BAYANI GA MAZA MASU MATSALAR HAIHUWA SANADIYYAR ƘARANCIN MANIYYI [LOW SPERM COUNT]

0
24

Duk wanda kaga matarsa da juna biyu toh hakan na nuna cewa shi wannan magidancin yana da wadatattun kwayoyin maniyyi cikin ruwan da yake samarwa.

Yawan ruwan maniyyi daban, hakazalik yawan kwayoyin maniyyi daban. Toh kwayoyin sune mafi muhimmanci fiye da yawan ruwan maniyyin da kake tsirtarwa inhar ana maganar samun ciki. 

Domin kai de ciki kurum ka gani, toh amma fa kasani kafin ka iya yiwa Mace ciki ta haifo lafiyayyen jariri ko jaririya sai maniyyinka ya cika sharruɗa guda Bakwai “7”

  1. Wadatattun kwayoyin maniyyi [Count] 
  2. Yalwataccen ruwa [Volume] 
  3. Kyakkyawar suffa da yakwar girma [morphology] 
  4. Motsi da Karsashin tafiya [Motility] 
  5. Kuzari [Vitality] 
  6. Rashin guba a jikinka [PH]
  7. Rashin kwayoyin cuta a mararka wato sanyin mara (UTI). 

Dole kana buƙatar tattara wannan kafin ka iya yiwa mace ciki, saide kwai wanda ko basu ana iya dace da cikin amma kuma kar ai mamaki don ya zube ko an haifo yaro nakasasshe. 

Domin karanta bayani akan VAGINAL DISCHARGE (FITAR DA RUWA AGABAN MACE) Danna nan

Mafi muhimmanci sune wadatattun kwayoyi da kuma karsashi.

Idan namiji ya fitar da ruwa, kai tsaye abinda mutane kan kira shi shine Maniyyi. Toh amma fa ba lallai maniyyin bane, bakowa ke samar da maniyyi ba.

– Shi iya wannan ruwan da kake gani da ido sunansa: Semen

– Idan kuma acikin ruwan ya tabbata kwai kwayoyin maniyyi to sunansa: Sperm, a sannan ne ya masa sunan maniyyi.

Sai kana iya samar da kwayoyin maniyyi sama da MILYAN SHA BIYAR zuwa ɗari da Ashirin [>15million–120million/m]° Sannan zaka iya yiwa Mace ciki. Matukar ka Gaza samar da wannan adadin tohfa kai juya ne, saide wani yaiwa matarka ciki amma bade kai ba.

Wannan matsalar idan maniyyi ya gaza kaiwa 15.million shine ake cewa Ƙarancin maniyyi [LOW SPERM COUNT]… Bawai rashin ganin namiji na fitar da ruwan me yawa irin yadda ake kallo a finafinan Batsa ba…. Sai kace wanda yake fitsari.

Shi wannan ejaculates Inka gama dama kai Release na abinda yakai kofi guda ko fin haka a yawa [volume] matukar babu kwayoyincan sama da 15million bazaka taɓa iya yiwa mace ciki ba.

Domin karanta bayani akan Ciwon Zuciya Tsantsa (Heart Failure) Danna nan 

Hakazalik inkaga dama ka fitar da maniyyi wanda baifi yawan murfin kwankwalati ba… muddin kwai wadataccen sperm cells ciki sai tayi ciki.

Muhimmin abu de anan shine, koda kana da wadataccen maniyyi sama da Milyan 15, babban abin so kai shooting numbar ya zamto baka kusa da BORDER ZONE, Yanzu Milyan 16 zuwa 20 ai bai wadatar ba, zaka iya ruftawa kasa, kuma gwargwadon Ƙarancin, gwargwadon rasa sauran abubuwa shida din.

Duk Ɗan maraina guda ɗaya [Golo/Testes] kullum na iya samar da kwayoyin maniyyi Milyan 60, kaga Kwaya biyun kana iya samar 120 million total. Shiyasa ko Golo daya mutum garesa zai iya yiwa mata in sun kai 4 ciki baki daya. A lafiyayyen mutum kenan. So, gara ace akalla kana iya samar da Milyan 40 zuwa sama.

Yana dakyau kuranta Jan Hankali Ga Masu Cin Smoked Fish (Bandar Kifi)

Don haka a likitance mun tabbatar da Kunga wannan abar Wato kankana ko watermelon tana haɓɓaƙa ruwan maniyyi, koda ga masu qarancinsa in muka dora mutum yai amfani da ita tsawon wata guda kullum daga baya in muka kuma sashi yai masturbation muka ɗau sample Zaka samu ya qaru.

Toh amma fa bawai kankanar bace kai tsaye… Galibi in munje sayenta ana redeta acire mana JAN ayar da farin me Koren ɓawo. Toh wannan farin da ake yarwa wato WATER MELON RIND shine ake bukata. Shine ke taimakawa wajen haɓɓaƙa ruwan maniyyi.

Inka sami me sana’ar koda sankelarsa kwaya 4 na wannan farin da suke yarwa bayan cire jan ya riƙa aje ma, kana reɗe koren bayan ka yayanka ko kaci haka ko ka kwaɗa da ƙuli-ƙuli zaka sha mamaki insha Allahu. 

Shi ko batun fitar da maniyyi sosai na faɗa muku kwanaki ka lura da kyau duk ranar da kasha ruwa a wadace sosai ka zamo hydrated toh ko masturbation kake aikatawa sai kaga bambanci a yawan ruwan da ka fitar. Ballantana mutum ya zamo me cin albasa sosai, tana qara yawan maniyyi, da sashi fresh, da gyara wancan morphology da kuzarinsa.

Albasa walau dafaffiya a abinci ko sanya a yayyanka da salads sosai aci. Duk randa Kasha ruwa a wadace ko kaci albasa sosai ko ka haɗa duk biyun sai kaga canji. Ballantana Fannin iyali. 

Sannan yana dakyau ku karanta wannan Kawar Da Fargaba Kan Dalilan Sanya Robar Hanci Ga Mara Lafiya

labarin da ya wuceVAGINAL DISCHARGE (FITAR DA RUWA AGABAN MACE)
Labarin na GabaAbubuwan Da Sukan Iya Taimakawa Wajen Raguwar Warin Baki