Category: WikiHausa

Yadda ake amfani da WikiHausa

  • Maƙala Mai Taken Kasuwanci A Duniyar Intanet: Ƙalubalen Hausawan Ƙarni na 21

    Maƙala Mai Taken Kasuwanci A Duniyar Intanet: Ƙalubalen Hausawan Ƙarni na 21

    Cite this Article as: Sani, A-U., Yankara, M.M. & Baba N. (2023). Kasuwanci a duniyar intanet: Ƙalubalen Hausawan ƙarni na 21. Yobe Journal of Language, Literature and Culture, 11, 224-253. ISSN: 2449-0660.

    Kasuwanci a Duniyar Intanet: Ƙalubalen Hausawan Ƙarni na 21
    Na
    Abu-Ubaida Sani
    Department of Languages and Cultures
    Federal University Gusau, Zamfara State, Nigeria
    Mail: abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng, abuubaidasani5@gmail.com
    Phone: +2348133529736
    Da
    Muhammad Musa Yankara
    Hausa Department
    Federal University Dutsin-Ma
    mymuhammad@fudutsinma.edu.ng
    Da
    Nasir Babba
    Hausa Department
    Federal University Dutsin-Ma
    babbanasir@gmail.com

    Tsakure

    Sannu a hankali al’ummun duniya na ƙara rungumar kasuwancin duniyar intanet. Ciki har da Hausawa. Wannan ne babban dalilin gudanar da binciken inda aka nazarci nau’uka da yanaye-yanayen kasuwancin kan intanet da alfanu da ƙalubalen da ke tare da su da kuma hanyoyin fuskantar waɗannan ƙalubale.
    Manyan dabarun da aka yi amfani da su wajen tattaraa bayanai su ne nazartar bayanan kan intanet kai tsaye da kuma hira da Hausawan da abin ya shafa. An ɗora aikin a kan ra’in Pulatoriyya (Platonism) inda aka kalli kasuwancin duniyar intanet a matsayin mai cin gashin kansa daga kasuwancin duniyar zahiri (duk da cuɗanyar da suke yi da juna a waɗansu lokuta). Binciken ya gano nau’ukan kasuwancin intanet guda biyar da Hausawa ke gudanarwa.
    A ɓangare guda kuwa, binciken ya gano cewa, kasuwancin kan intanet ya kasance cigaba duk da waɗansu ƙalubale da ya ƙunsa. Daga ƙarshe binciken ya ba da shawarwari da suka haɗa da sa hannun gwamnatoci da hukumomi da ɗaiɗaikun mutane domin bin matakai da amfani da dabarun kauce wa gurɓata muhalli da yanayi yayin gudanar da hada-hadar kasuwanci a duniyar intanet.
    Fitilun Kalmomi: Kasuwanci; Intanet; Pulatoriyya

    1.0 Gabatarwa

    Kamar yadda duniya ba a wuri guda take tsaye ba, [1]haka ma al’amuran da ke cikinta kullum na kan sauyawa. Waɗannan sauye-sauye sun shafi dukkannin ɓangarorin rayuwa da wanzuwar dukkannin halittu. [2] A ɓangarori da dama na rayuwa, sababbin abubuwa da zamani ke zuwa da su na kasancewa hanjin jimina, wato akwai na ci sannan akwai na zubarwa.
    Hakan ne kuma ya sa yake da matuƙar muhimmanci da a riƙa nazartar sababbin abubuwan da zamani ya samar. Wannan zai ba da damar cin gajiyar alfanin da ke tattare da sauye-sauyen tare da samar da nagartattun matakan fuskantar ƙalubalen da ke tattare da su.
    Fannin kasuwancin Hausawa babban bagire ne da har kullum ke sanya rigar zamaninsa. Ƙarni na ashirin da ɗaya (Ƙ21) ya zo da sauyi na musamman a wannan fannin. A ƙarnin ne aka samu bunƙasar intanet. Sannu a hankali intanet ya mamaye ɓangarorin rayuwa, ciki har da lamarin kasuwanci. Sannu a hankali har aka kai bagiren da a yau kasuwanci ba ya bunƙasa ya kai matakin ƙoli har sai ya rungumi duniyar intanet.
    Hausawan wannan zamani ba a bar su a baya ba wajen tsunduma harkar kasuwanci da ke da alaƙa da duniyar intanet. Wannan kuwa ya kasance cikin salailai daban-daban, tun daga kan dillanci, talla, har zuwa nau’ukan ayyukan da ke buƙatar ƙwarewa da ilimummukan fannoni na musamman.
    Bisa wannan, akwai buƙatar gudanar da bincike domin nazartar yanaye-yanayen kasuwancin Hausawa a duniyar intanet. Kai tsaye wannan takarda ta mayar da hankali kan:
    (i) nazartar nau’uka da fasalce-fasalcen kasuwancin Hausawa a duniyar intanet,
    (ii) ƙalubale da alfanun da ke tattare da kasuwancin, da kuma
    (iii) matakan fuskantar ƙalubalen tare da inganta harƙallolin.

    1.1 Dabarun Gudanar Da Bincike

    Kadadar wannan bincike ta taƙaita ne ga kasuwanci da ke da alaƙa da intanet. An sake taƙaita kadadar ga kasuwancin Hausawa. Ba a iyakance waɗansu kafafe da za a mayar da hankali a kansu ba. Dalili kuwa shi ne, binciken ya ƙudiri aniyar waiwaitar duk  nau’ukan hada-hadar kasuwancin kan intanet da ake damawa da Hausawa.
    An tattara bayanan majiyar farko (primary source) ta hanyoyi guda biyu. Hanya ta farko ita ce binciken kai tsaye a kafafen intanet da ake gudanar da hada-hadar kasuwanci. Hanya ta biyun kuwa ita ce hira da Hausawa da ke gudanar da sana’o’i masu alaƙa da intanet domin samun bayanai daga tushe.
    An bi dabarun tantance bayanan da aka samu daga tattaunawar ta hanyar maimaita tattaunawa da waɗansu mutane na daban da kuma ta hanyar tabbatar da bayanai daga ƙididdigar alƙaluma da ke wallafe a kafafen intanet.
    Wuraren da aka tattara bayanai da ke matakin majiya ta biyu (secondary data) sun haɗa da littattafai da mujallu da muƙalu da kuma bidiyoyi da hotuna da rubuce-rubucen da ke kafafen intanet daban-daban. Duk waɗannan sun taimaka wajen share hanya da ƙarin haske tare da yin jagoranci wajen fayyace muhamman batutuwa da suka shafi binciken.

    1.2 Ra’in Bincike

    An ɗora wannan bincike a kan ra’in Pulatoriyya (Platonism).[3] Kamar yadda Gerson, (2005: 253) ya bayyana, wanann ra’i ne da ya ginu kan fahimta da falsafofin Plato, [4]duk kuwa da cewa yakan samu sauye-sauye daga lokaci zuwa lokaci. Ra’in na iƙirarin cewa, duniya tamkar kashi biyu take; duniyar zahiri (bayyananniyar duniya) da kuma ta baɗini (ɓoyayyiyar duniya). Lamura na gudana a waɗannan duniyoyi sannan suna iya cuɗanya da juna. Haka kuma, al’amuran da ake gudanarwa a ɗaya daga cikin duniyoyin na iya shafar ɗayar.
    A bisa wannan ra’in, takardar na da hasashen cewa, akwai nau’ukan kasuwancin da ake gudanarwa a duniyar intanet ta sigogi makamantan yadda ake gudanar da su a duniyar zahiri. Haka kuma, kasuwancin da aka fara a duniyar zahiri na iya komawa duniyar baɗini (intanet). Ana kuma iya ɗauko kasuwanci daga duniyar baɗini a dawo da shi duniyar zahiri.
    Ra’in Pulatoriyya ya yi jagoranci a binciken ta fuskar fito da nau’in alaƙa da ke tsakanin kasuwancin duniyar zahiri da duniyar intanet. Ya kuma nuna wuraren da ɓangarorin biyu ke cin gashin kansu da kuma wuraren da suke cuɗanya da juna cikin salon shigar giza-gizai. Bugu da ƙari, ra’in ya taimaka wajen ƙwanƙwancewa da ƙalailaice bayanan da binciken ya tattara.

    2.1 Taliyon Kalmar “Kasuwanci” A Kadadar Al’adun Hausawa

    “Kasuwanci” da “sana’a” kalmomi ne masu tafiya kafaɗa da kafaɗa. Duk da alaƙar da ke tsakanin kalmomin biyu, akwai marubuta da suka yi ƙoƙarin ba da ma’anar sana’a da ta kasuwanci a keɓance.
    Rumbun Ilimi (n.d.) ya bayyana cewa Hausawa na sana’a tun wajajen shekarar 1349, inda kuma ya ce sana’a: “kalma ce da aka aro ta daga Larabci, kuma take ɗaukar ma’ana ta samar da wani abin amfani ta hanyar hikima a Hausance.” Ya ɗauki kasuwanci abu mai cin gashin kansa a matsayin hanyar saye da sayarwa. Wannan ra’ayi ya yi daidai da na Buhari, (2021: 1)1 inda yake cewa:
    Kasuwanci dai yana nufin saye da sayarwa na wani abu ko kuma haja wanda abun nan yana iya kasancewa wanda ake gani ne kuma wanda ba a gani[5] ne kamar mutum ya yi wani aiki a biya shi to duka suna ɗaukar ma’anar kasuwanci. Buhari, (2021: 1)1
    A fahimtar wannan takarda, tattauna kasuwanci a kadadar al’adun Hausawa ba zai kammala ba har sai an haɗa shi da sana’o’in Hausawa. Hasali ma a bagire da dama suna iya wakiltar juna. Muhammad, (2020: 224) ya bayyana ma’anar sana’a a matsayin “hanyoyin da ake gudanar da saye da sayarwa.
    “Kai tsaye za a iya cewa wannan ma’ana tana bayani ne a kan kasuwanci. Ta yiwu cuɗeɗeniyar da ke tsakanin sana’a da kasuwanci ne ya ja hankalin Muhammad wajen ba da wannan ma’ana.
    Ko Rumbun Ilimi, (2020: 1) da Buhari, (2021: 1)1 da Buhari, (2021: 1)2 da suka rarrabe tsakanin kasuwanci da sana’a, akwai wuraren da bayanansu ke nuna ba a iya rabe su. Misali, Buhari ya kawo “noma” da “kiwo” da “ɗinki” a cikin misalan kasuwanci. Ya yi hakan ne a ƙoƙarin nuna yadda Hausawa ke samun kuɗi da su.
    Idan har sai an ƙalailaice bambancin da ke tsakanin sana’a da kasuwanci, to ana iya cewa sana’a ita ce hanyar amfani da fasaha da hikima da kuma kayan aiki domin sarrafa wani abin amfani da za a iya sayarwa ko a musanya da wani abu mai daraja. Kasuwanci kuwa fasaha ce ta saye da sayarwa ko musanyen abubuwa masu daraja domin samun riba.
    Ko ba komai, za a tarar da cewa duk sana’ar da za a gudanar (kamar ƙira, saƙa, wanzanci da sauransu) to sai kasuwanci ya shiga ciki (ciniki, talla, da sauransu). Haka kuma duk kasuwancin da za a gudanar, to ana yi ne ta amfani da kayayyakin da an same su ne sakamakon sana’o’i.

    2.2 Kasuwancin Hausawa A Duniyar Zamani

    Cuɗanyar Hausawa da baƙin al’ummu musamman Larabawa da Turawa da kuma sauyawan zamani sun samar da sauye-sauye da dama a fannin kasuwancin Hausawa.[6] Haka kuma, a har kullum Hausawa na ƙara samun wayewa ta fuskar kasuwanci tare da faɗaɗawa da bunƙasa sana’o’insu. Bunƙasar kasuwancin Hausawa na kasancewa cikin manyan sigogi guda biyu kamar haka:
    Bunƙasar kasuwanci: Bunƙasar kasuwanci na faruwa ne yayin da ribar da ɗan kasuwa ke samu a cikin wani ayyanannen lokaci (misali wata guda) tak. Wannan na iya kasancewa sakamakon ɗaya daga cikin abubuwan da aka zayyano a ƙasa:
    • Faɗaɗar kasuwanci
    • Ɗaukakuwar darajar kasuwanci
    • Raguwar kuɗaɗen da ake kashewa kan sana’a[7]
    Faɗaɗar kasuwanci: Kasuwanci na samun faɗaɗa ne yayin da kayayyakin da yake samarwa ke isa hannun adadin mutane sama da yadda abin yake a baya. Wannan ma na iya kasancewa ta fuskokin da suka haɗa da:
    • Faɗaɗar kasuwanci na cikin gida[8]
    • Faɗaɗar kasuwanci na waje[9]
    Dukkannin matakan biyu (bunƙasa da faɗaɗar kasuwanci) na samuwa sakamakon tasirin zamani. Dalilan samuwarsu sun haɗa da:
    (i) sauƙaƙar hanyoyin sufuri da
    (ii) bunƙasar hanyoyin sadarwa da
    (iii) sababbin matakan sarrafawa da makamantansu.
    Ana iya kallon tasirin zamani kan kasuwancin Hausawa ta fuskoki daban-daban kamar haka:
    • Ƙare-Ƙare
    • Ƙirƙire-Ƙirƙire
    • Hulɗayya
    Kamar yadda masu iya magana ke cewa “ruwa ba ya tsami banza,” akwai dalilai daban-daban da ke samar da waɗannan sauye-sauye a sha’anin kasuwancin Hausawa. Idan aka ce “tasirin zamani,” dunƙulallen zance ne da ke tattare da abubuwa mabambanta. Yayin da aka fasa cikinsa, za a tarar da ɗaiɗaikun sabubban da suka haɗa da:
    Ɗaukar hannu: Wannan ya shafi kwaikwayo daga fasahohin waɗansu al’ummu na daban. Misali, a yau maƙeran Hausawa na samar da kayayyaki daban-daban ta hanyar ɗaukar hannu daga ƙere-ƙeren ƙasashen ƙ Haka ma kafintoci Hausawa ke ƙera abubuwa ta hanyar ɗaukar hannu. Babban misali shi ne bodin babbar mota (roka) da ake amfani da kataki da ƙarafa wajen ƙerawa.
    Yanayi/Tilasci: Sauyin yanayi da ya shafi rayuwa ko muhalli na kai ga an samar da sababbin kasuwanci tare da sauye-sauye a waɗanda ake da su. Kasuwancin sayar da datar intanet da ta POS da Hausawa suka runguma a yau, duk misalai ne na sababbin nau’ukan kasuwanci da suka samu a sakamakon tasirin yanayi. Haka kuma awara/wara/ƙwai-da-ƙwai da ke ƙara mamaye ƙasar Hausa na da alaƙa da yanayin yunwa da talauci da Hausawa ke ciki. A lokacin annobar korona kuwa (2019-2022), Hausawa da dama sun tara kuɗi ta hanyar kasuwancin takunkumin fuska (face mask).
    Yayi: Akan samu lokutan da yayi ne kawai ke sauyawa. Sannu a hankali sai a saki wani abu da aka yi riƙo da shi a koma wani daban. Irin wannan sauyi na kasance cikin yanayin da abu ne mai wuya a iya bayanin mene ne haƙiƙanin dalilin da ya sa aka saki al’adar baya. Sau da dama sai dai a ce “wayewa.”[10]

    3.0 Kasuwancin Hausawa A Duniyar Intanet

    A wannan bagire, kasuwanci na nufin duk wani abin da za a yi domin samun kuɗi ko wani abu mai darajar da zai iya wakiltar kuɗi ko wanda za a iya musanya shi da kuɗi. Wannan ya kasance saɓanin duk waɗansu ra’ayoyi da ke ɗaukar “sana’a” da “kasuwanci” a matayin nau’ukan harƙalloli guda biyu masu cin gashin kansu.
    Takardar ta tsaya kan wannan ra’ayi ne kasancewar harƙallolin biyu na da alaƙa da juna ta yadda ba za su iya cin gashin kansu ko ware kansu daga juna ba musamman a bagiren duniyar intanet.
    Sani, Buba da Mohammad (2019 p. 48) sun rawaito  Poon da Swatman na cewa: “Amfani da intanet a tsakanin masu ƙananan sana’o’i ya zama wani fitaccen lamari (batu) ga manazarta a fannin ilimin kimiyyar intanet da na kasuwanci.” Duniyar intanet shakundum ce ta fuskar tattara kasuwanci daban-daban.
    Mafi yawan motsi/lamura da ke kan intanet kasuwanci ne. Kusan komai da ke kan intanet na da darajar da za a iya sarrafa shi domin samun kuɗi – wato dai za a iya gudanar da kasuwanci da shi. A intanet akan samu har tsofaffin sana’o’in Hausawa da aka fara mantawa da su. Sannan akan iya yin kasuwanci da waɗannan tsofaffin sana’o’i ta hanyoyi daban-daban, kamar sayar da bayanan, sayar da hotuna da bidiyoyin, ko ɗora tallace-tallace a kafafen da suke.
    Wannan ɓangare na takardar zai tattauna lamarin kasuwancin Hausawa a duniyar intanet ƙarƙashin muhimman kanu guda uku, wato nau’o’in kasuwancin da nasarorinsu da kuma ƙalubalen da suke fuskanta.

    3.1 Nau’o’in Kasuwancin Hausawa A Duniyar Intanet

    Tuni Hausawa da dama suka tsunduma cikin hada-hadar kasuwanci da suka shafi duniyar intanet. Nau’ukan kasuwancin kan intanet da ake samun Hausawa ciki na da matuƙar yawa. Duk da haka, ana iya bayanin su cikin manyan rukunoni guda biyar kamar haka:
    • Firilancin na Kan Intanet (Online Freelancing)
    • Baje Haja/Koli
    • Dillanci
    • Kasuwancin Kuɗin Intanet
    • Talla (Advertisement)

    3.1.1 Firilancin Na Kan Intanet (Online Freelancing)[11]

    Aikin wucin gadi na kan intanet ya shafi duk wani nau’in aiki da ke buƙatar wata ƙwarewa ta musamman domin gundanar da ita. Manyan hajojin da masu ire-iren waɗannan kasuwanci ke kasawa su ne basirarsu da ƙwarewarsu. [12] A wannan fannin, ɓoyayyiyar gaskiya ba ta taƙaita ga kasa hajar baɗini ba. A maimakon haka, farfajiyar kasuwancin ma ta baɗini ce, wato duniyar intanet. Ɗaya daga cikin alfanun irin wannan aiki shi ne kamar yadda Downey, (2022 p. 1) ke cewa:
    A freelancer is not an employee of a firm and may therefore be at liberty to complete different jobs concurrently by various individuals or firms…
    Fassara: Firilanca ba ma’aikaci ne da wata ma’aikata ta ɗauka aikin dindindin ba, don haka yana da damar gudanarwa da kammala ayyuka daban-daban a lokaci guda, waɗanda yake karɓa daga mutane ko ma’aikatu daban-daban…
    Daga cikin ire-iren sana’o’in akwai:
    Firilancin da suka shafi kimiyyar harshe (language and linguistic services)
    Ma’aikatan firilancin ƙarƙashin kimiyyar harshe na gudanar da ayyuka da suka haɗa da:
    • Bin ƙwaƙƙwafin ma’ana (linguistic evaluation)
    • Fassara (translation)
    • Fassara da ƙirƙira (transcreation)
    • Karatun bita (proofreading)
    • Ƙirƙirar rubutu (content writing)
    • Subtitling (fassarar kan sikirin)
    • Tafintanci (interpretation)
    • Tsara rubutu (typesetting)
    • Maye sauti (voice over)

    Firilansin da suka shafi intanet da na’urori

    Ma’aikatan firilancin ƙarƙashin intanet da na’urori na gudanar da ayyuka da suka haɗa da:
    • Ba da tsaro ga kafafen intanet da na’urori (cyber security)
    • Gina kafafen intanet (website design)
    • Gina manhajoji (software programming)
    • Gwada inganci da amincin manhajoji da kafafen intanet (beta testing)
    • Gwada kutse (penetration testing)

    Firilancin da suka shafi gyaran hotuna da bidiyoyi

    Ma’aikatan firilancin ƙarƙashin gyara hotuna da bidiyoyi na gudanar da ayyuka da suka haɗa da:
    • Gyara hotuna da bidiyoyi (photo and video editing)
    • Tsara hotuna da zane-zane (graphic design and illustration)
    • Firilancin da suka shafi bincike
    Masu firilancin da ke ƙarƙashin rukunin bincike na gudanar da ayyuka da suka haɗa da:
    • Ƙalailaice bayanai (data analysis)
    • Neman bayanai (data sourcing)
    Ko bayan waɗannan akwai waɗansu masu tarin yawa da suka haɗa da: Jami’in talla (Marketing agent) da watsa labarai (media) da aiki a matsayin ƙwararren jami’i mai ba da shawarwari da suka shafi kuɗaɗe (finance expert) ko shawarwari da suka shafi doka (legal expert) ko mai jigila (gig work) da dai makamantansu.
    Da yawa daga cikin waɗannan nau’ukan sana’o’i akan same su a duniyar zahiri. Sai dai na duniyar zahirin sun yi ƙaranci sosai idan aka kwatanta da yadda hada-hadar kasuwancin take a duniyar intanet. Akwai dalilan da suka sa aka fi samun su a duniyar intanet kamar haka:
    • Domin taƙaita kashe kuɗi ga kamfanoni[13]
    • Domin nisan ƙwararru a fannonin da ake buƙata[14]
    Duk waɗannan nau’ukan firilancin ɗin kan intanet da aka zayyano a sama, a yau akwai Hausawa da suka rungume su.[15] Ƙin ƙarawa ma, har an samu ma’aikatu da kamfanonin Hausawa waɗanda ke gudanar da ire-iren ayyukan nan na firilancin. Daga cikinsu akwai Amsoshi Language Serices (https://www.amsoshilanguageservices.com)[16] da Shawsec (https://shawsec.com)[17] da 3logy (https://3logy.com.ng)[18].
    Duk wanda aka ɗauka daga cikin nau’ukan kasuwanci da ke sama na samar da kuɗin shiga sosai (duk da ya dogara ga alƙaluma daban-daban kamar su lokaci da yanayi da ƙwarewa da sauransu).[19] Nicol, (2022 p. 1) ta kawo cewa, kuɗin hada-hadar kasuwar duniyar fassara kaɗai ya haura dalan Amurka miliyan arba’in ($40,000,000). Yana da wuya a fitar da ƙididdigar kason da Hausawa suka ɗauka daga cikin alƙaluman.

    3.1.2 Baje Haja/koli

    A kullum Hausawa na ƙara rungumar intanet a matsayin kasuwar baje hajojin da suke sayarwa. Wannan na daga misalan harƙallolin da ake gudanarwa a duniyoyi guda biyu (na zahiri da na baɗini). Tun a shekarar 2021, Oyekanmi, (2021 p. 1) ya bayyana cewa rahoton National Bureau of Statistics (Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa) ta nuna cewa kashi 22% na masu ƙananan kasuwanci ne ke amfani da intanet wajen gudanar da kasuwancinsu.
    Hausawa masu ƙanana da manyan kasuwanci da dama na amfani da kafafen intanet daban-daban domin tallata kasuwancinsu. Waɗansu na amfani da kafafen sada zumunta (WhatsApp, Facebook, Instagram, TikTok, da sauransu),[20] waɗansu kuwa na buɗe kafafensu na kansu ko su haɗa guiwa da waɗansu masu kafafen intanet domin sama musu gurabu. A duba misalai a hotunan da ke ƙasa:
    Hoto na 1: Tallan hajoji a kan sitatus ɗin WhatssApp
    Tushe: An ɗauko su daga sitatus ɗin waɗansu Hausawa a WhatssApp.
    Hoto na 1 da ke sama na ɗauke da haɗakar hotuna 4 da aka ɗauko daga sitatus ɗin WhatsApp na mutane daban-daban. 3 na farko mata ne da ke sayar da kayan kwalliya (hoto na 1), takalma da jakukkuna (hoto na 2), da kuma turamen zannuwa (hoto na 3). Hoto na ƙarshen kuma an ɗauko daga sitatus ɗin namiji da ke sayar da shaddodi da yaduna. Duk waɗannan kasuwanci ne ƙanana.
    Hoto na 2: Shafin sayar da littattafan Hausa da ke kan kafar intanet ta WikiHausa.
    Madogara: Daga https://wikihausa.com.ng/product-category/hausa-novels/.
    Saɓanin hoto na 1, hoto na 2 misali ne na kafar intanet ta Hausawa da ke ba da dama ga waɗansu ‘yan kasuwa daban su baje hajojinsu. Yayin da aka yi ciniki, masu kafar za su ɗauki wani kaso daga ribar a matsayin ladan aikinsu.
    Hoto na 3: Kasuwancin katin waya da data da katin lantarki (da sauransu) a kan intanet
    Madogara: Kafar intanet ta Malam Ahmad Ali Galadima (https://sahabdata.com.ng)
    Hoto na 3 da ke sama an ɗauko shi ne daga kafar kasuwancin kan intanet ta Sahab Data. Wannan nau’in kasuwanci ne na kan intanet mallakin Bahaushe. Malam Ahmad Ali Galadima haifaffen jahar Kano ne wanda yanzu ke gudanar da kasuwancinsa a jahar Bauchi. A da dole sai mutum ya je ofishi ko shago ko ya kira waya kafin a saka masa katin waya ko datar burawuzin ko katin talabijin ko na wutar lantarki da sauransu. Da fikira irin ta Malam Ahmad, yanzu mutum zai iya hawa kafar intanet ɗin kasuwancin masu irin wannan kasuwanci ya sayi duk abin da yake buƙatar saya da kansa ba tare da sai ya yi magana da wani ba.

    3.1.3 Dillanci

    Manyan kamfanonin kasuwancin duniya da dama na da tsarin dillancin kan intanet. Wannan binciken ya gano cewa Hausawa masu yawa na cin gajiyar wannan tsari. Yana da sigogi daban-daban sannan ana iya samun bambancin sunaye da kamfanoni mabambanta suka yi masa.
    Duk da haka, a gama-gari an fi kiransa affiliate marketing, wanda a fassarar kai tsaye zai kasance “kasuwancin ɗosane,” amma a haƙiƙanin yadda lamuran ke gudana, “dillanci” ne kai tsaye.
    Kamfanoni da suka haɗa da masu sayar da littattafai, na’urori, ababen hawa, tufafi, abinci, mayuka, da sauransu, duk suna ba da damar dillanci. Dillali zai tallata kayan kamfani. Idan aka saya ta dalilin tallar da ya yi, to yana da kaso cikin ribar, wato dai la’ada (royalty). Akwai manyan nau’ukan dillancin kan intanet guda uku kamar haka:
    • Buɗe reshen kasuwanci
    • Ɗora liƙau da samfuran hajoji a kan kafar intanet ɗin dillali
    iii. Yaɗa liƙau da samfuran hajoji a kafafen sada zumunta
    Hoto na 4: Dillanci ta hanyar ɗora liƙau a kan kafar intanet
    Madogara: An ɗauko daga kafar Amsoshi (www.amsoshi.com).
    A hoto na 4 da ke sama, za a ga misalin yadda aka ɗora liƙau da ke ɓoye cikin hoto a kan kafar intanet da ta kasance ta Hausawa. Yayin da masu ziyarar wannan kafa suka bi liƙau ɗin zuwa kafar masu kamfanin har suka yi hulɗayyar kasuwanci, to masu wannan kafa za su samu kamasho.
    Hoto na 5: Dillanci a kan kafar Paxful.
    Madogara: An ɗauko daga https://paxful.com/ha/buy-bitcoin-kiosk.
    Paxful babbar kafa ce ta hada-hadar kasuwancin kuɗin intanet. Ita ma na da tsarin dillanci. A hoto na 5 da ke sama, an ga yadda Paxful ke ba da damar a buɗe abin da ta kira “shago” a kan kafarta. Wato zai zama tamkar wani ƙaramin shago da mai shi zai riƙa samun kayayyakin da zai riƙa dillanci daga asalin babban kantin Paxful.[21]
    Dangane da tura liƙau ta kafafen sada zumunta kuwa, Hausawa da yawa sun samu kuɗaɗe daga dillancin PalmPay da Kuda da Manhajar Abeg da Chipper Cash da makamantansu.[22]

    3.1.4 Kasuwancin Kuɗin Intanet

    Kuɗin intanet (crypto currency) nau’i ne na kuɗin baɗini da ke wanzuwa a duniyar intanet. Buhari,3 (2021 p. 1) ya bayyana shi a matsayin “kuɗi da ake amfani da su a cikin kwamfuta wanda za a iya saye da saidawa da su a cikin hanya mai sauƙi.” Wani abin burgewa shi ne, ana iya sayen kuɗin intanet ta amfani da kuɗin zahiri, ana kuma iya sayen su ta amfani da wani nau’in kuɗin intanet na daban. Ƙididigar Tripple A (2023 p. 1) ya nuna cewa, ya zuwa 2022, kashi 10.34% na ‘yan Nijeriya sun mallaki kuɗin intanet.
    Batey, (n.d.) ta tabbatar da cewa, kuɗin intanet na farko shi ne Bitcoin wanda aka samar tun a shekarar 2008 sannan aka fara amfani da shi a shekarar 2009.[23] Ya zuwa yau akwai nau’ukan kuɗaɗen intanet daban-daban waɗanda kuma kullum ke ƙara yawa saboda sababbi da ake samarwa. Pi na ɗaya daga cikin waɗanda suka fi ƙaurin suna tsakanin Hausawa, inda har aka samu waƙoƙi[24] da maganganun malamai da masana daban-daban game da shi. Bayan haka, har fim sukutum aka yi game da Pi, mai suna ‘Yan Pi Network.
    Akwai manyan nau’uka ko hanyoyin kasuwancin kuɗin intanet guda biyu da wannan bincike ya ci karo da Hausawa da dama na gudanarwa. Na farkonsu shi ne trading wanda a nan aka fassara shi a matsayin cinikayya. Na biyun kuwa shi ne holding, wanda aka fassara shi da riƙewa.
    Cinikayya shi ne tsarin da ake saye da sayar da kuɗin intanet nan take domin samun ƙaramar riba. Wannan na buƙatar lissafi da kyakkyawan hasashe. M.M. Manga, (keɓantacciyar tattaunawa, 7 ga watan Fabarairu 2023) ya bayyana yadda ake wannan cinikayya. Mutum zai sayi wani nau’in kuɗin intanet bayan yin lissafin cewa darajarsa za ta ƙaru bayan ‘yan kwanaki kaɗan, domin ya sayar ya samu riba. Haka kuma, mutum na iya saya a wurin ɗan kasuwa mai sauƙin farashi, sannan ya sayar wa ɗan kasuwa mai farashin da ya fi inda ya saya domin samun riba.
    Riƙewa shi ne tsarin da mutum zai sayi kuɗin intanet sannan ya ajiye shi na tsawon lokaci. Ana yin haka ne domin bin babbar riba. Akan saya a lokacin da ake kira red market (jar kasuwa – wato lokacin da darajar kuɗaɗen intanet ta faɗi) sannan a sayar a lokacin da ake kira green market (koriyar kasuwa – wato lokacin da darajar kuɗaɗen intanet ta tashi).
    Daga cikin manyan kafofin hada-hadar kuɗaɗen intanet akwai:
    Binance – https://www.binance.com/
    Gate – https://www.gate.io/
    Crypto – https://crypto.com/
    OKX – https://www.okx.com/
    KUCOIN – https://www.kucoin.com/
    Paxful – https://www.paxful.com
    An samu Hausawa da dama da ke bayani game da lamuran da suka shafi kasuwancin kuɗin intanet. Yawanci sukan yi ne a tashoshin kan intanet masu zaman kansu. Daga cikinsu akwai Mujahid Muhammad Manga da ke da kafar TikTok mai suna Abumaher. Shi kuwa Sunusi Danjuma Ali tasha yake da ita a kan YouTube mai suna SunusiCryptoTV.

    3.1.5 Talla (Advertisement)

    A wannan bigiren talla na nufin tallata haja ko ra’ayi ko aƙidar wani ko waɗansu domin samun kuɗi. Kusan wannan nau’in talla ba a samun sa a duniyar zahiri – duk da akan samu makamantansa da ake gudanarwa a gidajen talabijin da na rediyo da kuma cikin finafinai. A yau Hausawa da dama sun yi nisa a wannan harkar kasuwanci. Ana gudanar da tallar kan intanet ta fuskoki daban-daban da suka haɗa da:

    Talla a kan kafafen intanet (Websites and blogs)

    Wanda ke da kafar intanet da ta gawurta, yana da damar ɗora tallace-tallace a kai. Tallar na iya kasancewa ta fuskoki guda biyu, ko dai Adsense[25] ko kuma keɓantattun tallace-tallace.[26]
    Hoto na 6: Talla a kafar intanet
    Madogara: An ɗauko daga https://www.isyaku.com/search/label/FADAKARWA
    A hoto na 6 da ke sama, za a ga yadda aka ɗora talla a kafar Isyaku. Mamallakin wannan kafa Bahaushe ne ɗan jahar Kebbi, mai suna Isyaku Garba.

    Talla a shafuka da zaurukan kafafen intanet

    Waɗanda ke da zauruka da shafuka a kafafen intanet na da damar ɗora tallace-tallace idan sun cika ƙa’idojin da ake buƙata. Waɗannan ƙa’idoji sun danganta da kafar da kuma mutum ko mutane ko kamfanonin da za su ba da tallar. Sannan ƙa’idojin na sauyawa lokaci zuwa lokaci.
    Hausawa da dama na samun kuɗi a YouTube da Facebook da Instagram da TikTok a dalilin irin wannan nau’in tallar. Mawaƙan Hausa na zamani da ‘yan barkwanci Hausawa da dama ta wannan hanyar suka fi samun kuɗi. Tuni masu tsara finafinan Hausa ma suka rungumi wannan nau’in kasuwanci inda suke sakin finafinansu a kan YouTube tare da ɗora tallace-tallace domin samun kuɗin shiga. Fitattun finafinan Hausa masu dogon zango da ake sakewa a kan YouTube sun haɗa da Labarina da Izzar So da Amaryar TikTok da Asin da Asin da makamantansu.
    Daga cikin ‘yan barkwancin Hausa kuwa da suka shahara da kafafen YouTube da TikTok (waɗanda ke ɗora tallace-tallace kan tashoshi ko shafukansu) akwai Abubakar Sadauki da aka fi sani da Aibs_Fulani. Akwai kuma Mu’azu Muhammad da aka fi sani da Bushkido. Sannan akwai Ali Muhammad Idris da aka fi sani da Maɗagwal, I.A. Adam (keɓantacciyar tattaunawa, 11 ga watan Maris, 2023).

    Talla Ta Hanyar Raba Liƙau

    Wannan nau’in kasuwancin kan intanet ya shafi tura saƙonnin talla na wani kamfani a kafafen sada zumunta ta sigar liƙau.[27] Mai wannan kasuwancin na ɗaukar liƙau da za a riƙa ba shi a kowace rana (ko wani lokacin da aka ƙayyade) sannan ya raba a kafafen sada zumunta irin su Facebook, TikTok, WhatsApp, da sauransu.
    Hausawa da dama sun samu riba mai yawa daga wannan kasuwanci. Duk da haka wannan nau’in kasuwanci tamkar caca yake. Dalili kuwa shi ne, sau da dama ire-iren waɗannan nau’ukan kasuwanci na yin ɓatar dabo na farat ɗaya. A haka ake rufewa da kuɗaɗen waɗanda suka yi aiki ba a biya su ba, da kuma kuɗaɗen waɗanda suka sanya hannayen jari.[28] Daga cikin ire-irensu da aka ci kasuwarsu kuma suka watse akwai:
    • Uwork
    • Insme
    • MyBonus

    3.2 Abubuwan Da Mai Kasuwanci A Kan Intanet Ke Buƙata

    Daga cikin nau’ukan ayyukan kan intanet da aka tattauna a ƙarƙashin 3.1.1 zuwa 3.1.5, akwai waɗanda suka kasance gama-gari tsakanin mutanen duniya. Waɗansu daga cikinsu kuwa, ana sa ran su kasance keɓantattu ga Hausawa. Misali, duk aikin firilancin da ya shafi harshe ko al’ada, kai tsaye an fi son ɗan gado ba ɗan haye ba.
    Ma’ana dai, an fi son wanda Hausa ke matsayin harshen uwa gare shi. Ana hakan ne don gudun abin da Bunza, (2015) ya kira “Grammatical Rift” (p. 5) da “Cultural Lacuna” (p. 11) wato “Giɓin Nahawu” da “Giɓin Al’ada.” Bayan haka, abubuwan da ake buƙata na iya bambanta daga kasuwanci zuwa kasuwanci. Duk da haka, akwai waɗanda suka kasance gama-gari kamar haka:
    Na’ura mai sauri da inganci daidai da nau’in kasuwancin da za a gudanar[29]
    Sabis ɗin intanet mai ƙarfi da rashin yankewa
    Wuri mai sirri da rashin hayaniya[30]
    Ƙwarewa sosai a fannin da aka sa a gaba
    Tallar haja (ƙwarewa) a kan intanet[31]
    Girmama lokaci
    Gaskiya da riƙon amana

    3.3 Allah san barka a kasuwancin Hausawa a duniyar intanet

    Samuwar damarmakin kasuwanci a kan intanet ya zo da alfanu ta fuskoki daban-daban ga Hausa. Daga ciki akwai:
    Hutun jiki: Waɗansu daga cikin nau’ukan kasuwanci na da sauƙin gudanarwa. Misali, kasuwancin sayar da data da katin waya da na wutar lantarki da talabijin duk saita su kawai ake yi a bar su a kan intanet. Ɗan kasuwa ba ya buƙatar wata wahalar ciniki ko miƙa kaya. A maimakon haka, kwastomomi su ne za su biya kuɗi kawai su ɗauki kaya. Yana kwance sai dai ya ji shigar kuɗi a akawun ɗinsa.[32]
    Ƙarancin jin rauni sakamakon aiki: Saɓanin ayyukan bayyane da dama da ana iya samun rauni ta dalilinsu (daga kayan aiki, ko faɗuwa, ko haɗari a hanyar zuwa wurin aiki da sauransu), mai aikin kan intanet na da ƙarancin fargabar samun wani rauni sakamakon aikin.[33]
    Cikakken ‘Yanci: Koma bayan ayyukan duniyar zahiri, mai aikin firilancin na da ‘yanci kan lokacinsa. Yana da zaɓi kan ya karɓi aiki ko kada ya karɓa. Yana da damar tsara lokacinsa yadda yake so sannan ya karɓi ayyuka lokacin da ba shi da waɗansu hidimomin rayuwa a gabansa kawai.
    Jari: Akwai nau’ukan kasuwancin kan intanet da ke buƙatar ƙaramin jari kawai. Waɗansu kuwa ba sa ma buƙatar jarin. Misali, a firilancin da ya shafi yaɗa liƙau, ba a buƙatar wani jari. Game da abin da ya shafi fassara kuwa, ɗan jarin bai wuce na sayen waya ko kwamfuta ba, sai kuma ‘yar datar burawuzin da za a riƙa sakawa.
    Sauran alfanu na gama-gari sun haɗa da:
    • Rage cunkoso a kan tituna
    • Rage fitar da sinadaren ababan hawa masu cutar da muhalli

    3.4 Ƙalubale A Kasuwancin Hausawa A Duniyar Intanet

    Duk da ɗimbin alfanun da ke tattare da kasuwancin kan intanet, akwai ƙalubale ko naƙasu da ke tattare da shi. A ƙasa an kawo waɗansu daga ciki.
    Rashin ingantaccen sabis: Har yanzu babu ingantaccen sabis a ƙasar Hausa. Ko wuraren da ke da sabis mai ƙarfin 4G, a waɗansu lokuta akan samu matsaloli.[34] Wannan babban naƙasu ne a harkar kasuwancin kan intanet kasancewar akwai lamuran da ke da ƙayyadden lokacin kammalawa. Sannan akwai kamfanoni da ke buƙatar rahoton ƙarfin intanet ɗin mutum kafin fara harƙalla da shi.
    Matsalar wutar lantarki: Har ya zuwa lokacin kammala rubuta wannan takarda (Maris 2023) babu ingantacciyar wutar lantarki a ƙasar Hausa. Hakan kuwa ƙalubale ne ga nau’ukan kasuwancin kan intanet.
    Talauci da ƙarancin tallafi: Da dama daga cikin nau’ukan kasuwancin kan intanet na buƙatar jari. Wannan ya shafi sayen kayan aiki da datar intanet da waɗansu manhajoji da dai makamantansu (wanda ya danganta ga nau’in sana’ar). Hausawa na fuskantar ƙalubale a wannan ɓangare sakamakon talauci da ƙaranci ko rashin tallafi.
    Rashin koyar da zamanantattun darrusa: Zamani ya fara tsere wa tsarin karatun Nijeriya a matakin ƙasa bai ɗaya, da kuma ƙasar Hausa a keɓance. Misali, wanda ya karanci harshe na da babban gurbi sosai a kasuwancin intanet, domin zai iya shiga a dama da shi a dukkannin nau’ukan kasuwanci da aka tattauna a ƙarƙashin 3.1.1 zuwa 3.1.5 da ke sama. Duk da haka, waɗanda suka karanci Hausa da dama na kasancewa ba tare da aikin yi ba saboda rashin gogewa ta fuskar ire-iren waɗannan nau’ukan kasuwanci.
    Illata muhalli da yanayi: Daga cikin harkoki da hada-hadar kasuwancin intanet akwai waɗanda ke cutar da muhalli. Misali, haƙon kuɗaɗen intanet irin su Bitcoin na illata muhalli matuƙa. Rahoton Osborne, (2022 p. 1) ya nuna cewa, illar da haƙon Bitcoin ke yi wa muhalli na iya kai wanda man fetur ke yi ta fuskar fitar da sinadarin kabon.
    Cutar da lafiya: Duk da babu wani bincike da ya tabbatar da cewa yawan kallon sikirin na haifar da dauwamammen ciwon ido, masanan ido irin su Dakta Colman Kraff sun tabbatar da cewa zai iya haifar da matsalolin da suka haɗa da kallo dishi-dishi da ciwon kai har ma da ciwon wuya idan abin ya yi tsanani.[35] Abiola, (2021 p. 1) ya tabbatar da cewa radiyeshin da ke fita daga jikin kwamfuta na haifar da illoli da dama, ciki har da hana haihuwa ga maza.
    4.0 Sakamakon bincike
    Lamarin kasuwanci ya yi daidai da ikirarin ra’in Pulatoriyya, domin kuwa akwai kasuwancin da ke gudana a duniyar zahiri, akwa kuma waɗanda ke gudana a duniyar intanet. Duniyar zahiri na kan tarewa zuwa nau’in kasuwancin duniyar intanet. Hausawa ma da dama sun bi sahun wannan cigaba.
    Kasuwancin kan intanet  ya rabu zuwa nau’uka daban-daban kamar yadda aka tattauna a ƙarƙashin sashe na 3.1 da ke sama. Binciken ya gano cewa ana damawa da Hausawa cikin dukkannin waɗannan kasuwanci. Waɗanda suka karanci harshen Hausa sun fi samun rawar takawa a abin da ya shafi firilancin da ke da alaƙa da harshe (ciki har da fassara da tafintanci da sauransu da aka kawo  ƙarƙashin 3.1.1).
    Waɗannan kasuwancin kan intanet na da ɗimbin alfanu ga al’ummar Hausa tun daga kan samar da aikin yi har zuwa nisantar haɗurra, da dai sauransu da aka zayyano a ƙarƙashin 3.3 da ke sama. A ɓangare guda kuwa, duk da ɗimbin alfanun da kasuwancin kan intanet ya zo wa Hausawa da shi, yana tattare da ƙalubale kamar yadda aka gani ga ƙarƙashin 3.4 da ke sama.
    Dangane da waɗannan ƙalubale, Hausawa ‘yan kasuwan kan intanet na iya riƙo da dabarar amfani da hanyoyin samun sabis ɗin intanet sama da guda. Wannan zai ba su damar kauce wa shiga halin ƙaƙanikayi sakamakon gushewar ƙarfin sabis ko sabis ɗin kacokan a lokacin aiki. Sannan kada su bari a bar su a baya wajen rungumar sababbin sabis ɗin intanet na zamani masu ƙarfi, musamman yanzu da ake sauraron ƙarasowar sabis ɗin 5G da na Starlink.
    Game da wutar lantarki kuwa, ya kamata gwamnati ta ninka ƙoƙarinta na tabbatar da samuwar ingancin wutar lantarki musamman domin samun cigaba mai ɗorewa. Yayin da gwamnati ke ƙoƙarin wannan, ‘yan kasuwan kan intanet na iya amfani da dabarun da suka haɗa da wutar sola da rumbun cajin kwamfuta (computer power bank) da sauran hanyoyin da ba sa illata muhalli da yanayi.
    Ya kamata a mayar da hankali wajen koyar da abubuwan da suka shafi kasuwancin kan intanet musamman a matakin manyan makarantu. Hakan zai ba da damar samun ƙarin aikin yi tare da rage zaman banza. Da taimakon wannan, Hausawa da yawa musamman waɗanda suka karanci harshen Hausa na iya samun hanyar dogaro da kai a sauƙaƙe.
    Dangane da illolin lamuran kasuwancin intanet a kan muhalli da yanayi, akwai buƙatar gwamnatoci da hukumomi da ɗaiɗaikun mutane su yi huɓɓasa wajen ganin an samu mafita mafi dacewa. Wannan ya haɗa da fito da dokoki da ƙa’idoji da suka dace daga ɓangaren gwamnati, bincike da faɗakarwa daga ɓangaren hukumomi, da kuma bin kyawawan matakai da ke da akwai daga ɓangaren ɗaiɗaikun mutane.

    4.1 Kammalawa

    Nau’ukan kasuwancin kan intanet na da matuƙar yawa. Da wuya a iya nuna wani abu a kan intanet da ba za a iya kasuwanci da shi ba. Sannu a hankali ‘yan kasuwan duniyar zahiri na zamanantar da kasuwancinsu ta hanyar mayar da ita ko wani ɓangare nata zuwa duniyar intanet.
    A yanzu haka duk manyan kasuwancin duniya sun yi gurbi sosai a kan intanet. Da yiwuwar a shekaru masu zuwa duniyar intanet na iya ƙwace ta zahiri a fuskar kasuwanci, inda za a samu mafi rinjayen kasuwanci na gudana ne a duniyar intanet saɓanin ta zahiri.

    Manazarta

    Abiola, R. (2021). Laptop radiation does not cause skin cancer but it can contribute to male infertility. https://dubawa.org/laptop-radiation-does-not-cause-skin-cancer-but-it-can-contribute-to-male-infertility/.
    Batey, N. (n.d.). A brief history of Bitcoin. https://www.jmco.com/articles/tax/brief-history-bitcoin.
    Buhari, I. (2021)1. Samun kuɗi: Kasuwanci guda 10 wanda aka fi saurin samun kuɗi da su. https://www.hausawasite.com.ng/2021/09/samun-kudi-kasuwanci-guda-10-wanda-aka.html.
    Buhari, I. (2021)2. Ma’anar sana’a da kuma amfaninta. https://www.hausawasite.com.ng/2021/11/maanar-sanaa-da-kuma-amfaninta.html.
    Buhari, I. (2021)3. Cryptocurrency da yadda ake samun kudi da shi. https://www.hausawasite.com.ng/2021/10/cryptocurrency-da-yadda-ake-samun-kudi.html.
    Bunza, A.M. (2015, October 20 – 21). Grammatical rift and cultural lacuna: Constraints on English-Hausa and Hausa-English translation busines. National Conference On Translation, Center for Research in Nigerian Languages and Folklore, Bayero University, Kano & Nigerian Institute of Translators and Interpreters (NITI).
    Cropley, D.H. (2019). Problem-solving man: A history of Hunan creativity. Springer.
    Downey, L. (2022). What is a freelancer: Examples, taxes, benefits, and drawbacks. Investopedia. https://www.investopedia.com/terms/f/freelancer.asp.
    Gerson, L. (2013). “Was Plato a Platonist?” From Plato to Platonism (pp. 3-33). Cornell University Press. www.jstor.org/stable/10.7591/j.ctt32b4gd.5.
    Gerson, P. L. (2005). “What is Platonism?” Journal of the History of Philosophy, 42, 253-257. www.doi.org/10.1353/hph.2005.0136.
    Hukumar Binciken Tarihi Da Al’adu Ta Jihar Katsina da ‘Yan Ƙyaure, S.S.F. (n.d.). Ilmin falaki da sanin yadda ake tsara jadawalin watannin Musulunci. Hukumar Binciken Tarihi Da Al’adu Ta Jihar Katsina.
    Kraff, C. (2022). How to protect eyes from mobile and computer screens. https://kraffeye.com/blog/how-to-protect-eyes-from-mobile-and-computer-screens.
    Meinwald, C. C. (2020). Plato (Greek Philosopher). Encyclopedia Britannica. https://www.britannica.com/biography/Plato.
    Muhammad, M.S. (2020). Bahaushiyar al’ada. Bayero University Press.
    Na, S. (2013). Earth rotation – Basic theory and features. http://dx.doi.org/10.5772/54584.
    Nguyen, A. (n.d.). 10 Best freelance websites to hire top talent. Time Doctor. https://www.timedoctor.com/blog/best-freelance-websites.
    Nicol, V. (2022). Translation industry trends and statistics. My Language Connection. https://www.mylanguageconnection.com/translation-industry-trends-and-statistics/.
    Osborne, M. (2022). Bitcoin could rival beef or crude oil in environmental impact. https://www.smithsonianmag.com/smart-news/bitcoin-could-rival-beef-or-crude-oil-in-environmental-impact-180980877/.
    Oyekanmi, S. (2021). Only 22% of Nigerian informal businesses use internet in their business operations – NBS. Nairametrics. https://nairametrics.com/2021/09/23/only-22-of-nigerian-informal-businesses-use-internet-in-their-daily-business-operations-nbs/.
    Rumbun Ilimi. (n.d.). Sana’o’i a ƙasar Hausa. https://www.rumbunilimi.com.ng/HausaSanaa.html#gsc.tab=0.
    Sani, A-U. (2022). Zamani zo mu tafi: Al’adun Hausawa a duniyar intanet. [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya.
    Sani, A-U., Buba, U. & Mohammad, I. (2019). Wanda ya tuna bara…: Biɗa da tanadi a tsakanin hausawa matasa a yau. Global Academic Journal of Humanities and Social Sciences, 1(2), 44-50. www.doi.org/10.36348/gajhss.2019.v01i02.001.
    Thein, K. (2018). “Soul and incorporeality in Plato.” Eirene Sudia Graeca Et Latina, LIV, 53–95. Centre for Classical Studies Institute of Philosophy of the Czech Academy of Sciences, Prague.
    Triple A. (2023). How many crypto owners are in Nigeria? https://triple-a.io/crypto-ownership-nigeria-2022/.
    Kafafen da Aka Duba
    https://3logy.com.ng
    https://crypto.com/
    https://sahabdata.com.ng
    https://shawsec.com
    https://shehuawwal.com
    https://www.abu-ubaida.com
    https://www.amsoshi.com
    https://www.amsoshilanguageservices.com
    https://www.binance.com/en
    https://www.fiverr.com
    https://www.gate.io/
    https://www.isyaku.com
    https://www.kucoin.com/
    https://www.linkedin.com
    https://www.okx.com/
    https://www.paxful.com
    https://www.proz.com
    https://www.upwork.com
    [1] Ilimin kimiyya da addini da al’ada duk sun tabbatar da cewa duniya na kan juyawa cikin waɗansu nau’uka da salailan tafiya da kowanne ke da tasiri ko sakamako da yake samarwa. Domin ƙarin bayani, ana iya duba Hukumar Binciken Tarihi Da Al’adu Ta Jihar Katsina da ‘Yar Ƙyaure, (n.d.) ko Na, (2013).
    [2] Babu wata halitta da lokaci ba ya tasiri a kanta. Nau’ukan tasirin da ake iya samu na iya kasancewa waɗanda halittun ke da iko a kansu (misali ƙirƙire-ƙirƙire da ƙere-ƙere), ko waɗanda ba su da iko a kansu (misali raguwar girman jikin ‘yan’adam da raguwar yawan shekaru da suke yi a duniya).
    [3] Domin ƙarin bayani kan wannan ra’i ana iya duba Gerson, (2005: 253); Gerson, (2013); Thein, (2018); da Sani, (2022).
    [4] Plato ya kasance ɗaya daga cikin fitattun masana falsafa da suka rayu ƙarnuka huɗu zuwa biyar kafin zuwan Annabi Isa. Domin samun cikakken bayani kan tarihinsa da ayyukansa, ana iya duba Meinwald, (2020).
    [5] Lallai wannan ma’ana ta kasuwanci da Buhari (2021) ta ƙara fito da iƙirarin Pulatoriyya ta cewar gaskiya nau’i biyu ce, wato wacce ake gani da wacce ba a gani. Ma’anar ta Buhari ta ƙara tabbatar da hakan kamar yadda ya bayyana daga cikin kasuwanci akwai waɗanda ba a ganin su.
    [6] Wannan takarda na da ra’ayin cewa, ko da Hausawa ba su yi cuɗanya da kowace al’umma ba, za su samu sauye-sauye da cigaban zamani a harkokin rayuwarsu. A har kullum halin rayuwa na tilasta wa ɗan’adam amfani da fikira wajen sama wa kansa sauƙi da mafita daga ƙalubalen da ke dabaibaiye da matakan rayuwarsa. Saboda haka, yadda kullum yanayin duniya ke sauyawa tare da ɓullo da sababbin ƙalubale da ɗan’adam bai taɓa cin karo da su ba, haka shi ɗan’adam ke ƙara ƙirƙiro hanyoyin fiskantar matsalolin. Waɗannan su ke haɗuwa su samar da cigaban zamani. Cropley, (2019) ya kawo cikakken bayani kan wannan falsafa.
    [7] Ana iya samun raguwar kuɗaɗen da ake kashewa wurin gudanar da sana’a ta hanyoyin da suka haɗa samun kayayyakin sana’a mafiya sauƙi ko samun sauƙaƙan hanyoyin jigilar kayayyakin sana’a zuwa wurin sarrafa su, da dai makamantansu.
    [8] Wannan na faruwa yayin da aka samu ƙarin mutane a muhalli ko maƙwabta ko cikin al’ummar mai sana da suka fara amfani da kayayyakin da mai sana’ar ke samarwa.
    [9] Wannan na faruwa yayin da waɗansu al’ummu na nesa suka fara amfani da kayayyakin da mai sana’a ke samarwa.
    [10] Babban misalin wannan shi ne yadda matasan Hausawa suka riƙi babban wando (fantalo) a matsayin kwalliya (tsukakken wando kuma ya kasance ƙauyanci), har zuwa wajajen shekarar 2008. Daga baya kuma sai yayi ya sauya inda aka ɗauki fantalo a matsayin ƙauyanci, shi kuwa tsukakken wando ya koma wayewa. Duk lokacin da irin haka ya faru, masu kasuwancin wandunan dole su sauya domin samar da abubuwan da mutane za su saya ba waɗanda za su yi kwantai ba.
    [11] Kasancewar wannan takarda ba ta ci kawo da wata amintacciyar fassara ta “online freelancing” ba, an baddala ta zuwa “firilancin na kan intanet.”
    [12] Waɗannan hajoji na daga cikin misalan ɓoyayyun gaskiya da ra’in Pulatoriyya ke magana a kansu.
    [13] Idan kamfani na aiki da ma’aikatan firilancin, to ya huta biyan su albashi kowace wata. A maimakon haka, zai riƙa biyan su ne kawai yayin da ya ba su aiki.
    [14] Misali, kamfanonin fassara da ke nahiyoyin da ke nesa da ƙasar Hausa, ya fi musu sauƙi su riƙa aiki da ma’aikatan firilancin don yi musu fassarori ta kan intanet a maimakon zuwa ƙasar Hausa domin samun mai fassara ko kuma buƙatar mai fassarar ya je can domin samun su.
    [15] An tabbatar da wannan bayani ta hanyar tattaunawa da waɗansu Hausawa gogaggu a harkar firilancin, da kuma bincikawa a waɗansu manyan kafafen baje kolin firilancin na intanet da suka haɗa da Fiverr (https://www.fiverr.com) da LinkdIn (https://www.linkedin.com) da ProZ (https://www.proz.com) da Upwork (https://www.upwork.com).
    [16] Sun shahara a fannin firilancin da ya shafi kimiyyar harshe da bincike (M.U. Arabi, keɓantacciyar tattaunawa, 5 ga watan Maris, 2023).
    [17] Sun shahara a fannin firilancin da ya shafi tsaron kafafen intanet da na’urori (S. Auwal, keɓantacciyar tattaunawa, 5 ga watan Maris, 2023).
    [18] Sun shahara a fannin koyar da ilimummukan zamani kamar na’urori, intanet, saƙago da sauransu.
    [19] A bisa dalilai na sirrantawa, wannan bincike ba zai iya kawo misalan ƙididdigar kuɗaɗen da waɗansu Hausawa masu harkan firilancin ke samu ba. Amma binciken ya ci karo da Hausawan da suke iya aikin har sama da miliyan biyar (#5,000,000) a cikin wata guda.
    [20] Da wuya mutum ya karaɗe sitatus ɗinsa na WhatssApp ba tare da cin karo da hajojin da waɗansu ke tallatawa ba, irin su tufafi, turare, na’urori, da sauransu.
    [21] Fassara illahirin shafin zuwa Hausa na ƙara nuni da yadda Hausawa ke cikin wannan harkar dillanci.
    [22] A. Sani (Keɓantacciyar Tattaunawa, Maris 6, 2023).
    [23] Wanda ya samar da Bitcoin ya bayyana sunansa a matsayin Satoshi Nakamoto. Sai dai har yanzu ba a san mai wannan sunan ba. Ba a ma san mutum guda ne ko ƙungiya ce ba. Domin samun ƙarin bayani, a duba, Batey, (n.d.).
    [24] https://www.amsoshi.com/2021/12/yan-pi-network.html
    [25] Wannan nau’in talla ne inda ake rajista da kamfanin Google. Kamfanin na Google ne zai riƙa karɓar tallace-tallace sannan ya riƙa ɗora waɗanda suka dace a kafar wanda ya yi rajistar (ta la’akari da nau’ukan mutanen da ke ziyartar kafar tasa).
    [26] Wannan nau’in tallace-tallace ne da ake karɓa daga ɗaiɗaikun mutane ko kamfanoni ko ƙungiyoyi. Kai tsaye akan yi ciniki da yarjejeniyar yadda tallar za ta kasance (kamar abin da ya shafi farashi, da shafukan da za a ɗora su da tsawon lokacin da za su ɗauka kafin a sauƙe su).
    [27] A waɗansu lokuta yakan kasance bidiyo ko hoto.
    [28] An samu waɗannan bayanai daga tattaunawa da aka yi da Hausawa da suka ci wannan kasuwa. A. Sani (keɓantacciyar tattaunawa, 11 ga watan Maris, 2023) ya yi cikakken bayanin yadda harƙallolin ke gudana.
    [29] Abubuwan da ake dubawa a wannan fannin sun haɗa da saurin na’ura, girman ƙwaƙwalwarta, faɗin sikirin ɗinta, da nau’inta. Akwai nau’ukan ayyukan da kai tsaye kamfani na iya ba da bayanin nau’in na’urar da za a yi amfani da ita domin gudanarwa. Misali, daga shekarar 2020 har zuwa 2023 Hausawa da dama sun yi aiki da kamfanin Appen. Aikin na buƙatar tattara bayanai ne ta amfani da wayar salulula. Haka kuma, duk wanda ya gwada buɗe manhajar XTM a kan waya domin gudanar da fassara, zai ga jan rubutu na masa gargaɗin cewa dole sai ya yi amfani da kwamfuta.
    [30] Mafi yawan ayyukan kan intanet na buƙatar sirri. Sau da dama akan buƙaci mutum ya cike abin da aka fi sani da NDA (Non-Disclosure Agreement) wato Yarjejeniyar Riƙe Sirri kafin ƙulla harƙallar kasuwanci da kamfani a kan intanet.
    [31] Akwai fitattun kafafen intent da suka shahara a wannan fannin. Masu firilancin na zuwa waɗannan kafafe su baje kolin fikirarsu. Kamfanoni daban-daban a faɗin duniya na ziyartar waɗannan kafafe domin duba hajar da ta musu. Nguyen (n.d. p. 1) ya zayyano waɗansu daga cikin fitattun kafafen kamar haka: LinkedIn da freelancer.com da Toptal da Guru da PeoplePerHour da FlexJobs da 99Designs da Fiverr da Upwork da Freelance Writing Gigs.
    [32] Duk da haka akwai abubuwan da ake buƙata daga gare shi kamar su ƙara kuɗi a lalitoci da duba daidaiton lamura da kuma sauraren koken kwastomomi.
    [33] Duk da haka akan iya samun rauni lokaci zuwa lokaci musamman idan ba a bi ƙa’idojin aiki ba. Misali, ana iya samun ciwon baya ko ciwon wuya sakamakon daɗewa ana zaune ko zama yadda bai kamata ba, da dai sauransu.
    [34] Game da wannan, binciken ya kasance ganau a yankunan Kano da Katsina da Sakkwato da Zamfara da Zariya.
    [35] Domin ƙarin bayani, a duba Kraff, (2022 p. 1).
    Edita@rumasau-kallamu
  • Tatsuniyar ‎Gizo Da Giwa

    Tatsuniyar ‎Gizo Da Giwa

    ‎‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    Wani mutum ne dai ya ba wani malami kuɗi don a yi masa asiri. Sai malamin ya ce sai an samo hauren giwa domin ya haɗa maganin da shi. Sai mutumin ya je cikin jama’a ya ce, ‘Wa zai iya samo min hauren giwa in ba shi kuɗi? ’Aka rasa wanda zai iya. Sai Gizo ya ce shi zai iya.

    Sai mutumin ya ce, ‘To shi ke nan sai ka samo ka kawo.’ Shi ke nan, sai Gizo ya je gida ya daka nakiya mai zaƙin gaske. Sai ya je gidan giwa da ɗan ƙunshin nakiyar a hannunsa, ya ce, ‘Gafaya dai.’ Sai giwa ta ce, ‘Maraba da Gizo.’

    ‎Ya ce, ‘Yauwa. Wata nakiya ce na kawo miki da na samo a pa.’ Shi ke nan sai giwa ta ce, ‘To’. Ta gutsiri nakiya ta kai bakinta. Da ta ji zaƙin nakiyar, sai ta ce, ‘Don Allah Gizo, ni ma ka raka ni in je in samo?’

    ‎Sai ya ce, ‘Haba yaya! Me zai hana? Ki zo gobe in kai ki.’ Shi ke nan, sai ta zo washegari suka je wajen kan pa. Sai ya ce da ita, ‘Idan kika doka bakinki sau ɗaya, kika doka sau biyu, a na ukun sai ki ga nakiya rubus a bakinki.’ Shi ke nan, sai giwa ta doka bakinta sau ɗaya fas a kan pa. Ta kuma dokawa.

    Da ta doka na ukun sai haƙorinta ya balle ya faɗo ƙasa. Sai jini shar. Sai Gizo ya ce, ‘Assha, assha. Yaya aka yi haka kuma?’ Ya yi maza ya ɗauki haƙorin giwar ya sa a aljihunsa. Ita ba ta gani ba. Tana ta kanta.

    ‎Shi ke nan sai gizo ya bar giwa a nan. Ya yi sauri ya kai wa mutumin nan haƙorin. Mutumin ya ba shi ladansa. Sai gizo ya je daji ya tattara namun daji suka je gidan da giwa ta ke a kwance. Suka tarar kanta ya kumbura, suntum.

    Sai gizo ya gaya wa namun dajin, ‘In na ce, “Babbanmu da giɓi,” ku ce, “Ɓurum ɓaɓurka.”’ Sai ya fara waƙar: Babbanmu da giɓi. Sai suka amsa: Ɓurum ɓaɓurka. Shi ke nan sai suka gama, suka koma. Gizo ya bar giwa a wahala. Shi kuwa ya karɓe kuɗinsa.

    Shi ke nan. Kurunk us.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Barewa Ta Auri Mutum

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Amfanin Kuɓewa Yake A Jikin Ɗan Adam

    Yadda Amfanin Kuɓewa Yake A Jikin Ɗan Adam

    Shin ko kun san Amfanin Kubewa A jikin Ɗan Adam? Mutane da dama suna amfani da kuɓewa a matsayin miya ba tare da sanin tarin amfanin ta ga jikin ɗan Adam ba . Bincike ya nuna kuɓewa na ɗauke da sinadarai kaman haka:

    Calories, Carbs, Protein, Fiber, Magnesium, Folate, Vitamin A, Vitamin C, Vitamin K , Vitamin B6, Wasu sinadaran sun haɗa da sinadaran kare cells da kuma lalata guba a jiki kaman: polyphenols, flavonoids, isoquercetin, lactin ga kaɗan daga cikin amfanin kuɓewa a jikin ɗan Adam:

    *Ƙara ƙarfin gani: Kubewa na taimakawa wajen  ƙara ƙarfin gani. Ko mai karatu ya san dalili, sabida yana ɗauke da sinadaran Vitamin A da carotene.

    *Yana taimakawa masu juna biyu: Kuɓewa na matuƙar taimakawa masu juna biyu wajen inganta lafiyarsu da kuma na jaririn da ke ciki, domin kuɓewa na ƙunshe da ɗimbin sinadaran Vitamin B da take samarwa da kuma inganta sabbin ƙwayoyin halitta na gina jiki da lafiyarsa.

    *Hana kamuwa da ciwon ƙoda: Wani bincike da aka gudanar a jami’ar Jilin ta ƙasar Sin ya tabbatar da cewa, yawan amfani da kuɓewa na matuƙar rage haɗarin kamuwa da ciwon ƙoda.

    *Maganin cutar Asthma: Kuɓewa na maganin cutar numfashi wato asthma, saboda sinadarin Vitamin C da ke tattare ta ita.

    *Maganin Ciwon Sugar: Ana amfani da kuɓewa wajen maganin cutar siga wadda ta zamo ruwan dare a tsakanin al’umma a yanzu. Tana ɗauke da sinadarin fibre a cikinta, wanda ke taimakawa wajen daidaita yawan siga a cikin jikin ɗan Adam.

    *Inganta Lafiyar Uwar Hanji: Kuɓewa na inganta lafiyar hanji da tumbi ta hanyar fitar da sanadaran da ka iya lahani ga hanji ko tumbin. Kuma sakamakon haka ne, take maganin kumburi da cushewar ciki wanda kuma ke rage ƙarfin ciwon siga ko ma maganinsa.

    *Kuɓewa Na Kara Karfin Garkuwan Jiki: Yawan amfani da kubewa na kara bunkasa tare da karfafa garkuwar jikin dan-adam. akwai wasu Sinadarai dake cikin kubewa masu matukar amfani a garemu da suka hada da, Bitamin C da Calcium da Magnesium da ke taimaka wa wajen yaƙi da kuma fatattakar cuta.

    ABDULLAHI ADO KOFA
    CEO KOFA NUTRI CONSULT NUTRITIONIST/DIETITIAN

    Danna nan don karanta Amfanin Rake Ga Lafiyar Ɗan Adam

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tarihin Kafuwar Ƙasar Jordan

    Tarihin Kafuwar Ƙasar Jordan

    Ƙasar Jordan (Al-Urdunn) tana daga cikin ƙasashen Gabas ta tsakiya da suka fi ƙaranci a girma amma suka fi zurfin tarihi. Tarihinta ya fara tun kafin rubutaccen tarihi, tun lokacin da bil’adama ya fara zaman ƙauyuka, noma, da kasuwanci a yankin. Jordan ta kasance gada ce ta haɗa Afirka, Asiya da Turai, lamarin da ya sa manyan dauloli da wayewaye suka riƙa wucewa, zama, da mulkar yankin.

    Tun kafin haihuwar Annabi Isa (AS), shaidu sun nuna cewa yankin Jordan ya kasance wurin zama tun zamanin Neolithic, kimanin shekaru 9000 kafin haihuwar Annabi Isa (AS), inda mutane suka fara noma da kiwo, da gina ƙananan ƙauyuka.

    A hankali, yankin ya bunƙasa, ya zama cibiyar hulɗar kasuwanci da al’adu tsakanin yankuna daban-daban. A tsakanin ƙarni na 12 zuwa na 5 kafin haihuwar Annabi Isa (AS), yankin Jordan ya kasance ƙarƙashin masarautu na gargajiya irin su Ammoniyawa, Moabiyawa, da Edomiyawa.

    Waɗannan masarautu sun yi tasiri sosai a addini, siyasa da yaƙe-yaƙe na yankin Sham, kuma ana ambatonsu a littattafan tarihi da na addini. Daga bisani, wata ƙungiya mai ƙarfi ta taso, wato Nabatiyawa, waɗanda suka kafa birnin Petra, wanda ya zama babbar cibiyar kasuwanci da ke haɗa kasuwannin Larabawa, Masar, da Rumawa.

    A shekarar 63 kafin haihuwar Annabi Isa (AS), Daular Roma ta karɓi iko da yankin Jordan. A wannan lokaci, birane kamar Jerash (Gerasa) sun bunƙasa sosai, inda aka gina manyan tituna, wuraren taro, haikalai, da gine-ginen gwamnati. Bayan rushewar Daular Roma, Daular Byzantine ta gaji ikon yankin, inda Kiristanci ya samu gindin zama tare da gina majami’u da cibiyoyin addini.

    Shigowar Musulunci a ƙarni na 7 Miladiyya ya zama sabon babi a tarihin Jordan. Bayan nasarorin Sahabbai a yankin Sham, Jordan ta shiga ƙarƙashin Khalifancin Rashidun, daga bisani Umayyawa da Abbasiyawa. A wannan zamani, yankin ya kasance muhimmin sashe na duniyar Musulunci musamman saboda kusancinsa da Madina, Dimishƙu, da Urushalima.

    Umayyawa sun yi tasiri sosai, har ma suka gina manyan fadoji a hamadar Jordan, irin su Qasr Amra. Daga baya, yankin ya sha wahalhalun Yaƙin Salibi, kafin Ayyubiyawa da Mamlukai su sake karɓar iko. A shekara ta 1516, Daular Usmaniyya ta mamaye yankin Jordan, inda ta yi mulki tsawon kusan shekaru 400.

    A wannan lokaci, Jordan ba ta kasance ƙasa mai cin gashin kanta ba, sai dai ɓangare na lardunan Sham. Mulkin Usmaniyya ya kawo ɗan kwanciyar hankali, amma ba a samu gagarumin ci gaban tattalin arziki da siyasa ba. Yankin ya kasance karkara mai dogaro da noma, kiwo, da hanyoyin kasuwanci na hajji zuwa Makka.

    Rushewar Daular Usmaniyya bayan Yaƙin Duniya na Ɗaya (1914–1918) ya sauya tsarin siyasar Gabas ta Tsakiya gaba ɗaya. Birtaniya ta karɓi ikon yankin Jordan a ƙarƙashin Mandate na League of Nations, inda aka kira yankin da suna Transjordan.

    A shekarar 1921, Birtaniya ta naɗa Amir Abdullah bin Al-Hussein, ɗan Sharif Hussein na Makka, a matsayin jagoran yankin. Wannan mataki ne ya kafa tubalin ƙasar Jordan ta zamani. A ƙarƙashin Amir Abdullah, an fara gina tsarin gwamnati, soji, da dokoki, duk da cewa Birtaniya na da tasiri sosai.

    Bayan shekaru na gwagwarmaya da tattaunawa, a ranar 25 ga Mayu, 1946, Transjordan ta samu cikakken ‘yancin kai, inda aka ayyana ƙasar da suna Hashemite Kingdom of Jordan. Amir Abdullah ya zama Sarki Abdullah I, wanda ya fara mulki a matsayin sarki mai cikakken iko.

    Bayan ‘yancin kai, Jordan ta fuskanci ƙalubale da dama, musamman rikicin Gabas ta Tsakiya. A yaƙin Larabawa da Isra’ila na 1948, Jordan ta mallaki West Bank, wacce ta riƙe har zuwa 1967. Amma a Yaƙin Kwanaki Shida, Jordan ta rasa yankin ga Isra’ila, abin da ya shafi siyasa, tattalin arziki, da demografiyar ƙasar. Duk da haka, Jordan ta ci gaba da neman kwanciyar hankali ta hanyar diplomasiyya da gina ƙasa.

    Tsarin mulkin Jordan shi ne sarautar Hashemiyya, inda iyalin Hashemiyya ke da ikirarin kasancewa zuriyar Annabi Muhammad (SAW) ta hannun Sharif Hussein na Makka. Wannan asali ya ba sarautar Jordan wata muhimmiyar daraja ta addini da siyasa.

    Daga Sarki Abdullah I, zuwa Talal, Hussein, har zuwa Sarki Abdullah II na yanzu, Jordan ta kasance ƙasa mai daidaito da ƙoƙarin kiyaye zaman lafiya a yankin da ke fama da rikice-rikice. A taƙaice, kafuwar ƙasar Jordan ba lamari ne na kwatsam ba.

    Tarihinta ya haɗa tsoffin wayewaye, shigowar Musulunci, mulkin dauloli, da gwagwarmayar ‘yancin kai. Wannan dogon tarihi ya samar da Jordan ta yau – ƙasa mai tarihin dubban shekaru, al’adu masu haɗuwa, da rawar da take takawa wajen samar da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya.

    Manazarta

    Abu-Lughod, J. L. (1989). Before European Hegemony: The World System A.D. 1250–1350. Oxford University Press.

    Hitti, P. K. (2002). History of the Arabs. Palgrave Macmillan.

    Alon, Y. (2007). The Making of Jordan: Tribes, Colonialism and the Modern State. I.B. Tauris.
    Cleveland, W. L., & Bunton, M.

    (2016). A History of the Modern Middle East (6th ed.). Westview Press.

    Rogan, E. (2007). The Arabs: A History. Basic Books.

    Lapidus, I. M. (2014). A History of Islamic Societies (3rd ed.). Cambridge University Press.

    Hourani, A. (1991). A History of the Arab Peoples. Harvard University Press.

    Kamrava, M. (2013). The Modern Middle East: A Political History since the First World War. University of California Press.

    Salibi, K. S. (1998). The Modern History of Jordan. I.B. Tauris.

    Shlaim, A. (2007). Lion of Jordan: The Life of King Hussein in War and Peace. Knopf.

    Yazigi, M. (1999). Jordan in the Twentieth Century. Garnet Publishing.

    Cleveland, W. L., & Bunton, M. (2016). A History of the Modern Middle East.

    Rogan, E. (2016). The Fall of the Ottomans: The Great War in the Middle East. Basic Books.

    Danna nan don karanta Tarihin Sarkin Musulmi Muhammad Bello

    Edita@rumasau-kallamu

  • Maƙala Mai Taken Tsattsafin Fanɗare wa Addinin Musulunci: Wata Yasasshiyar Gona a Gandun Waƙoƙin Baka na Hausa

    Maƙala Mai Taken Tsattsafin Fanɗare wa Addinin Musulunci: Wata Yasasshiyar Gona a Gandun Waƙoƙin Baka na Hausa

    Tsattsafin Fanɗare wa Addinin Musulunci: Wata Yasasshiyar Gona a Gandun
    Waƙoƙin Baka na Hausa

    Adamu Rabi’u BAKURA1, Abu-Ubaida SANI
    Department of Languages and Cultures, Federal University, Gusau, Zamfara State, Nigeria

    Tsakure: Rubuce-rubucen nazari da aka yi game da waƙoƙin Hausa sun fi shurin masaƙi. Duk da haka, mafi yawan rubuce-rubucen sun karkata ne kan zaƙulo fasahohi da ke cikin waƙoƙin tare da nuna yadda suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa. Wannan takarda na da fahimtar cewa an bar wani babban giɓi wanda shi ne nazarin fanɗare wa dokokin addini cikin waƙoƙin Hausa.

    Maƙalar nan na da manufar binciko muhallan da ɗiyan waƙoƙin baka na Hausa suka keta
    dokokin da Allah ya shimfiɗa wa bayinsa. An tattara bayanai ta hanyar sauraron waƙoƙin da tsamo misalan ɗiyan waƙoƙin da abin ya shafa, tare da ciro hukunce-hukuncen da suka yi bayani kansu daga Alƙur’ani da hadisan manzon Allah.

    Binciken ya fahimci cewa, akwai tarin misalan fanɗare wa addini a cikin waƙoƙin baka na Hausa. Daga ƙarshe an ba da shawarwarin da suka haɗa da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da ire-iren waƙoƙin ba su yi tasiri wajen gurɓata tarbiya nagartacciya ba.

    Fitilun Kalmomi: Waƙoƙi, Addini, Musulunci, Fanɗarewa

    GABATARWA

    Musulmi ba a bar shi kara zube ba. An kafa masa sharuɗɗan tafiyar da rayuwa dukkanta. Ire-iren waɗannan sharuɗɗan suna ƙunshe cikin littafin Allah (Alƙur’ani) da Hadisan Annabi S.A.W. Daga cikin dokokin akwai na tilas, wato abin da Musulmi mai hankali ba zai iya rabuwa da shi ba, komai tsanani.

    Akwai kuma abubuwan ƙi, wato waɗanda ba a so Musulmin ya aiwatar da su ba. Haka akwai haramun, waɗanda aka hana mutun ya aikata su. Idan dukkannin rayuwar mutum ta kasance cikin ɗa’a, kuma ya nisanci saɓo, babu shakka ya kiyaye dokokin Allah Maɗaukakin Sarki.

    A gefe guda kuwa, kamar yadda Chiromawa, (n.d. p. 5-10) ya bayyana, ko da addinin Musulunci ya iso ƙasar Hausa ya tarar da al’ummomi da dama suna aiwatar da kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe nau’i-nau’i da suka haɗa da:
    i. Kiɗan sana’a
    ii. Kiɗan jawo hankali
    iii. Kiɗan lallashi (rarrashi)
    iv. Kiɗan faɗakarwa

    v. Kiɗan zaburarwa
    vi. Kiɗan ƙarfafa zuciya
    vii. Kiɗan jaruntaka
    viii. Kiɗan farin ciki
    ix. Kiɗan ibada

    Duk ire-iren waɗannan kaɗe-kaɗe akan haɗa su ne da waƙe-waƙe. Kasancewar addinin Musulunci, addini ne mai sauƙi da sauƙaƙa wa mabiyansa, bai haramta waɗansu daga cikin nau’ukan kaɗe-kaɗe ba. Ya dai kawo gyare-gyare domin kare mutunci da martabar
    mabiyansa. Ya haramta shi ne yayin da aka aiwatar da abin da Allah ya haramta a cikinsa.

    Hasali ma akwai wuraren da Musulunci ya sunnanta kiɗa da waƙa, kamar a lokuttan ɗaura aure, tamkar yadda Imamu Buhari ya bayyana a “Babin Kaɗa Ganha” a ranar aure da walima. Bayan haka, akwai ranar kai amarya ɗakin mijinta, da ranar idi da ranar suna, da ranar zuwan wani shugaba da ranar komawarsa, da ranar kaciya (kugunu/kuidu).

    Akwai hadisai waɗanda Buhari da Muslim da Tirmizi da Hakimu da Nisa’i suka rawaito da ke nuni ga halaccin kiɗa da waƙa a babin aure da sallar idi. Halaccin kan tabbata ne matuƙar bai haɗa da alfasha ko motsawa zuwa ga saɓon Allah ba. A bisa wannan ne, maƙalar ta ƙuduri aniyar yin ƙwarya-ƙwaryar bincike a muhallan da makaɗan baka na
    Hausa suka keta ƙa’idojin da Allah ya shata ta hanyar kauce musu.

    Duk wasu ɗiyan waƙa da makaɗi ya yi za a yi ƙoƙarin kawo shi tare da auna shi da ma’aunin shari’a da aka ciro daga nassin Alƙur’ani da Hadisan Annabi S.A.W. domin tabbatar da hasashen. Ana iya samun ɗiyan waƙoƙin da ke ƙunshe da gurbin fanɗara a waƙoƙin makaɗan sarauta, da na jama’a da na maza da sauransu, kamar yadda za a gani ɗaya bayan ɗaya.

    Dabarun Gudanar Da Bincike

    Kadadar wannan bincike ta taƙaita ne ga waƙoƙin baka na Hausa a farfajiyar koyarwar addinin Musulunci. A ɓangaren waƙoƙin an ɗauko ɗiyan waƙoƙi da aka tattauna kansu kai tsaye ta hanyar sauraron odiyoodiyo da kallon bidiyoyinsu.

    A ɓangaren hukunce-hukuncen addinin Musulunci kuwa, an ɗauko su kai tsaye daga cikin Alƙur’ani mai tsarki da hadisan Manzon Allah (S.A.W.) ingantattu. An kuma nazarci rubuce-rubucen masana da manazarta a wannan fannin inda suka haska hanya ga binciken.

    Fanɗare wa Koyarwar Musulunci ta Hanyar Zambo

    Makaɗan saurauta sun shahara wajen yin zambo, domin ƙawata waƙoƙinsu. Masana da dama sun bayyana ma’anar zambo gwargwadon fahimtarsu. Gusau, (1984 p. 37) ya tafi kan cewa “Akan yi zambo don adanta waƙa da muzanta wanda ke hamayya da wanda ake yi wa waƙa.” Abba da Zulyadaini, (2000 p.63) sun bayyana zambo da cewa: “… nau’i ne na muzanta mutum ta hanyar ƙasƙantar da shi, ko wulaƙanta shi, domin a baƙanta masa tare da dusashe masa kwarjini a idon jama’a.

    Mawaƙan sun fi shahara da zambo don su aibanta duk wani ɗan sarki da ke ja da ubangidansu. Muhammad, (2005) kuwa na da ra’ayin cewa zambo zagi ne kai tsaye,
    … saboda akan ba da hoton wanda ake yi wa tare da bayyana cikakkiyar sifarsa ta hanyar ambaton duk wani abu da ya dace da shi. A lokacin da aka yi ma wani zambo akan fito da hotonsa ne zahiri, ta yadda duk wanda ya san shi zai gane cewa da shi ake. Muhammad, (2005 p. 28)

    A taƙaice kenan, zambo yana ƙunshe da ma’anar ƙaga wa mutun magana wadda za ta muzanta shi ta ɓata masa suna ba tare da bayyana wanda ake yi wa ba. A dubi misalin zambon da Alhaji Musa Ɗankwairo ya yi wa wani ɗan sarautar Tsafe:

    Kun san zamanin ga ya canza,
    Ga wani ɗan sarki da kandaye,
    Ya shaho hoda kamar Delu.
    (Ɗankwairo: Waƙar Sarkin Tsahe).

    Wannan zambon da Ɗankwairo ya yi wa ɗan sarki ya kai matuƙa wajen aibanta ɗan sarkin ta hanyar kamanta shi da ɗan daudu. Hakan ba ƙaramin muzantawa da dushe masa kima ya yi a idon al’umma ba. Tabbas kuwa hakan ya saɓa wa dokokin addinin Musulunci. An umurci Musulmi da ya tsare (kame) harshensa da yin furucin abin da bai halatta ba, kamar keta mutuncin ɗan uwansa Musulmi ba tare da wani abu mai wajabtawa ba na shari’a. Allah na cewa:

    Lalle Allah na yin umurni da adalci da kyautatawa, da ba wa ma’abocin zumunta kuma yana hani da alfasha da abin ƙi da zalunci. Allah yana yi muku gargaɗi ko da kuna tunawa. (Surar Nahli: 16:90).

    Idan aka dubi wannan ayar za a tarar ta yi hani ga yi wa wani mugun baki (mugun fata), sannan ta yi hani ga alfasha. Ya kuma yi umurni da tausayawa tare da yin abu bisa gaskiya. Daga ƙarshe ta yi hani a kan ha’intar wani ta kowane ɓangare. Wannan na iya
    kasancewa ta hanyar lafazi ko a aikace. Ta la’akari da wannan ɗiyar waƙar, za a tarar mawaƙin ya kauce wa dokar da Allah ya ɗora masa.

    Annabi S.A.W. Ya Ce: Haƙiƙa, mafi sharrin mutane a matsayi wurin Allah a ranar alƙiyama shi ne wanda mutane suka ƙyale shi don ƙiyayyar alfasharsa. (Muslim ya ruwaito). Wanda duk wani mawaƙi ya yi wa zambo, to zai guje shi tare da yin kaffa-kaffa da al’amarinsa.

    Sau da yawa akan ba su kyauta ne bisa tilas don gudun zambonsu. A irin wannan yanayin idan aka nazarci hadisin, za a ga a nan ma sun kauce wa koyarwar Annabi
    S.A.W. A wani Hadisin kuwa Annabi (SAW) cewa ya yi: “Mumini bai kasancewa mai yawan suka ba ko yawan la’anta ko yawan alfasha, ko mai sakin harshe” (Tirmizi
    ne ya ruwaito shi).

    Wannan hadisin ya fito ƙarara ya bayyana mana cewa, duk mawaƙin da ya ba da gaskiya
    ga Allah da ranar lahira da manzancin Annabi S.A.W., zai kasance mai bin dokokin Musulunci kamar yadda suke. Hakan kuwa zai sanya ya guji yi wa Musulmi zambo.
    Akwai misalan wuraren da makaɗan jama’a suka yi wa abokan hamayyarsu zambo ta hanyar zagi kai tsaye.

    A irin wannan lamari ne mawaƙin jama’a kan fito da halayen mutun a fili, sannan ya zage shi. Misali, a waƙar “Gagara Badau,” Alhaji Mamman Shata cewa ya
    yi:
    Shata: Allah ya tsine ma tsohon mazinaci,
    Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.
    Shata: Allah ya tsine ma da kai da iyalinka.
    Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.
    Shata: Yanzu babban ɗan bai gani,
    Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.
    Shata: Babban jikanshi kuma yana kama agwaginmu,
    Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.
    Shata: Gida ya lalace.
    Amshi: Gagara badau namiji tsayayyen ɗan kasuwa.

    Dubi yadda Shata yake zagin wani basarake tare da nuna ɗansa ya makance, ya kuma kira jikansa ɓarawon agwagi. Wannan ba ƙaramar fanɗarewa ba ce, domin a shara’ar Musulunci an umurci Musulmi da ya kiyaye da yin zance da bai halatta ba, kamar ƙarya, da zage-zage da keta mutunci Musulmi. Allah na cewa: “…Kuma yana hani da alfasha da abin ƙi da zalunci. Allah yana muku gargaɗi ko da kuna tunatuwa.” (Alƙur’ani,
    Suratul Nahl, 16:90).

    Fanɗare Wa Koyarwar Musulunci Ta Hanyar Habaici

    Habaici ko gugar zana salo ne ko azancin yi da wani a kaikaice ta yadda sai wanda ya san shi kuma ya san abin da ake magana game da shi ne kaɗai zai iya ganewa. Habaici wata hanya ce da makaɗan baka suke amfani da shi a cikin waƙoƙinsu domin ƙara musu
    armashi, ta hanyar ƙasƙantar da wani mutun ko kuma muzanta shi ko su zage shi ko kuma su soka masa wata magana a kaikaice. Misali, a cikin waƙar Mai Dubun
    Nasara Sardauna, Alhaji Musa Ɗankwairo yana cewa:

    Ga kare ga kura kowane ya hangi wani,
    Ga aura ya koma,
    Wagga nan hanya ba mu ga wurin wali ba.
    (Alhaji Musa Ɗankwairo, Waƙar Mai Dubun Nasara, ta Sardauna).

    Yayin da aka dubi ɗiyar wannan waƙar za a ga yadda Ɗankwairo ya siffanta Sir. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da kura. Ya yi hakan ne domin bayyana irin ƙarfinsa kamar yadda kura ke da shi. Wannan kuwa ya shafi yadda take iya tauna ƙashi da kuma kwarjini da waibuwarta na sanya rashin kuzari ga halittar da ta tunkare ta.

    A gefe guda kuwa, sai ya kira wanda yake yi wa habaici da kare, saboda ba sa zama
    inuwa ɗaya da kura. Hasali ma kare ba ya hangen nesa sosai, kuma mai gidansa yakan yi amfani da shi ne wajen farauta. Kiran mutun kare ba ƙaramin ƙasƙantarwa ba ne
    a al’adance. Wannan ne ya sa makaɗan baka sukan siffanta waɗanda suke son wulaƙantawa da kare saboda nhalayyarsa da ɗabi’unsa.

    Musulunci ya hana keta mutuncin Musulmi ko wulaƙanta shi ko zagin sa ko laƙa masa munanan sunaye, ba tare da haƙƙin shara’a ba. Allah na cewa: “… kuma kada ku jefi juna da miyagun sunaye” (Alƙur’ani, 49:11). Idan muka dubi wannan ayar, za mu ga cewa ta hana a kira Musulmi da sunan da zai kasance tamkar zagi ne gare shi. Yin haka kuma fanɗare wa umurnin Ubangiji ne.

    Annabi S.A.W. ya ce: “Zagin Musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙar sa kafirci ne” (Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi). Idan aka dubi wannan hadisin cikinsa da
    wajensa, aka kuma nazarci ɗiyar waƙar da ta gabata, za a tarar cewa, makaɗin ya kauce wa faɗar Annabin S.A.W., ya yi gaban kansa. Yin haka fanɗarewa ne ga dokokin addinin Musulunci.

    Bin dokoki da ƙa’idojin Musulunci kuwa dole ne, inda har Allah ke cewa: “Kuma abin da Manzo ya zo muku da shi, to ku riƙe shi, kuma abin da ya hane ku, to ku hanu” (Surah Al-hashr, 59:9).

    Fito-Na-Fito Da Koyarwar Muslunci

    Akwai misalan inda mawaƙa ke amfani da wasu kalmomin da suka kauce wa ƙa’idojin addinin Musulunci. Akan samu irin wannan fito-na-fito a fannonin da suka shafi sahihan aƙidojin da suka danganci ranar lahira, da matsayin mala’ikun Allah da makamantansu. Ya kuma haɗa da dokoki da ƙa’idojin addinin Musulunci ta fuskar hani da horo. Wannan
    ɓangare na aikin zai mayar da hankali wajen zaƙule irei-ren waɗannan misalai:

    Izgilanci

    Izgilanci ga abubuwan da addini ya zo da su nanuni ga halin ko-oho ga lamarin addinin. Musulunci kansa ya tsawatar da riƙo da dokokin da ke ƙunshe cikinsa ba tare da wargi (wasa) ba. Duk da haka, akan samu wuraren da mawaƙa suka yi izgilanci ga lamarin
    addini. Alhaji Muhammadu Ɗan’anace a waƙar Shago yana cewa:

    Jagora: In da lahira ana kasa dambe…
    ‘Y/Amsohi: Da Walakiri ya ji ƙwal ga gaba nai.
    Jagora: Duk wanda bai yi kallon Shago ba,
    Aradu yana da sauran kallo,
    Ya zaka duniya kamar bai zo ba,
    Kamar zuwan kare ga aboki,
    Tamkar mutum ya mari budurwa,
    Ko ya mutu ba a gafarta mai.

    In aka dubi wannan ɗan waƙar, za a tarar cewa, wannan makaɗin ba ƙaramar kasada ya yi ba. Ya nuna rashin jin tsoron aukawar wani haɗari (hatsari) ko shiga cikin abin da bai san sakamakonsa ba. Allah na cewa: “Kuma kada ka bi abin da ba ka da ilimi a kansa.” (Surar Isra’i, 17:36).

    Idan muka nazarci wannan ayar, za a ga yadda Mahaliccin sammai da ƙassai ya faɗakar da masu imani da su yi kaffa-kaffa ga dukkan lamarin da ba su san haƙiƙanin yadda yake ba. Ko bayan batu kan abin da mutum bai sani ba, batutuwan da ke ƙunshe cikin ɗiyar
    waƙar na tattare da izgilanci ga abin da ya shafi imani da mala’iku da ranar ƙiyama.

    Goyon Bayan Karuwanci

    Kalmar karuwa, suna ne na mace. Jam’i kuwa shi ne karuwai. Karuwa na nufin mace mai zaman kanta wadda mazan banza ke neman ta su ba ta kuɗi domin saduwa (zina) da ita. Zina kuwa tana nufin saduwa (jima’i) da matar da ba ta halatta ga mutum ba ta hanyar aure, wato wadda ba matarsa ba. Tun kafin bayyanar Musulunci a farfajiyar
    ƙasar Hausa, Bahaushe ya ƙyamanci zina.

    Don haka karuwanci bai samu bagiren zama ba, balle a yi zina. Duk da kasancewar akwai al’adar tsarance, a inda saurayi kan gayyaci budurwarsa ta je ɗakinsa har ma ta kwana. Sakamakon irin wannan al’adar ce, ya sanya su amfani da al’adun tsafi domin tabbatar da amarya ba ta taɓa sanin wani ɗa namiji ba (zina) kafin a yi mata aure. A irin
    wannan al’adar ce, idan yarinya ta san maza kafin a yi mata aure, za ta kunyata a cikin jama’a.

    Idan kuma ta ɓoye ba ta faɗa ba, ta mutu, kamar yadda Ibrahim, (1985 p. 5) ya nuna.
    Yayin da addinin Musulunci ya bayyana, sai ya haramta zina. Hasali ma ya sanya ta cikin manyan laifuka, bayan kafirci, wato haɗa Allah da wani da kashe ɗan Adam. Allah yana cewa: “Kuma kada ku kusanci zina, lalle ne ita ta kasance alfasha ce kuma ta munana ga zama hanya” (Alƙur’ani; Suratul Isra’i, 17:32)

    Haka kuma Musulunci ya yi ƙoƙarin toshe duk wata kafa da za ta iya zama sanadin aikata zina ta hanyar wajabta wa mata sanya hijabi. Sanya hukuncin jefe mazinaci da mazinaciya har su mutu a bainar jama’a, idan sun yi aure, ko a yi musu bulala idan ba su taɓa yin aure ba, na nuni da girman zunubin. Duk da wannan umarni na Ubangijin talikai da kuma uƙubar da aka tanadar wa mazinata, sai aka sami wani mawaƙi da ake kira Habibu Sakarci ya yi wa wata karuwa waƙa.

    A cikin ɗiyan waƙar yana cewa:
    Jagora: Shehuwar mata Safiya Kano, Ta gidan ‘Yajja
    Safiya Kano.
    Jagora: ‘Yan birni roƙo suke, Allah ba mu jaka bakwai,
    Mu gano ɗakin Safiya Kano.
    Jagora: Direbobi ma roƙo suke, Allah ba mu jaka
    bakwai, Mu gano ɗakin Safiya Kano.
    Jagora: Mutan birni yanga suke, Domin darajar Safiya
    Kano.

    Yayin da aka nazarci ɗiyan waƙar, za a ga cewa Habibu Sakarci yana tallar wannan karuwa ta hanyar bayyana ta a matsayin ƙasaitacciyar karuwa. Har ma ya nuna ‘yan birni da dirobobi na burin Allah ya ba su kuɗi masu yawa, don su tafi ɗakinta. Hasali ma ya bayyana ta fi sauran karuwan birnin kyau. Wannan ba ƙaramar fanɗara ba ce da keta dokokin Allah.

    Ya zo cikin hadisi
    Annabi S.A.W. yana cewa: Lalle ana rubuta wa ɗan’adam rabonsa daga
    zina, kuma lalle mai risker sa wancananka ne babu makawa. Idanu zinarsu ita ce kallo, kunnuwa kuwa zinarsu ita ce sauraro, harshe kuwa zinarsa ita ce zance. Hannuwa kuma zinarsu ita ce damƙa, ƙafa kuma zinarta ita ce taku, zuciya kuwa saƙa soye-soyenta ne, kuma tana guranta su, farji yana gaskata wancananka ko ya ƙaryata (Buhari da Muslimu ne suka ruwaito hadisin).

    Duk da irin waɗannan nassoshin Alƙur’ani da hadisan Annabi S.A.W., sai ga ya makaɗa na fanɗare musu ta hanyar gayyatar al’umma zuwa ga aikata fasiƙanci. Shi ma Alhaji Mamman Shata ya yi makamanciyar wannan waƙar, a inda ya yi wa wata mata da ake kira Karo Oma:
    Jagora: Duk ɗan birnin da ya riƙa,
    Ni kar ya yi mini yanga,
    In yana so ya isa
    In gan shi gidan Kara Oma.
    (Alhaji Dakta Mamman Shata: Waƙar Kara Oma)

    A nan Shata ya fito ƙarara ya tura ‘yan birni su tafi gidan wannan karuwa idan har sun isa. A ɗaya ɓangaren kuwa cicciɓa ta ya yi da cewa, sai manyan mutane wayayyu ne kawai suka isa su yi hulɗa da ita. Wannan waƙar ba abin da ya raba ta da fanɗare wa
    dokokin Allah da ya shata wa Musulmi.

    A shara’ar Musulunci, an san Musulmi da kunya. Hasali ma kunya tana cikin halayensa, kuma tana daga cikin Imani. Imani kuwa shi ne aƙida da rayuwar Musulmi. Manzon Allah yana cewa: “Kunya da imani suna zozozo da juna. Idan babu ɗayansu, ɗayan ma ba za
    a same shi ba” (Buhari da Muslim ne suka ruwaito shi).

    Goyon Bayan Shan Giya

    Giya, kalmar suna ce da ke cikin jerin sunaye jinsin mata. Ita kuma nau’i ce da ake yi da hatsi ko alkama ko inibi wadda ake sha a yi maye. Ana kuma kiranta barasa, kamar yadda ƙamusan CNHN (2006 p.168) ya nuna. Shan giya a tsakanin al’ummar Larabawa kafin bayyanar Musulunci abu ne sananne. Shi ne ƙashin bayan doron ginin tattalin arzikinsu, kuma giya na daga cikin kayan fataucinsu.

    Har matansu sun kasance shahararru wajen haɗa ta. Hasali ma kowane gida akan
    same ta. Wannan ya sa har suna yabon giya a cikin waƙoƙinsu. Su ma al’ummar Hausawa ba a bar su a baya ba, domin sun mayar da shan giya musamman a lokuttan
    bukukuwan aure da na haihuwa tamkar ƙawa. Yayin da suka samu rabauta na karɓar addinin Musulunci, sai suka guje ta a sakamakon hanin da addinin ya yi gare su.

    Kasancewar Musulunci addini ne mai sauƙi da ke ƙunshe da dabarun magance abubuwan da ke haifar da fitsara da ta’addanci a tsakanin al’umma, sai ya fara bayyana wa muminai rashin kyanta. Daga nan kuma ya hana kusantar wurin ibada yayin da aka sha ta Daga ƙarshe ne kuma ya sauƙar da hani kai tsaye game da shan giya inda aka ce:
    “Ya ku waɗanda suka yi imani, ku sani cewa, giya da caca da gumaka da ƙyaurayen duba ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nisance su don ku rabauta
    (Alƙur’ani; 5:90).

    A wannan ayar an bayyana wa masu imani munanan ayyuka da ake buƙatar mumini ya nisance su. Kuma duk al’ummar da ta rungume su za ta faɗa cikin masifa da rashin kwanciyar hankali. Ayar ce kuma ta zo da haramcin shan giya kai tsaye. Akwai hadisai da dama da suka tabbatar da haramcin shan giya da kuma abin da ake kira da giya.
    Annabi S.A.W. yana cewa: “Duk abin da ke bugarwa giya ce, kuma kowace irin giya haramun ce” (Muslim ne ya ruwaito shi).

    A Wani Hadisin Kuwa Cewa Ya Yi: Allah ya tsine wa giya, masu shan ta, da waɗanda suka zuba ta, da waɗanda suka sai da ita, da waɗanda suka saye ta, da waɗanda suka tatso ta, da waɗanda suka ɗauki kayan da ake tatsarta, da waɗanda suke ɗauke ta, da waɗanda aka kai wa ita, da waɗanda suka samu kuɗi a gare ta” (Abu Dawuda, da Al-Hakem a isnadi ingantacce, suka kawo shi)

    Yayin da aka dubi waɗannan nassoshi, za a tarar cewa, ƙin bin su sau-da-ƙafa keta shara’ar Musulunci ne, wato fanɗarewa faɗar Allah da annabinsa ne. Duk da haka, an ci karo da waƙoƙin da suka yi kira da a sha gida. Alhaji Mamman Shata Katsina ya waƙe giya. Har ma cewa ya yi:

    Jagora: Ka ji karatun masu bugun ruwa, Waɗanda…
    ‘Y/Amshi: Ke zikiri a Kuloniya, A sha ruwa ba laihi ba ne.
    Jagora: A nan muke sallarmu ta Juma’a, Mu tattara kayanmu mu kai Neja, Ku sha ruwan nan…

    Y/Amshi: Ba laihi ba ne, A sha ruwa ba laihi ba ne.
    Jagora: Ruwa na kwalba ba laihi ba ne, Ai kun ga…
    ‘Y/Amshi: Alhaji Shata sha yake. A sha ruwa ba laihi ba ne.
    Jagora: Yara mu koma wasa Kuloniya, Mu tashi kana
    mu koma Neja,
    ‘Y/Amshi: Nan ne muke zikirinmu na Juma’a. A sha
    ruwa ba laihi ba ne.
    Jagora: Malam ka sha ai ba laihi ba ne, Ga taka ga tau…
    ‘Y/Amshi: Kowa ya aje. A sha ruwa ba laihi ba ne.

    Idan muka nazarci waɗannan ɗiyan waƙar za a ga yadda mawaƙin ya yi fito-na-fito da dokokin Allah da Manzonsa. Allah ya haramta, shi kuma ya halatta. Dubi yadda mawaƙin ya ce a sha giya ba laifi ba ne, bayan Annabi S.A.W. ya ce kada a sha, a inda yake cewa:
    “Kada ku haɗa fulawa da dabino gaba ɗaya, kuma kada ku haɗa busasshen tafarnuwa da dabino sam-sam, ku bar su idan an niƙa su.”

    Yayin da aka niƙa su, nan take suna bugar da wanda ya sha su. Don haka ne Annabi ya umarci masu imani da kada su sha a haɗe yayin da suke niƙe, kamar yadda Munhajul Muslimu Jadawali na uku: Abinci da Abinsha ya nuna. Hasali ma mawaƙin ya bayyana cewa shi ma yana shan giyar tare da yaransa. Akwai hadisai da dama da suka nuna haɗarin Musulmi ya mutu yana shan giya, ko da bai halatta ta ba.

    To ina ga wanda ya halatta shan ta? Daga cikin ire-iren waɗannan hadisai akwai wanda
    Ibni Abbas ya ce: Manzon Allah S.A.W. ya ce: Duk wanda ya mutu yana cikin ɗabi’ar shan giya bai tuba ba, zai tarar da Ubangiji Allah Maɗaukakin Sarki tamkar wanda ya bauta wa gumaka (Muslim ne ya ruwaito wannan hadisin).
    A wata waƙar ta mawaƙin da ake kira Horo/Horu, an ga baitukan da suka nuna ba laifi ba ne shan giya da ma cin mushe. Mawaƙin na cewa:

    Jagora: Arnaaa ku sha giya ku ci mushe, Aljanna mai rabo zai sama.

    A wani wuri kuwa, har ya nuna ma kashi ne ga mutum ya sha giya ‘yar kaɗan kuma ta wahalshe shi. Yana cewa:

    Jagora: Kowa ya sha giya yai yi amai, Ba ɗan halas ba ne, shege ne!
    Jagora: Su wane ‘yan giyan ƙarya ne, Shegu, kwalba guda take ka da su.

    Don karanta Tarihin Garin Rimin Gado danna nan

    Goyon Bayan Sata

    Abubakar (2015, p. 431) ya bayyana cewa, sata “tana nufin ɗaukar abin wani ba da saninsa ko izinin ba. ”Sata na nufin ɗaukar wani abu da hukuncin shari’a ko hankalin tuwo bai mallaka wa wanda ya ɗauka ba, tare da amfani da shi ko musanyensa da wani abu mai daraja kwatankwacin na kuɗi ko kuma mai amfanarwa, ba tare da izinin wanda ko waɗanda ke da mallakin abun ba.

    Sata ta kasu zuwa nau’uka daban-daban. Sun fi danganta da salon yadda aka gudanar da satan. Fitattu daga cikinsu sun haɗa da:
    i. Cuta
    ii. Damfara
    iii. Fashi
    iv. Fizge/Wabce/Fauce
    v. Ƙwace
    vi. Sane

    Sata babbar abar ƙyama ce a farfajiyar Hausa da Hausawa, tun ma kafin bayyanar addinin Musulunci. Sauyawan al’amurra da cuɗanyar Hausawa da baƙin al’ummu sun wanzar da taɓarɓarewar tarbiyya da ƙoƙarin neman tara abin duniya ido rufe. Ta kai ga
    fanɗararru marasa kishin kansu cikin al’umma sun tsunduma a fagen wannan ta’addanci.
    Yayin da addinin Musulunci ya bayyana a ƙasar Hausa, sai ya ƙara ƙarfafa wa Hausawa ƙyamar wannan muguwar sana’a.

    Musulunci ya zo da dokoki domin kawar da duk nau’o’in sata. Allah na cewa:
    Ɓarawo kuma da ɓarauniya sai ku yanke hannayensu ya zama sakamako ne na abin da suka aikata, (wannan horo ne) daga Allah. Allah kuwa mabuwayi ne Gwani. (Alƙur’ani, 5:38). A addinin Musulunci ta kowace fuska ana ƙoƙarin kare dukkanin al’umma ta yadda za a zauna cikin aminci game da dukiyoyi da rayukan al’umma.

    Ita kuwa sata, mugun hali ce da ke haifar da rashin kwanciyar hankali da salwantar rayuwa a tsakanin al’umma. Don haka ne shari’a ta tanadar da hukuncin yanke hannun
    ɓarawo wanda zai hana watsuwar irin wannan muguwar ta’asa a tsakanin al’umma [14]. Allah na cewa: “Kuma kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku ta hanyar cuta ”(Alƙur’ani, 2: 188).

    Ayar tana tabbatar wa masu imani cewa, cuta haram ce. Ba ya halatta ga Musulmi ya yi zalunci ta hanyar zaƙin baki ko dabara. Haka kuma, bai halatta ya yi jagora don a cuci wani ba. Duk da irin waɗannan dokokin da Allah Maɗaukakin Sarki ya shimfiɗa domin samar da kyakkyawan zamantakewa da aminci a doron ƙasa, an samu gungun mawaƙa da ke jayayya da dokokin cikin lafuzzan waƙoƙinsu.

    Bunza, (2014) ya kawo baituka da dama daga bakin Alhaji Muhammadu Gambo Fagada.
    Gambo ya bayyana ƙarara cewa:
    Jagora: Don Waɗanda ka sata nay yi ganga, Ba do wani sarki mai naɗi ba.
    (Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Tsoho Tudu)
    A cikin waƙarsa ta Nazaƙi kuwa, an ga yadda hirarsu ta gudana da Nazaƙi bayan ya tuba daga sata.

    Sannu a hankali har Gambo ya sake zuga shi yadda har sai da ya dawo satan. Gambon da kansa ya bayyana cewa:
    Ɓarawo in ina kusa ba tuba yakai ba,
    Ko ya aje gemu, ko ya yi saje,
    Ko ya fidda farin gashi ga kaina,
    In Gambo na kusa ba tuba yakai ba,
    Ba ko batun shegantaka ba.
    (Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Waƙar Nazaƙi)

    A wannan ɗiyan waƙa, sai da ya jaddada cewa, batunsa ba “batun shegantaka” ba ce kawai. Wato dai haƙiƙanin gaskiya yake faɗa cewa idan yana kusa ɓarawo ba ya tuba domin kuwa zai ziga shi ya hana shi tuban. Wasu makaɗan sukan yi waƙoƙin yabo ne ga
    ɓarayin. Misali Alhaji Mamman Shata ya yi wa wani ɓarawo mai suna Mamman Ɗan’yarbayye waƙa, a inda yake cewa:

    Jagora: Mai hannun taɓa ƙofa in an bacci,
    Masu samame baƙon Ɗanmani.
    Na faɗa maka Mamman.
    In dai ka ɗauko sa’a,
    Har ka buɗe ƙofa,
    Ka tarar an bacci,
    To zari akwati tsakiyar shi ya fi kaya.
    Na saman hoto ne,
    Na ƙasan maganin ƙwari ne.
    Tafi zari akwatin tsakiyar shi ya fi kaya.
    Na Abdu ƙyale dangi sai an bacci,
    Iyalin Mamman, waɗanda ba su so a yi haske,
    Su sun fi so a tabka duhu da ruwa yaf-yaf-yaf.
    Wani don ya taka kara bai mai ƙara ba,
    Sannan ganyen ganji duk ya bi ƙasa.
    (Alhaji Dakta Mamman Shata: Mamman
    Ɗan’yarbayye)

    A waɗannan ɗiyan waƙar, mawaƙin ya yabi ɓarawon tare da ba shi shawarar yadda zai gudanar da sana’arsa ta sata. Wannan ya haɗa da yi masa ishara ga irin lokuta da yanayi da dabarun da zai bi wajen yin satar, da kuma nau’in abin da zai sata da ya fi saura daraja.

    Hakan kuwa karan-tsaye ne ga dokokin addini. Hadisin Manzo (S.A.W.) ya bayyana cewa: “Ɓarawo ba ya sata a lokacin da yake da imani” (Buhari ne ya ruwaito
    hadisin). Allah Maɗaukakin Sarki ya kawo nau’in hukuncin da ya dace a zartar wa masu fashi da makami, a inda yake cewa:

    Ba wani abu ne sakamakon waɗanda suka yi wa (Musulmi masu bin) Allah da manzonsa fashi ba, kuma suke tafiya a bayan ƙasa da ɓarna ba, sai kawai a kashe su ko kuma a tsire su ko a yanke hannayensu da ƙafafuwansu a tarnaƙe, ko kuma a kore su daga ƙasa. (Yin) wancan ƙasƙanci ne a gare su a duniya, a lahira kuma suna da azaba mai girma. (Alƙur’ani, 5:33).

    Allah ya bayyana mana cewa masu yin fashi da makami suna ƙoƙarin ɓata tsarin Allah da Manzonsa ne, saboda aiwatar da fashi ya kauce wa hanyar gaskiya da adalci, waɗanda Musulunci ke ƙoƙarin tabbatar da su a doron ƙasa. 3.5 Goyon Bayan Kisan Kai Kisan kai na daga cikin manyan zunubai masu matuƙar muni a Musulunci. A cikin Suratul Nisa’i, Allah na cewa:

    Wanda kuma ya kashe mumini da gangan, to Jahannama ce sakamakonsa, yana madawwamini a cikinta, kuma Allah ya yi fushi da shi, ya kuma tsine masa, kuma ya
    tanadi azaba mai girma a gare shi (Alƙur’ani, 4:93).

    An jiyo Makaɗa Muhammadu Bawa Ɗan’anace ‘Yar Tsakkuwa, Gandi, Sakkwato yana ziga fitaccen ɗan damben nan Shago domin ya yi kisa. A cikin Bakandamiyar Shago, yana cewa:
    Bayarwa: Yanzu inai maka kuka,
    Ba kukan tuwo ba, Ba na hura ba…
    ‘Y/Amshi: Kukan Ɓaleri ya raga bayi, Suna kirarin banza.
    Bayarwa: Ɗan Abdu ko ga girbin
    ‘Y/Amshi: Gero, bara-bara ta na hana wake….
    A wani wuri yana cewa:
    Bayarwa: Ɗan Abdu kashe mutum a gafarta ma. Ɗan Abdu…
    ‘Y/Amshi: Kashe mutum a gafarta ma.
    (Muhammadu Bawa Ɗan’anace: Bakandamiyar Shago)

    Ba za a ce maganar kisa a nan ta taƙaita ga buge mutum a dambe ba kawai. Ya haɗa da kashewa har lahira. Hakan zai ƙara tabbata yayin da aka yi la’akari da lafuzza da ya riƙa amfani da su cikin waƙar da suka haɗa da:
    i. Kusheyi
    ii. Lahira a kai miki gawa
    iii. Lahira tana yin baƙo
    iv. Uwar mutum ta haifi wani, da sauransu.

    Gambo ma ya yi makamanciyar zigar nan inda yake ziga inda yake cewa:
    Bayarwa: Duw wanda ya ishe mai kuɗi lahiya lau,
    Ya yi sata yab bar mai kuɗi da rai nai,
    In yaz zaka Allah ya isam min za ni ce mai,
    Don wagga ba sata ta ba Gambo.
    (Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Waƙar Kashe Mace)

    A nan, ko bayan ziga zuwa ga yin sata, mawaƙin ya nuna cewa satar ba ta cika har sai an yi kisan kai. Wannan kuwa fanɗarewa ne daga koyarwar addinin Musulunci.

    Goyon Bayan Kisan Kai

    Kisan kai na daga cikin manyan zunubai masu matuƙar muni a Musulunci. A cikin Suratul Nisa’i, Allah na cewa: Wanda kuma ya kashe mumini da gangan, to Jahannama ce sakamakonsa, yana madawwamini a cikinta, kuma Allah ya yi fushi da shi, ya kuma tsine masa, kuma ya tanadi azaba mai girma a gare shi (Alƙur’ani, 4:93).

    An jiyo Makaɗa Muhammadu Bawa Ɗan’anace ‘Yar Tsakkuwa, Gandi, Sakkwato yana ziga fitaccen ɗan damben nan Shago domin ya yi kisa. A cikin Bakandamiyar Shago, yana cewa:
    Bayarwa: Yanzu inai maka kuka,
    Ba kukan tuwo ba, Ba na hura ba…
    ‘Y/Amshi: Kukan Ɓaleri ya raga bayi, Suna kirarin banza.
    Bayarwa: Ɗan Abdu ko ga girbin
    ‘Y/Amshi: Gero, bara-bara ta na hana wake….

    A wani wuri yana cewa:
    Bayarwa: Ɗan Abdu kashe mutum a gafarta ma. Ɗan
    Abdu…
    ‘Y/Amshi: Kashe mutum a gafarta ma.
    (Muhammadu Bawa Ɗan’anace: Bakandamiyar Shago)

    Ba za a ce maganar kisa a nan ta taƙaita ga buge mutum a dambe ba kawai. Ya haɗa da kashewa har lahira. Hakan zai ƙara tabbata yayin da aka yi la’akari da lafuzza da ya riƙa amfani da su cikin waƙar da suka haɗa da:
    i. Kusheyi
    ii. Lahira a kai miki gawa
    iii. Lahira tana yin baƙo
    iv. Uwar mutum ta haifi wani, da sauransu.

    Gambo ma ya yi makamanciyar zigar nan inda yake ziga inda yake cewa:
    Bayarwa: Duw wanda ya ishe mai kuɗi lahiya lau,
    Ya yi sata yab bar mai kuɗi da rai nai,
    In yaz zaka Allah ya isam min za ni ce mai,
    Don wagga ba sata ta ba Gambo.
    (Alhaji Muhammadu Gambo Fagada: Waƙar Kashe Mace)

    A nan, ko bayan ziga zuwa ga yin sata, mawaƙin ya nuna cewa satar ba ta cika har sai an yi kisan kai. Wannan kuwa fanɗarewa ne daga koyarwar addinin Musulunci.

    Hani Ga Bautar Ubangiji

    Ko bayan kira zuwa ga aikata ɓarna da fasadi, akwai misalan ɗiyan waƙoƙi kuma da ke kira ga barin bautar Ubangiji. Na biyu a cikin shika-shikan Musulunci ita ce salla. Tana da matuƙar muhimmancin da har ya kasance kadarko tsakanin mutum da kuma shirka da
    kafirci. Duk da haka, sai ga ɗiyan waƙa da ke hani ga yin salla:

    Bayarwa: Ɗan Abdu ban da sallas swahe,
    ‘Y/Amshi: Domin yawan sallan nan yana rage maka ƙarhi.
    (Muhammadu Bawa Ɗan’anace: Bakandamiyar Shago)

    Sakamakon Bincike

    Ta la’akari da nassoshin Alƙur’ani da Hadisan Annabi S.A.W. da kuma ƙumshiyar wasu waƙoƙin baka na makaɗan Hausa, za a a iya cewa, mawaƙa na wuce gona da iri a waɗansu lokuta. Yawanci hakann na faruwa ne yayin da suka yi ƙoƙarin adanta waƙoƙin nasu domin burge wanda aka yi wa waƙar da kuma sauran masu nsauraro.

    A haka ake samu ɗiyan waƙoƙin sun yi wa dokokin Musulunci karan-tsaye. A wannan nazarin an fahimci cewa duk wani aikin da ɗan’adam ya aikata wanda Allah da manzonsa
    suka yi hani da shi, yin haka nau’i ne na fanɗare wa dokokin Allah. Ya zama tilas kowane Musulmi ya nemi ilimin duk wani lamarin da ya shafi rayuwarsa, (kamar yadda mai Ahalari ya bayyana) don gudun auka wa fushin Ubangiji.

    An kuma fahimci cewa, a Musulunci kowane irin al’amari an ɗora shi a kan mataki-mataki. Wannan ne ya wajabta wa kowane Musulmi ya yi umurni da aikata alheri da kuma hani ga mummunan aiki gwargwadon ƙarfin ikon mutun.

    Kammalawa

    Yin fice da waƙoƙi suka yi wurin ilimantarwa da faɗakarwa da nishaɗantarwa, ba shi ke nuna ba a samun fanɗarewa a cikinsu ba. Nau’ukan fanɗarewa da ake samu cikin waƙoƙin Hausa sun shafi ziga zuwa aikata abin da Ubangiji ya hana, ko izgilanci ga
    abubuwan da Musulunci ya zo da su, ko kuma hani ga abin da Ubangiji ya yi umarni da a aikata.

    Abu ne mai kyau manazarta su riƙa zaƙulo ire-iren fanɗarewa da ake samu a cikin waƙoƙi domin faɗakar da al’umma da su kansu mawaƙan. Malamai da ke jagorantar nazarcenazarcen waƙoƙi a makarantu kuwa, ya kamata su mayar da hankali wajen yin shiri na musamman na faɗakar da ɗalibai ta fuskokin da suka dace yayin da aka ci karo da ire-iren baitukan fanɗarewa a cikin waƙoƙin da suke nazarta.

    Gwamnatoci da hukumomin da abin ya shafa ma na da rawar takawa wajen samar da ƙa’idoji da tsaretsaren tace waƙoƙi kafin sakinsu. Haɗakar waɗannan za su tabbatar da al’umma ba ta rinjayu da kiraye-kirayen waƙoƙin fanɗara ba zuwa taɓewa.

    MANAZARTA

    • Abba, M., & da Zulyadaini, B. (2000). Nazari kan
    waƙar baka ta Hausa. Gaskiya Corporation Limited.
    • Abubakar, A. (2015). Ƙamusun Harshen Hausa.
    Zaria: Northern Nigeria Publishing Company LTD.
    • Al-Munajjid, M. S. (2004). Muharramat: Forbidden
    matters same people take lightly. International
    Islamic Publishing House, Saudi Arebia.
    • Bunza, A. M. (2014). In ba ka san gari ba saurari
    daka: Muryar nazari cikin tafashen Gambo Elkods
    Printing Hausa.
    • Chiromawa, U. A. U. (n.d.). Dalilin kiɗa a cikin
    Alƙur’ani da hadisi.
    • Gusau, S. M. (1984). Nazarin zaɓaɓɓun waƙoƙin
    makaɗan baka na Hausa, littafe na ɗaya.
    • Ibrahim, M. S. (1983). Kowa ya sha kiɗa. Longman
    Nigeria Limited.
    • Magaji, A. (2016). Kassu Zurmi da waƙoƙinsa.
    Spectrum Books Limited.
    • Muhammad, Y. M. (2005). Adabin Hausa. Ahmadu
    Bello University Press Limited.
    • Sani, A. U., & Jaja, M. B. (2019). Zamani Riga:
    Akalar Magungunan Gargajiya a Hannu Addini da
    Zamani. In The Nasarawa Journal of Humanities, 7,
    (1-2), 257-268. ISSN: 1118-6887.
    • Shehu, M., & Sani, A. U. (2019). Intra-Religious
    Conflicts within the Hausa Hausa-folk. In EAS
    Journal of Humanities and Cultural Studies, 1(3),
    145-150. ISSN: 2663-0958 (Print) & ISSN: 2663-
    6743 (Online) Available at:
    https://www.easpublisher.com/get-articles/344.
    • Umar, M. B. (1987). Dangantakar adabin baka da
    al’adun gargajiya. Kamfanin “Triumph” Gidan
    Sa’adu Zungur

    Danna nan don karanta Nazarin Hanyoyin Adana Kayayyakin Hausawa Na Gargajiya

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Budurwa Marar Tabo

    Tatsuniyar Budurwa Marar Tabo

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata yarinya kyakkyawa, wadda ko tabo ɗaya babu a jikinta. Shi ke nan, sai ta ce ita fa ba za ta auri wanda yake da tabo ko da ɗaya ne tak a jikinsa ba. Manema wannan ya zo, wancan ya zo, amma duk suna da tabo.

    Ana nan, sai ga wani saurayi wai shi Ɗandisheri wanda ba shi da tabo a jikinsa, in ban da wani ƙarami a kan ɗan yatsansa, shi ma ya je saran itace ne ya yi sartse. Da ya je, sai ta ce ba ta son sa. Ya haƙura.

    Rannan sai wani maciji ya ji labarin halin wannan budurwa, ya gayawa abokansa, suka rikiɗa suka zama mutane samari kyawawa, waɗanda ba ɗaya daga cikinsu wanda yake da tabo ko ɗaya a jikinsa. Sai suka je wurinta, ta bincike kowannensu sarai, ta ga babu tabo a jikinsa.

    Nan take ta ce ta yarda ɗayansu ya aure ta. Aka taru aka ɗaura aure da ɗayansu. Shi ke nan ta tattara kayan ta suka tafi da amaryarsu. Da suka je jeji sai suka ce: “Yawwa mun iso gida.” Ita ko tace: “Ina gidan a nan?” Sai suka ce da ita: “Ai nan ne gidan. Amarya ta yi zuru-zuru, babu yadda za ta yi domin ta riga ta auri ɗayansu.

    Kuma ga shi sun kai ta dokar daji, inda ba za ta iya komawa gari ba. Daga nan suka saka ta a kogon bishiya, suka rikiɗe macizai suna lasar jikinta har ta zama fara fat, babu kyan gani, kuma abin ƙyama. Ana nan kwanci-tashi har ta sami ciki. Bayan wani lokaci mai tsawo, sai wata rana Ɗandisheri suka yi ƙarancin ciyawar akuyarsu, sai ya tafi can cikin ƙungurmin jeji yana yankan ciyawa.

    Sai matar macizai ta hango shi, ta fara rera masa waƙa tana cewa:

    “Ɗandisheri – Ɗandisherina,

    Ɗandisheri ƙanin Babati.

    Idan ka je gida ka gai da iyata,

    Idan ka je gida ka gai da Babati.

    Ni mai zaɓar maza babu tabo,

    Ga ni yau a kogon kukati,

    Maciji na lasa ta mulai,

    Kunama na harbi na mulai.

    “Sai Ɗandisheri ya ɗau waƙa, ya amsa mata yana cewa:

    Ina ruwan Ɗandisheri,

    Daga fari ke aka bai wa ni,

    Daga gani sai kika raina ni,

    Domin tabon ɗan yatsana.

    Da ya je gida sai ya gaya wa iyayenta halin da take ciki. Da suka ji labari, sai suka yi shiri domin su je su gani. Da suka je sai suka same ta a cikin kogo. Suka rasa yadda za su fito da ita. Dole aka sare bishiyar, aka fitar da ita, iyayen suka tafi da ita gida.

    Daga baya ta haifi ɗa namiji, rabin jikinsa ɗan mutum, rabi ɗan maciji. Da mazanta macizai suka ji ta haifu sai suka ƙara zama mutane, suka zo karɓar ɗansu. Da suka isa gidan, sai danginta suka tona makeken rami, aka shimfiɗa musu tabarma a kai, aka kuma hura wuta a ƙarƙashi, aka yi wa ɗansu wanka aka yi masa kwalliya aka kira su, suka zauna suka karɓi ɗansu.

    Suna cikin hira sai su ji ‘nyas-nyas,’ sai suka ce: “Kai akwai abin cizo a gidanku?” Masu gida suka ce: “E wallahi. Jim kaɗan sai tabarma da yayin suka kama wuta, su da shimfiɗar suka faɗa cikin wutar. Yayin da suke ƙonewa sai suka wurgo yaron sama, aka cafe shi, aka ƙara wurga musu, haka dai suka yi ta yi har suka ƙone rumus da su da ɗansu.

    Da ba domin Gizo ba da na yi muku ƙarya. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Mai ruwan ido gama kasuwa da yawo.
    • Jiki magayi.
    • Ƙarya fure take ba ta ‘ya’ya.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Jarumin Sarki

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Jarumin Sarki

    Tatsuniyar Jarumin Sarki

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wani jarumin sarki wanda a fagen yaƙi ba ya ja da baya. Duk inda ya sa gaba sai ya sami nasara. Yana da mata uku: amaryarsa kitse ne, sauran kuma mutane ne. To Sarkin nan ya fi son Takitsen. Duk lokacin da zai je yaƙi sai da ita yake tafiya.

    Ana nan, sai wata rana wani yaƙi mai haɗari da zafi ya taso. Sai ya yanke shawarar cewa wannan yaƙin ba irin wanda zai je da mata ba ne. Amma kuma yana tsoron barin amaryarsa a gida. Da sauran matansa biyu suka ji haka, sai suka ce ya bar ta a gida, babu komai za su kula da ita kamar yana nan.

    Sai ya amince da alƙawarin da suka yi, ya hau shi da barade suka dunguma zuwa filin daga, ya bar amaryarsa a gida. Bayan tafiyar Sarki sai matan nan suka sa amarya girki. Tana nufar murhu sai ta narke saboda zafin wuta. Ganin haka fa sai suka fara kuka, suna cewa: “Takitse ta narke ta zama ruwa.

    “To daman akwai wani tsuntsu a gidan Sarki. Da ya ji abinda matan Sarki suke faɗa a cikin kuka, sai ya tashi ya nufi wajen yaƙin, yana cewa;

    Sarki. Sarki. Sarki ka mai da yaƙi baya,

    domin Takitse ta narke ta zama ruwa.

    Haka ya yi ta yi, har Sarki ya kasa kunnensa, ya ji ana cewa ya bar yaƙi ya koma gida, domin matansa suna can a gida suna yin kuka. Fadawa da baraden Sarki ma suka tsaya, suka ji abin da tsuntsu ke cewa. Sai ya tambaye su abin da suka ji daga bakin tsuntsu, sai suka ce, ai Takitse amaryarsa ce ta narke.

    Nanda nan Sarki ya karya linzami, aka koma garinsa. Da ya isa fadar, sai ya shiga cikin turakarsa, ya sa Jakadiya ta kira matan, ya dube su ya ce: “Wace ce ta sa Takitse girki?” Sai matar Sarki tatsakiyarta yi farat ta ce: “Uwar gida ce. A fusace, Sarki ya umarci dogarawa su sare mata kai. Nantakesuka fille mata kai. Ba a wasa da umarnin Sarki. Kurunkus.

    Abubuwvan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Karya al kawari cin amana ne.
    • Soyayya amanar zuciya

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Ɗankaɗafi

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tarihin Garin Kudan 2

    Tarihin Garin Kudan 2

    BABI NA HUƊU

    Rana ta fara haskawa a sararin samaniyar garin Kudan, tamkar zinaren take  ɗauke da albarkatu. Mutane sun tashi suna jin wani sabon ɗumi a zuciyarsu, ɗumin da ake ji, idan aka ga alheri yana gab da farawa. Kamar yadda ake cewa:

    “Idan gari ya fara motsi, ko tsuntsaye sukan san akwai abun da ake nema.”

    A wannan rana an fara da al’amura guda  uku:  tsaro, haɗin kai, da bunƙasar arziki. Wannan shi ne ginshiƙan sabon ginin da aka fara a Kudan.

    1. Dabarar tsaro (Jagorancin haziƙan mutane)

    A ƙofar kasuwar Kudan, matasa sun taru ƙarƙashin jagorancin Salmanu Faris da Nuhu Baushe, Nawalmu da Garba Ode. Sun kafa Kudan Community Watch, wata ƙungiya da ta haɗa matasa masu kishin gari.

    Salmanu ya tsai da kansa a gaban jama’a ya ce:

    “Tsaro ba na gwamnati kaɗai ba ne. Tsaro tamkar alwala ne, kowa ya tsarkake nasa ɓangaren.”

    Nuhu Baushe, fitaccen mafarauci mai hikima, ya ƙara da cewa:

    “Mutum da ke iya bin sawu a daji, ba zai kasa gano matsala cikin gari ba.”

    Sun rarraba matasa zuwa rukuni-rukuni:

    1. Rukuni na dare, ‘yan sintiri masu bin layi har da mafarauta.

    2. Rukuni na kasuwa,  waɗanda ke kula da kasuwar gari.

    3. Rukuni na hanya, masu taimakon mata da yara wajen tsallaka tituna, musamman a lokacin cankuso.

    Garba Ode, wanzamin gari, ya zama mai lura da lafiyar matasa. Kullum yana cewa:

    “Idan ka so ka yi gudu mai nisa, to ka ci gaba lafiya.”

    Mutane suka ji daɗi, suka fara hango kwanciyar hankali.

    A farfajiyar babban masallacin Juma’a na Kudan, malamai suka fara gudanar da babban taron da ya tattara ɗalibai, matasa da manya. Malam Aliyu ya tashi ya fara magana cikin nutsuwa:

    “Haɗin kai tamkar tukunya ce; ko an yi girki mai daɗi, ba za ku ci ba , dan tukunya ta karye.”

    Daga nan malamai suka kafa shirin da suka kira “Tattalin Zumunci” , inda kowane gida zai ziyarci wani gida a kowane mako, domin sada zumunta. Wannan ya rage rigingimu da rashin fahimta. Sannan kuma duk Alhamis ɗin ƙarshen wata, malamai zasu dunga taru wa a masallacin Juma’a na cikin gari, don yin musaffa tare da addu’o’in zaman lafiya da ci gaban gari.

    Mal. Auwal da Mal. Salim suka shigo da darussan boko, cewa matasa su koyi rubutu, fasaha, kimiyya da ilimin zamani. Suna yawan cewa:

    “Karatu shi ne ido, idan ka rasa shi, koda kana da ƙafa za ka yi tafiya cikin duhu.”

    Malam Abdulhafiz ya koyar da matasa dabarun tattaunawa da sauraro.

    Malam Yasir ya koyar da “Tsarin gina gari ga matasa”.

    Malam Salisu ya shigo da dabarun zama lafiya.

    A hankali, mutane suka fara fahimtar cewa:

    Haɗin kai ba maganar baki ba ce. Aiki ce.

    BABI NA BIYAR

    A kasuwar Kudan, ana ta hayaniya cikin nishaɗi. Abubakar mai kamfanin shinkafa ya kawo sabuwar na’urar tacewa. Ya ce:

    “Shekara da yawa muna da fili, kuma muna samun amfanin gona mai yawa, amma ba mu da fasahar sarrafawa ta zaman, wacce za ta tace mana kayan amfanin gonan mu cikin sauƙi da kuma tsabta”.

    Nan take sai ya ɗauki matasa 25 suka zama ma’aikatansa, mata 10 suka zama masu tace shinkafar da aka noma, sauran mutane 15 kuma masu noma kayan amfanin gona gami da samar da taki mai inganci.

    Muzammil da Mas’ud suka haɗa ƙungiyar mazauna garin da ke noma.

    Nafi’u da Isma’il suka fara shirin Noman Zamani da amfani da injina.

    Mutane suka fara jin cewa tattalin arziki zai farka daga sumar da ya yi. Kasuwa ta zama wuri mai cike da motsi.

    Mutum ya je kasuwa ya ji ana cewa:

    “Kudan ta tashi, Wallahi Kudan ta tashi tamkar aure da ya zo da annuri.”

    Ƙungiyar Mawaƙa

    A gidan Labaran Adamu, aka yi zaman mawaƙa. Su Ashiru, Salahu, Ali Na Annabi da Rabilu sun rubuta sabuwar waƙa mai taken: “Uban arziki ”

    Waƙar ta kama hankalin mutane sosai. A cikin baitocin waƙarsu akwai karin magana mai zurfi:

    “Idan rana ta fito a gefenku, kada ku ce ba ku dace ba, ku tashi ku yi aiki.”

    Wannan waƙa ta zama tamkar tutar motsa zuciyar al’umma.

    Daga Ƙarshe

    Yayin da rana ta doshi yamma, mutane suka tsaya a kan ƙaramin tudu suka kalli hasken rana tana faɗuwa. Kamar furen da ya buɗe, zukatan al’umma suka yi fari.

    Farfesa Mu’azu ya tsaya ya ce: “Daurin mu a yau ya zama ginshiƙin gobe. Idan mu ka dage, Kudan zata zama abin koyi.”

    Salmanu Faris ya ce: “Gari ba ya giɓi idan kowa ya ɗora nasa tubalin.”

    Mutane suka ce gaba ɗaya: “Mu tashi, mu gina Kudan! Don tuƙa Tuwon gobe lafiya”.

    Yayin da tashin hankali ya fara raguwa

    A kwanakin da suka biyo baya, garin Kudan ya fara samun nutsuwa fiye da da. Ayyukan Salmanu Faris da tawagarsa: Nuhu Baushe, Nawalmu da Garba Ode, sun riga sun bazu a cikin gari kamar wutar daji a zukatan mutanen gari. Kowa ya fara kallon gaba, domin an fara ganin tabbas gari ya fara komawa bisa turba.”

    A daren ranar Asabar, bayan taron tsare-tsare da suka gudanar a unguwar Kintonho , suka fito suna tafiya cikin farin wata mai haske. Kamar yadda Hausawa ke cewa:

    “Idan dare ya yi tsawo, sai ya kai ga wayewar gari.”

    Wannan kenan. Wayewar gari ta kusa.

    Ginin Sabon Masallacin Juma’a

    Washegari da safe, jama`a suka taru a babban fili yayin da ake ƙaddamar da ginin babban Masallacin Juma’a da Rt. Hon. Isa Ashir ya ɗauki nauyi. Ya yi wani jawabi wanda ya cika zukatan mutane:

    “Garin da ya rasa tsaro, ya rasa komai. Amma garin da ya nemi ilimi, tarbiyya da haɗin kai, to ya kama sahun cigaba.”

    Sadaukarwarsa ta ja hankalin kowa. Salmanu ya kalli masallacin yana murmushi. Ya ce a zuciyarsa:

    “Ginin masallaci ba katanga ba ce kaɗai. Gina zuciyar al’umma ne.”

    Makarantar Sana’o’i ta Tashi Tsaye

    Ranar da suka fara shigar da kayan aiki makarantar koyon sana’o’i, sai yaran gari suka yi tsalle da murna. Wani yaro mai suna Zailani Sambo ya ce:

    `Wallahi zan koyi gyaran waya in taimaka wa iyayena!”

    Nawalmu ya yi murmushi yace:

    `Ai haka ake so! Sana`a kamar garkuwa ce, mai shi baya jin yunwa.

    Bisa ga dalilin haka,sai aka samar da wasu rassa kamar: gyaran lantarki, ɗinki, walda, girki da fasahar kwamfuta. Gari ya fara cika da hayaki na cigaba, ba na rikici ba.

    Makarantar ƴan Sanda (Police Academy)

    Garba Ode, wanda ke da ƙwarewa a ilimin ladabtarwa, shi ne aka ba alhakin tsara tsarin horo. Ya ce wa Salmanu:

    “In an so zaman lafiya, dole a gina jami’an tsaro masu hankali, ba masu daga bindiga kawai ba.”

    A can an samar da aji-ajin koyar da:

    1. Magance rikici.

    2. Dabarun tattaunawa.

    3. Kare haƙƙin ɗan adam.

    4. Sahihiyar bincike.

    Ginin ya zama tamkar wuta da ake iya ganin hasken ta daga nesa.

    Asibitin shakatafi (Primary health care)

    Rt. Hon. Isa Ashir ya kuma aika injina da ma’aikata wurin gina sabon asibiti, domin ya ce:

    “Ba tsaro ba tattali idan babu lafiya.”

    An kafa sashen haihuwa, daakin tiyata, da ɗakin taimakon gaggawa. Dattawa suka yi addu’a, mata suka yi hawaye na farin ciki. A wurin ƙofar asibitin wani dattijo ya ce:

    “ Turakun gari sun fara zama.”

    BABI NA SHIDA

    Matasa kuwa sun yi murna fiye da kowa da ginin filin ƙwallo na zamani. A ranar da aka fara dasa harsashin ginin wajen,ɗaruruwan mutane suka taro a wajen, don murna.

    Nuhu Baushe ya ce:

    “Matasa da ba su da abin yi, fitina na kiransu. Amma idan ka basu filin wasa,ka rage yawan ɓarna.”

    Filin ya zama wajen taron matasa, wuri mai ɗauke da annashuwa maimakon hayaniyar rikici.

    Sabon Tituna,

    An fara shimfiɗa tituna masu faɗi a manyan lunguna. Hakan ya sauƙaƙa zirga-zirga, ya hana ‘yan fashi yin ƙwanton-bauna.

    Salmanu ya ce lokacin da suka tsaya kallon injinan da ke aiki:

    “Idan ka gyara hanya, ka gyara zuciya. Domin hanya ta haɗa ɗan Adam da ɗan Adam.”

    Nawalmu ya ƙara da cewa:

    “Hakika! In aka samu hanya, ko rikici na iya tserewa!”

    Yayin da rana ta faɗi kan sabbin gine-ginen da suka ƙawata garin Kudan, Salmanu Faris ya kalli Nuhu Baushe, Nawalmu da Garba Ode, sai ya ce:

    “Haɗuwar al’umma waje ɗaya, da shawo kan rikic, shi ne jigon abin da zamu sa a gaba. Mu ci gaba, kar mu tsaya.”

    Gari ya yi shiru mai cike da salama. A cikin wannan shiru akwai wata magana ta gargajiya da ta dawo masa daga zuciya:

    “Gari da alheri ya bunƙasa, ko tsuntsu na leƙen damar zama.”

    Wɗancan dalilai sun sa garin Kudan ya samu cigaba fiye da shekarun baya. Saboda garin ya kafu shekaru ɗari biyu tun kafin jihadin Usman Ɗanfodiyo, wato a ƙarni na goma sha huɗu, wanda a yau (2025) garin ya samu shekaru ɗari shida da ashirin da biyar da kafuwa (625).

    A makonnin da suka biyo baya, sabuwar duniyar Kudan ta fara bayyana a fili. Mutane suna yawo cikin kwanciyar hankali, yara na wasa a sabbin tituna, mata na fita kasuwa cikin kwanciyar hankali, dattawa na zama ƙarƙashin inuwa suna tattaunawa da nishaɗi.

    A wani yammaci, Salmanu Faris ya tsaya a saman wani ɗan tudu yana kallon garin. Yana jin wani irin shauƙi da jin daɗi a zuciyarsa. Nuhu Baushe ya taho daga baya ya ce masa:

    “Kai Salmanu, garin nan ya zama abin kallo! Haka ake so, idan rawani ya yi kyau, sai a yabawa mai ɗaure shi.”

    Salmanu ya yi murmushi:

    “Mu dai mun yi niyya ne, Allah ya daidaita. Kowa ya bada gudunmawa.”

    A kwanakinnan, an ga wani sabon yanayi na haɗin kai wadda ba a saba gani ba.

    Matasa suna taimakon juna wajen tsaftace titi. Mata suna koyon sana’o’i a makarantar horo. Dattawa na bada shawarwari a majalisa.

    Kowane yanki na gari yana kama da sabon fure da ya fara buɗewa.

    Ƙofar Arewa, Ƙofar Gabas, Ƙofar yamma (Kintonho), Ƙofar yamma ko Zaria.

    Har’ila yau, kuma an kafa kwamiti na kowace unguwa, don tabbatar da tarbiyyar yaran unguwar gami da warware matsalolin zamantakewar auratayya. Waɗancan unguwannin sun haɗa da: Unguwar Makera (farfaru), unguwar Maƙera (babbaƙu), Ƙofar Arewa, Saidawa, Unguwar Zaɓi, Ƙofar Gabas, Unguwar Liman, Unguwar Bela, Juga (Kintonho), Yan Gishiri, Unguwar Malamai, Unguwar Ƴan Takalma, Tudun Wada, Ƙofar Fada, Sabon garin Kudan, Unguwar Malam Talatu, Rimin Baima, Kuka, Tartibu, Unguwar Tsauni, Unguwar Ma’aji, tsohuwar Kasuwa, Shagari Quarters da sauransu.

    Garba Ode, wanzamin gari kuma ɗaya daga cikin shugabannin ci gaban al’umma, ya tsaya gaban jama’a a kasuwa ya yi magana cikin hikima:

    “Idan mutum ya ceci mutum guda, tamkar ya ceci duniya ne. Mu ci gaba da taimakon juna ko kaɗan ne. Da kaɗan-kaɗan ne ake tara tsaba a rumbu.”

    Kowa ya yi dariya, domin Garba Ode yana da hikima mai fara’a.

    Ginin masallacin Juma’a, asibiti, makarantu da tituna sun ba mutanen Kudan sabon yanayi. Mutane suna yawan cewa:

    “Ashe idan mutum mai hangen nesa yana mulki, gari ya kan yi kyau kamar hatsi a kwando!”

    Rt. Hon. Isa Ashir ya sake ziyartar wuraren da ake gine-gine. Yara suka ruga suna ta murna suna kiran sunansa. Ya tsaya ya ce:

    “Na gina gine-gine, amma ku kun gina haɗin kai. Ku ne jarumai.”

    Kalmar nan ta sanya mata da maza yin kabbara da farin ciki.

    A wata laraba, an gayyaci Salmanu Faris zuwa babban taron Majalisar ci gaban Kudan.

    Duk jama’a suna jiran jin me za a ce masa.

    Shugaban majalisa ya miƙe ya ce:

    “Mutumin da ya jagoranci zaman lafiya, ya haɗa matasa, ya haɗa dattawa, ya ƙarfafa tsaro, ya samar da cigaba, ba wanda ya cancanci yabo kamar Salmanu Faris.”

    Jama’a suka yi tsalle da tafi.

    Salmanu ya miƙe cikin ladabi. Ya ce:

    “Na yi abin da na iya ne kawai. Gari ba na mutum guda ba ne, gari tamkar tabarma ne, kowa zai iya samun zama.”

    Jama’a suka amsa da cewa:

    “Hakane! Gaskiya ka faɗa!”

    Wannan dare, a ƙofar masallacin Juma’a, an shirya liyafar godiya. An kunna fitilu, yara suna murna, matasa suna ta kabbara.

    An miƙa kyaututtuka ga jarumai uku na gari:

    1. Nuhu Baushe, saboda tsayuwar tsayin dakan da ya nuna wajen kare jama’a.

    2. Nawalmu, saboda hikimarsa gami da ƙwazon, wajen bincike gami da tabbatar da zaman lafiya.

    3. Garba Ode, saboda basirarsa da kuma ƙwarewarsa wajen ladabtar da mutanen marasa jin magana.

    Dukkaninsu sun yi jawabi ɗaya bayan ɗaya.

    Nuhu Baushe ya ce:

    “Rana ɗaya bata ƙona duka jirgi, haka rikici ba zai ɗauki gari gaba ɗaya ba idan muna tare.”

    Nawalmu ya ce:

    “Hikima tamkar haske ce; idan ka kunna ta, duhu ya gudu.”

    Garba Ode ya yi dariya ya ƙara da :

    “Ai ni Garba Ode, na saba da aiki da mutane. Idan kana so su nutsu, ka fara nutsuwa da kanka.”

    Jama’a suka yi banƙwana da dariya.

    Fitilu suna haske, tituna suna sababbi, masana’antu sun tashi, gidaje sun gyaru, kasuwa ta bunƙasa, matasa na neman ilimi da sana’a.

    A hankali, mutane na ko’ina suna cewa:

    “Kudan ta dawo.”

    Salmanu ya tsaya gefe yana kallon wannan canji. Yana jin kamar an saka masa nauyin al’umma a kafaɗarsa, ba nauyi mai wahala ba, amma na alfahari.

    Ya ce a zuciyarsa:

    “Idan mutum bai yi wa gari ba, gari zai yi masa.”

    Saboda haka ya yi addu`a:

    “Allah ka saka da alheri, ka dauwamar da zaman lafiya.”

    Fitilar gari ta haska fuskarsa, kamar wani sabon jarumi da zai ci gaba da jagorantar al`umma zuwa gobe mai haske.

    Salmanu Faris, ya tashi tsaye cike da murna. Sannan yace ” al’ummar wannan gari mai albarka, na shirya wata waƙa, don taskance unguwanninmu da kuma wasu ayyuka na mu”. Ga waƙar nan kamar haka:

    1.

    A ƙasar Kudan mai daraja, mai farin taurari a samanta,

    Tarihi ya haɗa ƙofofi huɗu, kowacce na ɗauke da alherinta,

    Ƙofar Arewa mai kwanciyar hankali da nutsuwa babu tata,

    Ƙofar Gabas mai mazan jiya, uwa ce ga arziki da rabonta.

    2.

    Ga Ƙofar Yamma, wurin jarumai tun kaka da kakanta,

    Zaria ce ta gefe, mahaɗar ilimi da sadar da zumunta,

    Duk mai shiga sai ya ji ƙamshi mai daɗi daga gadonta,

    Kofofi mai tarihi, wanda ba ta gushewa har lokacinta.

    3.

    Makera farfaru,masu fasaha tun da, fitila ce ga sana’arta,

    Makera babbaƙu, masu hikima wanda ba sa yin gorinta,

    Saidawa da Zaɓi, unguwanni masu sana`a da himmata,

    Unguwar Liman, Bela, da Juga,suna ɗauke da kamalarta.

    4.

    Yan Gishiri, unguwar arziki, mai ƙara armashi a miyarta,

    Unguwar Malamai, maɓuɓɓuga ilimi, haske ke iliminta,

    Unguwar Ƴan Takalma, ƙwararru ne masu zaratar fata,

    Tudun Wada da Ƙofar Fada, wuraren mutunci da nagarta.

    5.

    Sabon Gari, sabuwar duniya mai ci gaba da inganta.

    Rimin Baima, Kuka, Tartibu, kowacce tana da hikimarta,

    Unguwar Tsauni da Ma’aji,wuraren tarihi masu basirarta,

    Tsohuwar Kasuwa da Shagari Quarters, wurare masu limanta.

    6.

    An kafa kwamiti a kowanne yanki, don lafiya ta tabbata,

    Tarbiyyar yara, warware matsalolin aure ban da salwanta,

    Dattawa da dattijuwa na ba da shawara cikin tafiyarta,

    Domin ƙauye ba na mutum ɗaya ba ne,” don cigabanta.

    7.

    Salmanu Faris ne ya tsara wannan waƙa mai nagarta,

    Domin tunatar da sanin darajar unguwanni da ƙauyenta,

    Duk inda ka juya, alheri yana haskawa tamkar alfijir a wajenta,

    Allah Ya kare Kudan, Ya tsare ta da kwanciyar hankalinta.

    BABI NA BAKWAI

    Washe gari bayan taron godiya, garin Kudan ya tashi cikin nishaɗi da annashuwa. Mutane har suna cewa: “Gari idan ya samu shugabanni masu gaskiya da jama’a masu haɗin kai, sai ya zama kamar rijiya: kowa zai sha, amma ba ta bushewa.

    A wannan safiya, Salmanu Faris ya samu kira daga Farfesa Muazu wanda ya ce: “Salmanu, lokaci ya yi da za mu tattara tarihinku tun daga zaman lafiya zuwa gyaran gari. Ba a barin tarihi ya yi bacci. Sun zauna a cikin Babban Masallacin Juma’a, gini sabo, fenti sabo, ƙamshi yana tashi kamar sabon harsashi. Farfesa ya ce:

    “Wannan ginin da ka ke gani ba bango ba ne kaɗai. Al’umma ta gina shi da addu’a, haɗin kai da gaskiya.” Salmanu ya gyaɗa kai, yace ” gaskiya ne”. A gefen masallacin, yara suna fitowa daga sabuwar makarantar koyon sana’o’in dogaro da kai. Wacce ake koyar da:

    1. Ɗinki.

    2. Walda.

    3. Gyaran waya.

    4. Noman zamani.

    5. Tsabtace muhalli.

    Nawalmu da Nuhu Baushe su ne jagororin tsaro a wajen. Nawalmu ya ce:

    “In ka koya wa matashi sana’a, ka cire masa yunwa da rashin aikin yi a lokaci ɗaya. Tsaro ya fara da cikakkiyar” Mutane suka yi murmushi, domin kalamansa suna da kaifi, amma mai zaƙi.

    A gabas da gari kuma, titin da Rt. Hon. Isa Ashir ya gina ya sake raya kasuwanci. Baburan haya suna yawo, masu sana’ar shinkafa suna kai kaya, manoma suna kawo hatsi. Garba Ode yana tsaye da wuƙarsa a gefe yana karɓar biki. Ya kalli sabuwar hanya ya ce:

    “Kai! Idan hanyar mutum ta gyaru, al’amuransa sukan gyaru. In ka gyara hanya tsakaninka da mutane, ka gyara zaman duniya.” Mal. Mujaheed da Auwal, Salim da Abdulrazaƙ suna koyar da matasa darussan:

    1. Yadda ake kawo rahoto cikin ladabi.

    2. Yadda ake lura da abin da ya saɓa da al’ada.

    3. Yadda ake guje wa hayaniya da tada husuma.

    4. Yadda ake tsare unguwa ta hanyar sa-ido da bin doka.

    Shi kuma Nuhu Baushe yana kula da masu sintiri daga maraice zuwa safiya. Yana kiran wannan aiki: “Kayan kwana tamkar halacci kare gari. Idan gari ya kwana lafiya, kowa ya huta. A asibitin da sabuwar na`ura ke aiki, Furaira (Hajiyayye) da Sha`awanatu suna kula da marasa lafiya.

    Mutane sun saba cewa: “Asibiti tamkar zuciya ce ga gari. Idan zuciya ta yi ƙarfi, mutum ba ya faɗuwa.” Likita ya ce Salmanu ya kawo rubutu kan yadda aka inganta aikin jinya. Salmanu ya amince.

    A ɓangaren ɗaya kuma, lokacin da ranar ta yi sakaliya, filin ƙwallon da Rt. Hon. Isa Ashir ya gina ya cika da mutane. Matasa suna motsa jiki, yara suna kallo. Muryar masu ihu ( zuga) tafi tana ƙara karaɗe garin, a lokacin da Ibrahim (Henry) da Zubairu ( Eto) suka ci wata ƙwallo ta ban al’ajabi. Isma’il ya kalli Malam Mujaheed ta yi murmushi:

    “Ka ga idan matasa suna motsa jiki, ba su da lokacinnda za su bi maganganu marasa amfani.

    Karanta Tarihin Garin Kudan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Asalin Kishi Yake

    Yadda Asalin Kishi Yake

    GABATARWA

    A shekarar 2013, wani rahoton binciken masana da Farfesa Daniel Freeman na Jamiar Oxford tare da marubuci Jason Freeman suka wallafa a jaridar ‘The Guardian’ ta ƙasar Amurka, mai taken ‘Jeolousy: It’s in your gene’, ya nuna cewa kishi gadajjen abu ne wanda kowanne ɗan adam ke tare da shi a cikin ƙwayoyin halittar sa.

    Binciken da masana suka gudanar  ya nuna cewa mata sun fi bayyana kishi sama da maza, wannan kuwa a kimiyyance muna iya danganta shi da yanayin mutumtakar jinsinan biyu wajen jure yanayai na zuciya da ɗaukar matakai a game da su.

    Mujallar BBC Science Focus ta taɓa yin nazari game da dambarwar masana a kan ‘shin kishi abu ne da ɗan Adam ya yo gadon sa ko wanda ya koya bisa zamantakewar sa a muhallin sa?’.

    Shi ne har suka kawo hujjojin kowanne ɓangare, ciki har da masu kallon yadda wasu sarakuna a zamanin baya su ke bai wa baƙinsu matayen su don su tara da su, da yadda wasu ke faɗin cewa ba su taɓa jin kishi game da abokan tarayyar jima’in su ba, sai dai bisa la’akari da hujjojin masu cewa ‘gadon kishi ɗan Adam ya yi’, waɗanda suka haɗa da yadda maza a mafi yawan lokuta suke son kyakkyawar mace (satirical theory) mai jiki sama da sauran mata, da yadda wannan soyayyar ta maza kan haifarwa da mata daraja musamman daga ‘ƴa’ƴayen da dangantakar ta samar musu saboda tarawar jima’i.

    Sai ya zamana wajibi ga mata su fi buƙatuwar samun kaɗaitacciyar dangantaka wadda za ta ba su ‘ƴa’ƴaye, wanda hakan kan tilasta jikkunan su samar da ƙwayoyin halittun da za su fi son wanzuwar su kaɗaitattu ababen so a wurin abokanan zaman su (maza).  Wannan ne silar samuwar kishi a ɓangaren mata, wanda kan faru da zarar mace ta hangi yiwuwar faruwar wani abu wanda zai iya dakushe mata wancan muradi nata da ta yi gado daga ƙwayoyin halittu.

    Sai kuma yadda aka lura da samun ɓurɓushin kishi daga wasu dabbobi misalin Gibbon waɗanda dangantakar su ta ƙwayoyin halittu ke tuƙewa da ɗan Adam, don haka aka fi danganta kishi ga ‘Natural Selection’, watau watsuwar ƙwayoyin halittu.

    Ƙarin hujja a kan haka shi ne yadda a baya-bayan nan wani rahoton bincike ya tabbatar da cewa kishi shi ne silar da yara ƙananu ke yawan kuka/rikici da dare domin kange mahaifansu daga tarawa wadda za ta kai su ga samar musu da ƙani ko ƙanwa, da kuma yadda yara ke ƙara yawaita rikici bayan mahaifiyar su ta sake haihuwa.

    Mutane da yawa da zarar an ambaci kishi sun fi danganta shi a tsakanin ma’aurata, musamman tsakanin kishiyoyi, amma a zahiri kishi ya wuce haka. Don haka a taƙaice, wannan ɗan rubutu zai kalli wasu daga taƙaitattun zantuka game da asalin kishi a kimiyyance da tasirin sa gami da yadda ya kamata a tunkare shi.

    MA’ANAR KISHI

    Masana da dama sun fassara ma’anar kalmar kishi gwargwadon fahimtar su, amma bisa tamu fahimtar, kishi na nufin wani yanayi na zuciya wanda yake cike da tsoro da firgici da tsana da ƙyamata, wanda ya ke bijirowa a duk sa’ar da wani ya fahimci samuwar wani abu mai barazana ga darajar sa ko matsayin sa, ko damar sa, ko mabiyan sa ko wani abu muhimmi da yake tutiya da shi.

    ASALIN KISHI

    Ko da yake, masani mai bincike Emanuel Eisner ya faɗi cewa ƙwayoyin halittar mu kusan ɗaya suke da na kakannin mu waɗanda suka rayu kimanin shekaru 600 da suka gabata, amma haɓakar yanayin kishi a zuciyoyin mu yana da alaƙa da sauyawar abubuwan da suka rinƙa faruwa ga ɗaukacin jikkunan mu na tsawon waɗancan shekaru, wanda hakan ke nufin cewa akwai ɗaukacin banbanci a tsakanin abinda mutumin yanzu zai yi kishi a kansa da na mutumin da ya rayu shekaru 600 baya.

    Wannan ya samu ne daga sauyawar muhallai, da buƙatu da muradun mu ne, amma kuma ɗaukacin jigon kishin sam-sam bai sauya ba. Masani Aaron Sell na jamiar Griffith da ke Australia, ya yi nazari a kan asalin kishi, inda har ya gano kishi ne silar aikatuwar wasu munanan laifuka da rashin zama lafiya irin wanda ake fama da su a halin yanzu.

    Misali a kan haka shi ne KISA

    Kimanin kashi 90% na kashe-kashe da ake yi a wannan duniyar maza ke aikata su, amma an lura da cewa mata ne a kan gaba wajen kashe ƙananun yara (Infanticide) da kuma abokanan auratayyar su (spousal homicide).

    Mu kalli Spousal Homicide: Wananan kalma na nufin yanayin kisan kai da kan faru tsakanin ma’aurata, walau miji ya kashe matar sa, ko mata ta kashe mijinta. Bincike ya tabbatar da cewa mata aka fi samu da kashe mazajen su.

    Haka nan, Bincike ya nuna cewa sama da dubunnan shekaru, mazajen da suka rayu a wannan duniyar suna cike da kishin matayen su, don haka sun kasance cike da ƙoƙari wajen ganin sun mallaki akalar matayen su, watau sun kange su daga tarayyar da ba sa so.

    Wasu mazan kan yi haka ta hanyar tsoratarwa, ko nuna ƙarfi ga mata waɗanda akasari su ne a ƙarƙashin su, wannan ya sa har zuwa yanzu akan samu yanayan da namiji zai saki mace, sannan ya bi sabon mijin da ta aura ya kashe ko ya yi wa lahani, saboda ya sake ta ne cikin fushi, yana mai burin ta shiga wani yanayi wanda zai sa ta yin nadamar rabuwa da shi ba don ba ya son ta ba, amma da zarar ya ganta cikin yanayi mai daɗi saɓanin yadda ya yi muradi, sai kishi ya taso masa, wanda a wasu lokutan ya kan zama silar aikata munanan ayyuka.

    Su kuwa mata kasancewar su raunana ga maza, sai suka fi amfani da kisa a ɓangaren su wajen gudanar da nasu kishin na kange mazajen su daga tarayyar jima’in da ba sa so. Duk da cewa an lura da cewar mata masu ƙarancin shekaru kuma waɗanda ba su haihu da yawa ba ne suka fi aikata hakan, amma sau tari ɓacin ran da ke tunkuɗa su aikata wannan mummunan aiki daga gundarin kishi ya ke.

    Mai bincike Anne Campbel ta gudanar da cikkaken bincike game da silar rikicin mata, abinda ta tafi a kai shi ne mata sun ɗora rayuwar su kachokan ne a kan maza (uba, ɗan uwa, miji da sauran su), don haka matsawar mace tana da namijin da zai mata yaƙi, ba za a ganta cikin rikici ba.

    Saboda haka ana iya cewa babban abinda ke tunkuɗa mata aikata wancan ta’addancin na kashe mazajensu bai wuce yadda suke ɗaukar tozarci ne a gare su idan har suka samu raguwar daraja ko kawar da kai daga wanda suka ɗorawa so da aminci a garesu, don haka sukan gwammace halaka mazajen su duk a cikin kishi.

    Amma a game da kisan ƙananun yara da mata kan yi (infanticide), shahararrun masanan nan Martin Daly da Margo Wilson sun yi bincike a kai, inda suka bayyana cewa samuwar kishiyar uwa a gida na sanya yaro cikin haɗarin fuskantar kisa a ƙalla da kashi saba’in, da kuma haɗarin fuskantar cin zarafi da kashi 40. Wannan ma duk kai tsaye ana iya cewa daga kishi ne wanda ke faruwa a tsakanin matan gida wanda kuma yake shafar yaran.

    Don haka, a ƙarshen binciken Masani Aaron ya tafi a kan cewa ɗan Adam bai ginu da ƙwayoyin halittun yin kisa don kange wanda yake so daga wata tarayya da ta saɓawa son zuciyar sa ba, sai dai kisan ya kasance a matsayin makami da wasu yanayai munana na zuciya kan tunkuɗa wasu mutane su yi riƙo da shi gwargwadon juriyar su ga wutar kishin da ke ruruwa a zukatan su. Wannan kuwa yanayi akan same shi a sauran sassan rayuwa ba ga auratayya ba kaɗai.

    Haka nan, masana sun kalli yawaitar tashe-tashen hankula tare da danganta su da kishi, wanda yake faruwa sabili da tarayya a kan abu guda da wasu mutane ke son mallaka, ko kaɗaituwa da shi da makamantan irin haka, don haka duk wanda ya ga akwai yiwuwar ya rasa wata martaba da yake tinƙaho da ita ko wani na son tarayya da shi ko kuma wani ya hau turbar fifita a wani lamari sama da nashi, sai kawai ya yi martani da ayyuka waɗanda suka saɓawa hankali.

    Akwai irin waɗannan abubuwa da yawa a cikin kasuwanci, siyasa, malantaka da sauran lamurori na zamantakewar al’umma. Akwai ƙarin hujjoji masu nuni da cewa kishi daɗaɗɗen abu ne da ke cikin jini wanda yake yawatawa a jijiyoyin ɗan Adam, daga misali shi ne kisan farko da ɗan adam ya soma aikatawa a duniya, watau tsakanin Ƙabila da Habila (Cain da Able), da kuma yadda ya zo a tarihi wurare daban daban inda ɗan’uwa ya kashe ɗanuwansa bisa wani dalili mai tuƙewa da kishi.

    Susan Dudley, masaniya ce mai bincike, ta gudanar da wani bincike dangane da wasu tsirrai (American sea rocket) wanda ya ƙara mana fahimta a game da asalin kishi. Susan ta ware wasu tukwane guda biyu ne, sannan a tukunya ta ɗaya ta shuka jinsin tsirrai guda guda biyu ‘ƴan uwan juna, a tukunya ta biyu kuwa sai ta shuka mabanbantan jinsinan tsirrai.

    Bayan tsawon lokaci sai ta samu cewa tsirran da aka shuka a tukunyar da ke ɗauke da mabanbantan tsirrai sun fi saurin girma fiye da ɗayar. Wannan na nuna cewa akwai kishi har a tsakanin tsirrai, domin ga shi tsirran da suke da alaƙa da juna sun hana junan su girma yadda ya kamata. Wannan fa ya faru ne a tsakanin tsirrai wanda kowa ya sani kashi 25 zuwa 30 na ƙwayoyin halittar su ɗaya yake da na bil’adama. Ina ga shi kansa ɗan Adam?

    Don haka fahimtar ainihin yadda kishi ya samo asali na da buƙatar dogon nazari mai tuƙewa da asalin samuwar ɗan Adam, amma dai a mafi rinjaye, ƙwayoyin halittar ɗan Adam ne ke ɗauke da shi.

    A INA AKE SAMUN KISHI

    An fi samun kishi a tsakanin abubuwa biyu masu alaƙa da juna. Misali, mutum ya fi kishi da mutum, dabba ta fi kishi da dabba, haka ma tsirrai sun fi yi a tsakanin su. Haka kuma, ko a cikin mutane, yawan zurfin alaƙa ke nuni da yiwuwar samun zuzzurfan kishi.

    Ko kuma a ce, kishi ya fi samuwa a tsakanin wasu mutane da suke tarayya da wani abu, misalin jinsi, ƙabila, harshe, gari ɗaya ko ƙasa ɗaya, ko ‘ƴanuwa da abokanai, ko a tsakanin wasu rukunin al’umma masu aiki ko sana’a iri ɗaya, da dai makamantan su.

    Don haka za a ga cewa mace ta fi kishi da mace ‘ƴaruwarta sama da namiji. Haka kuma sau tari, Bahaushe ya fi jin kishi ga abinda ya shafi ɗan’uwan sa Bahaushe. A wani yanayin ma akan samu cewa mutum ya fi samun maƙiya daga ƴanuwan sa na jini .

    AMFANIN KISHI

    Masana sun kalli tasirin kishi, sun kuma tabbatar da cewa abu kamar sa wanda ya daɗe a duniya yana ta bibiyar ƙwayoyin halittar ɗan Adam ba zai taɓa kasancewa mara amfani ba. Babban amfanin da aka fi dangantawa kishi shi ne; ankararwa da kuma zaburarwa domin tashi tsaye bisa naƙasun da akan iya haɗuwa da shi a lokacin da buƙatar hakan ta taso.

    Don haka, ɗan kasuwar da ya fahimci yiwuwar wani abokin kasuwancin sa zai danne shi a fannin kasuwanci, zai ji kishi a zuciyar sa, wanda hakan na nufin ya zaburar da shi domin fahimta gami da gyara abubuwa na kuskure da yake aikatawa gami da ɗorarwa a kan ayyukan da za su ƙara riƙe masa martaba a kasuwancin sa. Irin haka ne ga kishiya ta aure, ko malanta, ko ta duk wani abu da kishi kan iya bijirowa a cikin sa.

    Saboda haka kyakkyawan kishi abu ne da aka lura da cewa zai iya samar da cigaba ga mutane ko ga yankuna ko ga duk wani abu da ake kishi a kan sa matsawar an yi amfani da shi bisa tsari kyakkyawa yadda ya kamata.

    ILLAR KISHI

    Mutane da yawa suna faɗawa cikin munanan ayyuka sabili da kishi. Wani kan kashe wanda yake kishi da shi, ko ya bi wasu hanyoyi da yake gani zai iya  wargaza lamurran abokin kishin sa. Wanda akan haka, wasu kan rasa rayuwar su, ko matsayi ko darajar su ko imanin su da Allah maɗaukakin sarki. Wasu ma na tsintar kawunan su a kurkuku ko a wani yanayi mara daɗi tun a nan duniya duk bisa mummunan aikin da aka aikata saboda kishi.

    Babban illar kishi ga ɗan Adam shi ne; hana girma ko haɓaka. Sau tari, mummunan kishi ne silar durƙushewa da rashin cigaban al’umma. Shi ne kuma kan zama silar yawaitar munanan ayyuka da rashin zama lafiya.

    MAFITA GAME DA KISHI

    Yana da kyau a sani cewa babu wani ɗan Adam da ba ya jin kishi matsawar yana da lafiyar ƙwaƙwalwa. Sannan babu wata ni’ima ko fifiko da Allah zai yi ga wani ko wata wadda ba za ta sanya kishi a zukatan mutane musamman masu wani abu iri ɗaya da shi ba. Mafitar ɗaya ce; a mayar da dukkan lamurra ga Allah.

    Masani Berit Brogard yana da dabarar ‘normalism the feelings’ wajen kashe mummunan kishi, watau ɗaukar irin waɗannan yanayi a matsayin abu gama gari wanda bai kamata a tayar da hankali a kan sa ba.

    Don haka da zarar tunanin sa ya bijirar masa da wani abu na kishi, sai ya kwantarwa da zuciyar sa hankali, ya faɗa mata wannan abin fa ‘is normal’ ba abu ne mai buƙatar ɗaga hankali ba.

    Sanin kowa ne cewa kowanne ɗan Adam yana da ƙaddarar sa, wani mai kyau wani mara kyau. Don haka, sunnar rayuwa ce irin abin nan da ake cewa ‘yau gareka gobe ga wanin ka’. Wato komai na tafiya da lokaci. Idan yanzu kai ne ke sharafi, to ai a baya ba kai ba ne, don haka nan gaba ma wani ne zai yi ba kai ba.

    Abu na gaba shi ne buƙatar rage abinda masana ke kira ‘endowment effect’, wato yanayi da kan sa mutum ya ji cewa shi kaɗai ya isa da abu kaza ko jin cewa abu kaza mallakin sa ne shi kaɗai tilo, kamar yadda aka fi samu a tsakanin ma’aurata.

    Ya kamata mace ta sani cewar an halartawa namiji ƙarin aure a duk sanda ya samu sukuni, haka shi ma namiji ya sani cewar mace na da damar samun annushuwa da wanin sa idan ƙaddarar rabuwa ta auku a auratayyar su.

    Kuma ya kamata kishi ya zamo silar zaburar da mutane aikata kyakkyawan ayyuka ba munana ba. Sannan mutum ya ɗora faruwar lamurra dukkan su ga Allah maɗaukakin sarki, walau ga kansa ko ga wanin sa.

    Ƙarshen wannan muƙala kenan.

    Ina mai adduar Allah ya jikan babban marubuci Alh Bashir Usman Tofa wanda aka yi jana’izar sa a yau litinin 2/1/2022.

    Ga masu buƙatar ƙara samun sani game da wannan muƙala, akwai kwas mai taken ‘Introduction to Mental Health’ wanda muka samar kyauta a kwalejin Hausa ta yanar gizo mai suna AAGHOLI a kan adireshin (https://www.aagli.com.ng)

    Nine naku Sadiq Tukur Gwarzo (Public Health Nurse, mamba Global Goodwill Ambassadors)

    Danna nan don karanta Kimiyyar Siyasar Uban Gida: Tasiri, Makoma Da Silar Rabuwa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Nazarin Hanyoyin Adana Kayayyakin Hausawa Na Gargajiya

    Nazarin Hanyoyin Adana Kayayyakin Hausawa Na Gargajiya

    TUN KAFIN A HAIFI UWAR MAI SABULU, BALBELA TAKE DA FARIN GASHINTA: NAZARIN HANYOYIN ADANA KAYAYYAKIN HAUSAWA NA GARGAJIYA

    Daga

    Magaji Ahmad Gaya PhD

    Sashen Koyar Harsunan Nijeriya,

    Jami’ar Northwest, Kano

    magaya@nwu.edu.ng /magajiahmadgaya@gmail.com

    08066009039

    Takardar Da Aka Gabatar A Taron Makon Hausa Wanda Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya Jami’ar Arewa Maso Yamma (Northwest) Kano Ta Shirya. Wanda Aka Gabatar A Babban Ɗakin Taro Na ‘Yanganau Da Ke A Farfajiyar Jami’ar. Ranar Alhamis 29/01/2026

    Tsakure

    Al’ummar Hausawa, mutane ne waɗanda tun fil’azal suna da hikimominsu da suka gada tun iyaye da kakanni, waɗanda suke aiwatar da su har ya zuwa yau. Suna amfani da fasahohinsu da hikimimominsu da basirarsu ta hanyar sarrafa albarkatun da suke kewaye da muhallansu, waɗanda suka haɗa da adana kayayyakin Hausawa na gargajiya domin su samar da kayayyakin amfanin kansu.

    Manufar wannan takarda ita ce bayyana wasu hanyoyin adana kayayyakin gargajiya wanda suke amfani da su tun kafin haɗuwar su da baƙin al’ummu. An yi amfani da hanyoyin gudanar da bincike, waɗanda suka haɗa da tattaunawa da ziyarar gani da ido da karantawa daga wasu rubutattun bayanai.

    An ɗora wannan bincike ne bisa ra’in Adana Al’adu da Cigaban Al’umma wato (Cultural Sustainability Theory), shi ya fi dacewa da wannan bincike. Gusau (2015:55) ya kira makarantar da ta fito da wannan ra’i da suna ‘‘Mazahabar Adana Al’adu’’. Shi kuma Sha’aibu (2013:78), ya kira makarantar da ke da’awar wannan ra’i na Adana Al’adu da suna “Mazahabar Muhafaza”.

    Sakamakon takardar ta nuna cewa al’ummar Hausawa suna da hanyoyin adana kayayyakinsu a gargajiyance waɗanda suka gada tun kafin zuwa ko haɗuwa da baƙin al’ummu. Hausawa suna amfani da su wajen adanawa tare taskacewa don gudun lalacewa ko salwanta.

    Muhimman Kalmomi: Adana da Kayayyaki da Hausawa da Gargajiya.

     Gabatarwa

    Wannan takarda za ta yi duba ne a kan kayayyakin da al’ummar ƙasar Hausa suke amfani da su wajen adanawa. Waɗannan kayayyakin gargajiya da za a yi nazari a kansu, na su ne, kuma har gobe suna amfani da su wajen aiwatar da ajiye-ajiye da aikace-aikace. Akwai tarin fasahohi da hikimomi ta yadda Hausawa suka samar da su, musammanma idan aka yi la’akari da yadda suke taimaka musu wajen adana kayayyakinsu cikin sauƙi, ba tare da wata matsala ba.

    Haka kuma, an nazarci yadda masu sana’ar suke amfani da su, kuma an kawo bayanin yadda suke  samar da su da kuma nau’o’in aikace-aikacen da ake yi da su. Hausawa sun inganta wasu kayayyakin, domin su dace da buƙatun mutanan, da ma na wannan zamani. Har ila yau sun yi ƙoƙari matuƙa wajen rage tsofaffin kayayyaki, waɗanda maimakon su yi wasarere da su gaba ɗaya, akwai buƙatar ƙara inganta su domin tafiya da zamani.

    Manufar Gudanar da Bincike

    Manufar wannan takarda ita ce, bayyana wasu hanyoyi  da al’ummar Hausawa suke amfami da su wajen adana ko taskce kayayyakinsu domin gudun lalacewa ko salwanta ko kuma domin tarihi da makamantansu.

    Haka kuma, wata manufar ita ce, domin bayyana ko fayyace wasu tsofaffin kayayyakin da ake adanawa haɗi da amfani da su. Sannan kuma, wata manufar ita ce, domin fito tare da bayyana alfanun da kayayyakin suke da shi wajen adanawa da kuma mai da hankali wajen nazarinsu ga masu bincike domin gujewa gushewarsu.

    Ra’in Bincike

    Wannan bincike an ɗora shi ne a kan Ra’in Haƙiƙa, wannan bincike ya bibiyi ra’o’in binciken al’adun Hausawa daban –daban don tantance wanda ya dace da wannan bincike: inda aka gano cewa Ra’in Adana Al’adu da Cigaban Al’umma wato (Cultural Sustainability Theory), shi ya fi dacewa da wannan bincike.

    Gusau (2015:55) ya kira makarantar da ta fito da wannan ra’i da suna ‘‘Mazahabar Adana Al’adu’’. Shi kuma Sha’aibu (2013 :78), ya kira makarantar da ke da’awar wannan ra’i na adana al’adu da suna ‘‘Mazahabar Muhafaza’’.

    Salsalar Ra’i

    Wannan ra’i ya samo asali ne ta hanyar gudummawar masana da hukukmomi da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, wanda John Hawkes ya assasa a matsayin jagoran wannan ra’i.

     Mabiya Ra’i

    Ko da yake John Hawkes ne ya fi shahara wajen gabatar da wannan ra’i, amma akwai masana da hukumomi da dama da suka rungumi tare da bunƙasa wannan ra’in na adana al’ada. Wasu daga cikinsu su ne:

    • Unesco da UNDP (United Nations Development Programme)
    • David Throsby,
    • Jown Hawkes Australian Coucil For the Art
    • Katrilna Soini & Inger Birkeland
    • Nancy Duxbury
    • Keith Nurse
    • Graham Fairclough

    Ayyukan da aka Ɗora Ra’in a kai

    Akwai bincike masu dama da aka gudanar a baya, waɗanda suka yi amfani da wannan ra’i na adana al’ada daga cikin su akwai John Hawkers (2001) ya yi littafi mai suna The Fourth Pillar of Sustainability: Cultures Assencial Role in Public Planning. Ya jaddada cewa dole ne a haɗa al’adu cikin tsare-tsaren cigaba.

    Sannan da David Throsby (2008-2010), Linking Cultural and Ecological Sustainability. The Economic of Cultural Policy: ma’ana dangantakar da ke tsakanin Al’adu, Tattalin Arziki da Ɗorewarsu. Sannan kuma akwai binciken da UNESCO ta tallafa a shekara ta (2003-2015), mai taken “Al’adun Gargajiya Marasa Ganuwa (Intengible Cultural Heritage), da ilimin gargajiya na asali, sai kuma Harsuna da suke fuskantar shuɗewa.

    Haka kuma akwai binciken da aka gabatar a jami’o’in gida a kan al’adun Hausawa da suka haɗa da:

    • Aminu Lawan, ya yi bincike a kan “Ɗorewar al’adun Hausawa a Zamanin Zamani”. Jami’ar Bayero, Kano.
    • Zainab Sadiq, ta yi bincike a kan “Rawar Bukukuwan Gargajiya Wajen Raya Al’adu”. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.
    • Abdullahi Musa. ya yi bincike mai taken “Tasirin Zamani da Adabin baka na Hausa”. Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya
    • Hadiza Bello, ta yi bincike mai taken ‘‘Rawar ‘Yammata Wajen Kare da Ɗorewar Al’adu a Arewacin Najeriya”. Jami’ar Ilorin
    • Sani Ibrahim, ya yi bincike a kan “Gudummuwar Sarautun Gargajiya Wajen Ɗorewar Al’adu”. Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua Katsina.

    Dangantakar Ra’i Da Nazari

    Bayanan cikin wannan ra’i suna da dangantaka ta kai tsaye da wannan nazari, sannan za su zamo wani dandamali da wannan bincike zai taka ya hau har wannan bincike ya samu kammaluwa. Saboda ra’in yana bayani ne kan yadda za a tseratar da al’adu daga salwanta, wanda wannan shi ne ƙudirin wannan bincike da za a gudanar.

    Hanyoyin Gudanar da Bincike

    Kamar yadda aka sani, babu aikin da za a yi ba tare da bin wasu hanyoyi na gudanar da shi ba. Fayyace waɗannan hanyoyi a bincike irin wannan yana da matuƙar muhimmanci, domin zai taimakawa wajen tabbatar da sahihancin bayanan da aka kawo a cikin aiki.

    Ba a bar wannan binciken a baya ba ta wannan fuska, domin shi ma an yi amfani da wasu hanyoyi wajen tattara bayanan da suka taimaka wajen aiwatar da shi. Daga cikin hanyoyin, akwai tattaunawa da mutanan da aka samu damar tattaunawa da su domin samun nasarar wannan bincike.

    Wajen gudanarwa an yi la’akari da matsayi da kuma shekaru. Mutanen da aka tattauna da su sun haɗa da tsofaffi maza da mata, waɗanda suka taimaka wajen fito da wasu muhimman bayanai na waɗannan kayayyakin aiki. An kuma kai ziyarar gani da ido, inda kai tsaye aka ziyarci masu gabatar da ayyukan kaba da maginan ƙasa da fatu da sauransu, kuma aka tabbatar da wasu bayanan da aka samo daga gare su.

    Baya ga waɗannan hanyoyi, an kuma tuntuɓi masana na sana’o’in gargajiyar Hausawa, kuma an bibiyi rubuce-rubucen magabata inda aka samu tarin bayanai da suka taimaka wajen rubuta wannan takarda.

    Nazarin Hanyoyin Adana Kayayyakin Hausawa Na Gargajiya

    Akwai hanyoyin da ake amfani da su wajen adana kayayyakin Hausawa na gargajiya masu yawan gaske, waɗanda lokaci ba zai bayar da damar kawa su gaba ɗaya ba, sai dai a kawo misalan wasunsu tare da bayani.

    Rumbu

    An bayyana kalmar rumbu da shi ne, “ɗakin da ake ginawa da ƙasa ko karan dawa ko gamba domin adana hatsi” (Sa’id, B. da wasu 2006). Ana saƙa rumbu ne da ciyawar gamba wadda take da tsawo da ƙwari, akan ɗora bisa dirkoki ko kuma manyan duwatsu saboda gudun  ƙwari ko ɓeraye.

    Akan ɗora masa  ɗan boto a sama a matsayin murfi domin adana kayan amfanin gona irinsu gero ko dawa ko gyaɗa ko wake ko ɗauro cikin zangarniya. Idan ana buƙata sai a tsakura ko kuma a ɗebo domin biyan bukatar yau da kullum.

    Randa

    Wannan wani mazubi ne da ake ajiye ruwa a cikinta.  Sa’id da wasu, (2006) sun bayyana ta da cewa” “Wata ƙatuwar tukunya da galibi ake zuba ruwa a cikinta ko kuma ta zamanto taskar ajiye kuɗi. Har ila yau tana iya zama rijiyar karofi ta rini. Randa tana daga cikin kayayyakin da Hausawa suke amfani da ita, magina ƙasa ne suke gina randa.

    Yayin da za a gina ta magina, suna samo taɓo da ƙasa ta jangargari haɗi da ruwa a cakuɗa har dai a samar da ita. Yayin da aka samar da ita akan ajiye ruwan sha da kuma adanawa domin tanadin abubuwan da za su iya tasowa haɗi da abubuwan yau da kullum.

    Ruzu

    Wata irin ƙaramar jakace saƙaƙƙiya. Ruzu wata jaka ce wadda ake saƙa ta da kaba ko zare, tana da ɗan faɗi da tsayi sannan tana da maratayi, ana rataya ta a kafaɗa, mafarauta sukan saka naman daji idan sun kamo a ciki, yayin da suka fita farauta ko sharani ko ƙuloto. Sannan idan suka dawo gida akan ajiye naman da suka samo a cikinsa (Tattaunawa da Baba Sayyadi).

    Taskira

    Ana saka ta dominn aikin kaɗin zare da abawa, tana da faɗi kamar faranti ƙarami ko filet na zamani, sai a shimfiɗa mata fatu riɓi-riɓi kamar talatin ko talatin ko ashirin, mai ɗakin kan ajiye wasu abubuwa masu muhimmanci da suka haɗa da; kuɗi da ‘yankunnaye da sarƙoƙi da sauransu.

    Ana yi wa taskira kirari da: “Taskira Asirin Mai Ɗaki. ”Don haka za a iya cewa, taskira, wani ɗan ƙaramin kwando ne da aka saƙa da kaba wanda mata ke amfani da shi wajen zuba auduga da mazari da alli don yin kaɗi (Sa’id, B. da wasu 2006).

    Gajiran/Gajirami

    Wannan shi ma wata ma’ajiya ce ta gargajiya wadda Hausawa, suke ginawa tare da jera su a ɗaki. Akan yi rami matsakaici kamar yadda tukunya ƙarama za ta shiga cikin ramin sai a layanta su a bango da ƙasa, sai kuma abinne amma bakinsu yana kallon sama, akan adana wake ko gyaɗa ko riguna ko zannuwa ko hatsi da sauransu, wasu ma har kuɗi suke ajiyewa (Tattaunawa da Maisalati Durɓindai).

    Adudu

    Wannan kuwa, ya kasance ɗaya daga cikin kayayyakin da Hausawa suke amfani da shi musamman wajen ajiye ko adana wasu hajoji da nufin kaucewa salwanta ko kuma lalacewa. Wata ma’ ajiyin sutura mai zurfi da kuma murfi wanda ake yi da kaba (Sa’id, B. da wasu 2006). Adudu wata fasahar Hausawa ce, wanda ake amfni da kaba da gazari wajen saƙa shi domin adana sutura domin kaucewa ɓarnar ƙwari.

    Lefe

    Mazaubi ne da ake saƙawa da kaba don kaɗar auduga ta zama zare. Yayin da Sa’id da Wasu (2006) suka bayyana shi da cewa: “Wani makai da ake saƙawa da kaba don saka ko ajiye kayan kaɗi ko zuba kayan aure”. Haka kuma, wannan ya sanya Hausawa suke zuba sutura a ciki don kai Toshi gidan su amarya kafin a yi aure.

    Kuratandu

    Kuratandu wani ɗan ƙaramin tandu ne ake yinsa da jemammiyar fatar akuya ko tinkiya ko wata ƙaramar dabbar domin sa kwalli da mishiyi da akan sa kwallin da shi. Sannan kuma a sa matashi haɗi da murfi domin gudun ka da ya zube ko kuma ya salwanta.

    Akurki

    Akurki ana saƙa shi ne da itacen geza, za a zubar da ganyayyakin da ke maƙale a jikin itacen, sai kuma a tsaga itacen gezar gida biyu ko uku a tsaye. Ana saƙa kamar yadda ake kife ƙwarya, ana yi masa ƙofa daga ƙasa, yayin da aka kammala sai a samo kashin shanu sai a baibaye shi ciki da waje.

    Yana daga cikin kayyakin Hausawa na gargajiya da ake amfani da shi musamman wajen ajiye da kuma adana tsuntsaye nau’in kaji ko agwagi da zabbi da agwagi da makamantansu. Yayin da aka saka su ciki ko kuma suka shiga da daddadare sai a saka murfi a rufe ƙofar ta yadda wani abin cutarwa ba zai sami damar cutar da su ba irin su maciji ko muzuru ko cimola da makamantansu.

    Cali

    Wannan wani abu ne raga-raga, wanda ake saka tuluna ko ƙore da makamantansu. Wasu lokutan akan ɗora wa jaki idan za a kai su kasuwa. Sannan kuma a wasu wuraren cali kan kasance mazubin kayan amfanin gona kamar albasa ko yalo, ana saƙa shi ne da igiya, yana da ƙofofi don kayan su sha iska. Ana amfani da cali a ɗora kan jaki ko takarkari don ɗaukar kaya.

    Taiki

    Mazubi ne na jemamiyar fata wadda ake ɗinkawa, wadda za a ɗura tsabar gero ko dawa ko shinkafa wadda zai kwanta kan jaki ko takarkari mai siffar mangala domin kai kayan amfanin gona kasuwa ko kuma wurin da ake da buƙata. Akan zuba tsabar gero ko dawa ko rimi da makamantansu.

    Kwatanniya

    Kwatarniya wani matsakaicin mazubi ne wanda masu sana’ar ginin ƙasa suke samarwa. Ana samun taɓo da jangaggari da ruwa sai a haɗa a kwaɓa, sai kuma a samo wata tsohuwar kwatarniyar a mamaye bayanta da wannan taɓon da jangargarin da aka kwaɓa, ana bi ana bugawa kaɗa-kaɗan har ta zama ta yi kwafin ta farko, sai a bi a gyaggyara har ta zama abin da ake so.

    Ana zuba ruwa musamman idan za a yi wankan jego, haka kuma ana amfani da ita wajen wanki ko wankin kalwa. Haka kuma ana ajiyewa dabbobi irinsu awakai da tumakai ruwan da za su sha idan sun dawo gida daga kiwo. Ana yi mata kirari da cewa: “Kwatarniya kin fi arfin roro”.

    Akushi

    Akushi kwanon da ake cin abinci ne da shi ne a gargajiyance, sai dai shi ana sassaƙa shi ne da gungumen itace, ana zuba abinci a cikinsa kamar tuwo da miya, kasancewar itacen mai kauri ne yakan sa abincin ya daɗe bai huce ba.

    Ƙwarya

    Ƙwarya ana samunta ne daga ɗan duma, yayin da ya zama babba ya riƙa. Bayan an ɗebe kayan amfanin gona, sai masu sana’ar fafar ƙwarya su raba ta biyu, inda za su fitar da totuwar da take cikinta, sai kuma su fafe ciki sarai  sannan a barta har ta bushe, sai kuma a sake fafewa yayin da za a fitar da dukkan wata totuwar da take cikinta.

    Ita ma ana amfani da ita wajen adana kayyayaki masu yawan a gargajiyance, misali dawa ko gero ko wake ko deɓo hatsi daga rumbu, sannan kuma ana amfani da ita wajen shiqar hatsi idan an yi casa ko kusa zuba mararrakin tuwo idan an kwashe.

    Tallen Miya

    Maginan gargajiya na Hausawa su ne suke gina tukwanen ƙasa. Tallen tukunyar ƙasa, na daga cikin kayayyakin da ake amfani da su wajen adana ko ajiye kayayyaki wanda Hausawa suke saka suturarsu ko kuɗi ko ko kuma abinci domin gudun salwanta ko ɓata.

    Kamar yadda, Sa’id, da wasu (2006). Suka tabbatar cewa, makai da aka gina da laka aka gasa don dafa abinci ko zuba ruwa ko ajiyewa wani lokaci ma da adanawa. Shi kuwa Talle, wata ƙaramar ‘yar ƙaramar tukunya ce da ake dafa miya a cikinta.

    Ya kasance kamar tukunya sai dai, bai kai ga tukunya girma ba, da shi ake amfani wajen yin miyar abinci, yayin da aka gama miya akan ajiye ta saboda ka da ta lalace ko kuma ta salwanta wasu lokutan akan adana saboda akuya ko yaro ko wata dabbar ta zubar da ita.

    Asusu

    Wannan ya kasance wurin ajiyar kuɗi da ake ginawa a jikin bango ko ɗan kurtun yamɓu mai ƙaramar tsaga, ko gwangwani da aka yi masa ‘yar tsaga. Asusu wata ma’ajiya ce da Hausawa suke samarwa ta hanyar sarrafa ƙasa ta yumɓu haɗi da sauran kayyayakin samar da shi.

    Za a yi masa ‘yar ƙofa kaɗan yadda hannu ba zai iya shiga ba, duk abin da aka zura cikinsa ya shiga ke nan idan har ana da buƙata sai dai a fasa ko kuma a ɗauki lokaci mai tsawo kafin wani abu ya fito, sannan kuma daga sama ana yi masa mariƙa ta ƙasa. Akan zuba kuɗi domin yin ajiya (Tattaunawa da Mukhtar A. Isma’ila).

    Ragaya

    Ita ma hanya ce da Hausawa suke amfani da ita wajen ajiye tare da adana kayayyaki domin gudun salwanta ko lulubewa. Sa’id, B.da Wasu (2006). Sun ce: “Ragaya ita ce maratayin ƙore ko kaya da ake ɗaurawa ko ajiye wani a jinkar ɗaki daga ciki, wanda kuma ake saƙawa da tufkarkiyar kaba ko yawa.” Ragaya ita ce wadda ake saka ƙoƙuna ko akusai a ciki, yadda za ta zama an sarrafa ta da kaba sannan a yi mata gida-gida ko kuma hawa-hawa musamman domin ajiyar wani abu.

    Kula

    Kula ita ce babbar butar ƙasa da ake zuba ruwan sha a ciki domin ya yi sanyi. Ta kasance tana daga cikin jerin kayayyakin ajiyar Hausawa na gargajiya. Ana yin ta da taɓo da jangargari da ruwa. Maginan tukwane da sauran nau’o’in sarrafa ginin ƙasa ne suke samar da ita.

    Kula ita ce butar da ake yi da ƙasa, akwai ƙarama sannan kuma akwai manya, ƙananan su ne ake amfani da su wajen sayar da ruwan alwalla a kasuwannin ƙauyuka, Manyan kuma su ake zubawa ruwan sha domin ya yi sanyi, musamman a lokutan bazara yayin da ake tsananin rana. A lokutan sanyi kuwa akan ɗora ta a kan garwashin wuta don a sami ruwan xumi. (Tattaunawa da Muhammad Sani ).

    Ƙaho

    Ƙaho ya kasance wani abu ƙashi-ƙashi guda biyu da yakan fito a kan dabba, kamar saniya ko rago ko akuya ko barewa (Sa’id, B. da wasu 2006) musamman ma ƙahon rago ko kuma ƙahon wata dabbar daban, sukan sanya layun da aka rufa su da fata ko farin ƙyalle su rataya shi inda suke buƙata kamar a ƙofar gida ko a tsakar gida ko a binne domin yin kafi ko kuma wani muhimmin dalili, domin neman kariya daga al’ajanu ko ɓarayi da dai sauransu.

    Adada

    Wannan wata rumface wanda ake yinta a tsakar gidan Bahaushe, ana yin ta da gwafanni da bunu ko ciyawa, wasu lokutan kuma akan haɗa da zana da igiya da sauransu, akan ajiye kayayyaki irin su fatun buhuna ko kayayyakin aikin gona da suka haɗa da; magirbi da sungumi da garma da fatanya da gatari Har ila yau akan ajiye karbi da dai sauran kayyakin da ake da buƙata a ajiye (Tattaunawa da Kawu Mu’azu).

    Batta

    Wani ɗan kuttu ne na ƙirgi wanda ya ɗan ɗara girman kuratandu wanda ake zuba taba gari a ciki ( Sa’id, B. da wasu 2006). Shi ma yana ɗaya daga cikin kayayyakin Hausawa da suke yin ajiya haɗi da adanawa domin ka da su salwanta. Haka kuma matan Hausawa sukan yi ajiyar kayan kwalliya da sauran wasu abubuwa muhimmai, kamar tozali, gyatuma raɗau ko kuma aɗaɗa ko janbaki ko hoda ko jar koya da makamantansu.

    Don haka Batta tana da siffa kamar haka, akan shirya da tsara ta tare da yenta kamar siffar adaka, sai dai da katako ko kuma itace, sai kuma a lulluɓe ta da fata wanda Dukawa wato masu sana’ar sarrafa fata suke samar da ita (Tattaunawa da Malam Gambo.)

    Angara

    Kamar sauran kayyayin ajiyar Hausawa, Angara ta kasance wata ƙaramar jaka ce mai kama da zabira ta wanzamai, galibi maharba ne suka fi amfani da ita, domin adana kayayyakin harbinsu kamar, ’ya’yan date da toka da tsakuwa da ashana da sauransu. Dukawa ne suke samar da ita, saboda ta kasance ta fata ta kowace dabba in dai ta kasance mai faɗi (Tattaunawa da Malam Gambo).

    Akwatsa

    Wani ɗan ƙaramin wuri ne da ake samarwa mai kama da kanta, sai dai bai kai kanta girma ba, wani lokacin ma ana yin ta daf da ƙofa daga cikin ɗaki ko kuma daga waje. Akan yi ajiyar kayyayakin buƙata kamar su guntun manguli da ashana da kuka da manda da kanwa da gishiri da barkono da sauransu (Tattaunawa da Sa’idu Nakande).

    Bankaɗe

    Yana daga cikin kayayyakin da Hausawa suke yin ajiya a cikinsa, sannan ya kasu gida-gida akwai bankaɗen tabarma da bankaɗen gado da bankaɗen lefe da bankaɗen mataki da bankaɗen faifai da sauransu. Hausawa sukan yi masa waƙa da cewa: “Bankaɗan lefe na ka zuba mini ba ni bari sallah ta wuce ni” (Tattaunawa da Adamu Isyaku).

    Kuikuita

    Wata hanya ce ta Hausawa da suke yin ajiya a ciki, ana yin ta da kaba, sannan tana da siffar kuttu, sai dai ba ta kai kuttu girma ba.  Kuikuita tana da ɗan zurfi kaɗan, tana da murfi, sannan akan yi mata ‘yar mariƙa kamar yadda jaka take. Akan adana kayan kwalliyar mata kamar ‘yan kunnaye da barima da’yan hanci da duwatsu da murjani da sarƙa da awarwaro da zobba da tagulla da azurfa da sauransu (Hira da Maisalati Durɓunde).

    Salka

    Wata sarrafaffiyar fata ce da mahauta kan yi wa dabba fiɗar zuga-zugi, inda za su zare fatar ba tare da an yanka ta ba, musamman daga wuya zuwa ƙasa. Yayin da su kuma Dukawa suke jeme ta, wato su kawar da gashin da take ɗauke da shi, sai kuma su rina ta don ta bayar da kalla.

    Sai kuma a ɗaure dukkanin ƙofofin ƙafar ko a ɗinke su domin ka da abin da aka ajiye ko adana su zube. Akan ajiye muhimman abubuwa kamar ruwa da mai da hatsi da gari da sauransu. Sannan kuma a wasu lokuta matafiya ko kuma fatake  kan yi jagami da ita, ko kuma su ɗora a kan jakuna ko alfadarai (Hira da Maisalati Durɓinde).

    Sanho

    Shi ma yana daga cikin  kayayyakin da ake yin ajiya ko adanawa wasu muhimman abubuwa wanda al’umar Hausawa suke amfani da shi a cikin al’amuransu na yau da kullum.

    Sanho wata saƙaƙƙiyar kaba ce da masu sana’ar saƙar kaba suke samarwa, yana da siffar saƙa irin takumkumi, amma ya kasance ba shi da ƙofofi ko raga irin ta takumkumi, ya kasance haɗaɗɗiyar saƙa ce irin ta mangala. Akan ajiye kayayyakin amfani gona kamar su gero da dawa da alkama da dankali da wake da sauransu (Hira da Abdullahi Madaki).

    Kammalawa

    Wannan takarda ta karkata akalarta ne a kan kayayyakin da ake amfani da su wajen adanawa ta hanyar gargajiya, inda aka kawo bayanansu da kuma yadda Hausawa suke amfani da su a lokacin da buƙatar hakan ta taso. Kayayyaki ne na gargajiya, kuma suna da inganci da sauƙin samuwa haɗi da sauƙin sarrafawa.

    Amfani da waɗannan kayayyaki ya haifarwa Hausawa samun hanyoyi masu yawan gaske wajen adana kayayyakinsu domin amfanin yau da kullum. Takardar ta mayar da hankali kan kayyayaki da ake amfani da su wajen adanawa da kuma bayyanawa masu nazari da ‘yan baya masu tasowa su san su don ka da su wofantar da su.

    Sakamakon Bincike

    Bayan kammala wannan takarda. Babu aiki mai manufa da za a gudanar a kasa samun sakamakon da ya haifar ba. Daga cikin sakamakon da aka samu bayan kammaluwar wannan maƙala, sun haɗa da yadda aikin ya gano waɗansu hanyoyi da Hausawa suka bi cikin hikima da fasaha suka ƙirƙiri kayayyakin aikinsu waɗanda suka dace, kuma suka yi daidai da yadda za su yi amfani da su, ba tare da wata barazana ba.

    Da farko, takarda ta gano cewa ta hanyar amfani kayayyakin da ake yin ajiya ko kuma adanawa ake samar da wasu abubuwan da suke taimakawa wajen taskacewa don gudun lalacewa ko salwanta. Misali, kamar sanho da randa da rami da makamantansu.

    Haka kuma, takardar ta ƙara fito da sunayen wasu kayayyakin gargajiya masu amfani waɗanda ake samarwa, sannan kuma al’umma suke amfani da su don gudun ɓacewarsu. Misali kuikuito da salka da sanho da rumbu da makamantansu.

    Haka kuma takardar ta gano cewa mutane masu sarrafa kayayyakin adanawa ko ajiyewa suna bayar da gagarumar gudummawa wajen kyautata al’adu da kuma haɓaka tattlin arziƙin ƙasa. Domin sakamakon amfani da su na samar da abubuwan gargajiya don amfanin yau da kullum.

    Bayan nan kuma, takardar ta lalubo waɗansu kayayyaki waɗanda a yau Hausawa sunayensu kawai suka sani ko suke ji. Amma a da suna ganinsu tare da amfani da su yadda ya kamata. Misalin irin kayayyakin su ne irin su: zunguru da akwasa da tulu  da sauransu.

    Bayan da aka ƙare wannan takarda, an gano cewa har ma gwamnati da sauran hukumomin gwamnati na sayen wasu kayayyakin da aka sarrafa na gargajiya, suna adanawa a gidajen adana kayan tarihi na jihar Kano da sauran jahohin ƙasar nan da  nuna su a wajen taron baje kolin al’adu ko lokatan nunin kayan amfanin gona da ma sauran tarurruka.

    Shawarwari

    Wannan takarda tana bayar da shawara ga wasu rukunnan al’umma da ƙungiyoyin cikn al’ummar ƙasar Hausa kamar haka:

    Da farko, ana bayar da shawara ga al’umma, musamman waɗanda suke amfani da waɗannan kayayyakin a cikin gonaki da gidaje baki ɗaya, da su ci gaba da amfani da su. Dalili kuwa shi ne, rashin amfani da waɗannan kayayyaki zai iya janyo  sakaci da lalaci da karya gwiwar masu yin su wanda daga ƙarshe ma suna iya yin fatali da su baki ɗaya.

    Haka kuma, ana bayar da shawara ga hukumomi da mahukunta, musamman gidajen tarihi da gidajen sarauta da cibiyoyin koyar da al’adun Hausawa da cibiyoyin ilimi na kwalejojin ilimi da jami’o’i na jihohi da na tarayya da su riƙa ba masana da manazarta ƙwarin gwiwa da goyon baya a duk lokacin da suka je yin irin wannan bincike a wurarensu.

    Haka zalika, ana bayar da shawara ga ɗaliban ilimi, musamman matasa masu jini a jika da su tashi tsaye, tsayin daka, su ba da himma da ƙwazo wajen yin nazari da bincike dangane da abin da ya shafi irin wannan ɓangare. Dalili kuwa mafi yawan ɗalibai sun karkata ne a kan jigo da salo da sarrafa harshe. Abin, ya kamata mu fuskanci al’adunmu na gargajiya kar mu guje su mu faɗa ga na waɗansu.

    Bayan haka kuma, wannan takarda tana shawartar masana da manazarta da su ƙara ba ɗalibai ƙwarin gwiwa dangane da yin nazarce-nazarce waɗanda suka danganci irin waɗannan al’adu musamman amfani da kayayyakin da ake adanawa, don ta yin haka ne za a gano waɗansu abubuwa da aka riga aka manta da su. Sannan a san waɗansu sababbi waɗanda ba a san da su ba. Amma hakan ba zai yiwu ba har sai  an zurfafa bincike a wannan fage. Sannan za a iya cim ma wannan buri.

    Wata shawarar ita ce ga gwamnati da masu hannu-da-shuni da su tallafa wa masu irin waɗannan sana’o’i na sarrafa kayayyakin da ake amfani da su, a riƙa ba su tallafi na jari ko kayan aiki, za a samu ci gaban da ba a tunani.

    Haka kuma, gwamnati ita ce ya kamata ta tabbatar da aiwatar da koyar da sana’o’in gargajiya a manhajojin ilimi tun daga matakin firamare har ya zuwa matakin jami’a, wannan zai ƙara haɓaka sana’o’in gargajiya da bunƙasa al’adu da tattalin arziƙi baki ɗaya.

    Manazarta

    Ado, A. (2019). Ra’o’in Bincike Kan Al’adun Hausawa. Katsina: Government Printing Press, Nigeria.

    Akodu, A. (1985) A Comparative Study of The Traditional and Contemporary Arts of The Maguzawa of Kano and Kaduna states Ph.D. Thesis, Department of Fine Arts, Faculty of Enviroment Design. Zaria: Ahmadu Bello Uniersity.

    Alhassan H. Da Wasu, (1982).Zaman Hausawa. Bugu na Biyu, Kaduna: Islamic Publication Bureau.

    Bargery, G.P.(1934).English Hausa Vocabulary. London: School of Oriented Studies, University Press.

    Bunza, A.M. (2006). Gadon Fexe Al’ada. Lagos: Tiwal Publication Company.

    Sa’id, B. da wasu,(2006).Qamusun Hausa.Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

    Muhammad, M.S. (2020).Bahaushiyar Al’ada.Tetfund. Kano: Bayero University Press.

    Soba, S. A. (2012). “Muhallin Bahaushe Jiya da Yau”.Kundin Digiri na Biyu da Aka Gabatar ga Sashen Harsunan Nijeriya.Sokoto:Jami’ar Usman Xanfodiyo.

    MUTANEN DA AKA TATTAUNA DA SU

    Lamba Suna Shekaru Sana’a Gari Rana
    1. Saidu Nakande 60 Manoni Ɓangashe 20/1/2026
    2. Ibrahim Abubuakar 65 Manomi Aku 21/1/2026
    3. Mustapha Ibrahim 40 Maƙeri Gaya 2/1/2026
    4. Malam Gambo 65 Baduku Gaya 13/1/2026
    5. Tabawa Adamu 61 Sana’ar Kaba K/ Gabari 11/1/2026
    6. Baba Sayyadi 43 Maƙeri Gaya 5/1/2026
    7. Mukhtari A.Isma’ila 45 Magini Ƙwanadroso 11/1/2026
    8. Dr. Abdullahi Madaki 62 Malamin Jami’a Gaya 6/1/2026
    9. Kawu Mu’azu 57 Wanzami Tarauni 3/1/2026
    10. Maisalati Durɓindai 58 Sana’arTukwane SRCOE 1/1/2026
    11. Adamu Isyaku 68 Masanin Al’adu Gamoji 15/1/2026
    12. Sadiya Sabo 60 Saƙar Kaba Aku 29/1/2026
    13. Dauda Yusif 50 Manomi Gaya 26/1/2026
    14. Muhammad Sani 65 Sana’ar  Fafa Shagogo 19/1/2026
        15. Mu’azu Adamu      72 Mai Unguwa Matamawa 20/1/2026

     

     

    Danna nan don karanta Tarihin Dr. Magaji Ahmad Gaya (PhD)

    Edita@rumasau-kallamu