Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wani mutum da ba ya aikin komai sai ya fita farauta, yana haƙar ramukan Ɓera. Idan ya kamo ɓeraye yakan yanka ya yi bandar naman ya kai kasuwa ya sayar. Wani lokaci yakan fita wannan farauta tare da wani maƙwabcinsa, har ma sun yi suna ƙwarai wajen wannan sana’a tasu.
Wata rana shi da maƙwabcinsa sun fita farauta, sai suka ga wani babban rami. Da suka tsaya za su haƙa sai maƙwabcin ya ce: “Wannan fa ramin Kura ne bana Ɓera ba. Kada mu tono abin da zai cuce mu.” Sai ya ce da shi: “Kai dai ka cika tsoro, idan dai kai ba za ka haƙa ba, ka tafi ka ba ni wuri.” Da maƙwabcin nasa ya ji haka sai ya tafi abinsa, ya bar shi yana tona ramin.
Da ramin ya yi zurfi sosai, sai yasa ƙwaryarsa domin ya kama ɓerayen da yake zato suna cikin ramin. Sai ya ji an buge ƙwaryar. Da ya duba sai ya ga ashe Kura ce, har ma ta miƙo ƙafarta waje. Nan da nan ya jefar da kayan haƙan ya kama gudu. Yana cikin gudu ne ya tarar da wasu manoma a gona, sai ya ce da su: “Ku taimake ni ku ɓoye ni mana, ga Kura nan ta biyo ni za ta cinye.”
Da suka ji haka sai suka ce: “A a, ka yi gaba, ba za mu iyaba.” Haka ya ci gaba da gudu, har ya tarar da wasu mutane masu noma da hanci, ya roƙe su da su ɓoye shi; su ma suka ce ya yi gaba. Ya sake yin gaba da gudu, har ya tarar da masu noma da duwawu, sai ya tsaya ya ce su taimake shi, amma su ma suka ƙi.
Sai ya ci gaba da gudu, har ya hango wata ’yar bukka sai ya matsa kusa ya leƙa; amma
ba komai a ciki sai Kunkuru yana zaune. Sai ya dubi Kunkuru ya tambaye shi: “Ina mai bukkar nan? Ina so ya taimake ni ya ɓoye ni.” Sai Kunkuru ya ce: “Ai ni ne mai bukkar, shigo zan ɓoye ka.”Sai mutumin ya ce da Kunkuru: “Manya ma ba su ɓoye ni ba sai kai da karambani za ka ce ka ɓoye ni?”
Kunkuru ya ce da shi: “Kai dai shigo mana ka gani.” Mai neman Ɓera dai ya tsaya da gardama, har ma ya juya zai tafi, amma kafin ya fara tafiya sai ya hango Kura ta doso bukkar, kuma ya san idan ya fita za ta kama shi. Ai bai san sanda ya kutsa bukkar Kunkuru ba, kuma ya ɓoye shi. Da Kura ta ƙaraso sai ta ce da Kunkuru:
“Da namana a ɗakin nan.” Kunkuru ya ce: “Babu namanki a ɗakin nan.” A nan Kunkuru da Kura suka kama faɗa, kafin wani ɗan lokaci Kunkuru ya kashe Kura. Da mutumin nan ya ga haka, abin ka da halin ɗan Adam sai kawai ya ce da Kunkuru: “Ni kuma ai nama ya samu a araha; bari ma in feɗe shi, kuma ina son ƙwaryar.”
Da Kunkuru ya ji haka sai ya ce da shi: “Ka haƙura da fatar Kurar nan mana, ta fi maka amfani. Ka ma kwashe naman nata ga baki ɗaya.” Mutumin nan dai ya ƙi, ya dage shi dai ƙwaryar Kunkuru yake so. Kunkuru dai ya yarda, ya kuma ce da shi: “To, zan haɗa ka da karnuka su raka ka garinku, domin duk sanda fatar Kurar nan za ta cinye ka sai su kama ta da ci.”
Da ƙyar dai mutumin ya yarda ya tafi da karnukan. Mutumin nan shi da karnuka sun kama hanya sun yi nisa, sai ya ji ya gaji, ya ajiye fata a gindin wata bishiya zai huta. Ajiye ta ke da wuya sai ta fara motsi tana kukan Kura. Da karnuka suka ga haka sai suka rufar mata, suka murƙushe ta, ta daina kukan, kuma ta daina motsi, ya tashi ya ɗauka suka ci gaba da tafiya.
Bayan wani lokaci kuma, sai ya tsaya zai yi fitsari, fata kuma ta fara motsi. Karnuka kuma suka fara haushi fiye da irin wanda suka yi a baya. Sai mutumin wai ya ji haushi, ya daka musu tsawa, har suka tsorata suka gudu. Kafin ka ƙifta ido, ai fatar nan ta rufe mutumin nan ta cinye shi, kowa ya huta da taurin kansa. Kurunƙus.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
- Taurin kai da rashin ɗaukar nasiha babu abinda yake jawo wa mai shi sai cutarwa da faɗawa halaka.
- Wanda bai ji bari ba, ya ji hoho.
- Kowa ya ɗebo da zafi, bakinsa.
Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.
Karanta Tatsuniyar Makauniya Da Ɗanta
Edita@rumasau-kallamu










