewa da sauƙi yayin saduwa ta farko, inda hakan ke iya kawo jini.

    Amma a wasu mata, hymen ɗin ta kan yage tun kafin aure ta hanyar wasanni, hawa keke, motsa jiki, ko wasu ayyuka. A wasu kuma, hymen ɗin yana da sassauci har ma saduwa ba ta sa ya yage ba.

    ME ADDINI DA ILIMI KE CEWA ?

    A yau, ilimi da addini sun bayyanar da cewa ba dole ba ne a ga jini don a tabbatar da budurci. Tsarkakakkiyar mace ita ce wadda ta guji zina ko saduwa da namiji kafin aure, ba sai an ga jini ba. Don haka, fahimtar cewa sai an ga jini kafin a yarda da budurcin mace ra’ayi ne da bai dace da gaskiya ko tausayi ba.

    A taƙaice budurci ba wai jinin da ke fita ba ne, budurci hali ne da tarbiyya. Dole ne al’umma su fahimci wannan domin guje wa zargin da ɓata, da cutar da waɗanda ba su da laifi. Allah yasa mu dace.

    Karanta Yadda Ƙullutun Da Ke Fitowa A Gefen Ƙofar Farji Yake
    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Ƙullutun Da Ke Fitowa A Gefen Ƙofar Farji Yake

    Yadda Ƙullutun Da Ke Fitowa A Gefen Ƙofar Farji Yake

    Kullutun “bartholin’s cyst”, wanda wasu suke ƙiransa “bartholin’s duct cyst”, wani abu ne mai kamar ƙurji wanda yake gundar ruwa da yake fitowa mace a gefen mashigar farji. A gefen mashigar farji akwai wata ‘yar ƙaramar jaka wacce ake kira “bartholin’s gland”.

    Amfaninta shi ne tana ɗauke da wani sinadarin maiƙo da kuma majinar mucus waɗanda suke samar da damshin ni’ima a ƙofar farji, waɗanda suke sanya santsi a lokacin saduwar aure.

    Jakar bartholin’s gland tana da ƙaramar ƙofa wacce maiƙo da majinar ni’ima suke fitowa daga cikinta. To, abinda yake sanya kumburin jakar bartholin’s gland har ta rikiɗe ta zamo ƙullutun ciwo a bakin farji shi ne toshewa (blockage) na ƙaramar kofar jakar bartholin’s gland ɗin.

    ABUBUWAN DA SUKE SANYA TOSHEWAR JAKAR BARTHOLIN (CAUSES OF BARTHOLIN’S GLAND BLOCKAGE)

    Toshewar ƙofar bartholin’s gland yana faruwa ne sakamakon:

    1. Kamuwa da ƙwayoyin cuta (infection), kamar escherichia coli (E. coli), streptococcus, ko kuma cututtukan da ake ɗauka a wajen jima’i (STIs), kamar gonorrhea, da chlamydia. Idan waɗannan ƙwayoyin cutar suka shiga cikin jakar bartholin, za su iya sanya ta ta toshe, daga nan sai ta kumbura ta zamo ƙullutu.

    2. Rashin tsabtar farji (lack of vaginal hygiene), sakamakon rashin yin tsarki bayan fitsari, ko rashin tsabtar farji lokacin al’ada da jinin biƙi, ko rashin wankewa da canza underwears, ko cushe-cushen magungunan gargajiya, da sauransu.

    ALAMUNSA (SYMPTOMS)

    Alamun da mace za ta gani ta fahimci cewa ta sami matsalar bartholin’s cyst su ne:

    1. Ƙaramin ƙullutu a mashigar farji (small lump) wanda ba ya yi mata ciwo da farko. Amma idan ya cigaba da girma, to, zai fara yin ciwo.

    2. Rikiɗewa ya zamo ciwo (infection). Hakan yakan faru ne idan ƙwayoyin cutar da suke cikinsa suka yawaita. Daga nan sai ya kumbura, ya yi ja-zur, ya riƙa yin ciwo sosai, ya ja ruwa, sa’annan ya sanyawa mace zazzaɓi.

    YADDA AKE GANE SHI A ASIBITI (DIAGNOSIS)

    Idan mace ta je asibiti domin a duba ta, to, likita zai tabbatar da cewa abinda yake faruwa da ita bartholin’s cyst ne ta hanyar duba yanayin ƙullutun, tare da yi mata tambayoyi a kan yadda abin ya faru, da kuma neman sanin ko ta taɓa samun irin wannan matsalar a can baya.

    YADDA MACE ZA TA KARE KANTA (PREVENTION)

    Mace za ta iya kare kanta daga kamuwa da bartholin’s cyst ne ta hanyar tsabtace farji a kowane lokaci ta hanyar yin tsarki da ruwan ɗumi, canza audugar ƙunzugu (sanitary pads) a kai-a kai lokacin al’ada ko jinin biki, canzawa da kuma tsabtace ɗan-kamfai (pants), da sauransu.

    MAGANI (TREATMENT)

    Hanyoyin magance bartholin’s cyst su ne:

    1. Gasa wurin da ruwan ɗumi (warm compress) a kai-a kai a cikin yini. Hakan zai iya sanya bakin ƙullutun ya buɗe, kuma ruwan gunyar da ya taru a cikinsa ya fito, daga nan sai sauƙi ya samu.

    2. Zama a cikin ruwan ɗumi (sit bath), tare da zuba gishiri kaɗan a cikin ruwan. Wannan zai iya sanya bakin ƙullutun ya buɗe kuma ruwan gunyar da yake cikinsa ya fito.

    3. Yanka bakin ƙullutun (incision). Ana yinsa ne a asibiti, wato likita ya yanka bakin ƙullutun domin ya fitar da ruwan gunyar da ya taru a cikinsa.

    4. Yin tiyata (surgical procedure) wacce ake kira “marsupialization” domin a cire bartholin’s gland gaba-ɗaya. Ana yin hakan ne idan ya zamo ƙullutun yana yawan faruwa da mace kuma yana haifar da wasu matsalolin masu yawa.

    5. Amfani da magungunan kashe ƙwayoyin cuta (antibiotics) domin kawar da ƙwayoyin cutar da suka shiga cikin bartholin’s cyst ɗin.

    A duk lokacin da mace ta ga wani abin da ba ta gane ba a gabanta, to, ya kamata ta je asibiti domin a yi bincike a gane abinda yake faruwa da ita.

    Karanta Hanyoyin Shayar Da Jaririn Da Mahaifiyarsa Ta Rasu
    Edita@rumasau-kallamu

  • Mijin Marigayiya Babi Na Takwas

    Mijin Marigayiya Babi Na Takwas

    Shi da yara suka zauna suka gama shan ruwan sanna ya sa Afaf ta kwashe kwanukan, nan suka zauna suka cigaba da kallo suna wasannisu. Har lokacin kwanciyar bacci babu wanda ya ba shi matsala a yaran. Ya tasa su a gaba ya raka su ɗakinsu domin su yi shirin bacci; yana shiga ɗakin zarni ya doki hancinsa.

    Ya dubi Afaf yace ‘Ba na ga Ummi ta fitar da katifun nan ba? Me yasa suke zarni?’ ‘Ta fitar Abba, sai da yamma sannan ta shigo da su gaba ɗaya. Ban sani ba ko katifar Habib ce ba ta bushe ba don ba mu san an yi fitsari ba sai wajen la’asar sanna ya gaya mata Shukra ta yi masa fitsari bayan asuba da ka kwantar da ita.

    Shi ne aka shanya, to ina jin ita ce ba ta gama bushewa ba.’ Ya ƙarewa ɗakin kallo, ko shimfiɗa ba a yi ba a kan gadon don haka ya sa Afaf ta yi musu shimfiɗa yayin da shi kuma ya wuce da su banɗaki don su yi brush. Nan da nan kowa ya shirya bayan sun fito sun kwanta ya cewa Afaf ‘Wai sai yaushe katifun nan za su daina zarni ne?’

    ‘Ni ma ban sani ba Abba, kuma fa idan ba ka saka su sun yi fitsari da daddare ba haka gobe ma za su sake yin fitsarin nan fa. Dama Anti ce kullum take tashinsu, Nasreen sau ɗaya ita kuma Shukra sau biyu shi yasa basa yi a kwancen. ‘To ƙarfe nawa take tashinsu?’

    ‘Wallahi Abba ni ma ban sani ba, kawai dai tana tashinsu.’ Ya amsa sannan ya fito ya dawo parlor ya zauna; to shi yanzu ya za a yi ya san ƙarfe nawa zai saka su wani fitsari, ga shi kuma ga dukkan alamu idan ya bar su suka cigaba da fitsarin nan a kwance to lallai gidan zai daina zaunuwa.

    To amma ƙarfe nawa zai saka su? Wataƙila sai dai kawai idan ya tashi kwanciya bacci ya saka su shikenan. Nan ya zauna a parlor ɗin ya cigaba da kallonsa yana chatting, har ya sami Khadeejan ma online suka ɗan yi hira.

    Ba su fi awa ɗaya da kwanciya ba ya jiyo kukan Shukra daga ɗakin, da sauri ya dire wayar da take hannunsa ya nufi ɗakin. Tana zaune a kan gadon tana ta faman kuka har da hawaye. Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita yana cewa ‘Menene Shukra?’ ‘Kashi zan yi.’

    ‘To ai ba sai kin yi kuka ba Shukra, sauko mu je na saka ki a toilet.’ Ya sauke ta daga kan gadon ya ja hannunta suka wuce banɗaki, suna shiga ya cire mata wando ya fara ƙoƙarin ɗora ta a kan toilet ta dafe duwawu tana juyi tana cewa ‘Ina fo na Abba a shi zan yi.

    ’Cikin muryar lallashi yace ‘To ai ba a ganshi ba ki yi haƙuri ki hau toilet. ‘Mu je ka duba banɗakin Anti fo ɗina yana nan Abba a shi zan yi kashin.’ Ya ɗauke ta gaba ɗaya ya ɗora a kan toilet yana cewa ‘To ki gama kashin kada ya fito in ya so idan kika gama sai mu je mu dubo fo ɗin.’

    Kafin ya rufe bakinsa ta zame ta sauka daga kan toilet ɗin, tana kuka. Ta cigaba da bubbuga ɗuwawunta tana shirin ficewa daga banɗakin tana cewa ‘Fo na yana banɗakin Anti bari na ɗauko a shi zan yi kashin.’ Cike da tsananin mamaki da takaici yake kallonta, ga dukkan alamu kashin ya matse ta amma ita ba ta da niyyar zama a toilet ɗin nan so take dole sai ya ɗauko mata fo; fo ɗin da ya riga ya jefar ba tare da kowa ya sani ba.

    Ya kai hannu ya damƙota tana shirin ficewa daga banɗakin, ya mayar da ita kan toilet ɗin ya zaunar da ita yana cewa ‘Anti ta kulle ɗakinta ta tafi da mukullinta sai ta dawo za ta buɗe mana, ki yi kashin a nan.’ Ta sake direwa ta sauka daga kan toilet ɗin tana buga ɗuwawu har da juyi saboda yanda kashin ya matse ta tana cewa ‘Ka zo na nuna maka Abba ba ta rufe ba, a buɗe ɗakin yake ɗazu ma na shiga.’

    Kafin ya yi wani abu kashin ya ƙwace mata, ɗan kaɗan ya faɗo ya zame daga ɗuwawunta ya ɓata tsawon ƙafarta sanna ya dire a ƙasan toilet ɗin. Ya yi wuf ya ɗauketa ya daka mata tsawa yana cewa ‘Ki zauna a nan ki yi kashin nace, kalli yanda kika ɓata jikinki kika ɓata toilet ɗin da kashi.’

    Ta sake fashewa da kuka tana yi tana shessheƙa, takaici ya sa ko magana ba zai iya yi mata ba don haka ya ƙyale ta kawai yana tsaye tana rungume da ƙafarsa yana jira ta gama. Ko minti ɗaya ba ta yi ba tace masa ta gama kashin, ya leƙa toilet ɗin shi bai ga komai ba. Yace ‘Idan fa kika yi min kashi a wando zane ki zan yi Shukra gara ki gama kashin nan a nan.’

    ‘Na gama. Ya ɗauketa cak ya ajiye ta a wajen wanka, ya ɗauki sprayer ɗin yin tsarki ya fesa mata ruwan da ƙarfi ta yanda ruwan ya wanke kashin jikinta, sannan ya saɓi sabulu ya wanke mata da hannunsa. Ya ɗauke ta ya fitar da ita ya shirya ta ya kwantar da ita sannan ya koma banɗakin; ya tsaya daga bakin kofa ya ƙarewa banɗakin kallo.

    Ga guntun kashin da ta jefar a ƙasa sannan gashi duk ta shafe na jikinta a jikin toilet ɗin banɗakin har ya fara wari. Ya yi tsaki ya juya ya fice, jimawa kaɗan ya dawo ɗauke da tissue paper, ya warware kusan rabinta sannan ya yi amfani da ita ya ɗauke guntun kashin jefe a toilet ɗin. Sannan ya sake warwarowa ya goge toilet ɗin ya yi flushin sannan ya fito ya dawo parlor ya zauna cike da takaici da gajiya.

    A nan a parlor ɗin bacci ya kwashe shi, wataƙila saboda tsabar gajiya domin bacci ya yi masa nauyi sosai. Maganar Shukra ce ta farkar da shi wadda ta je tashinsa tana sanar da shi za ta sha shayi. Ya tashi zaune yana mittsike ido, ya lalubi waya ya duba lokaci; ƙarfe ukun dare saura.

    Haka ya tashi ya haɗo mata shayin ya zo ya ba ta ta shanye sannan ya ja hannunta suka koma ɗakin. A nan ya tarar ita da Nasreen duk sun riga sun yi fitsarinsu a kwance; ya canzawa Shukra kaya ya lallaɓa ya kwantar da ita a gefen da bai jiƙe ba kusa da Afaf. Ya ɗan tsaya ya ƙarewa ɗakin kallo, sai kuma ya juya ya fice.

    Gaba ɗaya kansa ya kulle; wai dama haka yaran nan suke ko kuwa don sun ga mahaifiyarsu ba ta nan ne kuma Khadeeja ba ta nan suka saka shi a gaba suka hana shi sakat, domin wasu abubuwan da suke yi ma kamar da gayya musamman Shukra.

    Har zai zauna a parlor ɗin kuma ya tuna sai ya dafa abinda zai yi sahur don haka y wuce kitchen, ya janyo indomie ya ɗebo park uku sannan ya nemi tukunya ya ɗora; Afaf da Habib sun yi ta fushi a kan jiya bai tashe su sahur ba don haka yau idan ya gama dafa abincin sai ya tashe su.

    Nan da nan ya dafa idomie ya zubawa kowa a plate ya ɗora a dining table sannan ya haɗawa kansa shayi. Bayan ya gama ya wuce ɗakinsu, ya kunna fitila sannan ya ƙarasa ya tashi Afaf, ta zauna a kan gadon tana mittsike ido sanna ya wuce ciki ya tashi Habib. Yana juyawa ya buɗe ido yace ‘Abba asuba ta yi ne?’

    ‘No da saura, sahur za mu yi tukunna ga indomie can na dafa.’ Ya ba shi amsa. Ya gyara kwanciya yana janyo abun rufarsa yana cewa ‘Ni ba zan yi azumi ba Abba, sai gobe.’ Ya rufe ido ya cigaba da baccinsa ba tare da ya sake bi ta kan Abban nasa ba. Afaf wadda take zaune a bakin gadonsu ta juyo tace ‘Abba wai sahur za mu yi.’

    ‘Eh.’ ‘To Abba ai jiya ne ya kamata mu yi azumi kuma ba ka tashe mu ba, ni ma dai gaskiya yau ba zan yi azumin ba sai gobe. Dama haka muke yi da Anti; mu yi ɗaya mu sha ɗaya.’ Ta faɗa cikin halin ko in kula. Ba ta ma tsaya ta saurari amsar shi ba ta koma ta kwanta ta rufe ido.

    Nan ya tsaya yana kallonsu cike da mamaki; wai su yaran nan me yake damunsu ne? yanzu za su ce za su yi abu kafin wani lokaci sun canza ra’ayi. Gaskiya ya jinjinawa mata, ai idan ba mace ba babu wanda zai iya raino; jiya fa Afaf fushi ta yi da shi saboda bai tashe ta ba amma yau kuma ita yake tashi tana ce masa wai yau bai kamata ta yi azumi ba.

    Yana fitowa daga ɗakin ya haɗa indomie ɗin ya juye a tukunyar ya rufe ya ajiye musu a kan idan gari ya waye sa ci abincin safe, sannan ya dawo ya ƙarasa sahur ɗinsa.

    Kamar yanda suka saba yau ɗin ma da tun asuba suka tashe shi a kan yunwa suke ji, haka ya shiga kitchen Afaf ta taimaka masa ya haɗawa kowa cereal domin duk sun ce ba za su ci indomie ba don ta yi sanyi kuma ba sa son ɗumame, da ya takura musu ma sai Nasree cewa ta yi ‘Abba kai fa idan ka dafa indomie ba ta daɗi, ka bari idan Anti ta dawo ta koya maka.’

    Don haka kawai sai ya mayar da indomie ɗin ya rufe. Tun wajen goma na safe yake sa ran shigowar Ummi don ya riga ya gaya mata yau ma ta zo, sai dai ga mamakinsa har wajen sha ɗaya saura ba ta shigo ba; gashi har na fara yi masa ƙorafin yunwa kuma ana ba shi warning ba za a ci indomie ba sai da taliya ko macaroni.

    Yana shirin fita ya je gidan su Ummin aka buga gate; ƙanwarta ce wadda suke kira Nana, wadda ba ta fi shekaru bakwai ba. Bayan ta gaishe shi tace ‘baba yace na gaya maka Ummi ba za ta sami zuwa wajen su Afaf ba yau don ta tashi da mura me zafi tana kwance, yace sai dai ko zuwa gobe idan ta sami sauƙi za ta shigo.’

    Jiki a sanyaye ya amsa ‘To, kice ina mata sannu kuma ki ce ina gaida Baban. ’Ya rufe kofar ya koma cikin gidan gwiwarsa a sanyaye; ya zai yi da yaran ga gidan kace-kaca musamman kitchen ɗin, ko ina kwanuka. Tukunna ma; mura fa aka ce Ummi take yi. Inna lillahi wa inna ialaihi raji’un! Allah ya sa yarinyar nan ba Covid-19 ta kwaso ba garin yawon tsiya, don tabbas idan ta kwaso to ta shafawa yaransa.

    ‘Subhanallah!’ ya faɗa a fili yana daf da ƙarasawa cikin gidan. Bayan ya shiga gidan ya yi musu bayanin Ummi ba ta da lafiya. Yana ji yana gani haka ya haƙura Afaf ta dafa musu jallof macaroni, bayan sun gama ci kuma ta kwaso wanke-wanke ta fice da shi waje ta wanko; duk da ƙoƙarinsa na hana ta amma haka ta dage ta wankesu.

    Sannan ta umarci Halifa da ya share cikin gidan wanda shi ma nan da nan ya yi, suka dawo suka zauna. Wunin ranar haka ya yi shi yana gyangyaɗi domin ko ya rufe ido da niyyar bacci haka wani zai rugo kai ƙara har Afaf ɗin ma, ko kuma a zo a ce masa ana buƙatar wabi abu; ita kam Shukra haka kawai ma da ta ga ya shiga ɗaki binsa take yi, idan kuam a parlor ne da ya rufe ido za ta kirawo sunanshi tace ya buɗe ido ta nuna masa wani abu.

    Haka har aka kusan magriba sannan ya samu da taimakon Afaf ya soya musu dankalin bature kuma ya dafa musu indomie ta ɗan yi daɗi. Wuni yaran suka yi suna ciye-ciye amma ko da ka sha ruwa ma saka shi suka yi a gaba ana cin abinci suna masa surutu da rigingimu kala-kala; shi dai zai iya cewa ba a hayyacinsa ya ci abincin nan ba. Haka ya dinga ci yana ƙwarewa.

    Ya cika bakinsa da dankali Shukra ta miƙe ta jefar da dankalin da yake hannunta tana dafe ɗuwawu tana cewa ‘Kashi Abba.’Ji ya yi wani malolo ya tokare masa maƙogoro; wai ita Shukra ba ta tashi kashi ne sai mutum yana tsaka da wata sabga? Lallai yanzu ya tabbatar Khadeeja tana da ƙoƙari don kusan tunda aka fara azumin nan sai ana tsaka da cin abinci sannan Shukra take cewa za ta yi kashi kuma ta tashi ta sakata; idan ma ta yi jinkiri shi ne yake nuna damuwarsa.

    Ya dubi Afaf wadda ya kula kamar ta ɓata rai ne yace ‘Yaya Afaf ki saka ƙanwarki a toilet ta yi kashi.’ Ta tashi a fusace ba tare da ta amsa ba ta dire kofin shayin da take sha a ƙasa, tana ɗaga kafa ta yi fatali da kofin shayin ya zube ya fallatsa ya ɓata Habib wanda yake kusa da ita. Ya miƙe a fusace yana nunata ‘Dalla malama ji yanda za ki ƙona ni da shayi saboda kashin wata.’

    Ita ɗin ma a fusace tace ‘To ka matsa mana, ko ba ka gani ne?’ Abbansu ya buɗe baki zai yi magana Shukra tace ‘Kashi Abba.’ Ya tuna yanda suka yi cikin dare ya tabbatar bai shirya wanke kashi a parlor ba don haka ya miƙe ya wuce su ya ja Shukra ya nufi banɗaki da ita. Sai da ta gama kashin ya wanke mata ya fito sannan ya saka su a gaba ya yi musu faɗa, ya sa Afaf ta gyara inda ta ɓarar da shayi.

    Ya kurɓi shayinsa da ya bari ya ji ya yi sanyi, haka dai ya haƙura ya shanye ya ɗan ƙara cin abincin. Haka ya haƙura ya nemi waje ya zauna yana tunani don zai iya cewa ba ƙoshi ya yi ba ya dai haƙura da abincin ne kawai, haka ya dinga bin su da kallo suna ta wasanninsu har loakcin kwanciyar bacci.

    A cikin wannan halin Mustapha ya ƙarasa kwanaki biyu shi da yaran a jigace, ga shi duk wanda ya yi atishawa ko tari a cikin yaran sai ya firgita saboda gani yake kamar corona ce ta kwantar da Ummi kuma su ma sun shafa a wajenta.

    Karanta Mijin Marigayiya Babi Na Bakwai

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tarihin Kafuwar Ƙasar Kuwait

    Tarihin Kafuwar Ƙasar Kuwait

    Tarihin Kafuwar Kuwait, Gwagwarmayar Ɗorewarta da Ci Gaban Tattalin Arziƙinta

    1. Asalin Kafuwar Kuwait

    Kuwait ƙasa ce ƙarama a gabar Tekun Fasha (Persian Gulf). A ƙarshen ƙarni na 17 da farkon ƙarni na 18, ƙabilar Bani Utub daga Najd ta yi hijira zuwa yankin, inda suka kafa wani gari da ake kira Kuwait.

    A shekarar 1756, aka zaɓi Sabah bin Jaber a matsayin shugaba na farko, wanda ya kafa gidan sarauta na Al-Sabah. Wannan tsarin mulki ya cigaba har zuwa yau. A farkon lokaci, tattalin arzikin Kuwait ya dogara da cinikayya, kamun kifaye, da haƙo lu’u-lu’u (pearling).

    2. Dangantaka da Birtaniya da Kariya (ƙarni na 19 – 1961)

    A 1899, Sheikh Mubarak Al-Sabah (Mubarak the Great) ya rattaba hannu kan yarjejeniya da Birtaniya (Anglo-Kuwaiti Agreement). Wannan ya sanya Birtaniya ta kula da harkokin waje da tsaro, yayin da gidan Al-Sabah ya ci gaba da mulki a cikin gida.

    Wannan kariya ta kare Kuwait daga mamayar Usmaniyya da makwabta, amma ta rage mata cikakken ’yanci har zuwa ƙarshen ƙarni na 20.

    3. Samun ’Yanci da Tsarin Mulki (1961–1962)

    A 19 ga Yuni, 1961, Kuwait ta sami ’yancin kai daga Birtaniya. Sheikh Abdullah Al-Salim Al-Sabah (Father of the Constitution) ya jagoranci kafa kundin tsarin mulki a 1962, wanda ya samar da Majalisar Dokoki (National Assembly) – ɗaya daga cikin na farko a yankin Larabawa.

    4. Gano Mai da Juyin Tattalin Arziƙi

    An gano filin Burgan a 1938 – ɗaya daga cikin manyan filayen mai a duniya. Bayan fitar da mai cikin kasuwanci daga 1946, tattalin arzikin Kuwait ya sauya gaba ɗaya:

    Gina tituna, gidaje, asibitoci, da makarantu.

    Samar da ayyukan gwamnati da walwala.

    A 1960, Kuwait ta shiga cikin OPEC tare da sauran ƙasashen masu mai.

    5. Mamayar Iraƙi da Yaƙin Gulf (1990–1991)

    A 2 ga Agusta, 1990, Saddam Hussein ya mamaye Kuwait yana iƙirarin cewa ƙasar tana cikin Iraƙi. Wannan ya haifar da Yakin Gulf (Operation Desert Storm, 1991), inda haɗin gwiwar ƙasashen duniya ƙarƙashin jagorancin Amurka suka fatattaki sojojin Iraƙi.

    Illolin Mamayar:

    • Ƙonewar rijiya 700 na mai, gurɓacewar muhalli, da asarar arziƙi.
    • Kwace kuɗaɗen baitulmali da lalata ababen more rayuwa.
    • Bayan yaƙi, Kuwait ta fara sake gina tattalin arziki da gyara kayan more rayuwa.

    6. Sake Gina Tattalin Arziƙi da Vision 2035

    Bayan yaƙin, Kuwait ta ƙarfafa Kuwait Investment Authority (KIA), ɗaya daga cikin tsoffin asusun saka jari na gwamnati a duniya. Wannan ya taimaka wajen kare tattalin arziƙi daga dogaro da mai kawai.

    A 2017, aka ƙaddamar da Vision 2035 – “New Kuwait” domin rage dogaro da mai, haɓaka sashen ilimi, kiwon lafiya, da kasuwanci. Babban shirin gine-gine: Silk City (Madinat al-Hareer) da Jabr Al-Ahmad Bridge.

    7. Tsarin Kuɗi da Darajar Kuwaiti Dinar

    A lokacin ’yanci (1961), Kuwait ta ƙaddamar da Kuwaiti Dinar (KWD), wanda ya maye gurbin Gulf Rupee.

    Dinar ɗin ya samu ƙarfi saboda:

    1. Arziƙin mai mai yawa.

    2. Ƙananan bashi na gwamnati.

    3. Tsarin kuɗi mai tsauri (currency peg to basket of currencies).

    4. Babban asusun saka jari a waje (KIA).

    5. Ƙarancin jama’a idan aka kwatanta da kuɗin shiga.

    Jadawalin Kuɗaɗen Duniya (2025)

    Kudi = Daraja a USD (kimanta)

    • Kuwaiti Dinar (KWD) ≈ 3.25 USD
    • Bahraini Dinar (BHD) ≈ 2.65 USD
    • Omani Rial (OMR) ≈ 2.60 USD
    • Jordanian Dinar (JOD) ≈ 1.41 USD
    • British Pound (GBP) ≈ 1.27 USD
    • Euro (EUR) ≈ 1.09 USD
    • US Dollar (USD) 1.00 USD
    • Saudi Riyal (SAR) ≈ 0.27 USD

    Kuwaiti Dinar shi ne kudin da ya fi kowanne daraja a duniya a yau (2025).

    Kammalawa

    Kuwait ta tashi daga ƙaramin gari na kamun kifi da haƙo lu’ulu’u zuwa ƙasa mai arziƙin man fetur, daga nan kuma ta zama cibiyar siyasa da kuɗi a Gulf. Duk da mamayar Iraƙi da ƙalubale na dogaro da mai, ƙasar ta sake farfaɗo, ta kafa asusun saka jari na duniya, kuma a yau tana kan tafarkin bambance hanyoyin arziƙi ta hanyar Vision 2035.

    Alamar nasarar tattalin arziƙinta ita ce Kuwaiti Dinar – kuɗin da ya fi kowanne daraja a duniya.

    Karanta Gudunmawar Sarki Abdulazeez Da Birtaniya Wajen Kafa Ƙasar Saudi Arabia

    Edita@rumasau-kallamu