Tambaya
Assalamu alaikum. Mal ina da tambaya,
Shin in an haifi ‘ya mace wajibi ne sai an mata aski⁉
Amsa
Wa’alaikumus Salam Warahmatullah, Game da aske kan jariri a ranar 7, Hadisai ne 2 suka zo
NA FARKO: Lokacinda Fatima (R.A) ta haifi jaririnta Alhassan sai Annabi (S.A.W) ya ce da ita “Ki aske kansa” (MUSNAD-AHMAD)
NA BIYU: Annabi (S.A.W) ya ce “Kowane yaro abin jinginawa ne da abin yankansa, a yanka masa yinin 7, kuma a raɗa masa suna, kuma a aske masa kansa” (AHMD, ABU DWD, NASA’IY, IBN MAJAH)
Hadisin farkon yayin da aka haifi Alhassan ne shi kuma namiji ne,
Hadisi na biyu kuma ya zo da lafazin (غلام) shi kalmar (GULAM) yana nufin yaro namiji,
Don haka ba a shar’anta aske kan jaririya ta mace ba, sai in namiji ne, وبالله التوفيق
(FATAWAL LUJNAH- no-17,998)
ALLAHU A’ALAM.
Ansawa : Sheikh Abubakar BN Mustafa Biu
13/10/2019