Yadda Za A Ci Jarrabawar Bala’in Da Ya Tsananta A Cikin Sauƙi

0
1508

A duk lokacin da ka samu kanka cikin wani hali na matsi a rayuwa, to ka tuna daman can Allah yana jarrabar bayinsa da masifu daban-daban.

Allah Ya ce:

“Wallahi sai mun jarraba ku da wani abu na daga tsoro da yunwa da tawayar dukiya, da asarar rayuka da na kayan marmari, kuma albishir ga masu haƙuri”.
(Baqara:115).

Ka ga tunda mun fahimci kowane irin tsanani daga Allah ne; To, ka ga mun san babu mai yaye mana, sai Allah Maɗaukakin Sarki.

Mene ne abin yi kenan?

Abin yi shi ne mu rungumi wannan ƙaddara, da yin haƙuri, da koyi da yadda Annabi (S.A.W) ya ce mu yi.

Jarrabawa na iya zama mabambanta a tsakaninmu. Wani rashin iyaye, wani cuta, wani talauci, wani rashin ‘ya’ya da dai sauransu.

Wani lokacin kuma, ya zama Annoba ce da Allah ya jarrabi dukkanin al’umma. Wato kamar ciwon sarƙewar numfashi (Corona).

Shi Musulmi duk abin da ya same shi na sharri da wahala ba za ka same shi yana raki ba. Kuma yai ta mita ko laƙanawa wani shi ya ja masa. Koda yake rauni irin na ɗan Adam ba a hana mutum baƙin ciki ba. Amma dai zai zama mai dogaro ga Allah.

Matakan cin jarrabawar bala’in da yayi tsanani

  • Mu ƙasƙantar da kawunanmu. Mu tuba, mu yi nadama. Mu yawaita istigfari.
  • Mu yawaita karatun Ƙur’ani.
  • Mu bincika tsakaninmu da iyayenmu mu gyara. Mu dinga kyautata musu.
  • Ma’aurata su gyara tsakaninsu.
  • Mu yawaita sadaka.
  • Mu yawaita addu’a Allah Ya yaye mana. Ya kawo mana mafita.
  • Mu yawaita: Hasbunallahu wa ni’imal wakeel.
    Lahaula wala quwwata illa billah.
    La’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimn.

A ƙarshe mu sani, mai sauƙi ne a wajen Allah ya yaye mana kowanne irin bala’i. Saboda haka, mu gaggauta gyara tsakaninmu da Mahaliccinmu. Sannan kuma ga dukkanin jarrabawa irin ta Annoba; Mu bi shawarar malamai, da shugabanni, da ma’aikatan lafiya.

Da bin waɗannan in sha Allahu sai ka ga mun yi nasara. Mun ci jarrabawar bala’in da ya tsananta cikin sauƙi.

Wallahu A’alam.

Duba Yadda Ake Tsaftace Baki

labarin da ya wuceYadda Ake Tsaftace Baki
Labarin na GabaYadda Za Ki Koya wa Mijinki Ko Matarka Wasanni.
Amin Yusuf Gwamna
Sunana Amina Yusuf Gwamna Shugaba Kungiya Mace ta Musamman da ke kokari inganta rayuwar Mata da kanana Yara. Marubuciya litattafai hausa. Kuma Shugaba Makarantu Abu-Nusaiba Da ke Ring road, kano.