Category: WikiHausa

Yadda ake amfani da WikiHausa

  • Abubuwa Goma Da Mai Azumi Ya Kamata Ya Sani

    Abubuwa Goma Da Mai Azumi Ya Kamata Ya Sani

    ZAFAFA GOMA: ABUBUWA 10 DA MUSULMI YA KAMATA YA SANI SANNAN YA KIYAYE A LOKACIN AZUMIN WATAN RAMADANA.

    GABATARWA:
    Alhamdulillahi Rabbil ‘Alamin. Tsira da amincin Allah (SWT) su tabbata ga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم, iyalansa da sahabbansa baki ɗaya. Muna yi wa Allah (SWT) godiya da Ya raya mu har muka sake gamuwa da watan Ramadan, watan rahama, gafara da tsira daga wutar Jahannama.

    Ibadar azumin ramadana ibada ce wacce ta samo asali da umarni daga Allah (SWT) kuma ibada ce wacce aka umarci al’ummomin baya da ita. Dalilin haka shi ne faɗin Allah (SWT) “ya ku waɗanda suka yi imani an farlanta muku azumi kamar yadda aka farlanta ma waɗanda suka gabace ku domin ku yi taƙawa”. Duba bakara: 2:183.

    Haka kuma Allah (SWT) yana cewa “watan ramadana shi ne wanda aka saukar da alkur’ani a cikinsa domin zama shiriya ga mutane……”Duba bakara: 2:185. Haka zalika, An ruwaito manzon Allah (SWT) yana cewa: “ haƙiƙa watan Ramadana ya zo muku. Wata ne mai albarka. Allah yana lulluɓeku (da rahamar sa) a lokacin sa.

    Yana saukar da jin ƙan sa, yana kankare zunubai kuma yana karɓar addu’o’i. Allah yana kallon tsere da kuke yi ta ɓangaren kyawawan ayyukan ku sannan ya sanar da mala’iku cikin girmama ku. Saboda haka ku nuwa Allah nagartar ku. Tabbas matsiyaci shi ne wanda ya kasa samun rahamar Allah a lokacin Ramadan ”Duba “ Majma’uz-zaw’id 3:142

    Haka kuma Manzon Allah صلى الله عليه وسلم yace “duk wanda ya azumci Ramadana yana mai imani da kwaɗayin samun lada, za a gafarta masa dukkan zunuban sa da suka
    gabata….”.Duba Bukhari 2014 da muslim 759-760. A wani hadisin ƙudusi Allah (SWT) yana cewa “ dukkanin aiki (mai kyau) na ɗan-adam da ya yi yana da lada goma kwatankwacinsa har zuwa ɗari bakwai amma banda azumi.

    Haƙiƙa azumi nawa ne kuma ni zany ni sakayyarsa. Shi mai azumi ya bar cinsa da shansa, da sha’awarsa saboda umarni na” manzon Allah ya cigaba da cewa “ mai azumi yana da farin ciki har guda biyu. Farin ciki lokacin da yake buɗa baki da kuma farin ciki lokacin da zai haɗu da ubangijinsa” ….Duba Bukhari 1904 da muslim 161-1151

    A cikin wannan taƙaitacciyar tunatarwa, na ambaci abubuwa goma da Musulmi ya kamata ya kiyaye domin azuminsa ya zama karɓaɓɓe mai cike da falala. Allah (SWT) ya ba mu ikon amfana da wannan tunatarwa da kuma ikon aiki da waɗanan abubuwa (ZAFAFA GOMA) domin rabauta da dacewa.

    NA FARKO: NIYYA

    Azumi ibada ce, kuma ibada ba ta inganta sai da niyya tun daga dare kafin a tashi
    da azumi. Wajibi ne mutum ya ƙulla niyyar azumi da zarar an ga wata tun kafin ya
    kwanta bacci ko kuma kafin fitowar alfijir.

    Hujja: Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce:“Duk wanda bai yi niyyar azumi da dare ba, babu azumi a gare shi.” (Abu Dawud, Tirmizi)

    NA BIYU: ƊAUKAR AZUMI DA GANIN WATA

    Azumin Ramadana yana farawa ne da ganin wata ko kuma cikar wata (sha‟aban zuwa 30) kuma yana ƙarewa da ganin wata (na shawwal).

    Hujja: Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce:“Ku yi azumi idan kun ga wata, ku buɗa azumi idan kun gan shi. ”(Bukhari da Muslim)

    NA UKU: TSAYAWA DA SALLOLIN FARILLA

    Ko da mutum yana azumi, idan ya raina sallah, ya jefa kansa cikin haɗari. Allah (SWT) yana cewa “ ku kiyaye sallolin ku musammam sallar (tsakiya) La‟asar….. Duba bakara 2:238

    Hujja: Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce:“Abu na farko da za a tambayi bawa a ranar Alƙiyama shi ne sallah….” (Tirmizi)

    NA HUƊU: YAWAITA KARATUN AL-KUR’ANI

    Ramadan wata ne na Al-Kur‟ani, don haka ake ƙwaɗaitar da musulmi da ya dage
    wajen yawaita tilawa da sauraron alkurani ba dare ba rana. Karatun alkurani shi ne
    zikiri mafi girma kuma a watan ramadana aka saukar da shi.

    Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya kasance duk watan ramadana mala‟ika Jibril yana zuwa sau biyu wajen sa domin tilawar alkurani tare da shi kuma an ruwaito sahabbai da magabata sun kasance suna duƙufa ba dare ba rana wajen raya dukkan kwanaki da karatun alkurani. Ana so mutum ya shagaltu sosai da karatun alkurani kuma ya zama shine mafi yawan ibadar sa acikin ramadana.

    Hujja: Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce:“Ku karanta Al-Kur‟ani, domin lallai shi zai zo ranar Alƙiyama yana yi wa masu shi ceto.” (Muslim)

    NA BIYAR: YAWAN ZIKIRI

    Zikiri yana rayar da zuciya kuma yana ɗaga darajar bawa.
    Hujja: Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce:“Kalmomi biyu ne masu sauƙi a harshe, masu nauyi a sikeli, masu soyuwa ga Rahama…” (Bukhari da Muslim)

    NA SHIDA: YAWAITA SALATI GA ANNABI صلى الله عليه وسلم.

    Salati hanya ce ta samun rahamar Allah. Don haka yawaita salati ga manzon Allah
    صلى الله عليه وسلم a kowane lokaci ibada ce mai albarka da ɗimbin lada musammam kuma a lokacin azumi.

    Hujja: Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce:“Duk wanda ya yi mini salati sau ɗaya, Allah zai yi masa sau goma.” (Muslim)

    NA BAKWAI: YAWAITA ADDU’A, MUSAMMAN A SAHUR DA BUƊA BAKI

    Mai azumi yana da matsayi na musamman wajen Allah. Lokacin da bawa ke azumi
    lokaci ne na addu’a gaba ɗaya amma kuma akwai keɓaɓɓun gurare da aka ayyana cewa
    ana so a yawaita addua kamar lokacin buɗa baki da lokacin sahur da sauransu.
    Hujja: Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce:“Mai azumi yana da addu‟a wadda ba a mayar masa da ita ba a lokacin buɗa bakinsa.” (Tirmizi)

    NA TAKWAS: SALLAR TARAWIHI DA TSAYUWAR DARE

    Wannan wata dama ce ta gafara da gyaran rayuwa.
    Hujja: Annabi صلى الله عليه وسلم ya ce: “idan mutum ya tsaya domin sallar dare (tarawih ko ƙiyamul laili) tare da liman har aka ƙare sallar, Allah zai rubuta masa lada kamar wanda ya raya daren gaba ɗaya da sallah.” (Abu dawud 1375)

    NA TARA: SADAKA DA CIYAR DA MAI AZUMI

    Ramadan wata ne na tausayi da taimakon juna.
    Hujja: Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce: “Duk wanda ya ciyar da mai azumi, zai samu irin ladan azuminsa.” (Tirmizi)

    NA GOMA: I’ITIKAFI, ZAKATUL FITR DA UMARA GA MAI HALI

    Goman ƙarshe lokaci ne na ƙara kusanci da Allah da dagewa sosai domin ƙara yawaita ibadu musammam a kwanakin da ake sa ran dacewa da lailatul kadari watau daren 21, 23, 25, 27 da kuma 29. I’itikafi ibada ce mai tarin lada da samun kusanci da Allah (SWT) kuma ana shiga I’itikafi ne a goman ƙarshe a Ramadan.

    Haka, zakkar fidda kai (zakatul fitr) ibace wacce aka shar’anta ta a kan dukkan musulmi namiji ko mace, babba ko yaro ko ɗan jariri kowa ana fitar masa da zakkar
    fidda kai.
    Hujja: An rawaito cewa Annabi صلى الله عليه وسلم yana yin I’itikafi a goman ƙarshe na Ramadan.(Bukhari). Haka kuma ya wajabta Zakatul Fitr (zakkar fidda kai) domin tsarkake azumi, kuma ya ce: “Umara a Ramadan tana da ladan Hajji.” (Bukhari da Muslim).

    ‘Ƴan uwa masu girma haƙiƙa duk wanda ya kiyaye waɗannan abubuwa goma, ya yi azuminsa da ikhlasi, to da yardar Allah zai samu cikakkiyar falalar Ramadan wanda Allah kaɗai ne ya barwa kansa sanin irin tanadin ladan da zai ba shi. Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya gafarta mana zunubanmu, Ya sa mu dace da Lailatul Qadr.
    Ameen.

    Husain M. Inuwa.
    usainiskima@gmail.com
    09042152353

    Danna nan don karanta Shan Azumi Ga Matafiya

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kaza Da Muzuru

    Tatsuniyar Kaza Da Muzuru

    ‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    ‎Kaza ce dai ta ce ba ta son kowa a cikin duk ‘yan uwanta zakaru masu nemanta. Ta dage ita sai muzuru kawai ta ke so da aure. Iyayenta ma suka ce ba za su ba ta shi ba. Ita kuma ta ce shi take so.

    ‎Da suka ga ta dage, sai suka ce, ‘To, mu dai babu ruwammu. Kada ki je ki jawo mana abin da zai hallaka mu baki ɗaya. Kaza kuwa ta ce ita dai shi ta ke so, ba za ta sake ba.

    ‎Sai aka kirawo ƙawayenta suka rarraba goron biki. ‎Shi ke nan, aka yi biki. ‎Sai ‘yammatan amarya suka je suna waka suna cewa:

    ‎Ke kaza kar ki jawo mana tserereninya da muzuru.’ Sai kaza ta ce: ‘Shi ba ya cin kaji, mhn. Shi ba zai ci kaji ba, mhn. In ji dai ni na kai kaina, mhn.’

    ‎Shi ke nan, sai suka ce da makaɗin ya sauya musu kiɗa. Shi kuwa makaɗin zakara ne, saboda a dangin amarya ya ke. Sannan ga kuma angwaye muzurai sun jeru, suna jin waƙa.

    ‎Shi ke nan, sai ‘yar ƙaramar kaza ta shiga fage ta ce:

    ‘Ni auta, autar kaza,

    In waiwaya haka,

    In muskuta haka,

    Sai na kan ji kiɗan da daɗi.’

    ‎Sai ta fita. Wata kuma ta shiga ta ce:

    ‘Ni wake-waken kaza,

    Kazar da ba a duka,

    Kazar da ba a zagi,

    In waiwaya haka,

    In muskuta haka,

    Sai na kan ji kiɗan da daɗi.’

    ‎Shi kuma makaɗin zakara, yana cewa:

    ‎’Daga baya-baya nake tsaya, In na ji kaya-kaya in naƙe.’

    ‎Sai kuma kaza ta uku ta shiga ta ce:

    ‘Ni ja-ja ja-jar kaza,

    Kazar da ba a duka,

    Kazar da ba a zagi,

    In waiwaya haka,

    In muskuta haka,

    Sai na kan ga idon muzuru!’

    ‎Daga nan fa sai angwaye muzurai suka yiwo kan ‘yan biki kaji radadada. Muzurai suka fara ciran su kai, su fafa, su fukafiki na kaji. Ita kuwa amarya sai cewa ta ke yi, ‘Kar ka cire mini fukafiki. Kar ka cire mini kai.’ Suka isa gida da ƙyar, suna cewa: Ga shi ta jawo mana tsiya. Wanda bai ji bari ba, zai ji hoho. An ce ta bari ta  ƙi.

    ‎Kurunkus kan ɗan kusu.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin Tatsuniyoyi Da Wasanni wanda Ibrahim Yaro Yahaya Ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Kura Da Zomanya

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Kura Da Zomanya

    Tatsuniyar Kura Da Zomanya

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    A can cikin wani ƙungurmin daji akwai wata Zomanya mai ciki, wadda gidanta yake kusa da na wata Kura, ita ma mai juna biyu. Suna zaman lafiya da junansu irin na maƙwabta. Wata rana sai Zomanyar nan ta je wurin Kura ta ce mata: “Kin ga ni da ke mun kusa haihuwa, ya kamata mu nemi wurin da za mu rinƙa  ɓoye ‘ya’yanmu.

    “Sai Kura tace: “E, gaskiya ne, to amma bari mu tona rami babba domin mu saka ‘ya’yanmu a ciki.” Da suka tona rami sai suka zauna tare, har lokacin haihuwarsu ya yi. Da suka haihu, sai suka tara ‘ya’yansu a rami ɗaya, kuma suka yi alƙawari cewa Kura za ta rinƙa samo musu abinci, ita kuma Zomanya za ta rinƙa renon ‘ya’yansu.

    Suka zauna, in Kura ta tafi neman abinci ta dawo, sai ta miƙa wa Zomanya ta ci, kuma ta raba wa ‘ya’yansu. Kullum haka. Amma ita kuwa Zomanya, in an kawo mata abinci sai ta ba ‘ya’yanta su ci, in sun ƙoshi sai ta cinye sauran, ta hana ‘ya’yan Kura. Kullum haka, kuma in Kura ta zo ta ce za ta duba lafiyar ‘ya’yanta sai Zomanya ta ce ai sun ci abinci sun ƙoshi, suna barci.

    Haka suka yi ta yi, har dai wata rana Kura ta ce sai ta ga ‘ya’yanta. Da ta leƙa ramin ta jawo ‘ya’yanta sai ta ga duk sun rame. Sai ta tambayi ‘ya’yanta abin da ya same su, suka rame haka. Sai ‘ya’yan suka ce ai ba a ba su abinci, in an kawo abinci sai Zomanya ta hana su, ta bai wa ‘ya’yanta, su kuwa sai ta sa su yi barcin dole kullum.

    Da jin haka sai ran Kura ya ɓaci, ta yi kuka, ta yi gumani da ƙaraji mai tsanani, ta ce tun da Zomanya ta ci amanarta, to ita da ‘ya’yanta za su cinye Zomanya da ‘ya’yanta gaba ɗaya. Ko da Zomanya ta ji abin da Kura ta faɗa, sai ta rasa abin da za ta yi, idanunta suka raina fata.

    Tsoro ya kama ta. Sai ta dubi Kura ta ce: “To shi ke nan, tunda kin ce ni da ‘ya’yana mun zama nama, to ki yi haƙuri mu fito daga rami tukunna.” Zomanya ta shiga rami ta gaya wa ‘ya’yanta idan ta fita Kura ta bi ta, to su fita da gudu su yi nasu wuri. Da Kura ta sake magana, sai Zomanya ta haɗa manyan kunnuwanta biyu, ta ɗan miƙo su waje ta ce da Kura: “Don Allah ki riƙe mini takalmana kafin in fito.

    “Jin haka sai ya sa ran Kura ya ɓaci, ita a tsummaninta yaya za a yi kamar Zomanya ta ce ta riƙe mata takalmanta, bayan ta zama nama a wurinta. Sai ta kama kunnuwan Zomanya da ƙarfi ta finciko su ta jefar, wai ita a nufinta takalma ne. Sai kunnuwa suka sulluɓe, Zomanya da ‘ya’yanta suka ranta a na kare.

    Kamar wasa, Kura ta kasa kama ko ɗaya daga cikinsu. Da ba domin Gizo ba da na shara muku ƙarya. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    •  Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka.
    • Ƙarshen maci amana jin kunya.
    • Kowa ya ci zomo, ya ci gudu

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Mace Mai Ciki

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Mace Mai Ciki

    Tatsuniyar Mace Mai Ciki

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Wata rana wata mata mai juna biyu ta je ɗibar ruwa a bakin rafi. Bayan ta cika tulunta da ruwa, sai ta kasa ɗauka saboda cikinta ya girma sai nishi take yi, abin tausayi. Kuma ga shi ita kaɗai ce ƙwal a wurin.

    Haka ta haƙura ta zauna. Can sai ga wani mutum ya taho, sai ta dube shi ta ce: “Malam don girman Allah ka ɗora ni mana.” Sai yace shi ba zai ɗora ta ba sai dai idan za ta yi masa wani alkawari. Mai ciki ta dube shi ta ce: “Na mene ne?” Shi ko ya kaɗa baki yace: “Idan kin haihu, in namiji ne to abokina ne, idan kuma mace ce, to matar ɗana ce.

    ” Da jin wannan sharaɗi sai ta yarda. Ya ɗauki tulu ya ɗora mata ta kama hanya ta tafi gida. Da ta je gida sai ta yi wa mijinta bayanin yadda suka yi da mutumin. Da yake mijinta mai sauƙin kai ne, sai ya ce: “To shi ke nan, Allah ya sauke ki lafiya.

    ”Bayan ’yan kwanaki sai mutumin ya zagayo gidan matar, suka gaisa. Ya nuna mata ɗansa suka yi sallama ya koma gida. Bayan wata ɗaya sai matar ta haifi ’ya mace, amma jikinta na jaki ne. Da mutumin ya ga haka sai ya yi halin dattaku ya ce: “To shi kenan tun da an yi alƙawari ai sai an cika.

    ”Sai ya kira ɗansa aka ɗaura musu aure da yarinyar ya kai ta gidansu. Yaro ya zauna da mace mai jikin jaki, ya ɗaure ta a gida. Amma duk sanda ya tafi gona idan ya dawo gida sai ya tarar an yi masa shara, an dafa masa abinci an kuma kai masa ruwan wanka bayan ɗaki.

    Kullum haka, sai abin ya fara ba shi tsoro tun da ba kowa a gidan. Rannan sai ya je ya sami babansa ya gaya masa, amma sai baban ya ƙi kula shi sai ya kore shi. To da ma yaron yana mutunci da wata tsohuwa maƙwabciyarsa dangarsu ɗaya. Sai wata rana ya zauna a gindin bishiya, yana tunanin abin mamakin da ke samunsa.

    Da tsohuwar ta gan shi a zaune haka, sai ta kira shi ta ce: “Ɗanyaro me ke damunka ne?” Shi ko sai ya kwashe labari ya bai wa wannan tsohuwa. To da ma ashe tsohuwa tana ganin duk abin da yarinya take yi idan ya tafi gona. Watau rikiɗa take yi ta koma kyakkyawar budurwa, ta shiga yi masa waƙa, ta yi shara, ta yi wanke-wanke, ta dafa abinci, ta ɗebo ruwa a rijiya ta kai masa banɗaki.

    Duk bayanta gama kafin ya dawo sai ta mayar da jikinta na jaka, ta ɗaure kanta a turke.
    Da tsohuwa ta gama bai wa yaron labarin abin da take gani sai ta shawarce shi da cewa gobe ya kwashi kayan aiki kamar zai tafi gona, idan ya kama hanya sai ya ratse a hanya, ya zagayo gidanta.

    Bayan sun gama shirya zancensu, sai ya koma gida yana mamaki, ya shiga ɗaki ya kwanta. Da gari ya waye sai ya saka kayan aiki ya ɗauki fartanyarsa ya kama hanyar gona. Bayan ya tafi ya yi nisa sai ya ratse cikin ciyawa, ya zagayo ta gidan tsohuwa, ya same ta a ɗaki.

    Daga nan sai suka ɓuya suka shiga leƙen yarinyar. Jim kaɗan sai suka ga ta rikiɗa ta koma kyakkyawar mace, ta fara waƙa ta kama shara da sauran ayyukan gida, ta shirya miya, ta dafa abinci, ta zuba nasa, ta kai masa ruwan wanka banɗaki. A daidai lokacin da ta fito daga bayan gida sai mijinta ya tsallaka danga ya dira a gabanta.

    Sai kawai ta razana za ta rikiɗa sai ya kama hannunta ya fara yi mata waƙa yana roƙon ta. Da ta ji waƙarsa sai ta fara kuka tana roƙon ya yafe mata. Shi kenan suka yi zamansu cikin daɗi suka ci gaba da more rayuwarsu cikin ƙauna da farin ciki. Dan kan ɓarya, ba domin Gizo ba da na sheƙa muku ƙarya. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Alkawari kaya ne, in an sauke sai a huta.
    • Tsintar dami a kala.
    • Rabon kwaɗo ba ya hawa sama.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Cilakowa Da Kodokodo

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Cilakowa Da Kodokodo

    Tatsuniyar Cilakowa Da Kodokodo

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wasu tsuntsaye biyu a wani baƙin daji da ke ƙasashen Gabas. Ɗaya sunanta Cilakowa, ɗayar kuma Kodokodo. Ita Cilakowa tana da dogon baki, ita kuma ’yar Sarkin tsuntsaye ce.

    To tana so ta yi aure, amma saboda dogon bakin nan nata, ba wanda ya fito domin ya aure ta. Ana nan, sai rannan ta yi tunanin cewa bari ta je wurin Kodokodo ta yi mata dabara, ta ce za ta biki ta ba ta aron bakinta, idan ta gama harkar bikin za ta dawo mata da shi.

    Sai ta yanke shawarar haka, ta je ta yi bayani sai Kodokodo ta ba ta. To ashe daga bikin nan aure za ta yi. Sai ta gama biki, ita ma ta yi aure. Ana nan, ana nan sai Kodokodo ta ji shiru, ko labarin Cilakowa babu. Ga shi kuma bakin Cilakowa da ta karɓa ta ba ta aron nata, ya yi mata tsawo, ta yadda ma ba ta iya magana ko cin abinci da shi.

    Sai ta fara ramewa saboda ƙishirwa da yunwa, abin ya dame ta. Da ta ga ba dama, watau ba za ta iya ci gaba da jurewa ba, sai wata rana ta yanke shawarar cewa gara ta je ko ina ne neman Cilakowa.

    Duk inda ta je sai a riƙa cewa ai sunan Cilakowa Sheba. Kodokodo dai ta mai da hankalinta wajen neman bakinta. Tana cikin tafiya sai ta tarar da wasu mutane suna daka. Da ta ƙarasa kusa da su, sai ta durƙusa ta gaishe su, da waƙa kamar haka: –

    “Masu dakan nan, masu dakan nan;
    Ba ku gane min Sheba ba?
    ’Yar gidan su Dalailu.
    ’Yar Sarkin tsuntsaye. Ta karɓi aron bakina. Daga biki sai aure. Wutsiyata ta shinge. Bakina na talaka talak.”

    Suka ce: “A a, ba mu gan ta ba, ki yi gaba.” Da ta yi gaba sai ta ga wasu mutanen, su ma ta sake yi musu irin wannan waƙar. Sai suka ce da ita ta je ta shiga wani gidan, sai
    ta shiga.

    Tana shiga sai suka yi arba da Sheba, ta dube ta tace: “Na biyo bakina, daga aro sai aure?” Kafin ma Cilakowa ta yi wata magana sai fut, ta cire bakinta, ta ba ta nata, ta tafi. Da mijin Cilakowa ya dawo sai ya ga Sheba da dogon baki.

    Ganinta haka ya ba shi mamaki, sai ya dube ta yace, “Sheba ɗauke karan nan.” A cikin murya tattausa ta mayar masa da jawabi cewa: “Ba kara ba ne, bakina ne.” Sai ya dube ta ya ce: “To in haka ne ba zan iya zama da ke ba, bakinki ya yi tsawo da yawa.” Shi ke nan ya kore ta, ta koma gida. Ƙurunƙus.

    Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • In ba ki da gashin wance kada ki ce za ki yi kitson wance.
    • Kayan aro ba ya rufe ƙwauri.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar Daskin Dariɗi

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniyar Daskin Dariɗi

    Tatsuniyar Daskin Dariɗi

    ‎Ga ta nan ga ta nan ku.

    Da gero da dawa da maiwa da duk dai kayan abinci haka, su shinkafa, acca, iburu, alkama da burtuntuna, sai suka shirya za su tafi gun wani saurayi wanda ya ce duk wata wadda ta faɗi sunansa, ita zai aura.

    ‎Shi ke nan. Ko wacce ta ci kwalliya. Ita kuwa burtuntuna ba ta yi kwalliya ba don ba ta da kayan ado. Suka kama hanya suna tafiya. A kan hanyar da su ke wucewa sai suka ga wata ‘yar tsohuwa a tsugunne da ruwan wankanta.

    ‎Sai tsohuwa ta ce da dawa, ‘Don Allah yarinya, zo ki cuɗa ni mana? ‎Sai dawa ta ce, ‘A, don Allah ku ji ‎tsohuwa? In yi kwalliyar tawa haka sannan ki ce in zo in cuɗa ki? Sai ta wuce ta ki cuɗa ta.

    ‎Sai kuma shinkafa ta zo, tsohuwa ta ce da ita, ‘Don Allah yarinya zo ki cuɗa ni mana? Sai shinkafa ta ce, ‘Duk wannan kwalliyar tawa in tsaya in cuɗa ki?’ Sai ta ki cuɗa tsohuwa, ta shige abinta.

    ‎Sai su maiwa, su gero, su alkama suka zo da dai dai, kowacce tsohuwa ta tambaya ta cuɗa ta sai ta ki, ta yi wucewarta. Daga nan sai ga burtuntuna ta zo. Sai tsohuwa ta ce da ita, ‘Yarinya don Allah zo ki cuɗa ni mana?’

    ‎Sai burtuntuna ta ce da ita, ‘To.’ Ta shiga cuɗa ta. Tana cikin cuɗa ta, sai bayan ‘yar tsohuwa ya burme Yarinya ta ce, ‘Yau na shiga uku, na lalace. Sai ‘yar tsohuwa ta ce, ‘Mene ne?’ Burtuntuna ta ce, ‘Bayanki ne ya ɓurme.’

    ‎Sai ‘yar tsohuwa ta ce, ‘Me kika gani a ciki?’ Ta ce, ‘Na ga kwatashi guda biyu, babba da ƙarami. ‎Ta ce, ‘To, ɗauko ƙaramin.’ Burtuntuna ta ɗauko ƙaramin kwatashi. ‎Sai tsohuwa ta ce, ‘To, ajiye nan.’ Burtuntuna ta ajiye.

    ‎Can sai tsohuwa ta haɗiye burtuntuna. Ta mai da ita fara, ta fito da ita waje, ta duba ta ta ce, ‘Kai, ba haka na ke son ki ba. Sai ta sake haɗiye ta, ta mai da ita ja zur kamar tsada, ta fito da ita waje ta duba ta ta ce, ‘Yauwa, haka na ke son ki.’

    ‎Sai ta buɗe ɗan kwatashin nan, ta ba burtuntuna kayan ado irin na mata kamar su zannuwa, su fatala, su yari, su awarwaro. Burtuntuna ta ci ado da su. Da ta gama adon, sai tsohuwar ta ce, ‘To, ga shi na shirya ki. Kin san sunan yaron da za ku wurin sa?’ Ta ce, ‘A a, ban sani ba.’

    ‎Sai tsohuwa ta ce, ‘Sunansa Daskin-da-riɗi.’ Sai ta ce, ‘To. ‎Sai ta yi godiya, suka yi sallama. Shi ke nan. Sai burtuntuna ta tafi ta sami sauran ‘yan’uwanta a hanya. Da suka gan ta sai suka dinga cewa, ‘Kun ga waccan shegiyar.

    Wa ya ba ta aron kaya ta ɗaura?’ Sai kuma su ce, ‘Wa ya sani ne? Mu yi maza mu je kada ta riga mu. Ko da ya ke ma ko ta je me zai yi da ita? ‎Shi ke nan. Da suka je, sai suka jajjeru. Dawa ta fara zuwa kofar gidan saurayin. Ta ce:

    ‘Assalam alam ɗan yaro.

    Assalam alam.’

    ‎Sai ya ce:

    Wane ne nan ya ke mana,

    Assalam alam?

    Sai ta ce:

    ‎Dawarku ce ta ke maka Assalam alam.

    Mai tuwo da daɗi, ni dawa Mai tuwo da daɗi

    ‎Sai ya ce:

    Na ji naki suna yarinya, Ba ni nawa suna.

    ‎Sai ta ce:

    Ban san ka ba, ɗan yaro. Ban san ka ba.

    ‎Sai ya ce:

    Da ba ki san ni ba, yarinya, Koma da baya ki sha kuka.

    ‎Dawa sai ta koma da baya ta yi ta kuka saboda ba ta san sunan saurayin ba, kuma babu damar ta aure shi ke nan.

    ‎Sai kuma ga su maiwa, da gero, da iburu, duk dai suka zozzo. Kowacce ya ce ta faɗi sunansa, sai ta ce ba ta san shi ba. Suka yi ta kuka. Shi kuma ya ce sai wadda ta san sunansa zai aura.”

    ‎Shi ke nan, nan sai ga burtuntuna ta zo: Sai suka ce da ita; ‘Ke don Allah, mu ma ba mu san sunansa ba, balle ke! ‎Sai ta rabu da su. Sannan sai ta je kofar gidan saurayin ta ce:

    Assalam alam, dan yaro.

    Assalam alam.

    ‎Sai ya ce:

    Wace ce nan ta ke mini Assalam alam?

    ‎Sai ta ce:

    Burtuntunarku ce ta ke maka Assalam alam.

    Burtuntuna, ai ni ce, Mai ɓata kaya.

    ‎Sai ya ce:

    Na ji naki suna, yarinya. Ba ni nawa suna.

    ‎Sai ta ce:

    Daskin-da-riɗi dan yaro Daskin-da-riɗi.”

    ‎Sai ya ce:

    “Buɗe ki shigo, yarinya, Buɗe ki shigo.”

    ‎Shi ke nan sai ta buɗe ta shiga. Sai kuma sauran su dawa, su gero, su iburu su ke cewa, ‘Ni zan yi miki wanka.’

    ‘Ni zan yi miki wanke-wanke.’

    ‘Ni zan yi miki alwala.’

    ‘Ni zan yi miki shara.’

    Da sauran abubuwa dai na barance. Sai  burtuntuna ta yarda suka zama barorinta. Shi ke nan. Ƙurunƙus.

    Wannan tatsuniyar an ciro ta ne daga littafin Tatsuniyoyi da Wasanni wanda Ibrahim Yaro Yahaya ya wallafa.

    ‎Danna nan don karanta Tatsuniyar Budurwa Marar Tabo

    Edita@rumasau-kallamu

  • Maƙala Mai Taken Raujin Hikima: Gurbin Waƙoƙin Gargajiya A Rayuwar Hausawa

    Maƙala Mai Taken Raujin Hikima: Gurbin Waƙoƙin Gargajiya A Rayuwar Hausawa

    Manazarta: Sani, A-U. (2025). Raujin hikima: Gurbin waƙoƙin gargajiya a rayuwar Hausawa. Njinga & Sepé: Revista Internacional de Culturas, Línguas Africanas e Brasileiras. São Francisco do Conde (BA), UNILAB, Brazil, 5 (Especial I), 11-23. https://revistas.unilab.edu.br/index.php/njingaesape/article/view/2340

    Raujin Hikima: Gurbin Waƙoƙin Gargajiya a Rayuwar Hausawa

    By

    Abu-Ubaida Sani

    Department of Languages and Cultures,

    Federal University Gusau, Zamfara, Nigeria

    Email: abuubaidasani5@gmail.com | abu-ubaidallah@fugusau.edu.ng

    ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736

    Abstract

    Waƙoƙin Gargajiya (traditional songs) hold a significant and distinct place in Hausa culture, functioning as an informal educational system that imparts valuable lessons in both knowledge and social conduct. This paper examines the role of these songs in shaping the lives of the Hausa people, particularly in the past.

    It explores examples from various forms of traditional songs, including songs from folktales, community games, lullabies, and work songs sung by women during household chores. The study finds that Waƙoƙin Gargajiya have long played an essential role in teaching ethics, arithmetic, language skills, and in preserving cultural traditions and history.

    The paper concludes with recommendations for modernizing these songs through audio recordings, animated videos, and mobile applications, to ensure that they continue to provide valuable benefits for future generations.

    Keywords: Hausa, Hausa People, Hausa Traditional Songs, Hausa Oral Literature, Hausa Culture

    Tsakure

    Waƙoƙin gargajiya suna da gurbi na musamman a rayuwar Hausawa. Sun kasance tamkar makaranta mai zaman kanta wadda daga gare ta ake koyon darussa masu yawa na ilimummuka da zamantakewar rayuwa. Wannan takarda ta mayar da hankali wajen nazartar tasirin waƙoƙin gargajiya wajen daidaita alƙiblar rayuwar Hausawa, musamman a da.

    An zaƙulo misalan waƙoƙin da aka yi amfani da su daga tatsuniyoyi da wasannin dandali da wasannin tashe da kuma waƙoƙin reno da waɗanda mata suke rerawa yayin gudanar da aikace-aikace a cikin gidajensu. Binciken ya gano cewa, waƙoƙin gargajiya sun daɗe suna taka rawa wajen koyar da tarbiyya da lissafi tare da taimakawa wajen naƙaltar harshe da sanin al’adu da tarihi da makamantansu.

    Daga ƙarshe binciken ya bayar da shawarwari da suka haɗa da nuna dacewar zamanantar da waɗannan waƙoƙin gargajiya zuwa tsarin odiyo da bidiyoyin katun da manhajoji domin ci gaba da morar gagarumin alfanun da yake tattare da su.

    Fitilun Kalmomi: Hausa, Hausawa, Waƙoƙin Gargajiya, Adabin Baka, Al’adun Hausawa

    1.0 Gabatarwa

    Waƙa tsararren zance ne wanda ake shiryawa ta hanyar zaɓan kalmomi na musamman da jera su bisa wani tsari mai armashi da zai ba da wani ƙayataccen rauji.[1] Waƙoƙi sun kasance masu matuƙar jan hankali da tasiri a rayuwar Hausawa. Masana da manazarta sun gudanar da ayyuka daban-daban dangane da waƙoƙi, inda suka nuna alaƙarsu da sha’anonin rayuwar Hausawa.

    [2]Waƙoƙin gargajiya suna da tsohon tarihi a matsayin makarantar koyar da ilimummuka da kuma maƙerar sarrafa harshe da luguden kalmomin fasaha. Sauye-sauyen zamani sun yi matuƙar tasiri a kansu ta yadda har sun fara dusashewa, musamman yanzu da waƙoƙin zamani suka maye gurabunsu. A bisa haka, akwai buƙatar bitar waƙoƙin Hausawa na gargajiya domin ƙwanƙwance gudummawarsu ga cigaba da bunƙasar ilimi da zamantakewar Hausawa.

    1.1 Hanyoyin Gudanar Da Bincike

    Kadadar wannan binciken ba ta fita daga da’irar adabin Hausawa ba. Ko a cikin adabin, an taƙaita ta zuwa waƙoƙin gargajiya. An tsamo misalan da suka dace da takardar daga cikin ɗimbin waƙoƙin gargajiya da ake da su a Hausa. Sun haɗa da waƙoƙin da ake samu a cikin tatsuniyoyi da waƙoƙin reno da na wasannin dandanli da na tashe da sauransu.

    Bitar ayyukan da suka gabata masu alaƙa da adabi, musamman adabin gargajiya, ya taimaka wajen yi wa aikin jagoranci. Bayanai da aka samu daga karance-karancen rubuce-rubucen da aka yi masu alaƙa da aikin sun daidaita wa binciken alƙibla.

    An ɗora binciken a kan tunanin Hausa ta “da tsohuwar zuma ake magani.” A bisa wannan fahimta, binciken yana ganin cewa, sauyawar zamani bai kamata ya kawo ƙarshen ɗimbin alfanu da hikimomin da suke tattare a cikin waƙoƙin gargajiyar Bahaushe ba. A maimakon in an ci moriyar ganga a ya da kwaurenta, abin da ya fi dacewa shi ne,  a zamanantar da su domin ci gaba da tatsar hikimomin da suke cikinsu.

    Gurbin Waƙoƙin Gargajiya a Rayuwar Hausawa

    Waƙoƙin Hausa na gargajiya su ne waƙoƙin da Hausawa suka fara mu’amala da su a rayuwa. Sun mamaye dukkannin fannonin al’ada da adabin Bahaushe. Wannan ya haɗa tun daga wasanni da tashe da bukukuwa da ayyukan gida, har ma da fannonin zamantakewa da suka shafi aure da haihuwa da reno da sauransu.

    Kasancewar waƙa zancen hikima wanda yake tasiri a kan ruhi tare da sanyaya rayuwa ko saka mata karsashi ko ziguwa (wanda ya danganta da nau’in waƙar da muhallin da ake rera ta), Hausawa sukan samar da waƙoƙi a kusan kowace gaɓar rayuwa da suke gudanar da wata muhimmiyar al’ada.

    Kamar yadda Gobir & Sani (2021 p. 9) suka nuna, waƙoƙin gargajiya na Hausa sun haɗa da waƙoƙin tatsuniyoyi da wasannin dandali da na tashe da waƙoƙin aikace-aikace da makamantansu. Waƙar gargajiyar tana ɗaukar fasaloli daban-daban bisa manufar ƙirƙirar ta da muhallin da ake amfani da ita da kuma aikin da ake buƙata ta aiwatar.

    Wannan ya sa waƙoƙin gargajiya suka ɗauki manya da ƙananan jigogi daban-daban, tun daga kan koyar da lissafi da jarumta da nitsuwa da faɗakarwa da huce takaici har zuwa ƙarfafa guiwa da makamantansu. A ƙasa an kawo jerin alfanun waƙoƙin gargajiya ga rayuwar Hausawa.

    2.1 Faɗakarwa

    Faɗakarwa yana nufin jan hankali ko hannunka-mai-sanda zuwa ga aikata wani abu mai kyau ko hani kan aikata wani mummunan aiki. Faɗakarwa yana iya kasancewa tunatar da mutum game da wani abin da ya shagala. A irin wannan yanayi, akan ankarar da shi a fargar da shi daga shagalar da ya yi. Waƙoƙin gargajiya sun kasance babbar hanyar faɗakarwa da jan hankali. A duba misalin da aka kawo a ƙasa:

    Waƙar Tashen Ke Kika Je Ki Gidansu Direba

    Wannan wasan tashe ne wanda yara mata suke gudanarwa. Akan samu yarinya guda ta cusa tsummokara a cikin rigarta, daidai cikinta yadda zai yi tulu tamkar mace mai ciki. Za kuma ta shafe fuskarta da shuni ko gawayi ko baƙin bayan tukunya ko dai wani abu mai kama da wannan. Daga nan za ta shiga gaba yayin da sauran masu tashe suke biye a baya.

    Yayin da aka iso wurin gabatar da tashe, yaran za su riƙa zungurar wannan mai ciki tare da tuhumar ta da cewa, ita ta kai kanta gidansu Direba har ta samo cikin shege. Ita kuwa za ta riƙa bayyana dalilin da ya sa ta je (Gidansu Direba). Duk wannan yakan kasance ne cikin waƙa, kamar haka:

    Yara: Ke kika je ki gidansu Direba!

    Mai Ciki: Da ban je ba ina zan samu?

    Kullum biredi,

    Kullum Shayi

    Kullum tsire yanka goma,

    Yanzu likita ya auna ni,

    Ya ce cikin direbobi ne,

    Wayyo Direba ka cuce ni!

    Wayyo Direba ka ci amana!

    Idan aka lura da wannan waƙa, tana ɗauke da gargaɗi game da kwaɗayi. Wannan mai cikin shege ta bayyana da kanta cewa kwaɗayi ne ya kai ta, inda take lissafo abubuwan da suka ja ta gidansu Direba. Sun haɗa da biredi da shayi da tsire. Daga ƙarshe sai ake nuna irin halin ƙaƙa-ni-ka-yi da ta shiga a dalilin wannan kwaɗayi, wato samun cikin shege.

    Haƙiƙa wannan togaciya ce da kuma hannunka-mai-sanda ga ɗaukacin mata da ‘yanmata da kuma iyayensu. A ɓangare ɗaya kuwa, gargaɗi ne ga iyaye da sauran mariƙa da su riƙa kula da jin daɗi da walwalar waɗanda Allah ya damƙa musu a hannunsu.

    2.2 Nishaɗantarwa

    Nishaɗi yana nufin wani yanayi na jin daɗi ko farin ciki da annashuwa da ɗan’adam ko wata halitta takan iya shiga. Mai nishaɗi yana kasancewa cikin walwala da rashin damuwa. Nishaɗi yana da amfani matuƙa ga rayuwar ɗan’adam, domin yakan taimaka wurin kauce wa kamuwa da wasu cututtuka musamman waɗanda suka shafi zuciya da ƙwaƙwalwa.

    Kusan dukkanin waƙoƙin gargajiya suna ɗauke da nishaɗantarwa ta fuskokin da suka haɗa da:

    • Nishaɗantar da mai rera waƙar
    • Nishaɗantar da mai sauraron waƙar

    A duba misalin da aka kawo a ƙasa:

    Waƙar Wasan Tashe Ta Macukule

    Wannan wasan tashe ne na maza manya. Akan samu ɗaya daga cikin masu wasan ya yi shigar Gwari, sannan ya shafe fuskarsa da farar ƙasa ko wani abu mai kama da wannan. Zai kuma riƙe ƙwarangwal na kan wata dabba, kamar akuya ko tinkiya da makamantansu. Yayin da aka iso wurin gabatar da tashen, wannan mai shigar Gwarawa zai riƙa ba da waƙa, saura kuwa suna amsawa. Ga yadda abin yake:

    Bayarwa: Salamu’alaikum, ga baƙonku na Gwari,

    Amshi: Macukule.

    Bayarwa: Shekara ta dawo,

    Amshi: Macukule.

    Bayarwa: Ni ma na dawo.

    Amshi: Macukule.

    Bayarwa: Zan muku tashen Gwari,

    Amshi: Macukule.

    Bayarwa: A can ƙasarmu Gwari,

    Amshi: Macukule.

    Bayarwa: Kan kare da daɗi,

    Amshi: Macukule.

    Bayarwa: Romon kan jaki daɗi,

    Amshi: Macukule.

    Bayarwa: Tun ba wurin idon ba,

    Amshi: Macukule.

    Bayarwa: Tana ko taliya ce,

    Amshi: Macukule.

    Bayarwa: Kan ƙuda kuɓewa,

    Amshi: Macukule.

    Bayarwa: Majina kitse ne,

    Amshi: Macukule.

    Bayarwa: Tumbuɗi da daɗi,

    Amshi: Macukule.

    Haƙiƙa wannan wasa yana samar da nishaɗi musamman ga masu kallo. Idan mutum ya dubi yadda mai waƙar ya taƙarƙare yana maganar Gwari, dole abin ya ba shi sha’awa da dariya. Bugu da ƙari, zantukan cikin waƙar suna ɗauke da ban dariya da nishaɗantarwa, musamman yadda ake bayyana waɗannan abubuwan da Hausawa ba sa cin su a matsayin abinci mai daɗi.

    2.3 Koyar Da Lissafi

    Lissafi a nan yana nufin ƙidaya, wato ƙididdige adadin wani abu kamar kuɗi ko ‘ya’yan itatuwa, ko duwatsu da dai makamantansu. Abu ne mai kyau ya kasance mutum ya iya lissafi, domin kuwa lissafi yana ɗaya daga cikin gishirin rayuwa. Waƙoƙin gargajiyar da suke koyar da lissafi sun haɗa da:

    Waƙar Wasan Ɗura-Ɗura

    Ɗura-ɗura wasa ne na yara mata. Masu wasan za su nemo ƙananan duwatsu ko ɗanyun ‘ya’yan kanya ko makamancin wannan, kowa guda bibbiyu. Daga nan wadda za ta fara wasa za ta riƙe dutse ɗaya a hannun dama ɗaya kuwa a hagu – idan wasan ‘yar hannu biyu ce.

    Sai ta riƙa cilla su sama cikin ƙwarewa tare da canza musu hannu. Wato sai ta riƙe na hannun dama da hannun hagu, na hannun hagu kuwa ta cafe shi da hannun dama. Da zarar ta faɗi, sai abokiyar wasanta ta karɓa. Ana kuma gudanar da ‘yar hannu ɗaya, ko ‘yar duwatsu uku a maimakon biyu.

    Mai gudanar da wannan wasa za ta riƙa lissafi/ƙirge cikin waƙa. Waƙar ta danganta da ɗurawa take yi ko fanshewa. Ga misalin waƙar ɗurawa:

    Ɗura-ɗura ɗaya,

    Ɗura ya ban biyu,

    Ɗura ya ban uku,

    Ɗura ya ban huɗu,

    Ɗura ya ban biyar,

    Ɗura ya ban shida,

    Ɗura ya ban bakwai,

    Ɗura ya ban takwas,

    Ɗura ya ban tara,

    Ɗura ya ban goma.

    Goma ya ban ɗaya,

    Goma ya ban biyu,

    Ishina.

    Ishi ya ban ɗaya,

    Ishi ya ban biyu,

    Haka za a ci gaba da yi har a je: Talana wato talatin (30) ke nan; Arbana wato arba’in (40) ke nan, …. Riɗana wato ɗari (100) ke nan…

    Haka abin zai ci gaba har zuwa wurin da mai wasa ta faɗi. Haƙiƙa wannan hanya ce ta koyon lissafi, musamman ƙidaya.

    2.4 Ƙarfafa Danƙon Zumunci

    Zumunci ko zumunta yana nufin kyakkyawar alaƙa ko dangantaka ta jini ko ta abota da akan samu tsakanin mutane. Za a iya hasashen cewa kalmar ta samo asali ne daga zumu da ke ɗaukar ma’anar ɗan uwa ko sa’a ko aboki.

    Waƙoƙin gargajiya suna taka rawar gani matuƙa wurin ƙarfafa ɗanƙon zumunci tsakanin yara da kuma iyayen yaran kansu. Taruwa wuri ɗaya da ake yi domin rera waƙoƙin tare da yabon ƙawaye da aiki tare duk suna taimakawa wajen ƙarfafa danƙon zumunci. A duba misalin da aka kawo a ƙasa:

    Waƙar Wasan Gariye

    Yara mata ne suke gudanar da wannan wasa. Masu wasa za su yi da’ira mai faɗi ta hanyar barin ‘yar tazara a tsakanin juna. Daga nan ɗaya za ta shigo tsakiya. Za ta riƙa bayar da waƙa saura kuwa suna amshi tare da tafi. Waƙar ita ce kamar haka:

    Bayarwa: Duk garin nan,

    Amshi: Gariye.

    Bayarwa: Ba ni yaya,

    Amshi: Gariye.

    Bayarwa: Ba ni ƙanwa,

    Amshi: Gariye.

    Bayarwa: Sai ƙawata wadda muke mutunci,

    Mutuncin ma mutunci.

    Amshi: Gariye.

    Bayarwa: Sai ƙawata Laraba[3] zo mu cashe,

    Amshi: Gariye.

    Bayarwa/Amshi: Gariye na malilisi,

    Gariye,

    Girgiza wando, fatari, siket,

    Addinin ‘yanmata.

    Ke kika yarda? Aka sa miki?

    Girgiza wando, fatari, siket,

    Addinin ‘yanmata.

    A wannan gaɓa, yara za su taka rawa su cashe. Daga nan kuma wadda ta ba da waƙa za ta koma cikin sauran yara. Wata daban kuma za ta fito domin ba da waƙa. Haƙiƙa wannan waƙa tana ƙara danƙon zumunci tsakanin yara, kamar yadda ambaton sunan wata a matsayin ƙawa yakan faranta mata rai tare da nuna mata cewa an damu da ita matuƙa.

    2.5 Addu’ar Alheri

    Addu’a dai a taƙaice tana nufin roƙon wani abu daga Allah shi kaɗai ta amfani da waɗansu lafuzza na musamman (Ainu, 2007 p. 52). Akwai waƙoƙin gargajiya da dama da suke ɗauke da addu’ar alheri. A ƙasa an kawo misali:

    Waƙar Kaɗi Ta Allah Ba Ni Kaɗa

    Kaɗi ɗaya ne daga cikin daɗaɗɗun sana’o’in Hausa na gargajiya. Ya shafi sarrafa auduga domin samar da zare. Akwai waƙoƙi daban-daban da masu kaɗi suke rerawa yayin gudanar da sana’arsu. Ga misali daga ciki:

    Bayarwa: Allah ba ni kaɗa,

    Amshi: Ayeye ye ranaye.

    Bayarwa: In yi zare na kaina,

    Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

    Bayarwa: In yanke zugage,

    Amshi: Ayeye ye ranaye.

    Bayarwa: Dela nan tara nan talatin,

    Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

    Bayarwa: Allah ba ni kaɗa,

    Amshi: Ayeye ye ranaye.

    Bayarwa: In wa masoyi riga,

    Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

    Bayarwa: In wa masoyi wando,

    Amshi: Ayeye ye ranaye.

    Kamar yadda aka gani a sama, wannan waƙa tana ɗauke da addu’ar alheri. Mai rera waƙar tana addu’ar Allah Ya ba ta kaɗa saboda ta yi zare na kanta. Har ma tana bayyana ƙudurin alheri dangane da abin da za ta aiwatar da kaɗar idan ta samu, wato saƙa wa masoyinta sutura.

    2.6 Adana Kalmomi Da Al’adu

    Kalmar al’ada tana nufin tsarin rayuwa ta gaba ɗaya wanda ta haɗa da sanannun sababbun al’amuran da suke gudana yau da kullum bisa wasu tsararrun ƙa’idoji da matakai da kuma waɗanda aka saba da wanzuwarsu kara zube ba tare da wata ƙa’ida ta musamman ba. Waƙoƙin gargajiya masu yawa suna taimakawa wajen adana kalmomi[4] da al’adu. A duba wannan misalin:

    Waƙar Tashen Jatau Mai Magani

    Maza ne suke gudanar da wannan wasan tashe. Ɗaya daga cikinsu da ake kira Jatau zai yi shigar boka, har da layun wasa. A wurin wasa Jatau zai riƙa rera waƙa saura suna amsawa, kamar haka:

    Jatau: Jatau mai magani,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Kogo-kogo na shiga,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Kogon kura na shiga,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Kogon damusa na shiga,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Kogon ɓauna na shiga,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Balle na maciji ɗan tsiya,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: To iya wanne za ki sha,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Ko na ciki ko na haihuwa,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Ko na korar kishiya,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Idan na ba ki na haihuwa,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Yau ki haifo sha biyar,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Gobe ki haifo sha biyar,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Kin ga talatin sun cika,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Idan na ba ki na kishiya,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Larai ta zo ta fita,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Maimuna ta zo ta fita,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Kafin sati ko guda,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Kin kore mata ɗari,

    Amshi: Jatau.

    Akwai ɓangaren waƙar inda Jatau yake bayanin kayayyakin haɗin magungunan da suke cikin tarkacensa na bokanci, yana cewa:

    Jatau: Ka ga wannan gwanda ce,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Ko da ba ta magani,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Ko don zaƙi za ka sha,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Ka ga wannan zogala,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Ko ba ya magani,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: In an yi kwaɗo ai za ka ci,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Ka ga wannan yakuwa,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Ai ko ba ta magani,

    Amshi: Jatau.

    Jatau: Za a yi taushe za ka sha,

    Amshi: Jatau.

    Lallai wannan waƙar tana adana kalmomin Hausa da suka shafi dabbobi da magunguna. Bugu da ƙari, tana adana al’adu masu yawa ciki har da bayyanannu (magunguna[5] da tsirrai da tufafi da sauransu) da kuma ɓoyayyu (yarda da bokanci da sauransu).

    2.7 Bayyana Muradin Zuci

    Barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa! Yayin da wata damuwa ta dabaibaye zuciyar mutum, ba zai samu sukuni ba har sai ya furzar da ita. Ana amfani da waƙoƙin gargajiya wajen bayyana muradin zuci a bagiren da bayyanawar take da wahala ba domin albarkacin waƙoƙin ba. Ga misali a ƙasa:

    Waƙar Wasan Mama Ta Ƙi Shillona

    Yara mata ne suke gudanar da wannan wasa. Sukan yi da’ira, sai kuma yarinya ɗaya ta fito tsakiya. Za ta riƙa ba da waƙa sauran kuma suna amsawa tare da tafi da rangwaɗa. Suna cewa:

    Bayarwa: Ayyaraye iye dije,

    Amshi: Yaraye iye dije.

    Bayarwa: Jajjage ruwan lemo,

    Amshi: Arziki na Allah ne.

    Bayarwa: Mama ta ƙi shillona,

    Amshi: Baba ya ƙi shillona.

    Bayarwa: Tun da kun ƙi shillona,

    Amshi: Ni na tafi yawona.

    Bayarwa: Ran bikin Halimana,[6]

    Amshi: Don Allah ku aika min.

    Bayarwa: Ran bikin Umaimana,

    Amshi: Don Allah ku aika min.

    Bayarwa: Za mu je mu watsa kuɗi,

    Amshi: Sai ya fi dubu hamsin.

    Bayarwa: Za mu je mu taka rawa,

    Amshi: Sai ya fi na ‘yan bori.

    Wannan waƙa a kaikaice fitar da abin da yake damun ‘ya’ya mata ne a zuciya dangane da watsi da su da ake yi a rayuwa. A cikin waƙar suna barazanar tafiya yawon duniya, tun da arziki na Allah ne. A ƙarshe har suka nuna cewa idan bikin ‘yan uwansu ya zo, to za su zo da kuɗi mai yawa sannan su taka rawar da har ta fi ta ‘yan bori. Haƙiƙa wurin da za a samu kuɗaɗen nan sannan a koyi wannan rawa, ba wurin alkairi ba ne.

    2.8 Bin Doka Da Ƙa’ida

    Bin doka da ƙa’ida yana daga cikin abubuwan da suka bambanta rayuwar mutane da dabbobi. Waƙoƙin gargajiya masu yawa suna tafiya tare da dokoki. Ga misali a ƙasa:

    Waƙar Wasan Gidan Kurciya

    Wannan waƙa ce da ake gudanarwa yayin wasan dandali. Masu wasan suna tsayawa bisa tsarin da’ira, sannan su ba da ‘yar tazara a tsakankaninsu, tare da riƙe hannuwan juna. Daga nan kuma ɗaya daga cikin masu wasa zai riƙa sunkuyawa yana wucewa ta tsakankanin ‘yan wasa (ƙarƙashin hannunsu da suke riƙe da na juna). Yayin da yake shige da fice, za su riƙa rera waƙa kamar haka:

    Waƙa: Gidan kurciya,

    Amshi: Shaya.

    Waƙa: Wanda ya ɓata,

    Amshi: Shaya.

    Waƙa: Zai sha duka,

    Amshi: Shaya.

    Waƙa: Har da muntsini,

    Amshi: Shaya.

    Ƙarara a cikin wannan waƙar ana jaddada cewa, duk wanda ya ɓata “zai sha duka, har da muntsini.” Wannan yana nuna dole ne mai wasar ya kiyaye tsarin dokokin da aka gindaya domin wanyewa lafiya. Yayin da mai wasa ya yi kure, yana shan duka kamar dai yadda aka yi alƙawari a cikin waƙar. A taƙaice dai, wannan waƙa tana koyar da bin doka da ƙa’ida tare da nuna sakamako marar kyau ga wanda ya taka doka.

    2.9 Koyar Da Halaye Nagari

    Hali shi ne mutum! Na gari na kowa! Kowane uban ƙwarai yana son ganin zuri’arsa ta tashi cikin tarbiya mai kyau abar yabawa, haka ma uwa ga ‘ya’yanta. Wannan ya haɗa da kunya da gaskiya da riƙon amana da sanin ya-kamata da girmama na gaba da dai sauran halayen ƙwarai makamanta waɗannan. Wannan ne kuma ya sa Hausawa suke da waƙoƙin gargajiya masu koyar da halaye nagari. A duba wannan misalin:

    Waƙar Wasan Tsakiyata Ta Tsinke

    Yara mata ne suke gudanar da wannan waƙar yayin wasannin dandali. Sukan yi da’ira sannan su kakkama hannayen juna sannan su tsuguna yayin rera waƙa kamar haka:

    Tsakiya tsatsakiya,

    Tsakiyata ta tsinke,

    A ɗakin masoyina,

    In sunkuya in ɗauka,

    Abin na da kunya,

    Ba da kunya ba,

    Ala tsine ‘yar kunama,

    A cikin duhun ciyawa.

    Wannan waƙa tana nuna kunya ga ‘ya mace. Ga shi dai tsakiyar wannan yarinya ta tsinke, tana so ta sunkuya domin ɗauka, amma dole ta haƙura saboda kunya. Kunya kuwa abar so ce ga ‘ya mace, domin duk yarinyar da ba ta da kunya, tarbiyarta ragaggiya ce.

    2.10 Lura Da Mai Da Hankali Da Nutuswa

    Rayuwar ɗan’adam ba ta tafiya kan tsari sai idan ya kasance mai lura tare da mayar da hankali kan abubuwan da yake gudanarwa cikin rayuwarsa ta yau da kullum. Rashin Natsuwa ko mayar da hankali  yakan jefa mutum cikin halin yawan mantuwa (marar dalili) da yawan kuskure da dai makamantansu. Akwai waƙoƙin gargajiya da suke koyar da natsuwa da mayar da hankali. Misali:

    Waƙar Wasan Jini Da Jini

    Wannan waƙa ce da yara suke gudanarwa. Ɗaya daga cikinsu zai riƙa ambatar sunayen abubuwan da suke da jini. Yara kuma za su riƙa amsawa da “danja!” Ana cikin haka zai shammace su ya ambaci abin da ba shi da jini a jikinsa. A nan yara za su amsa da “babu!” Duk wanda ya yi kuskuren amsawa da “danja!” to ya faɗi, don haka hukuncin wasa zai hau kansa. Ga yadda abin yake:

    Liman: Jini da jini,

    Mamu: Danja!

    Liman: Rago da jini,

    Mamu: Danja!

    Liman: Akuya da jini,

    Mamu: Danja!

    Liman: Riga da jini.

    Mamu: Babu!

    Haƙiƙa wannan waƙa tana buƙatar natsuwa da mayar da hankali. Duk yaron da ya shagala da wani tunani na daban, zai samu kuskure wurin ba da amsar da ba ta dace ba.

    2.11 Motsa Jiki

    Motsa jiki yana da matuƙar amfani ga lafiyar ɗan’adam. Akwai waƙoƙin gargajiya waɗanda suke ba wa yara ƙarfin guiwar motsa jiki, musamman yayin wasannin dandanli. Ga misali daga cikinsu:

    Waƙar Wasan Karya Gaɗiɗi

    Wannan wasa ne na yara mata. Masu wasan suna tsayawa manne da juna a layi ɗaya. Ɗaya daga cikinsu kuma za ta fito gaba. Za su riƙa waƙa da tafi yayin da wannan yarinya da take gaba za ta riƙa faɗowa jikinsu. Su kuwa za su riƙa tallabar ta suna cillo ta gaba. Haka za a ci gaba da yi har sai an kai ƙarshen waƙar. Ga yadda take:

    Mai Direwa: Karya gaɗiɗi,

    Karya gaɗiɗi.

    Masu Cilli: Garya gaɗis!

    Kainuwa.

    Mai Direwa: Kainuwa dashen Allah,

    Masu Cilli: Kainuwa.

    Mai Direwa: Ba dashen mutane ba,

    Masu Cilli: In dashen mutane ma.

    Mai Direwa: Ko ruwa ba na sha ba.

    Masu Cilli: Kainuwa.

    Mai Direwa: Ko kunu ba na sha ba.

    Masu Cilli: Ya ishe ki ‘yar Malam Adamu,

    Ya ishe ki ‘yar Malam Adamu.

    Haƙiƙa akan motsa jini yayin gudanar da wannan wasa. Gishirin wasan kuwa, shi ne waƙar da ake rerawa a ciki, domin kuwa waƙar ta kasance linzamin wasan.

    2.12 Huce Takaici

    Takaici yana nufin baƙin ciki ko sosuwar zuciya ko haushi da mutum kan ji dangane da wani mutum ko wani al’amari da bai gamshe shi ba. Waƙoƙin gargajiya na Hausa sun kasance wata kafa da Hausawa suke bi domin huce takaicinsa. Ga misali:

    Waƙar Niƙa Ta Kishiya

    Wannan waƙa ce da take ɗauke da habaici. Kishiya tana iya rera wannan waƙa yayin da take niƙa da zummar caka wa kishiyarta baƙaƙen maganganu a kaikaice. Ko ba komai, zuciyarta takan yi fari yayin da ta yi hakan. Ana rera wannan waƙa kamar haka:

    Ayye yaraye iye nanaye,

    Ayye yaraye iye nanaye.

    Ga wata kishiya ruwan sanyi ce,

    Wata ko na zafi ya fiye mata.

    Kishi da ‘yar Malan nake gudu,

    Ta yi maka magani ta saka a hanya.

    Hanyar gidanku ta barkace maka,

    Allah ba ni kishiya mai yaji.

    Kamin ta dawo na ci duniya.

    2.13 Samun Abokin Hira/Abokin Taya Aiki

    Mata dai an san su da zaman kaɗaici a gida, musamman idan aka ce ba su da ‘ya’ya ko jikoki ko wasu abokan zama. A irin wannan yanayi, sukan kasance cikin kaɗaici yayin da mazajensu suka fita wurin fafutukarsu ta yau da kullum. Waƙoƙin gargajiya suna taimaka wa ire-iren waɗannan mata a matsayin abokan hira yayin da suke aikace-aikacensu a cikin gida. Ga misali a ƙasa:

    Waƙar Niƙa Ta Naƙuda Ta Tashi

    Wayyo naƙuda ta tashi,

    Ciwon naƙuda ya tashi.

    Kuma ciwon naƙuda ya motsa,

    Yau kam babu zama zaure.

    Wayyo Inna ki cece ni,

    Ciwon naƙuda ya tashi.

    Da kis sha daɗinki,

    Ke tuna da Inna ta cece ki?

    Ko ke tuna da baba ya cece ki?

    Wayyo naƙuda ‘yar ziza!

    Ciwon naƙuda bori ne,

    Ko ko naƙuda hauka ce!

    Wayyo naƙuda ta tashi,

    Wayyo naƙuda ta motsa.

    Idan aka lura da wannan waƙa, za a tarar cewa an gina ta ne kan raha. Za a fahimci hakan yayin da aka yi duba zuwa wasu daga cikin kalaman da aka yi amfani da su a cikin waƙar, misali naƙuda ‘yar ziza; ko wataƙila mota ce? Haka ma mai ƙorafin ciwon naƙudar, sai ga ta tana mayar wa kanta martani tamkar dai wadda take wa ƙorafin ne take mayar da martanin, wato tuhumar ta da cewa, ta tuna lokacin da ta ɗauki cikin?

    2.14 Bara

    Mabarata da suka haɗa da musakai ko miskinai da kuma almajirai sukan yi amfani da waƙoƙi daban-daban a wurin bara. Hakan yana ƙara armashi ga barar tasu tare da jawo hankalin wanda suke roƙa. Waƙoƙin suna ɗauke da kalmomi masu taɓa zuciya da kuma ban tausayi, wanda hakan kan sa a ba su sadaka. Daga cikin waƙoƙin da almajirai suke barar abinci da su akwai:

    Waƙar Bara Ta Iya Allaro

    Wannan waƙa dai almajirai na amfani da ita wurin bara, musamman lokacin da zuke zagayawa gida-gida domin neman abinci. Ga yadda waƙar take:

    Iya Allaro,

    Allaro iya,

    Iya Allah ba ku mu samu,

    Iya Allah sa mu ga Annabi,

    Iya ko loma ɗaya ma,

    Iya ko gaya ne ba miya,

    Iya ko loma ɗaya ba miya.

    Haƙiƙa wannan waƙa tana ɗauke da kalamai masu ban-tausayi da suke taɓa zuciya, musamman wurin da mai barar yake nuna ko da loma ɗaya, wadda kuma ba miya, to yana buƙata. Bugu da ƙari, waƙar tana ɗauke da addu’ar alheri zuwa ga wanda ake roƙa.

    3.0 Sakamakon Bincike

    Wannan bincike ya fahimci cewa, waƙoƙin gargajiya sun kasance wata kammalalliyar makaranta musamman ga yaran Hausawa a da. Suna ɗauke da fannonin ilimi daban-daban. Daga cikinsu har da ilimin ƙidaya da bin ƙa’ida da zurfafa tunani. Haka kuma, yana taimakawa wajen inganta zamantakewa da samar da gogewa a kan dabarun zaman duniya.

    Haka kuma, binciken ya gano cewa, waƙoƙin gargajiya suna tattare da ɗimbin alfanu inda tasirinsu ya karaɗe illahirin rayuwar Hausawa. A da, sun kasance masu muhimmin gurbi na musamman ta yadda ake damawa da su a kusannan duk wani al’amarin rayuwa.

    Wani hanzari ba gudu ba shi ne, yanzu waɗannan waƙoƙi sun dusashe matuƙa. Zamani da abubuwan da ya zo da su dangin intanet da na’urori sun kawar da ire-iren waɗannan gadaddun hanyoyin gudanar da rayuwa. Waƙoƙin zamani da ake sauraro a na’urori sun dusashe karsashin na gargajiya.

    Haka kuma, makarantun boko da na isilamiya da kallace-kallacen talabijin sun maye gurbin tatsuniyoyi da wasannin dandali waɗanda a cikinsu ne aka fi samun waƙoƙin. Haka kuma, dusashewar wasannin tashe sun haifar da ɓacewar waƙoƙin tashe.

    4.0 Kammalawa

    Sarki goma zamani goma! Haƙiƙa dukkannin alƙaluma sun nuna cewa, babu yadda za a yi waƙoƙin gargajiya su yi gogayya da sababbin sauye-sauyen da zamani ya kawo. A bisa haka, hanyar da za ta fi ɓullewa ita ce sanya wa waɗannan waƙoƙi rigar zamani. Za a iya hakan ta hanyar sabunta su cikin odiyo da bidiyoyi da bidiyoyin katun.

    Ana kuma iya samar da manhajoji ƙayatattu da suke ɗauke da waƙoƙin kamar yadda suke fitowa a cikin tatsuniyoyi da wasannin dandali da na tashe. Ta waɗannan hanyoyi za a iya ci gaba da cin gajiyar waƙoƙin gargajiya da suke ƙoƙarin ɓacewa baki ɗaya.

    Manazarta

    Ainu, A. H. (2007). Rubutattun waƙoƙin addu’a na Hausa: Nazarin jigoginsu da salonsu [Kundin digiri na uku da ba a wallafa ba]. Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

    Bashir, R. (2024). Bitar rabe-raben waƙoƙin Hausa: Laluɓen matsayin waƙoƙin ƙarni na ashirin da ɗaya a fagen nazari. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 381–389. https://doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.044

    Danhassan, F. A. (2024). Tubalin yabon mata a wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(2), 219–224. https://doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i02.028

    Gobir, Y. A., & Sani, A.-U. (2018, April). Traces of supernatural in Hausa oral songs: A special reference to Dr. Mamman Shata. International Journal of Recent Advances in Multidisciplinary Research, 5(4), 3755–3760. ISSN: 2350-0743. Available at: https://www.ijramr.com/issue/traces-supernatural-hausa-oral-songs-special-reference-dr-mammanshata

    Gobir, Y. A., & Sani, A.-U. (2021). Waƙoƙin Hausa na gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

    Gusau, S. M. (2015). Mazhabobin ra’i da tarke a adabi da al’adu na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Idris, Y., & Sani, A.-U. (2018). Future situation of Northern Nigeria from poetic mirror: The outstanding prophesiers from Hausa poets. The International Journal of Social Sciences and Humanities Invention, 5(10), 4998–5002. https://doi.org/10.18535/ijsshi/v5i10.01

    Sani, A.-U., & Bakura, A. R. (2023). The origin and spiritual distribution of Zamfara drummers and singers. South Asian Research Journal of Arts, Language and Literature, 5(4), 108–123. https://doi.org/10.36346/sarjall.2023.v05i04.003

    Sarkin Fada, I. (2024). Nazarin kalmomin ta’addanci a cikin wasu waƙoƙin baka. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 358–363. https://doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.041

    [1] Domin samun ƙarin bayani game da ma’anar waƙa a tunanin Hausawa ana iya duba Bashir (2024 p. 382) da Sarkin Fada (2024 p. 360),

    [2] Rubuce-rubuce da aka yi game da waƙoƙi sun haɗa da Gusau (2015) da Idris & Sani (2018) da Gobir & Sani (2018, 2021) da Bakura & Sani (2023) da Danhassan (2024)

    [3] A wannan gaɓa, mai waƙa takan ambaci sunan ɗaya daga cikin ƙawayenta. Wadda aka ambaci sunanta kuwa za ta ji daɗi tare da yin murna da farin cikin kasancewar an damu da ita.

    [4] Ɗaya daga cikin ɗabi’un harshe shi ne samun sauye-sauye daga lokaci zuwa lokaci. Akan samu kalmomin harshe sun karfafa, ko an maye gurbinsu da wasu.

    [5] Domin samun ƙarin bayani game da magungunan Hausawa ana iya duba Bunza (1995) da Abdullahi (2008) da Gobir (2012).

    [6] A nan za ta faɗi sunan wata ƙawarta ko ƙanwa ko kuma yarta.

    Danna nan don karanta Maƙala Mai Taken Kasuwanci A Duniyar Intanet: Ƙalubalen Hausawan Ƙarni na 21

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tunawa Da Yaƙin Santolo

    Tunawa Da Yaƙin Santolo

    (YAKI DON TABBATAR DA MUSULUNCI A ƘASAR HAUSA)

    9/12/2017

    DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

    08060869978

    Haƙiƙa, idan har tarihin ƙasar Hausa ba zai cika ba har sai an kalli tarihin Kano, to haka ma tarihin Kano da zuwan musulunci ƙasar Kano ba zai taɓa kammaluwa ba har sai an sanya wani yanki daga yaƙin Santolo. Santolo tsohuwar daular Hausawa ce, tsohuwar masarauta ce wadda salsalar ta take tuƙewa da salsalar asalin Hausawa.

    A cikin zantuka masu yawa na maruwaitan tarihin Kano, an gamsu cewar wani mai suna ‘Dala’ shi ne wanda ya soma zama a kan dutsen da a yau ake kira da suna ‘Dala’, a wajajen shekarar 700 miladiyya, tun a wancan lokacin kuma wasu na ganin akwai mutane da ke rayuwa a kan wani dutse mai suna ‘santolo’, wanda shi ma da alama, sunan ya samo asali ne daga mutumin da ya soma rayuwa a saman dutsen.

    Zuwa yanzu, babu takamaimen tarihin asalin kafuwar Santolo, sannan kuma yana da wuya a iya lissafa tsawon zamanin da mutane suka soma rayuwa a kan dutsen santolo, to amma tarihi ya auna cewar mazauna Santolo da na Dala da ke Kano suna da alaƙa da juna.

    Alaƙar kuwa na iya zamowa ta jinsi, ko ta addini ko kuma ta duka gaba ɗaya, tunda har ma an samu cewa a can baya alakar kasuwanci na shiga tsakanin mazauna waɗannan duwatsu biyu. Wasu kuma na ganin Santolo ta yi shaharar da har daga Borno ake zuwa yin fatauci a koma, to amma daga baya sai Allah ya fifita yankin Dala sama da ita Santolon.

    Babban abin tunawa dangane da Santolo shi ne ‘Yaƙin Santolo’ wanda aka gwabza tsakanin Sarkin Kano Ali Yaji ɗan Tsamiya da kuma shugaban Santolo mai laƙabin ‘Magajin Santolo’ wanda ya karɓi baƙuncin takwaransa ‘Magajin Dala’ bayan sarkin Kano ma goma sha ɗaya Ali Yaji ɗan Tsamiya ya karya tsumburbura da ke saman dutsen Dala, sannan ya kori Magajin Dala da mutanen sa.

    Tarihi ya nuna cewa asalin garin Kano ya faro ne daga dutsen dala, inda ake bautar gunkin wata aljanna mai suna ‘tsumburbura’ da ke saman dutsen, amma daga baya maɗatai ta kafu, har Bagauda ya zo ya soma sarautar ɗaukacin yankunan maɗatai da na yankin Dala, waɗanda suka haɗe da sunan Kano.

    Haka kuma, tsawon zamani a Kano babu addinin musulunci, daga masu bautar tsunburbura ƙarƙashin ikon magajin Dala (wanda ya yi gadon Barbushe) sai kuma maguzawa waɗanda ba sa bautar komai irin su Bagauda da salsalarsa da ke sarautar Kano.

    A haka Kano ta taho har aka zo kan mulkin Sarki Ali yaji ɗan Tsamiya a wuraren shekara ta 1349-1385 miladiyya, wanda ya karɓi baƙuncin ƙabilar fulani Wangarawa daga ƙasar Mali, waɗanda suka kawo musulunci zuwa garin kamar yadda Marigayi Maje Ahmad Gwangwazo ya faɗa a littafinsa da ya yi magana akan tarihin Kano da tarihin zuwan wangarawa birnin.

    To, bayan sarki Ali Yaji ya karɓi addinin musulunci, sai kuma ya jagoranci karya gunkin tsunburbura tare da umartar masu bauta masa su dawo musulunci, amma sai wasun su suka ce sam-sam ba za su bar addinin kaka-da-kakannin su ba su yi addinin dungure, don haka sai suka gudu izuwa Santolo domin cigaba da bautar da suka saba.

    Ga abinda ya zo a littafin Kano Chronicle game da wannan yaƙi:-

    Sarki ya umurci dukkan garururuwan Kanawa su yi salla, sai suka yi. Ya gina masallaci mai-kusurwa huɗu a ƙarƙashin itaciyar da muka ambata a baya, suna salla a cikinsa waƙati biyar, suna komawa gidajensu. Shi ko, Sarkin Gazarzawa yakan zo da jama’arsa, suna yin najasa suna shafe dukan masallaci da ita. Saboda wannan aka sa Ɗan-buje ya riƙa gewaya masallaci da dukan makamai iri iri tun daga lisha har hudowar alfijr, yana kururuwa.

    Kai duk da haka suka yaudare shi da mutanensa, waɗansu suka bi maganar arna, shi da sauran jama’a suka ƙi. Ba su daina najasa cikin masallaci ba, har Sheshe da Famore suka ce, “Babu maganin waɗannan kafirai sai roƙon Allah.” Sauran suka ce, “Hakanan ne.” Sa’an nan suka taru cikin masallaci daren Talata, tun daga magariba har hudowar rana suna addu’a a kan kafiran. Sa’an nan suka fito suka koma gidajensu suna masu rauni.

    A cikin wannan rana Allah ya karɓi roƙonsu, ya makantad da idanun babbansu, da kuma dukan wanda yake yin wannan aiki ya makance, duk da matansu. Daga nan sai sauran kafirai sukaji tsoro. Sa’an nan Yaji ya tuɓe babbansu daga sarautarsa, ya ce masa, “Kai ne Sarkin Makafi.”

    An ce a cikin zamanin Yaji ne Sarkin Dabi da Sarkin Daf da Sarkin Gano suka zo da dawaki cikin wannan gari, amma wannan zance ba shi da ƙarfi. Bayan haka sai Sarkin Kano Yaji ya ce da Wangarawa,”Ina so ku taimake ni da addu’a domin in rinjayi Santolo, idan na rinjaye ta dukan garuruwa za su bi ni, domin ita ce ƙusar ƙasashen Kudu. Suka ce, “To, ma taimake ka da addu’a amma ba za mu yi addu’ar ba sai a bakin ramin ganuwarta.

    Sa’an nan Sarki ya fita tare da Wangarawa zuwa Santolo, mayaƙan da ke tare da shi mutum ɗari da goma sha ɗaya, hamsin na fuskar Wangarawa, sittin na fuskar Sarki. Na farko daga cikin jarumawansa: Jarmai Gobara-daga-sama, da Jakada Kwalo, da Ragamar-giwa, da Makama Butaci, da Madawaki Kuamna, da Barde Shege, da Sarkin Zaura Gamaji, da Dan-buram Gantaroro, da Ɗan-makoyo Dagazau, da Galadima Tuntu, da Sarkin Sirdi Maguri, da Gauji, da Garuji da Tankarau, da Kargage, da Karfashi, da Kutunku, da Toro da Kamfashe, da Gwauron-giwa shine

    Galadima, da Zaki, da Bambauri, da waɗansu na Cikon sittin. Yayin da Suka kai Santolo, sarki ya zauna a Duji (Sunan mutum ne.) Da duhun dare ya tashi ya tafi tare da Wangarawa zuwa Santolo, suna kewaye ta suna yi mata addua har hudowar alfijir, sa’an nan suka komo sansani. Sa ad da rana ta hudo suka taso zuwa gare ta da niyyar yaƙi Mutanen Santolo suka fita suka tare su a sarari, suka soma yaƙi tun daga hudowar rana har faɗuwa ta ba wanda ya rinjayi wani.

    Kanawa suka koma Duji, mutanen Santolo suka koma gida. Sarkin Kano kuwa ya yi baƙin ciki. Famore ya ce, “kada ka yi bakin ciki, ma rinjaye Su in Allah ya so.” Sarkin Kano ya yi farin ciki saboda wannan magana. Daga nan Ƙosa bawan Sarkl, yace “Ya Ubangijina, ni na san asirinta. Akwai waɗansu mutum takwas cikinta, in ba a kashe su ba ba wanda zai iya shiga ramin ganuwarta”.

    Famore ya ce, Ka san sunan mutanen nan?”  Ƙosa Ya ce, “I na san sunan su”. Sai Famore yace, “Kaƙa sunayansu?” sai ya ce, “Sunan babbansu Hambari, da kuma Goshin-Ɓauna da Ka-fi-wuta, da Gugan-ƙarfe, da Gandar-giwa, da Hamburkin-toka da Zangada-kere, da Gumbar wake” Goje yace, “Idan na ga Hambare na kashe shi in Allah ya so”.

    Sa’ad da alfijir ya hudo Sarkin Kano ya fita tare da rundunarsa, zuwa dutsen Santolo da mashi a hannunsa, yana mai daurariyyar fuska, GoJe yana gaban sa, Zaite yana damar sa, Famore yana hagun sa, Sheshe yana bayansa, sauran Wangarawa da Kanawa suna binsa.

    Sa’ad da suka iso Santolo dukan kafirai suka fito. Da Goje ya ga Hambare sai ya zage dantsan sa ya zabura zuwa gareshi, dukan kafirai Suka zaburo wa Goje, sai ya yi musu tsawa suka watse. Sa’ad da ya kai wurin Hambare ya soke shi da mashi, Hambare kuma ya ribce wuyansa ya fizgo shi daga kan doki, sai Goje ya fid da ‘ƴar wuƙa ya soke shi da ita a ciki, ya mutu.

    Daga nan ya hau dokinsa ya shiga cikin ganuwar Santolo, Kanawa suka bi shi suka ci birnin dukkansa. Sarki ya yi umurni a yanka dukan wanda aka samu a cikinta, Sai mata da ƙananan yara. Goje kuma ya shiga cikin gunkinsu tare da Kosa da Gurgu, suka sami kuge da ƙaho biyu da barandami da mari.

    Goje ya ɗauki kugen da ƙahon nan biyu, Kosa ya ɗauki barandamı da mari, Gurgu ya ɗauki mari. Yaji ya zauna a cikinta kwana bakwai, ya rushe ta sarai, ta zama babu gini ko itace. Bayan wannan ya komo garinsa, ya ce da Goje, “Faɗi dukan abin da kake so, na ba ka. Goje yace “ba ni son kome sai ka naɗa mini sarautar Madawakin Kano”.

    Sarkin Kano ya ce. “Kai ne Madawakin Kano. Ya tube Madawaki Gasatoro, ya fita ya gina gida a gawo; saboda haka aka Kira shi da suna Madawakin Gawo, domin a rarrabe tsakaninsu. Dutsen Santolo gagarumi ne, faffaɗa da doro, tsayinsa ya tafi kamar hawan bene daga baya, daga gabansa kuwa goshi ya yi mai faɗi da santsi, tsakiyarsa yana da faɗi har ma akwai koguna da aka ce dabbobin daji misalin su kyarkeci, dila da macizai na rayuwa a ciki.

    Ko da yake, ba mu ji sunan gunki da aljanar da aka ce akwai a saman dutsen santolo ba, amma har yanzu mutanen da ke zagaye da wurin sun kiyaye cewar kakanninsu sun ba su labarin cewar a zamanin da, ana taruwa a hau kan wannan dutse don neman wata biyan buƙata. Sannan kuma akwai wata rijiya zuzzurfa da ke saman dutsen mai suna ‘Rijiyar Giɗaɗo’, wadda akan hana mutane zuwa kusa da ita saboda kuɓuta daga ƙwanƙwaman da ke wurin masu halaka mutane.

    Zuwa yanzu garin santolo ya kasu biyu, akwai sabon garin santolo wanda Kanawa (ƙabilar Hausawa) ke ciki, sai kuma santolon fulani, amma dukkan su suna ƙarƙashin ikon dagaci mai suna Santolo Da’u. Haka kuma dutsen yana nan a tsakiyar ƙauyukan sabon garin santolo, santolon fulani, Madawa, Koɗe, kyarmawa, da Tsakuwa waɗanda dukkanin su suke cikin gundumar Dawakin Kudu ta Jihar Kano.

    Danna nan don karanta Yadda Asalin Kishi Yake

    Edita@rumasau-kallamu

  • Shaiɗanin Wannan Ƙarni: JEFFERY EPSTEIN

    Shaiɗanin Wannan Ƙarni: JEFFERY EPSTEIN

    “Lallai shi – shaiɗan – yana umartanku ne da munanan ayuka da kuma alfasha”

    Jeffery Seymour Epstein an haife shi a 1953 a Brooklyn da ke birnin New York. Iyayensa, wato Seymour Epstein da Pauline Epstein yahudawa ne, kuma ba wasu shaharraru ba ne. Mahaifinsa ƙaramin ma’aikaci ne mai kula da wuraren shaƙatawa na birnin NewYork, Mahaifiyarsa kuma aiki take – ba koyarwa ba- a wata makaranta.

    Epstein ba shi da ‘yanuwa a wurin iyayensa wato ƙanne ko yayye. Ya taso a birni, kuma ya yi sakandare sannan jami`a, inda ya fara karantar lissafi da physics amma bai gama jami`a ba, duk da haka a 1979 ya sami karantarwa a wata makaranatar `ya`yan masu hannu da shuni mai suna Dalton School a Manhattan.

    A wannan makaranata ce ya haɗu da manayan mutane, ɗaya daga ciki kuma wanda ya taimake shi, shi ne Alan Greenberg shugaban kamfanin Bear Sterns. Wannan mutum shi ya fara shigar da Epstein harkar kuɗaɗe. Damar da masu shaidar karatu ma ba kowa ba, amma Epstein ya same ta a Vagas.

    Da goyon bayan Alan ne aka ɗauki Epstein a kamfanin Bear Stern a matsayin ƙaramin ma’aikaci amma nan da nan sai ya zama yana hada-hada da manyan masu kuɗi. Bayan nan Epstein ya bar Bear Stern, amma ba a san dalilin barinsa ba, lokacin ya ƙware wurin yadda ake hada-hada da manyan kuɗaɗe kuma ya ƙulla alaƙa da manyan masu kuɗi.

    A shekarun 1980 ya fara kula da kuɗaɗen manyan mutane, mafi muhimmanci a cikinsu shi ne wani shahararren biloniya mai suna Leslie Wexner wanda ya kafa Victoria`s Secret (L Brands) a wannan lokacin ne Epstein ya mallaki maƙudan kuɗaɗe, kuma ya sami damar ƙulla alaƙa da manyan ‘yan siyasa, sarakuna da manyaan ‘yan kasuwa na Amurka da sauran ƙasashen duniya.

    Esptein ya yi amfani da ƙwaƙwalwarsa da ƙwarewarsa wurin sarrafa kuɗaɗe, shirya tarruka na gani na faɗa, amfani da jiragen sa, wurare da gidaje na alfarma kuma na sirri wurin jan hankalin manayan mutane. Ya yi amfani da damar sa na attajiri, ya sami shiga jikin manyan attajirai na duniya, manyan sarakuna, shugabanni da jagorori al`umma.

    Epstein ya yi amfani da damar sa ya jefa waɗanda ya ƙulla alaƙa da su cikin wani irin mummunan tarko. Da yawa daga cikin waɗannan mutanen sun aikata aika aika da ta`asa marasa kyau marasa daɗin ji, kamar lalata da ƙanana yara, safarar ƙanan yara, tilasta wa mata da yara karuwanci da sauran badaƙala.

    Ana zargin sa da yin mafani da waɗannan aika aika na waɗannan manyan mutane don cimma burinsa na ƙashin kansa da kuma ci gaba da ɓarnarsa ba tare da damƙe shi ba ko an gurfanar da shi a gaban kuliya manta sabo. Sannan yana amfani da masha`ar da suka aikata ne dan tilasta musu yin abinda ya ke so ko kuma abinda wasu suke so.

    An fara tuhumar Epstein da laifuffuka na lalata da ƙanana yara, da sauran laifuffuka a 2008 wanda a wannan lokacin ya amsa wasu daga cikin laifuffukan, hakan yasa ya yi zaman wucin gadi na wata goma sha uku (13) a gidan yari cikin gata, har da ba shi kwana shida ya fita daga gidan yari dan zuwa hada-hadarsa. Daga baya ma aka sake shi.

    Bayan nan ya koma ya ci gaba da sharholiyarsa da harkokinsa a duniya. An sake buɗe wannan tuhuma a 2018, a wannan lokacin bai amsa laifinsa ba. A watan bakwai Yuli na shekaran 2019 aka kama shi aka tsare, bisa zarginsa da lalata da safarar ƙananan yara, haɗa kai da masu aikata manyan laifuffuka. An sami gawar Epstein a ɗakinsa na gidan yari ranar 10 ga watan tara 2019. Rahoto daga hukumomi ya tabbatar da ce wa Epstein ne ya kashe kansa.

    Wannan babban shaiɗani ne da an daɗe ba a sami kamar sa ba. Sannan ɓarnar sa ta yawaita, ta yi ambaliya, saboda an sami kundi kundi na ayyukan lalata da fasiƙancin sa da sauran manyan attajirai, sarakuna da shugabanni kimanin miliyan da wani abu.

    DALILAN DA KE JAWO AIKATA AYYUKAN ƁARNA

    Ayyukan fasiƙanci da lalata da sauran laifuffuka na keta alfarmar Allah sun zama ruwan dare a cikin alummar musulmi da ma waɗanda ba su ba. Daga cikin dalilan da yake sa ɓarna irin waɗannan ke yawaita, akwai ci gaban da aka samu a yanzu a duniya ta yadda komai yake yaɗuwa cikin sauƙi kuma ake samu cikin sauƙi ta hanyar kafofin sadarwa na zamani.

    ƘARANCIN TSORON ALLAH: tsoron Allah ya ƙaranta a zuciyoyin mutane, shi yasa ba sa ganin aikata laifi wani abu ne mai girma. Duk wanda tsoron Allah ya ƙaranta a zuciyarsa, to abu ne mai sauƙi a wajensa ya keta alframa Allah ba tare da ya ji komai ba. Allah Ta`ala ya ce: “Duk wanda ya girmama alamomin Allah, to lallai wannan yana daga cikin taƙawar zuciya” Tsoron Allah yana hana aikata ɓarna da laifi.

    ƘARANCIN ILIMIN ADDINI: Rashin sanin abinda Allah ya umarci mutum, da abinda Allah ya hane shi suna sa mutum ya faɗa cikin aikata ɓarna dumu dumu ba tare da ya san girman abinda yake aikatawa ba. Manzon Allah SAW ya ce: “…… wani bawa da Allah ya ba shi dukiya, amma bai ba shi ilimi ba, saboda haka yana ta ɗawainiya a cikin dukiyar, bai san Allah yana da haƙƙi a cikin dukiyar ba, ba ya jin tsoron Allah, ba ya sada zumuncinsa da wannan dukiya, ya ɗimauce, toh wannan yana cikin mummunar makoma” rashin sanin shari`ah yana sa bawa ya yi ta afkawa cikin laifi.

    YAUDARA TA SHEƊAN: Sheɗan babban abokin gaban ɗan Adam ne, Allah da kansa ya nusar da ɗan adam game da shi, Allah ya ja kunnen bawa game da haɗari, da makircin sheɗan. Allah ya ce: “kada ku bi tafarkin sheɗan, lallai shi babban abokin gabanku ne. Ba abinda yake umartanku da shi sai ɓarna da alfasha” a wani wurin Allah ya ce: “ Yana muku alƙawarin ƙarya, yana muku shigo shigo ba zurfi, ba abinda yake yi sai yaudara” saboda haka duk lokacin da sheɗan ya sami dama aka ɗan Adam ba abinda zai zuga shi sai saɓa wa Allah da tabka manya laifuffuka.

    ƘARANCIN KUNYA: kunya ɓangare ne na imani, wanda ba shi da kunya, toh ya rasa wani ɓangre na imani. Sannan wanda yake da ƙarancin kunya zai iya aikita duk abinda ya so. Manzon Allah SAW ya ce: “Duk wanda ba ya jin kunya toh ya aikata duk abinda ya so” musamman a yanzu za mu ga kunya ta ƙaranta a wurin matasa, musamman a kafofin sada zumunci, sai ɓarna kala kala ake yaɗawa saboda ƙarancin kunya.

    Waɗannan kaɗan ne daga dalilan da suke janyo keta alfarmar Allah, akwai wasu da yawa kamar rashin umarni da kyakkaywa da hani da mummuna, zama da abokan banza, rayuwar sharholiya, rashin tarbiyya ta gari, shagala da duniya da sauaransu.

    AƘIBAR AIKATA ƁARNA:

    Akwai aƙiba, wato sakayyar aikata ɓarna. Da yawa daga cikin mutane ba su san cewa aikata laifi da yawaita ɓarna su na da uƙuba ba. Daga ciki, aikata ɓarna da laifi yana jawo fushin Allah, da ƙarancin albarka a rayuwar mutane. Yawaitar masifu kala kala daban daban, kuma akai-akai, sannan rugujewar al`umma da rushewar gida da iyali, lalacewar matasa, taɓarɓarewar tarbiyya, da kuma uwa uba maƙikyanmu za su samu galaba a kan mu, su yi ta gasa mana aya a hannu ba kuma abinda za mu iya yi.

    HANYOYIN RAGE AIKATA ƁARNA:

    Akwai abubuwa da suke taimakawa wurin rage aikata ɓarna da laifuffuka ko kuma taƙaikta su, daga ciki akwai jin tsoron Allah kamar yadda ya dace, neman ilimin adddini, tarbiya ta gari, jin kunya da kamewa, umarni da kyakkaywa da hani ga mummuna, fifita lahira, girmama alamomin ubangiji da ganin alfarmarsa.

    RUFEWA DA SHAWARWARI

    A faɗin duniya ire-iren Epstein suna nan da dama, amma na shi ne yanzu ya fito fili, kuma manyan mutane da dama sun faɗa komar irin waɗannan mutanen, kuma sun rasa yadda za su fita. A yanzu haka akwai kundi na takardu, hotuna da bidiyo na wannan lalatar da ta ƙunshi mutane da dama wadda ta kai kimanin shafuka miliyan uku da dubu ɗari biyar wanda aka sake a yanzu.

    Babban abin lura a lamarin Epstein, shi ne yadda waɗanda suke rajin kare haƙƙin mata da yara, suke laɓewa suke tabka manyan laifukan lalata da ƙananan yara da safararsu kamar kayan gwanjo. Suna ta kururuwa game da auren wuri, amma sun ɓige da lalatar wuri a matsayin sharholiya. Wannan ya nuna cewa babu addinin da ya san `yancin mace da kare mata `yancinta kamar addini musulunci.

    Abu na biyu, manyan mutane da suka haɗa da attajirai, sarakuna, manyan malamai da mashahuran mutane su guji kutsawa cikin aikata abinda Allah ya hana don kawai suna da damar aikata laifi ba tare da wani ya sani ba. Su sani Allah ya ba su wannan mastsayi ne don taimakon al`umma ba don aikaita ɓarna ba. Allah ta’ala ya ce “ Waɗanda idan muka ba su mulki, shugabanci, jagoranci a bayan ƙasa, sai su tsai-da sallah, su ba da zakka, sannan su yi umarni da kaykkayawa, sannan su yi hani da mummuna”

    Sannan su guji ƙulla alaƙa da mutanen da ba su da gaskiya ko ba su da tarbiyya da mutunci, saboda faɗawa cikin komar mugayen mutane da za su rinƙa yi wa mutum barazana da masha’ar da ya aikata don biyan buƙatun kansu, ko dan irin wannan lokaci da ake ciki na bankaɗe bankaɗe da tonon silili.

    Da yawa daga cikin mutane sun faɗa irin wannan koma ta sheɗanu kuma sun rasa yadda za su yi su fita. Wasu sai dai su ƙara faɗawa cikin wata ɓarnar ta kisan kai dan su tsira. Kamar yadda ake zargin cewa wasu ne da suke cikin komar Epstein suka aika aka kashe shi don kawo ƙarshensa su samu su numfasa, saboda muddin yana raye, toh suna tafin hanunsa, sai yadda ya yi da su.

    Allah, muna roƙonka da ka kare mu daga keta alfarmarka, ka kare mu daga faɗawa komar sheɗanu. Allah ka shiryar da mu, ka sa mu cika da imani. Amin.

    Danna nan don karanta Ga Tsoro Ga Ban Tsoro

    Edita@rumasau-kallamu

  • Tatsuniya Mai Taken Marainiya

    Tatsuniya Mai Taken Marainiya

    TASKAR TATSUNIYOYI”. Babi Na Daya: Marainiya

    Ga ta nan, ga ta nanku.

    Akwai wata yarinya marainiya, watau wadda take ba uwa ba uba; kuma ita kaɗai ce a wurin mahaifiyarta, lokacin da mahaifanta suka rasu suka bar ta. Ta sha wulaƙanci a wurin kishiyar uwarta, wadda take da ‘ya’ya maza da mata, waɗanda duka suka taru a kanta suka rika yi mata wulaƙanci.

    A cikin wannan yanayin kullum da sassafe takan je gindin wata bishiyar kurna ta zauna, ta yi ta kuka. Wannan kurna tana yin ‘ya’ya masu yawa, ga kuma zaƙi zaƙwai. Abincinta ke nan daga safe har yamma, kuma idan za ta koma gida sai ta ɗebo waɗanda za ta ci da dare.

    To akwai wani dan sarki kyakkyawa, mai suna Aminu, wanda ‘yar kishiyar uwarta take so, to amma shi kuma ba ya son ta. Shi ma kuma yakan je shan iska, ya hau kan wannan bishiyar kurna da marainiyar take zama a gindinta, ta sha ‘ya’yanta, yana kallon kowa, amma babu wanda zai gan shi don ganyen bishiyar ya ɓoye shi.

    Shi ke nan, wata rana marainiya tana zaune sai ɗan sarki ya sauko daga bishiya sai ya ce: “Sannunki ‘yan mata.” Sai ta ce: “Yauwa samari.” Aminu ya ce: “Me ke damun ki ne? Kullum sai in zo in gan ki a gindin wannan bishiya, har ma domin tunanin da kike yi ba ki sanin zuwana, kuma ga shi kikan riga ni zuwa don ni sai da la’asar nake zuwa, har in hau bishiya ba ki gan ni ba.”

    “To yaya kake zama a kan bishiyar kurna mai ƙaya?” Ta tambaye shi. Sai ya ce: “Ni na san dabarar da nake yi.” Haka dai suka ci gaba da hirarsu har ya kawo ga maganar aure, sai ta ce: “Ni dai marainiya ce, ba ni da uwa, ba ni da uba.” Sai ɗan sarki Aminu ya ce: “Yau na zama uwa da uba a wurinki.” Suna nan yana kiran ta, har ya fara zuwa gidansu marainiya.

    Da ‘yar kishiyar ta gane dan sarki ne yake zuwa wurinta, sai ta ce ta san makircin da za ta yi. Sai ta sayo allurai da yawa ta je ta sossoka a inda Aminu yake zama idan ya zo wurin marainiya. Da zuwansa sai ya zauna a kan alluran nan, kuma gaba ɗaya alluran suka shiga jikinsa.

    Nan da nan ya fara jin zazzaɓi, ya tashi ya tafi gida. Ciwonɗan sarki dai ya gagara warkewa, babu irin maganin da ba a yi ba. Wata rana marainiya ta tafi ɗiban ruwa a rafi, sai ta ji aljanu suna maganar ɗan sarki ba shi da lafiya, amma da an samo kashin tsutsotsi masu cin mutane a bayan wani gari mai nisa, aka jiƙa masa ya sha to zai warke.

    Da marainiya ta ji sai ta yi maza ta ɗauki goranta, ta je gida, ta aske kanta ta shafe jikinta da baƙin tukunya, ta sa kayan maza, ta ɗauki kwano, kamar almajiri zai je bara. Ta kama hanyar wancan gari mai nisa, inda za ta samo kashin tsutsa mai cin mutum, har sai da ta yi tafiyar shekara biyu kafin ta isa wurin tsutsotsin.

    Sai ta je wurinsu a hankali, ta kwanta don in sun ji motsin tafiyarta za su cinye ta. A hankali ta yi ta lulubawa dai -dai. Bayan ta sami abin da ta je nema, sai ta kama hanyar garinsu, ta isa lafiya. Bayan ta ɗan huta, sai ta kama hanyar gidan Sarki, ta tarar
    mutane maƙil sun cika fada suna jiran mutuwar Aminu.

    Da zuwa fada sai ta fara bara, mutane sun ɗauka namiji ne, suka ce: “Kai kana ganin ɗan sarki babu lafiya amma sai ka zo ka yi mana bara don ba ka da kunya?” Sai ta ce: “Ku bar ni in duba shi ko zai warke. Akwai wani magani da nake tafe da shi.” Sai suka daka wa ɗan almajiri tsawa, suka ce: “Duk duniyar nan babu wanda zai warkar da shi sai kai?”

    Sai ta ce: “Abar ni mana in ɗan gwada.” Da ƙyar aka bar shi ya shiga. Da shiga sai ta ciro wannan kashin tsutsa, ta jiƙa, ta ba ɗan sarki, ya sha. Cikin ikon Allah nan take sai ya fara amai, duk ya amayar da ciwon da ke damunsa, ya warke sarai. Kowa yana mamakin ɗan almajiri. A cikin farin ciki Sarki ya ce: “Zan ba ka gida da dawakai da dukiya mai yawa.” Shi ma Sarki bai san da mace yake magana ba.

    Sai ta ce: “A a ba na son wannan.” Sai Sarki ya ce: “To me kake so?” Ba tare da ɓata lokaci ba, marainiyar da ake zato namiji ce tace: “Ni dai babu abin da nake so kamar zoben hannunsa.”Ɗan sarki Aminu bai taɓa zaton zai rabu da wannan zobe ba, amma sai ya cire ya ba ta.

    Ta karɓa ta tafi. Bayan kwana biyu sai ya je gidan su marainiya a cikin fushi, yace da ita: “A duk garin nan babu wanda bai san da rashin lafiyata ba, amma ke ba ki taɓa zuwa gani na ba.” A cikin tattausar murya ta kalle shi ta ce: “Zauna ka ji labari.” Ya zauna ta fara gaya masa yadda ta yi.

    Da ta gama sai ya ce: “Ƙarya ne, idan maganarki gaskiya ce, to me aka bai wa ɗan almajirin?” Ya ce: “Zobe.” Sai ta ce: “To idan ke ce, nuna min zoben. Ya duba zobe, ya tabbatar zobensa ne. Daga nan ya fara mamaki. Ya ɗauke ta suka je gaban babansa, suka gaya masa labarin kome.

    Ya sa aka ɗaura musu aure, aka yi gagaruimin biki, kuma aka basu kyautar gari guda da dukiya mai tarin yawa, suka ci gaba da cin duniyarsu da tsinke. Kurunkus.

    > Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

    • Rabon kwaɗo ba ya hawa sama
    • Mai nema yana tare da samu
    • Mai rabon ganin baɗi ko ana ha-maza ha-mata sai ya gani.
    • Hassada ga mai rabo taki ce.

    Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

    Danna nan don karanta Tatsuniyar ‎Gizo Da Giwa

    Edita@rumasau-kallamu