Tatsuniyar Samarin Ɓarayi Uku

0
4

Ga ta nan, ga ta nanku.

A can wani gari wai shi Komayya da ke kusa da Dajin Dila na yamma da ƙoramar Kada, akwai wasu samari su uku. Ɗaya ana kiran sa Ba-ka-son Asara; na biyunsu kuma Ɓarna; na uku Wayo.

Kullum ba su da aiki sai su shiga gonakin mutane su tono rogo, ko su yi ta karya dawa ko gero ko masara, su je wani gari su sayar. Yau da gobe, abu ya ishi mutanen gari, har aka ɓullo da dabarar yadda za a kama ɓarayin nan.

Da suka san an kafa doka a garin, sai Wayo ya ba su shawara a kan su je garin da ba a san su ba, su nemi abin yi. Suka yarda da wannan shawara, suka nufi wani gari. A wannan gari sai da suka yi shekara bakwai suna neman kuɗi, ba sa raba asusu.

Sannu a hankali, suka tara kuɗin da suka cika asusunsu maƙil. Ganin sun sami kuɗi, sai suka yanke shawarar komawa gida. Da ranar tashinsu ta zo, sai suka kama hanya, har dai Allah ya kai su garinsu lafiya.

Bayan sun isa gida, ba su ko shiga gari ba suka tarar da wata tsohuwa tana aikin sabulu. Sai suka ba ta ajiyar kuɗin a kan idan sun yi wanka, za su karɓa, tare da sharaɗin cewa kada ta ba kowa daga cikinsu kuɗin, sai su duka ukun sun haɗu.

Tsohuwa ta ce: “To, ku da abin ku, ai yadda kuka ce za a yi.” Ta karɓi kuɗi, ta ajiye musu. Ko da suka shiga wurin wanka, har sun tuɓe kayansu, sai suka tuna ba su da sabulu. Sai suka sa Wayo ya je ya karɓo.

Da Wayo yaje gun tsohuwa, sai ya ce mata: “Wai ki ba ni, ma’ana kuɗin.” Sai tsohuwa ta rantse, ta ce atafau, ba za ta ba shi ba. Sai Wayo ya koma ya sanar da ‘yan’uwansa, wai ta ce ba za ta bayar ba.

Jin bayanin Wayo, sai suka je gaba ɗaya suka ce da ita: “Ai mu ne muka ce.” Da ta ji daga bakinsu, sai ta ɗauki kudi ta ba Wayo. Da kuɗi suka shiga hannunsa, sai ya kama hanya, ya gudu. Suka jira, kamar zai zo yanzu ne, ko sai an jima ne, shiru.

Saboda sun gaji da jira, sai suka fito suka tambayi tsohuwa: “Ba ki ba shi sabulun ba ne?” Sai tsohuwa ta ce: “Wane irin zancen banza kuke yi, bayan kun ce in ba shi kuɗi, yanzu kuma ku ce sabulu?”

Da jin kalaminta sai suka tubure a kan cewa ba ta isa ba, sai ta nemo shi su amshi kuɗinsu. Daga nan sai suka tafi wurin alƙali. Alƙali ya tambayi tsohuwa yadda aka yi. Ta kwashe labarin abin da ya faru ta gaya masa.

Sai alƙali ya ce ta je ta nemo musu kuɗinsu a cikin kwana uku. Tsohuwa ta fita da kuka, tana tafiya. Sai ta haɗu da wani mutum, ya tambaye ta abin da ya faru. Sai tsohuwa ta ce: “Gara mutuwa da abin da ya faru da ni.”

Daga nan ta yi masa bayani daki-daki, ta gaya masa abin da ya faru sarai. Da ta gama, sai ya ce da ita: “Ai wannan abu mai sauƙi ne.” Ta ce: “Kamar yaya fa?” Sai mutumin ya ce: “Ki koma wurin alƙali ki ce masa kin samo kuɗin.

Idan ya ce ina suke, ki ce suna nan, amma sai samarin nan sun haɗu su uku kafin ki ba su.” Tsohuwa ta yi godiya. Washe-gari ta koma wurin alƙali, ta gaya masa cewa kuɗi sun samu, kamar yadda mutumin ya gaya mata, tare da bayanin cewa amma ba za ta bayar ba sai samarin nan sun hadɗ su uku.

Alƙali ya ce: “Kina da gaskiya. Ku kuma samari sai ku yi ƙoƙari ku samo ɗan’uwanku, ku zo gaba ɗaya, don ku karɓi kuɗinku.” Daga nan kowa ya watse, samari suka tafi cikin ɓacin rai, ita kuma tsohuwa ta tafi da murna.

Shi kuma Wayo yana tafiya har rana ta fadi. Sai ya yanke shawarar zai bi ta wata gajeriyar hanya, wadda ta ratsa ta cikin ɗaya daga gonakin da sukan je sata a da. Bai san cewa masu gona suna fakonta ba don yawan rogonsu.

Saboda haka yana shiga gonar zai wuce sai suka auka masa. Yana zaton abokansa ne suka gan shi, sai ya zura da gudu. A garin gudun tsira sai ya jefar da jakar kuɗi; ko garin ma bai shiga ba, ya wuce. Masu fako a gonar rogo suka ɗauki kuɗi.

Ba tare da wata fargaba ba suka rabe kuɗin tsakaninsu. Da wani daga cikinsu ya yi lissafi, sai ya gano kuɗin sun yi daidai da masararsu da rogonsu da dawarsu da wakensu da dai sauran amfanin gonakin da aka sace musu aka sayar.

Daga ƙarshe dai suka ce kuɗin nan sakamako ne daga Allah. Biyu daga cikinsu sai suka sayi shanun turka, ɗaya kuma ya ƙara gona. Yanzu haka suna can suna cin duniyarsu. Kurunƙus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Ba a cin amana a kwana lafiya.
  • Ba da umarni a duƙunƙune ba da cikakken bayani ba yakan janyo asara.
  • Duk wayonka akwai wanda ya fi ka wayo.
  • Wayo a kan rashin gaskiya wauta ne.
  • Kowa ya ɗauko da zafi, bakinsa.
  • Dubu ta cika.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Karanta Tatsuniyar Muwa Muwa

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Muwa Muwa
Labarin na GabaTatsuniyar Auta Da Dodanniya
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.