Category: WikiHausa

Yadda ake amfani da WikiHausa

  • ‎Tatsuniyar Yarinya Da Dodanni

    ‎Tatsuniyar Yarinya Da Dodanni

    ‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    ‎Wata yarinya ce dai mai tsananin kyau, duk garinsu babu mai kyanta, ta ce ba ta son kowa sai maras tabo. Sai dodanni suka ji labari. Sai suka yi wanka a gidan tururuwa. Sai suka zama samari kyawawa da su.

    ‎Da ta gan su, sai ta ce ta sami mazan aure. Sai duk ta dube jikinsu, sai ta ga jikin wannan da ɗan tabo ɗan mitsitsi, sai ta ce ba ta son sa. Da ta duba jikin ɗayan ta gan shi‎ sumul ba ko ɗigon tabo a jikinsa, sai ta ce shi ta ke so.

    ‎Shi kenan, sai aka shirya aka yi biki. Sai suka ce za su tafi da ita garinsu, su ba mazauna ba ne, Sai aka ce to za a ba ta ƙanwarta ta taya ta zaman ɗaki. Sai ta ce ita ba ta so, ta zauna ita kaɗai. Shi kenan, aka yi aka yi su tafi da ƙanwarta ta ƙi. Sai ƙanwar ta zama ƙuda ta maƙale mata.

    ‎Shi ke nan, da suka je gidan dodanni, sai dare ya yi suka shiga ɗaka suka rufe ƙofa. Sai ta ga ƙanwarta, sai ta rufe ta da faɗa, ta ce, ‘Ke wa ya kawo ki nan? ‎Ita kuwa ƙanwar sai ta yi shiru. ‎Shi ke nan sai yar ta ƙyale ta.

    ‎Ita yar kamar sokuwa ta ke. In dare ya yi, sai ta yi ta shirga barci. Ita kuwa ƙanwar sai ta zauna tangar har gari ya waye. Sai uwar mijinta ta zo da tsakar dare ta ce:

    ‎Sarma-sarma duf-duf.

    ‎Sai ƙanwar ta ce:

    ‎Wane ne nan ya ke mana Sarma-sarma duf-duf?

    ‎Sai uwar mijin ta ce:

    ‎Uwar miji ce ta ke mu ku Sarma-sarma duf-duf.

    Sai yarinya ta ce:

    Me ki ke so ki ke mu ku Sarma-sarma duf-duf?

    Sai ta ce:

    Wuta na ke so na ke muku Sarma-sarma duf-duf.

    Sai yarinya ta ce: Iya ga wuta nan.

    ‎Ki bar mana Sarma-sarma duf-duf.

    ‎Sai yarinya ta watso mata wutar. Tsohuwa ta je ta kashe wutar ta kuma dawo musu. Nan kuwa ashe ba wuta ta ke so ba. So ta ke yi ta cinye su idan ta tarar sun yi barci. Kullum haka, kullum haka. Duk sa’ad da yarinyar ta gaya wa yarta game da uwar mijin mai zuwa ɗiban wuta da daddare, sai yar ta ce ƙarya ta ke yi.

    ‎Ana nan a haka sak, ran nan yarinya ta ce da yarta, ‘To, yau dai ki zauna kada ki yi barci don ki ji yadda mu ke yi da tsohuwar da kunnenki. Shi ke nan, ya ta zauna. ‎Sai ita uwar mijin ta zo ta yi musu irin yadda ta ke yi kullum. ‎Shi ke nan, sai ya ta ji da kunnenta.

    ‎Shi kuma mijin nata yana wani ɗaki suna kwance tare da abokansa. Idan an yi abinci na aikin gona an kai musu, sai su yi haka su bunne. Sai su yi ta cin kwaɗi. Ita kuwa ƙanwar, wadda ta kai musu abincin, sai ta ce da su:

    ‎Mijin yata, ci kwaɗi.

    Mijin yata, ci kwaɗi.

    Mazan-wazata, ci kwaɗi.

    Sha da kwaɗi, ci kwaɗi.

    Sha da kwaɗi, ci kwaɗi.

    Su kuma idan sun ji wannan waƙar, sai su yi ta rawa suna cin kwaɗi. Shi ke nan. Da sun ga ƙanwar ta dawo daga gida, sai su zama mutane su ce, ‘Ga kwanukanki nan.

    Ki ce muna yi mata sannu da aiki. Shi ke nan. Da sun ga ƙanwar ta dawo daga gida, sai su zama mutane su ce, ‘Ga kwanukanki nan. Ki ce muna yi mata sannu da aiki. Shi ke nan, sai yarinya ta ɗebi kwanuka ta tafi da su gida. Kullum haka, kullum haka.

    ‎Sai rannan yar ta yi shawara da ƙanwarta don su gudu gida. Sai suka yi ta haƙa rami, tun daga nan gidan har ya zuwa hanyar ƙofar garinsu. Suna ta bin rami da ita da ƙanwarta har suka je gida.

    ‎Iyayenta suka ce da ita, ‘Lafiya?’ Sai ta ce wa iyayenta, ‘Ashe dodanni ne? Ni ca na ke mutane ne.’ Shi ke nan. ƘurunƘus kan ɗan ɓera. Ba don ƙarya ƙarya ce ba, wa zai zuba  ruwa a jallo, jallo ya fashe kuma ruwan bai zube ba?

    ‎Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafi mai suna TATSUNIYOYI DA WASANNI wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

    Danna nan don karanta Labarin Kalala Da Kalalatu

    Edita@rumasau-kallamu

  • Hadisi Na Uku A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    Hadisi Na Uku A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) ya ce: Na ji mai gaskiya abin gasgatawa mai wannan ɗakin baban Alƙasim (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Ba a cire tausayi sai daga zuciyar mara rabo a lahira”.

    Abu Dawud da Tirmizi ne suka rawaito shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisi Na Huɗu A kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu Akan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Hadisi Na Biyu A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    Hadisi Na Biyu A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    An karɓo daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Asi (Radiyallahu Anhuma) haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Masu tausayi Allah mai rahama zai tausaya musu. Ku tausayawa na ƙasa da ku wanda yake sama da ku zai tausaya muku.

    Abu Dawud da Tirmizi ne suka rawaito shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisi Na Uku A kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu Akan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikaken Littafin danna nan.

  • Hadisi Na Ɗaya A ƙan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    Hadisi Na Ɗaya A ƙan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    An karɓo daga Jarir ɗan Abdullahi (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Duk wanda ba ya tausayin mutane Allah ba zai tausaya masa ba”.

    Bukhari da Muslim da Tirmizi ne suka rawaito shi. Ahmad ma ya rawaito shi ya ƙara da cewa: “Wanda ba ya afuwa Allah ba zai yi masa afuwa ba”.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisi Na Biyu Akan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu Akan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Falalar Salla A Masallacin Haramin Makka Da Madina

    Falalar Salla A Masallacin Haramin Makka Da Madina

    An karɓo daga Abu Hurairah (Radiyallahu anhu) ya ce: Haƙiƙa Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) yace; “Salla a masallaci na ta fi salla a wani masallaci sau dubu ban da masallaci mai alfarma”(Bukhari 1190 Muslim 1394).

    An karɓo daga Abdullahi Ibn Zubair (Radiyallahu anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) yace: “Salla a masallaci na tafi salla dubu a sauran masallatai ban da masallacin harami, kuma salla a masallacin harami tafi salla dubu ɗari a wannan masallacin” (Ahmad, Ibn Khuzaimaha, Suhihul Jami’I 3841).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Zama A Madina Ya Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Sallar Idi danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Lallai Ne Shugaba Ya Nemi Yardar Allah Shi Kaɗai

    Lallai Ne Shugaba Ya Nemi Yardar Allah Shi Kaɗai

    An karɓo daga wani mutumin Madina ya ce: “Ma’awiyya ya rubutawa Aisha (Radiyallahu Anha) wasiƙa ya ce: “Ki rubuto min wata wasiyya amma a taƙaice”. Sai ta ba shi amsa da cewa: “Assalamu alaika, bayan haka haƙiƙa na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana cewa: “Wanda ya nemi yardar Allah da aikata abinda zai sa mutane su yi fushi da shi, Allah zai isar masa da wahalar mutane.

    Kuma wanda ya nemi yardar mutane da aikata abinda zai jawo masa fushin Allah, sai Allah ya ƙyale shi da mutanen. Ka huta lafiya.

    Tirmizi da Ibn Hibban ne suka rawaito shi da lafazin: “Wanda ya nemi yardar Allah da aikata abinda zai jawo masa fushin mutane, sai Allah ya yarda da shi, kuma ya sa mutane da su yarda da shi. Wanda ya nemi yardar mutane da aikata abinda zai jawo masa fushin Allah, Allah zai yi fushi da shi, kuma ya sa mutane su yi fushi da shi.

    ƘARIN BAYANI

    Ya zama wajibi a kan duk wani mai jagoranci ya zartar da hukunci na gaskiya wanda ya dace da dokokin Allah koda kuwa ɗaukar wannan matakin zai fusata mabiya ko kuma waɗansu daga cikinsu. In dai ya yi haka da kyakkyawar niyya to zai samu yardar Allah da falalarsa da taimakonsa kuma zai buɗa tunanin mabiyansa su fahimce shi su yarda da shi.

    Idan kuwa ya kasance ƙoƙarin shugaba shi ne ya farantawa mabiyansa ya yi musu duk abinda suke so, koda kuwa wannan abun ya saɓawa gaskiya da dokokin Allah to haƙiƙa zai gamu da fushin Allah da azabarsa, kuma daga ƙarshe sai su waɗanda yake ƙoƙarin farantawa ɗin sun juya masa ba ya sun yi fushi da su.

    Saboda haka, duk wani ƙuduri ko mataki da shugaba zai ɗauka ya kasance na gaskiya ne kuma ya yi shi da kyakkyawar niyya sannan kuma ya kasance tare da hikima da tausasawa, kada ya damu da sai ya farantawa kowa, wannan ba zai haifar masa da wani alhairi ba a wurin Allah da kuma wurin su kansu mabiyan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisai Na Ƙarya Da Raunana A Kan Ashura danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu Akan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Zikiri Kafin (Gabanin) Da Bayan An Gama Alwala

    Zikiri Kafin (Gabanin) Da Bayan An Gama Alwala

    Zikiri Kafin (Gabanin) Alwala

    “Bismillaahi”.

    {Da sunan Allah}.

    Zikiri Bayan An Gama Alwala

    “Ashhadu an laa ilaha illallahu wah dahu laa sharika lahu wa Ashhadu anna Muhammadu abduhu wa rasuluhu”.

    {Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaɗai, babu abokin tarayya a gare shi, kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wasallam) bawansa ne kuma manzonsa ne}.

    “Allahumma ja’alnii minat-tauwaabina waj’alnii minal mutaɗahhiriina”.

    {Ya Allah! Ka sanya ni a cikin masu yawan tuba, kuma ka sanya ni a cikin masu tsarkaka}.

    “Subhanakal-laahumma wabi hamdika Ashhadu an laa ilaaha illaa anta wa astagfiruka wa atubu ilaika”.

    {Tsarki ya tabbata gare ka ya Allah tare da yabo gare ka. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai kai, ina neman gafararka kuma ina tuba gareka}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Zikiri Yayin Fita Daga Gida danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Ayyukan Gida Domin Taimako Juna danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Rasuwar Makaɗa, Sarkin Kiɗan Maradun Alhaji Musa (Ɗanƙwairo)

    Rasuwar Makaɗa, Sarkin Kiɗan Maradun Alhaji Musa (Ɗanƙwairo)

    Rasuwar Makaɗa, Sarkin Kiɗan Maradun Alhaji Musa (Ɗanƙwairo) Usman Ɗankwanagga a 1991.

    Sarkin Kiɗan Maradun, Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun, bayan wata gajeruwar rashin lafiya; Allahu cikin ikonsa ya karɓi rayinsa a ranar Juma’a 13 ga watan Satumba, 1991. Ya rasu a gidansa a Gidan Kano, Ƙaramar Hukumar Maradun, Jihar Zamfara.

    Allahu, karimun rahimun, ya daɗa haskaka makwancinsa, ya hore masa ni’imomi na Raudhatun min Riyadhil Jannah.

    Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo bawanka ne, ya sami shekaru talatin (30) izuwa ga jinƙanka; Allahu ka daɗa yafe kurakuransa, ka yi masa afuwa, ka kwantar da shi cikin Rahamarka, madauwamiya.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Takaiceccen Tarihin Rayuwar Dr. Yahaya Tanko danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tarihin Rayuwa Da Halifofin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun A Aiwatar Da Sadar Da Waƙoƙin Baka Na Hausa; wanda Prof. Sa’idu Muhammad Gusau ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Waƙa Mai Taken Gudumar Dukan Rashawa

    Waƙa Mai Taken Gudumar Dukan Rashawa

    1. Ya Allah sunanKa farko,

    Don aikina ya yi ƙarko,

    Har al’umma duk su farko,

    Mu kauce hanya mai duɗewa.

     

    2. Na yi salati gun sa Manzo,

    Wanda ya ce duk mu yi ƙwazo,

    Biɗar halal duk inda mun zo,

    Shi ne tafarki mai ɓulewa.

     

    3. Waƙa zan yi a kan halinmu,

    Wanda ya zam shi jiki gare mu,

    Tamkar umarnin khaliƙinmu,

    Mun ɗauke shi muna riƙewa.

     

    4. Yin rashawa ko toshe baki,

    Don kwaɗayin ai wani aiki,

    Wanda ya kauce wa tafarki,

    Albarkarmu yake ragewa.

     

    5. Guba ce wallah in ka karɓa,

    Ko ko ka bayar anka karɓa,

    Dokar Allah ce ka saɓa,

    Ƙin gaskiya hanyar ɓacewa.

     

    6. Mutunci farko zai zubewa,

    Aiki ya zam ba kyautatawa,

    Sai amaja da sukurkucewa,

    Al’amuranmu su dagulewa.

     

    7. Mai haƙƙi ne an hana shi,

    Wanda take mai kyau niyarshi,

    An ba mai bayar da toshi,

    Wanda niyarsa abar gujewa.

     

    8. Muddin an haka ba amana,

    Ba adalci sai hiyana,

    Sannan babu zaman lumana,

    Sai ɗar-ɗar sai firgicewa.

     

    9. Kwai rashawar daɗaɗa zance,

    Wata da aiki kan kasance,

    Wata jaka ce za a sunce,

    Ɗan hasafi a zamo yiwowa.

     

    10. Wata ko kyauta za a ba ka,

    Iyaye ko ko a ba wa ɗanka,

    Domin biɗar wani abu gun ka,

    Ka yarda ko ko ka zam ƙiyawa.

     

    11. Kowane nau’i ya haramta,

    Annabi ya tsine wa yin ta,

    Mai karɓa har wanda yai ta,

    Dai dai ne suke ba rabewa.

     

    12. Ga lamura yau sun ƙazanta,

    Harka duk an sassaka ta,

    An rufe duk munin sifarta,

    Sunanta an kyautatawa.

     

    13. Na yi tunanin me ya sa ne,

    Ba ƙyamar ta wurin mutane?

    Duk mai cin rashawa mu gane,

    Har mai ba shi abin gujewa.

     

    14. Rashin kishi ni a ganina,

    Shi ke sawa har a raina,

    Halali sai a ga wai kaɗan na,

    Sai an ɗora haram daɗawa.

     

    15. Duk mai kishi ga ƙasarsa,

    Mai kishin kuma al’umarsa,

    Ba ƙofar rashawa a gun sa,

    Siraɗi gobe yake wucewa.

     

    16. Son kai yai kanta a zuci,

    Tai tsatsa sassanta ya ci,

    Shi ke sa rashawa ake ci,

    Ba ƙyama sai ƙawatawa.

     

    17. Ƙyashin samu ga waninmu,

    Da ci da zuci ke hana mu,

    Yin haƙuri bisa matsayinmu,

    Wanda Ilahu ya zam rabawa.

     

    18. Sai haɗama sa har da wannan,

    Son a fiye wancan da wannan,

    Su ke sa rashawa ƙasar nan,

    In mun bar su tana gushewa.

     

    19. Yaƙin halayen ga dole,

    Kishin ƙasa mu riƙe shi lalle,

    Sai lamuranmu su sake lale,

    Albarka ta isa ga kowa.

     

    20. Irin haka ne manyan ƙasashe,

    Da ke amo kowane sashe,

    Na duniya suka yi koyaushe,

    Al’umarsu take ta shewa.

     

    21. Ba su barin azzalumina,

    Sun taushe maciya amana,

    Ba sa ƙyashin ikhiwana,

    Cima gabansu suke biɗowa.

     

    22. Dubi yawan jama’a ta Caina,

    Sun haɗa kai babu hiyana,

    Sun aiki a dare da rana,

    Yau kayansu muke shigowa.

     

    23. Turawa haka sunka dage,

    Duk aiki nasu babu coge,

    Cin rashawa duk sunka toge,

    Ba sa yin sa suna ƙiyawa.

     

    24. Don haka ne duk al’umarsu,

    Tai bunƙasa arziƙinsu,

    Yai albarka kowanensu,

    Na fahari da abin da kewa.

     

    25. Mu ma dole mu ɗaura niyya,

    Yin aiki ja mui gamayya,

    Kowa ya zo yara da manya,

    Mu ɗau rashawa izuwa kushewa.

     

    26. Niyya ƙwaƙƙwara mu ɗaura,

    Don yaƙar duk asharara,

    Masu zagon ƙasa masu ƙera,

    Turakun ci bayan da kewa.

     

    27. Ba wasu ne maciya amana,

    Ga dukiya ta ƙasa su danna,

    Wasoso sun ƙi su daina,

    Ha’intar mu suna ta yowa.

     

    28. Ƙaunar ƙasa ta zamo gabanmu,

    Don bunƙasar arziƙinmu,

    Da ci gaban duk jama’armu,

    Alheri ya isar wa kowa.

     

    29. Lallai mu so wa ɗan uwanmu,

    Abin da muke ƙauna ga kanmu,

    Ko ma mu fifita shi kanmu,

    Babu ganin ƙyashi da rowa.

     

    30. Doka mai tsanani a yo ta,

    Kan rashawa duk masu yin ta,

    A kame don sun yo mugunta,

    A kai wa Yari ya zam tsarewa.

     

    31. A nusarshe da dukan mutane,

    Munin aikin don su gane,

    Su ƙyamaci mai yi ko wane ne,

    Don ba son mu yake yiwowa.

     

    32. Azzalumai ku mu yo rahoto,

    Zuwa hukuma don a ƙwato,

    Haƙƙoƙi kowane loto,

    Ba tsoro ko razanewa.

     

    33. Mutum ne zai tono masifa,

    Ba shi ɗai ne za ta shafa,

    Har kowa dole mu dafa,

    Ɓarnatai mu zamo hanawa.

     

    34. Cin rashawa ke sa talauci,

    Aikin ɓarna ya yi kauci,

    Duk lamura saura su ɓaci,

    Dole mu yaƙar ba gazawa.

     

    35. Aikin kowa ne da kowa,

    Hukumomi ku mu tallafa wa,

    Domin ƙasarmu ta zamowa,

    Abar fahari ba ha’inawa.

     

    36. Hukumomin jin ƙorafinmu,

    Sun tsaye domin taimakon mu,

    Yaƙar kaskar da ka cin mu,

    Cima gabanmu suna hanawa.

     

    37. Mu roƙi Allah taimakonsa,

    Kan yaƙi bisa ‘yan ta’asa,

    Masu ciye rashawa su ƙosa,

    Da ha’inai ‘yan handamewa.

     

    38. Allah ba mu yawan ƙana’a,

    Ƙaunar juna da muru’a,

    Cin rashawa mu yi mai bara’a,

    Don Manzo ɗan Hashimawa.

     

    39. Nasiru G. Ahmad ya yi ta,

    Don harkar rashawa mu bar ta,

    Mu soyi juna mu rabauta,

    Halinmu ya zamo yabawa.

     

    40. Goma huɗu baitinta jumla,

    Ce Arba’in na gode Allah,

    Allah tsare mu biye ralala,

    Amin sarki mai iyawa.

     

    Danna nan don karanta Waƙa Mai Taken Masha-Jini

    Edita@rumasau-kallamu

  • Waƙa Mai Taken Masha-Jini

    Waƙa Mai Taken Masha-Jini

    1. Allah ba ni buɗi in yi tsari na baituka,
    A kan ƙwaro wanda bai da tausai a duniya.

    2. Ƙwaron da yakan cutar da manya da ƙanƙana,
    Mai shanye jini na ɗan Adam ba shi tausaya.

    3. Gwanin zilliya yake da ɓoyo jikin tufa,
    Ko gashi na kai ya zam shi birni ya wataya.

    4. Gudun kar ku ƙosa Kwarkata ce nake nufi,
    Bai ƙyale baƙar fata fara ko ko rawaya.

    5. Abin da kan samar ta ƙazanta ce Lamba Wan,
    Haɗewar zufar jiki da dauɗa annakiya.

    6. Da wannan haɗi Allah kan samar da kwarkwata,
    Ta rayu tufar mutum gashin kansa kulliya.

    7. Tana sanya ƙwai ta ƙyanƙyashe shi da hanzari,
    Su zamto yawaita ɓamɓare ta akwai wuya.

    8. Abinci nasu jinin mutum za su yi ta sha,
    Ya kasa sukuni a dare ko ko safiya.

    9. Hanyar yaɗuwa tata kusantar jikin mutum,
    Da ya zam yana ɗauke da ta ko da sau ɗaya.

    10. Ko ko sanya rigarsa hula ko ko fattala,
    Hakan nan kwana da mai ita gun ɗaki ɗaya..

    11. Idan har ta samu sai a wanke dukan jiki,
    Da ruwa na kogi “Ma’ul Khalli” a gauraya.

    12. Mutum kan yi kwarkwata ba don ba shi tsaftace,
    Jikinsa sai Ibtila cire ta akwai wuya.

    13. Misali mutum Biyu cikin wanda anka wa,
    Busharar shiga Aljanna tun nan a duniya.

    14. Abdurrahamani Auf Sahabi attajiri,
    Zubairu ɗan Awwamu Sahabi abin biya.

    15. Allah ya jarabce su da ƙwaron ga kwarkwata,
    Tufarsu da gashin kai dare har da safiya.

    16. Har Manzo ya sauƙaƙa gare su halal yake,
    Rigar Alharini sunka sanya ta duniya.

    17. Hakan nan a Hajji ya halatta su aske kai,
    Su bayar da fiddiya ga nassin Ƙur’aniya.

    18. Dalili na Ukku nan ga samo na kwarkwata,
    Azaba ga kafirai su komo ga shiriya.

    19. Misali Fir’auna lokacin da ya kangare,
    Da shi da mutanensa ɓarna sun yi dulmiya.

    20. Aazabobin gargaɗi da anka saukar musu,
    Ciki har da kwarkwata jikinsu tufafiya.

    21. Har sai da sukai roƙon a janye ta za su bi,
    Musa Annabi ya roƙi Allah ta zam tsaya.

    22. Akwai wanda kwarkwata ba sa yin ta ko kaɗan,
    Luɗufi na Allah ne gare shi a duniya.

    23. Shi ne mai kuturta wanda ta ci yatsu nasa,
    Da ba yatsan kama ta gare shi ko da ɗaya.

    24. Ba a cin ta kwarkwata ƙwaro ne masha jini,
    Jini ko haramun ne umarnin kitabiya.

    25. Hakan nan abinci in ta faɗa ciki nasa,
    Ita da Kuɗin cizo barin cin sa lafiya.

    26. Jininta jikin tufar mai salla an sahhale,
    Ba ya ɓata salla ta dare ko ta safiya.

    27. Haka ma kashe ta nan a salla abin bari,
    Sai dai binne ta ka so ko ƙyale ta bai ɗaya.

    28. Ba a son a kamo ta a jefar abin ƙiya,
    Domin kar jikin wani ta hau tai ta wataya.

    29. Muna roƙon Allahu ya ƙare mu lafiya,
    Ya ije dukkan cuta gare mu baki ɗaya.

    30. Alfarmar Alƙur’ani da Sidi Muhammadu,
    Da an ba wa cetonmu a rana ta tambaya.

    31. A nan zan taƙaita ɗan bayanin da na shira,
    A kan kwarkwata masha jini babu tausaya.

    32. Sunana Muhammad Nasiru Garba Ahmadu,
    Almajir da ke biɗar sani kar ya sulmiya.

    33. Baitoci Talatin ne da Ukku ran Litinin,
    Alfaini da Isshirin Agusta yai gomiya.

    Alhamdu lillahi

    Karanta  Waƙa Mai Taken Nagartaccen Jagora

    Edita@rumasau-kallamu