Yadda Ake Vegetable Macaroni

0
1611

Abubuwan haɗawa

  • Tafasasshe macaroni (macaroni ya danganta da irin shape da kike so)
  • Kabeji
  • Koren tattasai
  • Tattasai
  • Attaruhu
  • Karas
  • Albasa
  • Lawashi
  • Kayan ɗanɗano
  • Gishiri kaɗan
  • Man gyaɗa ko butter
  • Soyayyen nama ko Kaza ko kifi

Yadda ake haɗawa

  1. Da farko ki gyara kabejinki, ki yanka, ki wanke da ruwan vinager ko ki sa gishiri wajen wankewar, sai ki tsane a matsami. Ki ɗauko karas ki cire dattin, ki goga a abun goge kubewa.
  1. Ki jajjaga attaruhu, sannan ki yanka albasa. Ki ɗauko Koren tattasai, jan tattasai da lawashi wankakke, sai ki yanka su sai ki ajiye a gefe.
  1. A ɗaura tukunyarki a kan wuta, ki sa butter ki yanka albasarki, ki soya sama-sama. Sai ki kawo taruhu ki sa, ki soya sama-sama shi ma, ki kawo kayan ƙamshi, gishiri da maggi. Ki sa daidai ɗanɗano da zai miki, sai ki sa ruwa kaɗan a ciki (daidai wanda zai karasa dafa miki macaroninki).

Ki rufe tukunya na ɗan wani lokaci, har sai ruwan ya fara tafasa, sai ki ɗauko tafasasshe macaroni, ki sa ki juya sai ki rufe na ɗan wani lokaci, har sai ruwan ya ɗan shanye.

  1. Sai ki ɗauko kabejinki da carrot naki, ki sa a ciki ki juya. Ki rage wuta ki rufe tukunyarki na ɗan wani lokacin kaɗan (ya turara) sai ki ɗauko koren, jan tattasai da lawashi ki sa ki juya sai ki sauke.

Ki sa a plate ki ɗaura soyayyen namanki ko na kaza a kai.

Ku karanta Yadda Ake Dashishi

labarin da ya wuceYadda Ake Zoɓo A Cikin Sauƙi Sabon Salo
Labarin na GabaYadda Ake Haɗa Sinasir
BHM Ninja
Sunana Buhari Ibrahim Aliyu [Googler] dalibin computer, digital marketer, technical crew a wikihausa dalibi mai kokarin yada ilimi na na'aura mai kwakwalwa tare da tabbatar cigaban kasuwancin zamani.