Masu hikima suna cewa: In mutum ya ce zai ba ka riga to ka dubi ta jikinsa kuma “wanda ba shi da abu ba zai iya bayar da shi ba.”
A kan haka ya wajaba a kan duk wani wanda nauyin tarbiyya ya hau kansa iyaye, malamai da shugabanni ya kasance mai tarbiyya ne shi a kan kansa.
Wani mutum ya tambayi malamansa cewa ya koya masa yadda ake yin tarbiyyar ‘ya’ya a lokacin ‘yarsa ta fari tana wata ɗaya da haihuwa, sai malamin ya ce da shi ai kuwa ka makara. Saboda ita tarbiyya tun kafin a yi aure ake fara yin ta ba sai an haifi ɗan ba.
Malamai sun yi bayanin siffofin da ya wajaba mai ba da tarbiyya ya siftantu da su in dai yana son ya sami nasarar aikin tarbiyya kuma ya yi tasiri.
A Taƙaice Ga Waɗannan Siffofin
Ya kasance mai haƙuri da juriya da naci, kada ya ɗauka cewa tarbiyya aiki ne na sha yanzu magani yanzu.
- Ya yarda cewa haƙƙi ne wajibi a kansa. Ya rinƙa jin haka a ransa a kowane lokaci. wannan zai hana shi yin watsi da tarbiyyar iyalinsa.
- Ya rinƙa sa ido da lura da bibiya, saboda tarbiyya kamar dashe ne in ba a bibiyarsa da kula da shi sai ya bushe ya lalace ko dabbobi da ƙwari su kashe shi.
- Yi dan Allah (Ikhlasi) kada mutum ya nemi wani lada ko yabo a kan tarbiyyar ‘ya’yansa da iyalınsa sai a wurin Allah kawai. Saboda haka ban da alfahari ban da fariya ban da gorantawa ‘ya’ya da iyali ban da raina ‘ya’yan wasu.
- Tarbiyya tana buƙatar tausasawa da bin al amura sannu-sannu daki- daki, tsanani da gallazawa kawai ba sa kawo gyara, dole sai ana cizawa ana hurawa.
- Mai ba da tarbiyya shugaba ne, saboda haka ya kamata ya siffantu da siffofi na shugabanci ya kasance jarumi, mai adalci, mai kwarjini, mai iya ɗaukar nauyin waɗanda yake jagoranta, mai kyauta, sauƙin kai da saussauci a inda ya dace, mai tsanani a inda ya dace, da dai sauran siftofi na jagora ko shugaba na gari.
- Harkar tarbiyya ba abu ne da ake yinsa da ka ba, lallai sai an yi karatun tarbiyyar saboda tana farowa, tun kafin a auri uwar da har ta haife shi ya balaga, za a yi masa tarbiyyar jiki, Imani, halaye, ladabai, haƙƙoƙi, siyasa da sha’awa. To in ba ilimi ta yaya wannan aiki zai yiwu.
- Wajibi ne mai tarbiyya ya kasance mai adalci.
- Ya kasance yana ɗaukar matakai na gasakiya a komai ya daidai ta tsakanin tsanani da sassauci da sakin hannu da rowa, ya kasance tsaka-tsaki a komai.
9 Wanda yake da tsananin rowa da ƙanƙamo da masifar son abin duniya ba zai iya tarbiyya ba. Dole ya kasance mai sakin hannu da sakin fuska. Kada ya ɗauka asarar kuɗi yake yi in ya biya kuɗin makaranta ko ya sai abinci da sauran buƙatun ‘ya yansa.
10 Ya kasance mai nuna ƙauna ta gaskiya ga’ ya’yansa maza da mata ‘ya’yan uwar gida da na amarya.
11 Dole ne mai tarbiyya ya kasance nutsattse mai hankali da tsari a rayuwarsa.
12 Wajibi ne mai tarbiyya ya kasance ya siffantu da kyawawan halayen da yake umarni da a aikata su, yana nisantar munanan ayyukan da yake hanawa. Kada ya zama fitina ga waɗanda suke a ƙarkashinsa.
13 Ya kasance mai kyakkyawan fata da sakakkiyar zuciya kada ya rinƙa camfa abubuwa ko saurin siƙewa da fidda rai kan samun nasara.
14 Ya kasance mai jin ƙai da tausayi.
15 Ya kasance mai tsoron Allah (Taƙawa) wannan sharuɗɗa muhimmancinsa ya gawurta.
Karanta Masu Rera Waƙa
Edita@rumasau-kallamu