Ana iya gane ɗan tsibbu, matsafi mai sihiri ta hanyoyi kamar haka:
1- Yakan tambayi sunan mutum ko na iyayensa.
2- Yakan nemi wani abu da ya shafi mutum, kamar hankici ko hula ko tufafi ko farce ko gashi da sauran su.
3- Yakan nemi wata dabba mai wata siffa ta musamman.
4- Yakan sa a rabuta harufa ko alƙaluma marasa ma’ana.
5- Yakan karanta wasu sunaye masu rikitarwa.
6- Yakan yi bunne a ƙasa.
7- Yakan ƙona wani abu da dai sauransu.
Domin karanta cikakken bayani a kan Nau’o’in Sihiri danna nan.
Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Da Ake Yi Ga Mamaci A Cikin Sallar Jana’iza danna nan.
Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya; Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.







![Halayen Dake Haddasa Lalacewar Ƙoda [Kinney Dx] Halayen Dake Haddasa Lalacewar Ƙoda [Kinney Dx]](https://wikihausa.com.ng/wp-content/uploads/2024/05/Halayen-Dake-Haddasa-Lalacewar-Ƙoda-Kinney-Dx-100x70.jpg)


![Larurar Dannau [Sleep Paralysls] Da Yadda Za a Magance Larurar Dannau [Sleep Paralysls] Da Yadda Za’a Magance](https://wikihausa.com.ng/wp-content/uploads/2024/05/Larurar-Dannau-Sleep-Paralysls-Da-Yadda-Zaa-Magance-100x70.jpeg)