Yadda Ake Ayyukan Gida Domin Taimakon Juna

0
1559

Akwai wata sananniyar hanya da ma’aurata ke bi domin ƙara donƙon soyayyar aurensu. Ita ce taimaka wa juna a wajen ayyukan gida. Yadda gidansu zai kasance cikin tsafta da tsari a koda yaushe.

A wajen maza da yawa, kula musu da gida ya fi komai muhimmanci a gare su. Yin shara, da wanke-wanke , da girki da dai sauransu.

Aikata wannan shi ne mafi muhimmanci a wajensa. Kuma da shi ne zai zama kin mallake shi.

Shi yasa idan namiji mai ɗabi’ar son a yi masa hidima ne, yake son wacce duk kika ajiye ta a mai aiki. ƙanwarki ce ko mai aikatau ce.

Shi yasa komai gatan ki. To ki bambance irin ayyuka da za a yi miki. Da irin wanda ke da kanki za ki dinga yi wa mai gidanki.

Burge irin wannan miji shi ne ta hanyar aiki.
Wato shi ne yi wa mijinki hidima da kanki. Har ma ki ƙara da kyautatawa.

Misali: Wanke masa ƙananan kayansa. Jallabiyya, da safa , da rigunan bacci.

Namiji na da kyakkyawan zato a kan matar da za ta kula masa da hidimar gidansa. Shi yasa namiji ba ya gamsuwa idan matarsa mai kasala ce. Sai yai ta ƙorafi , duk da irin kyawunta da kwalliyarta kuwa.

Yin hidimarta gare shi soyayya ce. Da kuma son kyautata masa.

To amma mene ne yake sanya wasu mata ƙyuiya. Ko kuma ince jin ganda. Har ma da masu jin ƙyashi. Wai don me zan ta aiki a cikin gidan nan ne?

Wata Matar ta taso cikin sakaci saboda dukiya. Ba ta komai a gidansu, ba ta iya aiki ba. Wata kuma ganin wadatar mijinta ne, ke sawa ta ƙi komai. Wata kuma mijin bai sayan ruwa, da omo, da sauransu. Dole ce ke sa ta bar gida da ƙazanta. Wata kuwa sai ta ce ma yadda mijinta ke tilastawa a yi ayyuka gida ba tausayi. Ta kan ji ya ɗauke ta tamkar baiwa. Wannan ke kashe mata karsashin ayyuka.

Mene ne kesa wasu yin aiki a gidan mijinsu, har ka ga tamkar ba sa gajiya?

Wata tana da ilmin addini, ta ɗauki dukkan hidimar gidanta a matsayin ibada. Tana duba irin matsayin Assayida Fadima (R.A) da yadda ta dinga hidima a gidanta, har hannunta na nunawa. Kuma Annabi (SAW) bai ba ta baiwa ba ,ya rarrashe ta da ta je ta cigaba da yi. Idan mace ta tuna wannan sai ta himmatu.

Yabawa ƙoƙarinta na ayyuka ne ke sa mata kwarin gwuiwa. Tai ta aiki ta ji kamar batirinta ya samu caji 60%.

Idan kuma ka shigo tana girki. Sai ɗanku ya tsala kuka. Sai ka ɗauke shi, ka sa shi a kafaɗa kana jijjigashi. Tana lekowa ka ce je ki ƙarasa aikinki. Sai ta ji batirinta ya samu cikakken caji 100%. Saboda a ɗabi’arta taimakonta ya fi komai muhimmanci.

Ka zama mai sauƙin kai, da kyautatawa matarka. Domin bin wasiyya da Annabi ( SAW) ya yi a kan Mata.

Annabi ( SAW) ya ce : Mafi cikar masu imani daga muminai, waɗanda suka fi kyawun ɗabi’a, sannan mafi alherinsu, su ne, waɗanda suka fi alheri ga matansu“.
(Tirmizi).

A wani gida za ka tarar da mata, ta yi ma yara wanka (2/3) . Miji ne zai shafa musu mai da sa kaya. Ita kuma ta wuce madafa ( kitchen) tana shara da girka abin karyawa.

Kafin rufe wannan batu na taimakon juna da ayyuka na gida. Akwai wani taimako daban. Shi ne taimakon juna a kan ayyuka na ibada. Mace ta dinga amfani da hikima wajen zaburar da mijinta ibada.

Mace kuwa dama renonta ake da cigaba da tarbiyyarta. Ya zama wajibi ga miji ya jajirce domin ganin matarsa na yin duk abin da Allah Ya ɗora mata.

Yana ƙara wa namiji daraja. Kuma cika umarni Allah ne.

Allah Ya ce: Ya ku waɗanda kuka yi imani! Ku Kare wa kanku da iyalanku wata wuta makamashinta mutane da duwatsu ne. A kanta akwai waɗansu mala’iku masu kauri, masu ƙarfi. Ba su saɓa wa Allah ga Abin da Ya umarce su, kuma suna aikata abin da ake umarninsu”.
( Tahreem: 6)

Annabi SAW ya ce: Allah ya jiƙan namijin da zai tashi cikin dare, ya tayar da matarsa don su yi sallah, ta ƙi tashi saboda barci sai ya shafa ma ta ruwa a fuska, har ta tashi, su ka yi sallah”.
( Abu Dawud)

A ƙarshen yin ayyuka na gida domin taimako juna na dasa soyayya. Ta zama ƙatuwar bishiya har ta yi rassa. Ta ba da ‘ya’yan farin ciki da girmama juna.

Tausayi da taimakekeniya a aure na zaburar da Ma’aurata sosai.
domin kara fahimta zaman aure dannna koren rubutu yadda ake shafa jiki na Musamman ga Ma’aurata ko yadda ake shagwaɓa maigida lokacin hutu ko yadda zaki mayar da gidaki masarautar ki.

Litattafai da aka duba:

Babul Wasiyyatu binnisa’i
Riyadus Salihina.

Lacca:M. Bashir Abubakar Takai.

Act of Service
The 5 love languages
Gary Chapman.

Abubuwa da ke sawa Mace ta Zamo mafi soyuwa a gurin mijinta.
Aure A Musulunci

Love and Respect
Dr. Emerson Eggerichs.

labarin da ya wuceMatakan Bunƙasa Ƙudurar Ɗan’adam
Labarin na GabaYadda Ake Shafa Jiki Na Musamman Ga Ma’aurata.
Amin Yusuf Gwamna
Sunana Amina Yusuf Gwamna Shugaba Kungiya Mace ta Musamman da ke kokari inganta rayuwar Mata da kanana Yara. Marubuciya litattafai hausa. Kuma Shugaba Makarantu Abu-Nusaiba Da ke Ring road, kano.