Category: WikiHausa

Yadda ake amfani da WikiHausa

  • Tarihin Garin Kudan

    Tarihin Garin Kudan

    BABI NA ƊAYA
    Allah mai yin yadda Ya so. Garin Kudan, tsohon gari ne da ya ginu bisa mutunci, tsoron Allah da kuma kishin al’umma. Tsuntsaye sukan tashi da sassafe suna rera waƙar alfijir, iska tana taɗa ganyayyaki kamar mai kiran mutane zuwa sabuwar rana. Ko da yake gari ne na tarihi, amma yana da zuciya mai sabuntawa kamar ruwan rafi da ba ya gushewa.

    A tsakiyar wannan gari ne ake samun jarumin da tarihinsa ya cika duniyar maƙwabta,wato mai girma Hakimin Kudan (Alhaji Ishaƙ Ashir), mutum mai tarbiyya, mai hangen nesa da kuma don ginshiƙin zaman lafiya. Hakimi mutum ne da ake cewa:

    “In ka ji ana yabon gida, to ka san akwai wanda ya kafa.”
    A zamaninsa, Kudan ya ɗauki salo na ci gaba, wanda ba kowa ba ne zai iya jagoranta ba. Mutanensa suna kiransa “Uban Kowa,” domin ko gida na makoki ne ko na suna, ko ɗaurin aure, ko taron al’umma, sai ka gan shi cikin mutane, ba tare da girman kai ko zunzurutun mulki ba.

    Allah ya yi masa tarin tulin baiwa ta samun ‘ƴa’ƴaye mata da maza kamar: Halima, Mariya, Hindatu, Usman (Ɗanladi), Nafi’u, Balarabe, Isma’il, Mas’ud, Gaddafi, Nasiru, Imrana, Abdulshahid, Umar, Abubakar, Yunusa, Muzammil, Sha’awanatu, Furaira (Hajiyayye), Karimatu, Aisha, Shamsiyya, Raliya… jerin sunaye da ke kamar gini-gini masu ɗora gari kan tushe.

    Hakimi kalmarsa ɗaya: “Gari ba ya ci gaba sai al’umma sun zama tamkar juna.”

    Ranar damuwa

    Ranar Lahadi, 3 ga Yuni 2024, wannan gari mai farin ciki ya shiga duhu. Rana ta fito, amma kamar ba ta da ƙarfi. Tsuntsaye ma sun yi shiru, tamkar suna jin wani abu mai nauyi na shirin faruwa. Sai labari ya bazu cikin ‘yan mintoci:
    “Hakimi ya rasu…!”

    Kalmar ta yanke zukata tamkar takobi. Mata suka zube suna hawaye, maza suka tsaya cak tamkar dutse. Kudan ta yi shiru, irin shiru mai ciwo. Wani dattijo ya ce:
    “Mutum mai kyau idan ya tafi, gari yakan yi kamar ya faɗi.”

    Mutanen garin sun yi zaman makoki, sun yi kuka, amma kuma suka yi nazari, domin Hakimi ya riga ya bar saƙon da ba ya mutuwa: al’umma su zama ɗaya.
    Bayan jana’iza, gari ya cika. Mutane sun tashi da kalmar:
    “Idan ka ga alheri ya dusashe, to ka san akwai wanda bai tsaya a kansa ba.”
    A wannan rana aka fara sabuwar tafiya.

    BABI NA BIYU

    Ranar da aka binne Hakimi, dare ya sauka da wata irin nutsuwa da ba a saba gani ba. Kafin wannan lokaci, Kudan gari ne da yake da annuri da hayaniya, amma wannan dare ya yi kamar an ɗaure shi da sarƙar jimami. Ko iska tana motsawa cikin ladabi saboda mutumin kirki ya yi hijirar da ba a dawo wa.

    Amma cikin wannan nutsuwa akwai wani haske da ba kowa ke gani ba, wato hasken da ke fitowa daga zukatan waɗanda Hakimi ya taɓa rayuwarsu da kyawawan ayyuka. Kamar wutsiyar wuta a duhun daji, hasken na neman ya tayar da mutanen gari daga dogon tunani.

    Farfesa Mu’azu (Makiyayi mai raya zukatan mutane da ilimi)

    Bayan sallar Isha’i, Farfesa Mu’azu ya zauna a gindin bishiyar ɗorawa a cikin gidansa, yana kallon taurari tamkar yana karanta tarihin mutane cikin sararin samaniya. Shi mutum ne mai nutsuwa, mai hikimar magana irin ta magabata. Ana cewa:

    “Idan ka ga dattijo yana shiru, ka sani yana magana da zuciyarsa.”
    Ya shaida rayuwar Hakimi, ya san jajircinsa, kuma ya yi imani cewa “labarin gari” ba zai kammala ba sai an rubuta tarihin waɗanda suka wakilci zuciyar jama’a. Saboda haka, ya zaro littafi ya fara rubutu cikin dare, yana cewa:

    “Ba don jarumtakarsa kaɗai ba, amma don darasin da ya bar mana.”
    Farfesa Mu’azu mutum ne da ke haɗa mutane, mai sauƙin kai, mai taimakon marayu, mai ɗaukar nauyin ɗalibai. Hakan ya sa mutane suke kallonsa tamkar hasken fitila a duhun daji. Mutane suna cewa:

    “Mai ilimi kamar ruwan sama ne; ko ka ƙi, ko ka so,idan ya sauka, ya yi maka alheri. Shi ne ya fara kiran al’umma zuwa taro a fadar masarauta, bayan kwana uku da rasuwar Hakimi.

    Malam Aliyu Labaran (Damo sarkin haƙuri)

    A cikin jama’ar Kudan, akwai gwarzon da ba shi da aiki sai ibada da ilimi, wato Malam Aliyu. Mahaddacin Alƙur’ani ne mai ladabi, mai haƙuri da juriya. Idan ya yi magana, harshensa ya yi taushi kamar ruwan zuma.

    A taron farko bayan rasuwar Hakimi, shi ya tsaya ya ce: “Gari kamar jiki ne, idan ɗaya ya ji zafi, dukkan su sun ji. Don haka mu yi aiki tare, don cike giɓi. ”Kalmar ta shiga zukata tamkar wuta a cikin busasshiyar ciyawa.

    Malam Surajo Yunusa (bango majingina)

    Kodayake Malam Surajo ya rasu tun 06/04/2017, amma mutanen gari suna yawan tuna wa da shi. Mutum ne da ya rayu wajen koyar da mutane Alƙur’ani, yana zuwa gidaje ɗaya bayan ɗaya yana cewa: “Ilimi shi ne garkuwar mai rai.”

    Rayuwarsa ta zama misali ga matasa. A wannan lokacin da ake neman sabuwar hanya, mutane da yawa suka fara tunanin yadda Malam Surajo zai yi da ya kasance a raye. Wannan tunanin ne ya fara tayar da sha`awar komawa makarantu da karatu.

    Idan ka yi tafiya cikin dare a Kudan, za ka ji matasa suna karanta Alƙur’ani a ƙananan makarantun allo da ya bari. Wani kamar ya ce: “Mutum ya mutu, amma alherensa suna raye.”

    BABI NA UKU

    A gefe guda kuma, Salmanu Faris wanda ya kasance matashi, marubuci, manomi, ɗan jarida kuma almajiri. Bayan bayan taron sai ya ɗora alƙalamin rubutu. Idanunsa sun yi ja, saboda rashin bacci, amma zuciyarsa cike take da wuta irin wutar da ta ratsa zuciyar mai son ci gaban gari. Shi ne ke cewa:

    “Idan ka ga gari ya tashi, to matasa sun ce ba za su yi shiru ba.”

    Faris ya ga mutanen gari sun shiga tunani, kuma ya yanke shawarar cewa wannan shi ne lokacin da zai tashi tsaye ya rubuta labarin mutanen gari, ya faɗaɗa tunani, ya tunzura matasa, ya yaɗa kiran ci gaba a kafafen sada zumunta da jaridun yankin.

    Shigowar Mawaƙa (Murya Mai Ƙarfafa Zuciya)

    Labaran, Ashiru, Salahu, Ali (Na Annabi) da Rabilu, su ne mawaƙa, sha’irai, kuma manoma. Sun saba da rubutu da waƙoƙi, amma wannan lokaci suka fito da wani sabon salo. Suna cewa:

    “Waƙa ba ta zama waƙa ba sai ta gina zuciya.”

    Suka shirya waƙar “Rayuwar Hakimi” wadda ta zama kamar taken sabon tafiya. Yara da matasa suka rera kanta a tituna, manya suka saurare ta cikin kukan sha’awa. Ta zama kamar ƙaho na farfaɗo da al’umma.

    Kungiyar Malamai (Garkuwar Zuciya da Ilimi)

    Auwal, Salim, Abdulrazaƙ, Abdulhafiz, Sani, Salisu, Abba, Yahaya, Abubakar, Muhammad (Prof), Yasir, su ne suke riƙe da guraben ilimi. Wanda suka kasance malamai na boko da na addini, duk masu haƙuri, nutsuwa da hangen nesa.

    Suka yi taro suka yanke shawarar:

    1. A buɗe darussa na koyar da rubutu da karatu.

    2. A ƙarfafa zaman lafiya.

    3. A koyar da matasa sana’o’in dogaro da kai.

    4. A fahimtar da al’umma mahimmancin zaman lafiya.

    Malam Auwal ya ce:

    “Idan ka ilimantar da ɗa, ka ilimantar da al’umma baki ɗaya.”

    Abubakar Suleiman (mutum na mutane)

    Abubakar, matashi mai arziki, kuma ɗan kasuwa. Ya yi na’am da wannan sabuwar tafiya. Mutum ne da ke da juriya da zuciya mai tausayin talakawa. Ya ce:

    “Ku kafa tsari, ni kuma zan tallafa.”

    Nan take ya ɗauki matasa 25 aiki, ya ba da kayan aiki, ya ba da tallafi ga makarantu da masu koyarwa. Mutane suka fara ce wa juna:

    “Gari zai tashi. Gaskiya gari zai canza.”

    Karanta Waƙa Ta 2 Ga Farfesa Mu’azu Sa’adu Muhammad Kudan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Ɗankaɗafi

    Tatsuniyar Ɗankaɗafi

    Ga ta nan ga ta nan ku.

    Wata mata ce dai ba ta taɓa haihuwa ba, tun da take. Sai ta ce, ‘Allah, Allah, ba ka ba ni ɗa ba, ko da Dankadafi ne? Allah sai ya karɓi roƙonta, sai ta haifi ɗanta namiji. Shi ke nan, yaro yana nan yana girma. Sai ran nan ta goya shi. Da ta gaji da goyo, sai ta ce da shi, ‘To, sauko ka kwanta Ɗan inna.’

    ‎Sai ya ce, ‘Mhm, a baya.’ Ta kuma cewa, ‘Sauko a wanke maka ido.’ Ya ce, ‘Mhm, mn, a baya.’ Kome dai ta ce, sai ya ce, ‘Mhm, Mn, a baya.’ Sai ran nan ta ce, ‘Kai ni dai na gaji.’

    ‎Gun malami za ni ko yana da abin da zai yi mini in rabu da ɗan nan na gaji. Sai ta je wajen malami. Malami ya ce, ‘Duk abin da aka gaya miki kya iya?’ Sai ta ce, ‘I, zan iya.’

    ‎Sai ya ce, ‘To sayo sa guda ki kawo mini.’ Sai ta sayo sa ta kai wa malami. Sai ya ce, ‘To, biyu za a raba, ki ɗauki rabi, in ɗauki rabi.’ Ta ce, ‘To.’ Aka raba naman sa kashi biyu, malami ya ɗauki rabi, ta ɗauki rabi.

    ‎Sai ya ce, ‘Ki soya wannan ki tafi da shi daji ki haɗa da majanyi da zane. In kin sauko yaron yana cin naman sai ki gudo ki baro shi can.’ Sai ta ce, ‘To.’ Ta je gida ta soya nama. Ta tafi daji da shi. Ta ce, ‘Dan Inna, Dan Inna, sauko ka ci nama.’

    ‎Sai ya ce, ‘Mn, a baya.’ Sai ta ce, ‘Ga naman naka nan sauko ka ci.’ Sai ya sauko. Da ya sauko yana cin naman, sai uwar ta waiga, ta waiga ba ta ga kowa ba, sai ta gudu ta bar shi da majanyi da zane. Fatar bayanta har ta kwaye saboda goyo.

    ‎Shi ke nan sai ga kura, ita da ’yan uwanta suna wasa. Sai ta ce, ‘Dan kanena, dan kanena, sam min dan naman in ci in goya ka.’ Shi ke nan, ya ba ta. Sai ta ɗauke shi ta goya shi suna wasa. Sai ta ce, ‘Sauko in huta.’ Sai ya ce, ‘Mn, a baya.’ Kome dai ta ce, sai ya ce, ‘Mn, a baya.’

    ‎Da ta yi ta yi ta cire shi daga bayanta ya ƙi, sai ta kira ’yan uwanta su cire mata shi. Da suka zo garin cire shi sai fatar bayan kura ta ciro, ta ce, ‘Na gamu da jaraba.’ Sai suka gudu suka bar shi nan.

    ‎Can sai ga dodo ya zo ya ɗauke shi ya ɗora a bayan dokinsa, shi kuma yana gaba yana cewa:

    Za ni za ni za ni,

    Za ni za ni,

    Za ni da namana,

    Za ni da namana,

    Za ni da kai sharɓa,

    ‎Dankaɗafi za ni da namana. Suna cikin tafiya a daji, sai Gizo ya ga dodo da yaro, sai ya sauke yaron, ya ajiye a ƙasa. Shi kuma ya hau kan dokin dodo. Dodo bai sani ba yana ta waƙa.

    ‎Shi ke nan sai ana ta tafiya da Gizo, sai kurciya ta ga Gizon a kan dokin dodo sun kusa da kogi, sai ta ce da Gizo, ‘Ku ne a yi muku rana, ku yi wa mutum dare.’ Gizo ya ce, ‘A’a, ba zan yi miki ba.’ Shi ke nan, sai kurciya ta ɗauke Gizo a fiffikenta.

    ‎Da dodo ya je bakin kogi, sai ya waiga don ya ɗauko yaro ya cinye ya sha ruwa, sai ya ga ba kome. Baƙin ciki sai ya sa shi ya faɗa cikin ruwan nan, ya zama gawayi. Shi kuwa Dankaɗafi kura ta cinye shi a can dajin da aka ajiye shi.

    ‎ Shi ke nan.

    Kurunkus.

    ‎Wannan rubutu an ciro shi ne daga littafi mai suna TATSUNIYOYI DA WASANNI wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

    Karanta Tatsuniyar Gizo Da Ɓaure

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Gizo Da Ɓaure

    Tatsuniyar Gizo Da Ɓaure

    ‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    ‎Wata rana ne dai wani sarki yana zance a zuci, yana cewa, ‘Gonata ta ɓaure ta yi kyau. Ɓauren yanzu duk ya nuna. Gara in sami wani ya je ya tsinke mini duk ɓauren, kar in bar shi ya ruɓe a banza. Amma fa wanda zai tsinke ɓauren ba zai sha ba, ko da ɗaya ma.

    Idan ya gama bai sha ba, zan ba shi ‘yata tare da gararta baki ɗaya’. ‎Shi ke nan. Kashegari sai sarki ya sa duk a yi shela a gaya wa mutanen gari sarki yana kiran su a ƙofar fada.

    ‎Mutane suka taru a ƙofar gidan sarki. Sai sarki ya ce, ‘Da ma ba wani abu ya sa na yi kiran ku ba. Gonar ɓaurena ce na ke so a tsinke min, amma ba za a sha ko ɓaure ɗaya ba. Sai dai zan ba wanda ya tsinke ɗin ladan tsinkewar. Watau zan ba shi ‘yata da gararta baki ɗaya.’

    ‎Sai kowa ya ce ba zai iya ba, domin bauren ya cika kyau, ga kuma ƙanshi da zaƙi. Ba wanda zai iya ba tare da ya sha ba. Can, sai Gizo ya zo; ya ce wa sarki, ‘Zan iya. ‎Shi ke nan, sai sarki ya ce, ‘To. Gobe ka yi shiri ka tafi’.

    ‎Da gari ya waye, sai Gizo ya dura ruwa a jallo, ya ɗauki madubi da kuma tsinkensa na sakace. Ya je gonar sarki ya kama tsinkar ɓaure. In yana cikin yi mutane suka zo suka ce, ‘Gizo barka da aiki’; sai ya tsiri tofar da yau, yana cewa, ‘Tuf! Kai wannan ɓaure! Ko warinsa ba na so’.

    ‎Idan sun wuce, sai ya ci gaba da tsinkar ɓauren, yana sha yana zubo wani a ƙasa. Shi ke nan, ashe bai sani ba, wata ‘yar tsuntsuwa tana kallon sa. Da ya gama tsinkar ɓauren tas. Ya sauko zai tafi gida, sai ya ɗauko jallon ruwansa ya kurkure bakinsa, ya ɗauko madubin nan da tsinken sakace, duk ya ciccire ɓauren da ya maƙe masa a haƙorinsa.

    Bakinsa ya yi tas, kamar bai ci kome ba. Sai sarki ya aiko mutane don su debe ɓauren da Gizo ya tsinke. Suka zo suka sami Gizo suka ce, ‘Sannu da aiki, Gizo’. ‎Ya ce, ‘Yauwa’. ‎Suka ce, ‘Har ka gama? Sai ya ce, ‘I. Amma da ƙyar’.

    ‎na gama. Kamar na yi amai, saboda warin ɓauren nan. Warin duk ya cika mini ciki’. ‎Sai suka zuzzuba ɓauren a buhunhuna suka tafi su kai wa sarki. Da suka je gida, sai sarki ya tambaye su labarin Gizo da tsinkar ɓaure. Suka ce, ‘Ai, yallaɓai, Gizo bai sha ɓauren nan ba, domin mun ga muna zubawa a buhu yana tofad da yau..

    Kuma da muka ce da shi, ‘Me ya sa ka ke zubad da yau?’ Sai ya ce warin ɓauren ne ya cika masa ciki. Sun gama faɗin haka ke nan, sai ga Gizo ya zo gidan sarki. Sarki ya ce da shi, ‘To, Gizo. Ka yi aiki mai kyau. Sai kuma ka je gida ka gyaggyara, za a kawo amarya da gararta.’

    ‎Shi ke nan. Gizo ya je gida ya gyaggyara sarai. Aka ɗauko amarya da gara aka zo da ita gidan Gizo. Kafin ‘yan ɗaukar amarya su tafi gida, sai suka ji tsuntsuwa tana waƙa tana cewa: ‘Kai Gizo, kai Gizo, A can ka ci ɓaurenka, Har ka kurkure bakinka, Har ka manto jallonka…’

    ‎Tana ta faɗar haka har sai mutanen suka ce, ‘Kai, ku tsaya mu ji abin da tsuntsuwar can take faɗa. ‎Sai Gizo ya ce da su, ‘Kai, ku rabu da ita don Allah, shirmenta ta ke yi’. ‎Sai mutanen suka ce, ‘Wane irin a rabu da ita? Kai! Mu tsaya mu ji’.

    ‎Shi ke nan, sai ‘yan kawo gara da amarya suka ji tana cewa: ‘Kai Gizo kai Gizo, A can ka ci ɓaurenka, Har ka kurkure bakinka, Har ka manto jallonka…’‎Sai suka ce, ‘La’ila! Ashe da ma ka ci ɓauren ka ce ba ka ci ba?’

    ‎Sai suka yi ta surutu da hayaniya. Shi ke nan. Sai suka mayad da amarya da gararta gida su ka gaya wa sarki abin da ya faru.

    ‎Shi ke nan. Ƙurunƙus

    ‎Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafi mai suna TATSUNIYOYI DA WASANNI wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

    Danna nan don karanta ‎Tatsuniyar Barewa Ta Auri Mutum

    Edita@rumasau-kallamu

  • ‎Tatsuniyar Barewa Ta Auri Mutum

    ‎Tatsuniyar Barewa Ta Auri Mutum

    ‎‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    ‎Wata barewa ce, sai ta rikiɗa, ta zama mace kyakkyawa. Sai ta ɗauki ɗan kwatashinta ta ɗora a ka ta tafi tsakiyar karofi ta ajiye. Da ta ajiye, sai ta ce duk wanda ya jefa ’yar tsakuwa ta buɗe kwatashin nan, shi ne mijinta.

    ‎Sai wannan ya ɗauki tsakuwa ya jefa bai buɗe ba, wancan ya jefa tsakuwa bai buɗe ba. Sai aka sami wani ya jefa ’yar tsakuwa, sai ya buɗe. Sai ta ce ta sami miji, shi za ta aura. Sai suka tafi garin ita yarinyar, wurin iyayenta za a ɗauro mata aure da wannan mutumin.

    ‎Sai aka ɗaura musu aure ta zo ta tare gidan mijin. Kullum ranar girkinta sai a ce ta je ta ciro kuɓewa a gonar mijin ta yi miya. Da ta je gonar, sai ta yar da zanenta ta yi birgima a ƙasa ta zama barewa ta yi kiran ’yanuwanta, ta yi waƙa ta ce:

    ‎Cinkalkal, cinkalkal kalaya,

    Turmin ’yan kale ya yi fure, ceɗiya.

    Tudu na korar Tudu, Marina.

    Tudu na korar tudu da ƙaho.

    Ban da kwatsa-kwatsan.

    Ban da ƙanƙan.

    Sai ’yan uwanta su zo su taru su ciccinye kuɓewa. Sa’an nan in sun gama sai su tafi gida. ‎Ita kuma sai ta yi birgima ta komo mutum ta ɗauki zanenta ta ɗaura. Sai ta koma gida ta dinga cewa, ‘Ni da gangan aka tura ni. Ga shi nan ban samo kome ba.’

    ‎To, ran nan sai mijinta ya bi ta gonar. Sai ya gan ta tana birgima. Da ta gama birgimar, sai ya ga ta rikiɗe ta zama barewa. Sai ya ga ta yi kiran ‘yan’ uwanta bareyi da waƙa. Bareyi suka taru a gonar jingim. Duk suka cinye kuɓewa.

    ‎Suna cikin ci sai ya fasa su. Sai ya ga matarsa, ta gan shi. Ya komo gida. Sai ta ɗauko kuɓewar ta biyo shi. Ta tarad da shi a gida. Ya ce, ‘Wace ce?’ Ta ce, ‘Ni ce.’ Ya ce, ‘Ina za ki?’ Ta ce, ‘Ɗaki za ni.’ Ya ce, ‘A a, koma daji.’ Sai ta ce ta ƙi. Sai ya biyo ta a guje ya kora ta daji.

    ‎Daga nan ba ta sake dawowa  ba. Shi ke nan. Kurunkus.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin tatsuniyoyi da wasanni wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Gizo Da Namun Daji

    Edita@rumasau-kallamu

  • Kimiyyar Siyasar Uban Gida: Tasiri, Makoma Da Silar Rabuwa

    Kimiyyar Siyasar Uban Gida: Tasiri, Makoma Da Silar Rabuwa

    A siyasa, a ko’ina a faɗin duniya ana amfani da harshen ‘biyayya, jagoranci gami da magajin mulki’. Shugabanni da dama su kan ce suna “gina shugabannin gobe”, ko “naɗa magaji”, ko kuma “tallafawa amintattun mabiyansu na siyasa”, amma a ƙarƙashin wannan zance akwai lamari mai tsauri.

    Siyasar ubangida (godfatherism) tsari ne da ikon siyasa ke zarcewa ta hannun mutane masu ƙarfin iko bayan cikar wa’adinsu, ba lallai ta hanyar hukumomi ko dokoki ba.
    A nahiyoyi daban-daban, wannan tsari yana bin salo iri ɗaya: uban-gida ya ɗora yaronsa na siyasa, yaron nasa ya samu iko, sannan daga baya rikici ya raba kawunansu.

    Wannan maƙala tana nazarin bayanai ne na duniya da na Najeriya game da silar rikicin siyasar ubangida da kuma dalilin da yasa Siyasar ubangida ke ci gaba da aukuwa, da dalilan da yasa take karyewa, da Kuma yadda take ƙarewa a mafi yawan lokuta.

    Don haka za mu fara yin nazarin ta waɗannan sigogi:

    1. a. Siyasar Uban-Gida a Matsayin Fasahar Siyasa ta Duniya
    Siyasar ubangida ba ta keɓanta ga Afirka ko Najeriya kaɗai ba. Ita wata fasahar siyasa ce ta duniya, musamman a wuraren da:

    • Hukumomi suke da rauni, samun adalci yake da tsada.
    • Jam’iyyun siyasa suke mallakar ɗumbin magoya baya,
    • Kuma samun iko yake da mafi tsadar farashi.

    A Latin Amurka, ana kiran Siyasar Ubangida da suna ‘caciquismo’, ma’anarta shugabannin yankuna masu sarrafa ƙuri’u da makomar mutane. A wasu sassan yankunan Asiya, musamman Philippines, Siyasar Ubangida na bayyana a matsayin siyasar gado, inda wani ahali kan mamaye muƙaman da ake zaɓe a kansu na tsawon ƙarni.

    A Amurka, a farkon ƙarni na 20, ƙusoshin siyasa kamar su Tammany Hall a New York suna aiki ne ta hannun shugabanni da suke “ƙirƙirar” gwamnoni da magajin gari.
    Duk da bambancin wurare, binciken siyasa da kamanceceniyarsa ya nuna abu guda:
    “A duk inda zaɓen ’yan takara ya dogara da masu hannu da shuni fiye da masu zaɓe ko hukumomi, siyasar ubangida tana bunƙasa”.

    b. Nazari: Bayanin ƙididdiga na duniya

    Binciken ƙasashe da dama ya nuna cewa a wasu ƙasashe masu dimokiraɗiyya mai raunin tsarin jam’iyya, kashi 60–75% na muƙaman majalisa ko kujerun zartarwa suna hannun mutanen da ke da alaƙa da manyan ahali ko wasu iyayen gida. Wannan haɗuwar iko ke sa rikicin ubangida da yaron gida ya zama babbar matsala mai girgiza tsarin siyasa baki ɗaya.

    2. Me Yasa Ubangida Ke Ƙirƙirar Yaron-Gida (Kuma Me Yasa Yaron gida ke Kware Masa Baya?)

    Ubangida ba ya ɗora yaron-gida saboda tsananin biyayya, ko tausayi ko kyautatawa kawai. Ilimi ta nuna hakan wani tsari ne na dabarar siyasa: Saboda dalilai kamar haka;-

    1. Kare iko – Mai mulki na son yaga ya cigaba da tasiri ko da bayan wa’adinsa ya ƙare.
    2. Tsaron tattalin arziki – kare kasuwanci, kwangiloli, da hanyoyin samun kuɗin shiga.
    3. Garkuwar siyasa – kariya daga bincike, cin zarafi ko samun babbar daraja a tsarin siyasa.
    4. Gina tarihi – mayar da iko na mutum zuwa “ɗariƙar siyasa” ko daular siyasa Wanda tarihin zai rinka tunawa dasu.

    Amma yaron gida yana gadon muƙami ne, ba ƙarƙashin biyayya kaɗai ba. Don haka da zarar ya hau mulki, matsin lamba za ta bayyana, biyayyar da ya jima Yana yi wa Ubangidansa na iya sauyawa Saboda dalilai kamar haka:

    1. Ikon kundin tsarin mulki da zai rinƙa yi wa biyayya,
    2. Haƙƙin jama’a da ya rataya a wuyansa na zuwa da muradai mabanbanta
    3. Hamayya daga manyan masu ruwa da tsaki na kusa da na nesa,
    4. Bujirowar burika na wannan mai mulki.
    Daga nan ne tsarin ke fara tsagewa..

    3. Yanayin Najeriya: Dalilin da Yasa Siyasar Ubangida Ta Fi Zafi a tsarin siyasar Najeriya ba ya rasa nasaba da dalilai guda huɗu:
    1. Tsarin “wanda ya yi nasara ya ɗauke komai” watau samun iko a Nigeria yana nufin samun iko da dukkan albarkatu.
    2. Raunin dimokiraɗiyyar jam’iyya – ’yan takara sunfi fitowa ta hanyar sulhu ko masalaha (nune), ba zaɓen gaskiya ba.
    3. Tsadar kamfen – Tun daga zaɓen cikin Gida, kudi sunfi tasiri wajen samun kuriun daliget Sama da nagartar ɗan takara. Haka Nan uwa uba babban zaɓe, masu dangwala kuriun sun fi zaɓar Dan takarar daya basu ihsani. Don haka ’yan kaɗan ne za su iya tsayawa takara har suyi nasara ba tare da masu kuɗi sun tallafesu ba.
    4. Ƙarfafa mutum fiye da karfafa doka – rigar mulki a Nigeria tafi ƙarfafa mutum fiye da bin dokokin ƙasa.

    Binciken zaɓukan Najeriya tun 1999 ya nuna cewa yawancin gwamnoni da suka yi nasara sun samu goyon bayan manyan ubangida ko ƙungiyoyi masu ƙarfi. Amma a lokaci guda, da dama daga cikin waɗannan alaƙa sun rushe bayan samun nasara.

    4. Yadda Siyasar Ubangida ta kasance a wasu Jihohin Najeriya
    i. Jihar Rivers: Daga Gado zuwa Yaƙi

    Rikicin da ya ɓarke tsakanin tsohon Gwamnan Nyesom Wike da Gwamnan mai ci Siminalayi Fubara a Jihar Rivers shi ne mafi tsanani a wannan zamanin. Tsarin gadon mulki mai kyau ya koma:

    • Toshe ayyukan majalisa,
    • shari’o’i a kotuna,
    • tsaikon kasafin kuɗi,
    • sa hannun gwamnatin tarayya.

    Abinda hakan ya haifar: lalacewar hukumomi na dogon lokaci, sulhu na ɗan lokaci, da rabuwar bangarorin siyasa abinda za a iya cewa har abada.. sai dai wasu na ganin kwatankwacin haka Nweson Wike ya yi ga waɗanda suka raine shi a siyasa.

    ii. Jihar Kaduna: Uban-Gida ga Gwamna
    A Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya tallafa wa Uba Sani wajen zamowar sa Gwamna. Bayan da ya hau mulki, sai gwamnan ya nemi ’yancin kansa, abin da ya haifar da:

    • zarge-zargen jama’a,
    • binciken majalisa ga Gwamna El-rufai
    • yaƙin cacar baka musamman a kafafen yaɗa labarai.
    • Abubuwan da hakan suka haifar: rabuwar manyan ’yan siyasa da ɓata suna daga ɓangarorin biyu.

    iii. Jihar Kwara:
    Daular Saraki — ƙarƙashin Olusola Saraki, daga baya Bukola Saraki — ta nuna wani tsari na daban.
    Uba (Sola) ya Dora ɗansa (Bukola), bayan cikar wa’adinsa ya yunkura maye gurbinsa da Kanwar Bukola.. Amma sai Bukola ya bijerewa mahaifinsa tare da ɗora Abdulfatah Ahmed..
    iv. Jihar Kano: Tafarkin Siyasa da Sarrafa Iko

    A Jihar Kano , Jagoran darikar Kwankwasiyya Engr Rabiu Musa Kwankwaso ya gina gagarumar ɗarikar siyasa. Amma gwamnan farko (Abdullahi Umar Ganduje) daya gajeshi ya raba gari dashi, sannan a yanzu haka Gwamna na biyu (Abba Kabir Yusuf) da ya ɗora shi ma ya raba sheƙarsa ta siyasa da jagoransa Rabiu Kwankwason

    v. A takaice, an samu irin wannan salo a yawa-yawan jihohin ƙasar Nan misalin Zamfara, Borno, Yobe, Kogi da makamantansu

    5. Ƙididdigar Sakamako: Abin da Bayanai Ke Nunawa
    daga siyasar jihohin Najeriya (1999–2025).
    Taƙaitaccen bincike ya nuna:
    1. ≈Kashi 70% na alaƙar ubangida da yaron-gida tana rushewa daga ƙarshe.

    Daga cikin waɗanda suka rushe:
    kaso~40% sun ƙare da sauya jam’iyya ko sake tsayuwa da ƙafafunsu.
    kaso ~25% sun kai ga rikicin shari’a na tsawon lokaci,
    kashi ~20% sun haifar da rugujewa ko tuge injin siyasar ubangida a zaɓe,
    ƙasa da kashi <15% ne kawai suka kai ga tsananin biyaya da sulhu mai ɗorewa misalin abinda ake gani ga Gwamna Ododo da Yahaya Bello a Kogi.

    A Siyasar duniya ma, waɗannan kaso suna kama da juna a ƙasashen da siyasar Ubangida ta yi ƙarfi.

    6. Me Yasa Rabuwa Kusan Dole Ce a Siyasar Ubangida?

    A kusan dukkan lamurra, abubuwa biyar ke haifar da rabuwa:
    1. Saɓanin ra’ayi wajen iko da albarkatu; misalin kasafin muƙamai, kwangiloli da sauransu.
    2. Tsoron dusashewar tauraro – a mafi akasari, Ubangida ba ya son a manta dashi ko a daina tuntuɓarsa akan kamurori.. don haka idan ya hango haka zata faru, yana iya yunkurin sauya shugabancun daya ɗora.

    3. Sauyin halaccin mabiya – yarongida yana iya samun iko daga ɗumbin jama’ar da yake shugabanta, hakan na iya bashi damar auna ƙwanjinsa da Ubangidansa.
    4. Fargabar magajin gaba – bayan kammala waadin mulkin yaron gida, shin wake da halascin sake ɗora magaji? tayaya hakan zai amintar da babban ubangida ko yarongida?.
    5. Tasirin mulkin mai mulki wajen sarrafa kansa da muradan zuciyarsa

    A taƙaice: siyasar ubangida tana haifar da cibiyoyin iko biyu a ofishi guda sai dai ita siyasa sam ba ta lamuntar iko biyu.

    7. Yadda Siyasar Uban-Gida Ke Ƙarewa Galibi

    Shaidu daga Najeriya da duniya suna da nuni da cewa mafi yawan Siyasar ubangida :
    * Ba ta ƙarewa cikin nutsuwa.
    * Tana raunana shugabanci.
    * Tana rarraba jam’iyyun siyasa.
    * Wani lokaci tana ƙarfafa jama’a idan suka haɗu (kamar Kwara).

    Abin mamaki, tsarin da aka ƙera don rage rashin tabbas shi ne ke haifar da rashin kwanciyar hankali na dindindin.

    8. Hasashe na Ƙarshe: Rikicin Siyasar Biyayyar Ubangida

    Siyasar uban-gida tana cigaba ne saboda tana magance matsalolin gajeren lokaci kamarsu cin zaɓe, tara kuɗi, kauce wa hukumomin bincike da sauransu. Amma tana karyewa bayan dogon lokaci saboda ta saɓa da ma’anar mukamin dimokiraɗiyya.

    > Da zarar yaron-gida ya zama gwamna, to fa Allah ɗaya ne kurum, babu mai iya tabbatar da ƙarshen lamarin. Har sai jam’iyyun siyasa, kuɗin kamfen, da hukumomi sun maye gurbin ubangida a matsayin hanyar samun iko, sannan zagayen zai ci gaba: amma abinda alƙaluma suka nuna, a duk siyasar ubangida huɗu, ɗaya ce kawai ake wanyewa lafiya, sauran ukun kuwa duk da ɓacin rai ake ƙarewa saboda saɓanin fahimta da bijirowar sabbin buƙatu masu sauya lamurori.

    Sadiq Tukur Gwarzo GGA.

    Karanta Falalar Malamai Da Ta&#8217;aziyyar Masani Shehu Ahmad Bamba (Ƙala Haddasana)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Hadisi Na Bakwai Akan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    Hadisi Na Bakwai Akan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    An karɓo daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Asi (Radiyallahu Ahuma) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Haƙiƙa masu adalci za su kasance a kan mimbarai na haske a daman Allah mai rahama, kuma duk hannayensa biyu dama ne. Su ne waɗanda suke yin adalci a cikin hukuncinsu da iyalansu da waɗanda suke jagoranta.

    Muslim da Nasa’i ne suka rawaito shi.

    ƘARIN BAYANI

    Haƙiƙa masu yin adalci da gaskiya a shugabancin da yake kansu da iyalansu suke kaucewa zalunci da nuna bambancin a tsakanin waɗanda suke jagoranta, za su samu babban matsayi a wurin Allah ranar lahira.

    Hannun dama da ya zo a wannan hadisin sifa ce daga sifofin Allah Ta’ala waɗanda ake yin imani da su kamar yadda suka zo, ba tare da an yi musu tawali ko canja su ko kore su ba ko kuma kamanta su da sifofin halittu ba.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisi Na Takwas Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu A kan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Hadisi Na Biyar A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musa

    Hadisi Na Biyar A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musa

    An karɓo daga Aliyyu (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Maganar ƙarshe da Manzon (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi ita ce: “Ku kula da sallah, ku kula da sallah, ku ji tsoron Allah ku kula da haƙƙoƙin waɗanda suke a ƙarƙashinku”.

    Abu Dawud da Ibn Majah ne suka rawaito shi.

    ƘARIN BAYANI

    Wannan hadisi yana daga cikin wasiyyoyin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bar wa al’ummarsa dab da wafatinsa. Ya yi wasiyyar a kula da sallah kuma a kula da haƙƙoƙin bayi da barori da duk waɗanda suke ƙarƙashin mutum.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu A kan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikaken Littafin danna nan.

  • Hadisi Na Huɗu A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    Hadisi Na Huɗu A Kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu

    An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Ba ya tare da mu wanda ba ya tausayawa ƙaraminmu, kuma ba ya girmama babbanmu, kuma ba ya umarni da kyakkyawan aiki, ba ya hani ga mummuna.

    Tirmizi ne ya rawaito shi.

    ƘARIN BAYANI

    Waɗannan hadisai guda biyar suna bayyana falalar tausayawa mabiya da jinƙan su da sauran masu rauni da haramcin gallaza musu, suna nuna cewa duk wanda yake da jinƙai da tausayi Allah zai tausaya masa, kuma rashin tausayi alama ce ta rashin imani da rashin rabo a lahira, har ma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: Ba ruwansa da maƙetaci mugu maras imani da tausayi da kuma wanda ba ya girmama na gaba da shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hadisi Na Biyar A kan Falalar Adalci Da Tausayawa Mabiya Da Illolin Gallaza Musu danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu A kan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Falalar Malamai Da Ta’aziyyar Masani Shehu Ahmad Bamba (Ƙala Haddasana)

    Falalar Malamai Da Ta’aziyyar Masani Shehu Ahmad Bamba (Ƙala Haddasana)

    Sahabi Aliyu R.A ya faɗa ga Jabir ɗan Abdullahi R.A cewa “Duniya ta dogara ne a kan abu huɗu; Addini, da Malami, da mai yin aiki da ilimin sa, sai Jahili wanda ba ya girman kai wajen neman sani, da kuma Mawadaci wanda ba ya rowa da dukiyar sa.

    Marigayi Sheikh Dr.  Ahmad Bamba ya faɗa mana cewa ilimi ba komai ba ne sai sanin abu a zuciya da kuma gaskatar sa a zahiri, yayin da jahilci ke nuni da kiyaye abu a zuciya wanda a zahirance ba gaskiya ba ne. Saboda haka a  cewar sa ba kawai rashin sanin abu ake kira jahilci ba, a a har ma da sani gami da riƙo na abinda bai gaskata ba.

    Rayuwa irin ta Dr Ahmad madubi ce ga ɗaukacin al’ummar musulmi. Shi mutum ne mai kyakkyawar fahimta ga lamurran addini, amma mai zafafawa wajen kare martaba irin ta Annabi Muhammad s.a.w.

    Mai kimanin shekaru 82 da haihuwa, wanda ya rasu a yau Jummu’a 7/1/2021, Marigayi Dr Ahmad Bamba ya shafe ɗaukacin rayuwar sa wajen nema da kuma bayar da sani. Ya shafe sama da shekaru 20 yana ɗaukar darasi a Madina, masallacin Annabi Muhammad s.a.w.

    Sannan ya fassara Littafin Muwaɗɗa wallafar Imamuna Maliku ɗan Anas daga harshen larabci zuwa harshen Hausa, baya da karantarwar sa ga manyan littattafai irin su Sahih Bukhari, Sahih Muslim, Sunnani Darimi, da makamantan su duk a cikin harshen Hausa.

    Tabbas, rasuwar sa babbar asara ce ga kafatanin al’ummar musulmi musamman Hausawa.Ya zo a cikin littafin ‘Al ilmu Huwal Imamu’ na Shekh Ibrahim Nyasi cewa Hanyar aljanna ta na hannun mutane guda huɗu; Malami, da mai gudun duniya da mai ibada da kuma mai jihadi fi sabilillahi. Shi Malami idan ya kasance mai gaskiya ne cikin zuciyar sa, tabbas Allah zai azurta shi da Hikima.

    Duk kuwa wanda aka bai wa Hikima alal haƙiƙa an ba shi gagarumar baiwa a nan duniya da gobe lahira kamar yadda yadda ya zo a cikin littafin Allah Alqurani. An tambayi Ɗan Mubarak cewa su wanene mutane?, sai yace ‘Malamai’, sai aka ce masa su wanene sarakuna?

    Sai yace masu gudun duniya, sai aka ce su wanene ƙasƙantattu?, sai yace masu cin duniya da addini. Don haka, ana iya cewa lallai malamai mutane ne masu daraja a cikin al’umma. Abdul-Aswad yana cewa babu wani abu wanda yafi Ilimi ɗaukaka. Sarakuna masu yin hukunci ne ga jama’a, yayin da Malamai ke yin hukunci a garesu.

    AHNAF R.A yana cewa Malamai sun kusa kasancewa iyayen giji.. dukkan ɗaukakar da ba a ƙarfafe ta da ilimi ba, ƙarshen ta ƙasƙanci ce. Annabi Muhammad s.a.w ya faɗa cewa “Malamai, su ne magada Annabawa” (Tirmizi, Abu Dawood da Ibn Maja duk sun ruwaito shi)

    Allah Ta’ala kuwa ya faɗa cewa “Iyaka dai masu jin tsoron Allah su ne Malamai” (Suratul Fathi, 28). Babu buƙatar zafafa yabo ga marigayi Mallam Ahmad Bamba, domin shi ba mai son yabo ko kwarzantawa ba ne a zamanin rayuwar sa, amma shi ne wanda ya jaddada Sunnah a ƙasar Hausa bayan da ta ɗauko dusashewa.

    Shi mutum ne wanda yake son Allah da Manzon sa, wanda yake tarbiyantar zukatan bayin Allah a kan bautar Allah ta tsanin manzon sa Annabi Muhammad s.a.w da mayar da lamurra a gareshi, kuma mutum ne maras kwaɗayi, mai darrajanta ilimi da darrajanta kansa, gami da faɗar gaskiya walau ga shuwagabanni ko ga mabiyansu.

    Allahu Akbar, shi mutum ne mai daraja a duniyar musulunci, tushen darajar sa kuwa bai wuce ga riƙon sa ga sunnar Annabi Muhammad s.a.w ba, da tsantsenin sa kai kace shi ne Imam Maliku bn Anas ko Imam Hasanul Basri. Haƙiƙa, rayuwar sa ta kasance abar koyi ga al’ummar musulmi.

    Wani sashen masana sun faɗa cewa An fifita Imam Hasanul Basri a kan sauran Tabi’ai, saboda abubuwa guda 5;-

    1. Ba ya umarni da aikata wani aiki face ya fara aikatawa.

    2. Ba ya hanuwa ga barin wani aiki face ya fara hanuwa daga gareshi.

    3. Duk wanda ya nemi wani abu daga abinda Allah ya hore masa zai ba shi.

    4. Ya kasance tana wadatuwa da ilimin sa ga barin neman wani abu a wajen mutane.

    5. Ya kasance ciki da wajen sa duk ɗaya ne.

    Tabbas, duk waɗannan siffofi guda biyar sun tabbata ga Marigayi Shekh Ahmad Ibrahim Bamba. Ga shi kuma ya samu cikawa irin tasa.. da fatan Allah ya rahamshe su duka amin.

    Abdullah bin ‘Amr Ibnul ‘Ash ya ruwaito daga Annabi Muhammad s.a.w cewa “Lallai, Allah ba ya ɗauke ilimi daga hanawar sa ga bayin sa. Sai dai yana ɗauke ilimi ne daga mutuwar malamai ta yadda tsarkakan mutane za su gushe, sai mutane su naɗa wawayen mutane a shugabanci. Sannan idan aka tambaye su, sai su yi magana ba da ilimi ba. Sai su taɓe kuma su yi asara.” (Al-Bukhari da Muslim suka ruwaito).

    Kaicho da rashin babban masani Dr Ahmad Bamba, to amma ya kamata kowa ya sani wannan duniya ba abar dawwama ba ce. Tabbas, kowanne mai rai zai ɗanɗana mutuwa. Kuma tabbas, yadda Dr Ahmad ya koma ga mahaliccin sa, kowannen mu lokaci yake jira domin komawa zuwa ga Allah. Don haka ya kamata mu shagaltu wajen aiki da koyarwarsa, da neman ilimi, da bin Allah da kuma neman dacewar Allah da samun Aljanna.

    Da fatan Allah ya gafartawa Dr Ahmad Ibrahim Bamba, Allah ya tallafi bayan sa amin.

    Danna nan don karanta Cin Zarafin Ƙananun Yara Da Kariya A Bisa Haka

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar ‎Gizo Da Namun Daji

    Tatsuniyar ‎Gizo Da Namun Daji

    ‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    ‎Gizo ne dai yana son ya ci nama, amma ba shi da shi. Ya rasa yadda zai yi. Sai ya ce a ransa, ‘Bari dai in yi wata dabara. Sai ya sayo goro ya rarraba wa namun daji da tsuntsayen gida.

    ‎Sai ya fara kai wa kaza, ya ce, ‘Ga shi. Goron wasa ne wanda za a yi a cikin daji. Naki ne wannan. ‎Sai kaza ta ce, ‘To. Amma fa kada ka kai wa muzuru. Sai ya ce, ‘Haba, me zai sa in kai masa?’

    ‎Da gizo ya fita, sai ya shiga gidan muzuru, ya kai masa goro. Sai shi ma muzurun ya ce, ‘To, amma kada ka kai wa kare. ‎Sai gizo ya ce, ‘Haba me zai sa in kai masa? ‎Da dai gizo ya fita, sai ya shiga gidan kare ya ba shi nasa goron. Kare ya ce, ‘To, amma fa kada ka kai wa kura.’ Gizo ya ce, ‘Haba me zai sa in kai mata?’

    ‎Da ya fita, sai ya kai wa kura nata goron. Kura ta ce, ‘To, amma fa‎ kada ka kai wa Zaki.’ Ya ce, ‘Haba kura, me zai sa in kai wa Zaki? ‎Shi ke nan, sai ya kai wa Zaki nasa goron, ya ce, ‘Ranka ya daɗe. Wani ɗan wasa za a yi na kawo maka goro.’

    ‎Da Zaki ya karɓa, sai ya ce, ‘To Allah ya kai mu. ‎Shi ke nan. Da ya fita, sai ya shiga ya kai wa damisa. Damisa ta ce, ‘In ce ko dai ba ka kai wa Sarki Zaki ba? Sai Gizo ya ce, ‘Haba, haba. Wane ni da gayyatar Sarki? Sai damisa ta ce, ‘To, Allah ya kai mu.’

    ‎Da ya fito sai kuma ya shiga gidan giwa ya kai mata nata goron. Sai giwa ta ce, ‘To, in ce ko ba ka kai wa manyan dawa ba? ‎Ya ce, ‘Mhm. Yaya zan kai? Ko kai masa ne ma ai ke zan bai wa ki kai masa.’

    ‎Shi ke nan. Ana nan ana nan, sai ranar wasa ta zo. Gizo ya bayyana musu wurin da za su haɗu a yi wasan. Ya ce musu, ‘To, ku tafi zan same ku. Ni daga baya zan taho tare da makaɗa. Shi ke nan. Sai kaza ta fara tafiya. Ashe ba su sani ba, gizo ya riga su isa can. Sai kaza ta isa can. Gizo ya yi mata maraba. Ya ce, ‘To shiga wannan bukkar kafin su zo.’

    ‎Shi ke nan. Kaza ta shiga, ta zauna. Daga can sai ga muzuru ya taho. Sai Gizo ya gaya wa muzuru cikin raɗa, ‘Maraba. Shiga tana nan a ciki. Shi ke nan sai muzuru ya shiga ya tasar wa kaza zai cinye ta. Ya cinye ta.

    ‎Can kuma sai ga kare ya taho. Shi ma dai Gizo ya gaya masa kamar yadda ya gaya wa muzuru. Sai shi ma karen ya cinye muzuru. Daga nan kuma sai ga kura. Ita ma ya gaya mata kamar yadda ya‎ gaya wa kare da muzuru. Sai kura ta shiga ta cinye kare.

    ‎Kura kuma tana zaune a cikin rumfa. Sai ga Zaki ya taho. Shi ma Gizo ya gaya masa haka. Ya shiga ya cinye kura. ‎Daga nan sai ga giwa da damisa sun jero sun taho. Sai Gizo ya ce, ‘To. Ku shiga nan bukkar mana.’

    ‎Daga shigarsu, sai suka kaure da faɗa. Suka yi ta faɗa tun daga cikin rumfa har suka yiwo waje. Idonsu duk ya rufe, suna ta faɗa. Sai Gizo ya samo ganga, ya soma kiɗa yana waƙa:

    ‎Zaki bari, damisa bari.

    ‎Giwa bari.

    ‎Faɗanku na manya,

    ‎Wa yake shiga?

    ‎Sai wawa, sai mahaukaci.

    ‎Sai ko ni da ba ni da hankali.

    ‎Suna ta faɗa, can da giwa ta ga abin ba dama, sai ta fito ta yi‎ tafiyarta gida, ta bar zaki da damisa suna karawa. Sai Gizo ya ci gaba da yi musu waƙa. Ya yi ta yi, su kuma suna ta faɗa. Ashe Gizo da ma ya zo da yaji a ƙunshe. Sai ya ɗauko yajin nan ya barbada musu a idanunsu. Sai fa faɗa ya rincabe, idanunsu suka rufe ruf.

    ‎Daga can sai Gizo ya ɗauko wuƙa ya ce, ” ‘Yan banza. Ana so a ci nama an rasa yadda za a yi.” Sai ya kama yankan naman jikinsu yana tarawa, har ya kashe su duka. Sai ya jide naman ya kai gida aka soya masa, ya ci ya  ƙoshi, ya ajiye sauran, yana ci lokaci-lokaci.

    ‎Shi ke nan. Ƙurunƙus.

    ‎Wannan rubutu an ciro shi ne daga littafi mai suna TATSUNIYOYI DA WASANNI wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

    Danna nan don karanta Ga Tsoro Ga Ban Tsoro

    Edita@rumasau-kallamu