Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wani sarki mai mata ɗaya da ’yarsu ɗaya mai suna Kulu. Kwanci-tashi, Allah ya yi wa matar sarkin nan rasuwa. Bayan ɗan wani lokaci, sai Sarkin nan ya auri wata bazawara. Ita kuma tana da ’yarta mai suna Zainab. Bayan amaryar Sarki ta tare, sai ta sa wa Kulu karan tsana. Kullum sai azabtar da ita take yi.
Wannan mata ta yi ta tunanin yadda za ta yi ta gama da Kulu, amma ta rasa. Daga ƙarshe sai tace da ’yarta, watau Zainab agolar Sarki, idan sun je rijiya ɗauko ruwa, ta sa Kulu jan ruwa. Idan ta zura gugar cikin rijiya ta fara jawo ruwa, sai ta tunkuɗa ta cikin rijiyar. Da suka je sai Zainab ta ba Kulu guga, kuma ta tsaya a bayanta.
Kulu na gama zura guga, tun ma ba ta fara jan ruwan ba, sai Zainab ta ingiza ta cikin rijiya, ta kuma kama hanya, ta koma gida. Da ta yi wa mahaifiyarta bayanin ta tunkuɗa Kulu cikin rijiya, sai ta ce: “Kin kyauta, mun huta da’yar banza.” Waccan rijiya kuwa da aka tura ɗiyar Sarki, tana kan hanyarsa ta komawa gida domin yana kan kewaya ƙasarsa.
A wannan rana kuma ya biyo sanda yake dawowa daga wani ɗan tattaki a kan dokinsa, makaɗa na bin sa a baya suna yi masa kirari suna cewa: “Sarki mai duniya, Sarki gatan Kulu.” Da Kulu ta ji sai ta ce: “Uban Kulu, ko uban Zainab?” Zainab ta ji daɗinta. Ga ubanta ya zo gida, Amma ga Kulu nan a cikin rijiya.”
Sai wani dogari ya ce: “Ku yi shiru ku ji.” Da suka yi kawai, sai suka sake jin waƙar. Nan take aka gane lallai muryar Kulu ce. Ba tare da ɓata lokaci ba aka shiga rijiyar, aka
tsamo Kulu. Ta ji jiki, domin ta sha bugun bangon rijiyar nan sanda aka tunkuɗa ta ciki. Mamaki da haushi suka kama Sarki, amma ya shanye, bai nuna fushinsa a bainar jama’a ba.
Amma fa tun a bakin rijiya ya tambaye ta yadda aka yi ta auka cikin rijiya. Sai ta yi masa bayani yadda matarsa ta turo su rijiya, aka ba ta guga ta jawo ruwa, da yadda agolarsa, watau Zainab ta ingiza ta ciki. Bayan Sarki ya koma fadarsa ya huta, sai ya kira amaryarsa, bai ma bari ya ji abin da za ta ce game da inda Kulu take ba, ya sanar da ita cewa zamansu ya ƙare.
Ya sa aka kwashe kayanta, ya ƙara mata da dukiya mai yawa, ya ce a mayar da ita ga mahaifanta. Ya ci gaba da zama da Kulu, kafin ya sami wata macen kirki ya aura. Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Ramin mugunta haƙa shi gajere wataƙila kai ne za ka faɗa ciki.
- Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai ya yi.
- Kishi kumallon mata.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Karanta Tatsuniyar Auren Kaza Da Muzuru
Edita@rumasau-kallamu









