Tatsuniyar Ɗantsintuwa

0
5

Ga ta nan, ga ta nanku.

Akwai wata mata da mijinta, suna zaune a wani ɗan kauye. Sun daɗe tare, to amma Allah bai ba su haihuwa ba. Wata rana matar nan ta je gona, sai ta tarar da jinjiri a kan dutse, sai ta ɗauko. Ashe wannan yaro ba mutum ba ne, ɗan aljani ne, ba ta sani ba.

Sai ta kawo yaron gida. Da mijin ya ga yaro, sai ya tambaye ta inda ta samo shi. Sai ta ce, ai ɗan tsintuwa ne, sai mijin ya ce, anya wannan mutum ne kuwa? Sai matar ta ce ai da ma ta san zai ƙi amincewa da yaron. Don gudun zuciyar matarsa, sai ya ce: “To, shi ke nan na yarda mutum ne, kuma ki riƙe shi.” Suka ci gaba da renon yaron.

To, matar kullum tana zuwa gona da yaron. Daga ƙarshe dai ta samo yarinyar da za ta riƙa yi mata reno a gidan idan ta tafi gona. Kullum idan za ta tafi sai ta dafa musu abinci. To, da zarar ta tafi gona ta bar su da mai renon, sai ya rikiɗa ya zama babba ya kama yarinyar nan ya ɗaure, ya cinye abincin duka ya hana ta, ya yi ta wasanni iri-iri da rawa.

Sai ya lura matar nan ta kusa dawowa daga gona, sai ya kunce mai renonsa ya koma yaro, ya yi ta birgima a ƙasa yana kuka. Idan iyayen sun dawo sai su hau kan mai reno da duka. Idan za ta yi magana ko bayani, sai su ce ta yi shiru, domin su a ganinsu yaron yana kuka ne saboda ta hana shi abinci, kuma tana dukan sa, har yana birgima.

Kullum haka, sai wata rana wata tsohuwa maƙwabciyarsu ba ta je gona ba. Tana ɗaure dangarta, sai ta hango ɗan jariri ya miƙe, ya ɗauko igiya ya ɗaure mai renonsa, ya fara waƙa, yana rawa. Ya kuma cinye abinci duka, ya hana ta, tana ɗaure. Haka tsohuwa ta yi ta leƙen su, har yamma ta yi.

Sai ta ga ya koma yaro, ya kama birgima, yana kuka, har iyayen suka dawo. Washe-gari sai tsohuwa ta yi kiran masu gidan, ta zana musu duk abin da ta gani. Ta ce idan sun shirya za su gona, su je gidanta su ɓuya, za su ga duk abin da yake yi. Sai suka amince. Washe-gari, suka shirya tafiya gona, amma sai suka shiga gidan tsohuwa suka ɓuya.

Can sai yaron ya fara yin abin da ya saba, suna gani, abin ya fara ba su mamaki, har ya gama. Da suka dawo gida, sai suka ƙi dukan mai reno, shi kuma sai ya ƙi barin kuka. Sai matar ta shirya, ta tafi gidan boka, ta yi masa bayani.

Sai boka ya ce, idan ta je gida washe-gari da safe ta sayo ɗan akuya ƙosasshe, ita da mijin su ja shi su yi ta tafiya, sai sun ga wata babbar bishiyar kuka. Ya ƙarasa da cewa: “Sai ku ajiye yaron, ku ce za ku huta. Sai ku ɗaure ɗan akuyan. Sai mijinki ya ce zai je ya yi fitsari, sai ya gudu. Ke kuma, sai ki ce za ki dubo shi, sai ki bi shi, kada ku juya”.

Sai suka amince. Da gari ya waye, sai suka je suka samo ɗan akuya ƙosasshe, suka ɗaura igiya a wuyansa. Sai suka ce za su je wani ƙauye gaisuwa, sai matar ta ɗauki yaro ta goya, suka kama hanyar daji. Suna cikin tafiya, sai suka hango wannan babbar kuka, sai mijin ya ce su je su huta a gindinta.

Da suka je, sai suka yi duk yadda bokan nan ya ce su yi, watau suka yi dabara, suka gudu. Da suka isa gida, sai tsohuwar ta sami matar ta ce to daga yau ta daina ƙwadayin sai ta sami ɗa ta kowace hanya, kuma ta rungumi ƙaddara sai abin da Allah ya yi da ita a rayuwarta.

Da ɗan aljani ya gaji da jira, ya ga shiru, sai ya miƙe ya kunce ɗan akuya, ya riƙe, ya kama hanyarsa, ya shiga ƙungurmin daji, bai sake komawa gidan mutanen nan ba. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Zafin nema ba ya kawo samu.
  • Yi haƙuri da godiya ga abin da Allah ya ƙaddara a rayuwarka ta duniya.
  • Tsintacciyar mage ba ta yin kyanwa
  • Son zuciya, ɓacin zuciya.

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Danna nan don karanta Tatsuniyar Ɓarayin Albagadadi

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Ɓarayin Albagadadi
Labarin na GabaTatsuniyar Dogarawa Uku
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.