RIYA A MUSULUNCI:
Duk wata ibada da musulmi zai yi don neman lada a wurin Allah, sharaɗi ne ya zama an yi shi ne saboda Allah Shi Shi kaɗai, ba tare da an haɗa Shi da wani mahaluki cikin wannan ibadar ba. Dole ne musulmi ya nufi Allah da kowace irin ibada da niyyar Allah ne Ya ba da umarnin a yi kuma Shi zai bada lada. Ya tabbata a hadisin Mahmud Bin Labid RA cewa Allah SWT zai faɗa wa waɗanda suka aikata wani aiki ba don Allah shi kaɗai ba, Allah zai ce musu ku je wurin waɗanda kuka yi aikin domin su a duniya su duba ko su na da ladan aikinku.
A hadisin Imam Ahmad, Manzon Allah SAW ya ce “ Babban abinda na fi ji muku tsoro, ƙaramar shirka. Sahabbai suka ce; mecece ƙaramar shirka? Manzon Allah SAW ya ce Riya” Riya ƙaramar shirka ce ta fuskar neman yardan Allah da kuma neman yabon mutane. Shi kuma Allah, in dai ibada ce, toh Shi kaɗai ƙwallin – ƙwal a ke yi dominSa ba a haɗa Shi da wani – ko waye shi. Ita wannan shirkar bata fitar da mutum daga musulunci, amma tana ruguje ladansa, ta sa ya rasa ladan gaba ɗaya, sai dai ma ya ƙare da zunubi.
Saboda haɗarinta, Manzon Allah SAW ya ja hankalinmu game da ita a hadisin Abi Musal Ash`ari, ya ma gargaɗe mu da mu guje ta. A wani hadisi Manzon Allah SAW ya ce: Riya tana shiga aiki – ba tare da mutum ya sani ba, kamar yadda Tururuwa ta ke tafiya akan dutse a cikin duhun dare” Jin tafiyar Tururuwa a kan dutse a cikin duhun dare abu ne mai wahala, toh haka tantance Riya cikin aiki, ta hanyar shin da wani nufi ko niyya aka yi aikin.
TASIRIN SOCIAL MEDIA:
Wannan dandali ko saha ta zama ruwan dare mai gama duniya, kuma tasirinsa ya wuce duk yadda mutum ya ke tsammani. Cikin `yan sakanni, duk wani abinda ya faru zai iya karaɗe duniya batare da bata lokaci ba. Wanɗanda su ke manyan birane ko cikin surƙuƙin daji duk zasu gani ko su ji. Sannan tasirin sa yanzu ya kai yana iya canza komai.
Tasirin social media, ya kai yana iya canza wani ra’ayi na manyan mutane ɗaiɗaiku, yana iya tasiri a kasuwanci a kasuwanci, siyasa kai har uwa uba yana canza ƙudurorin gwamnatocin ƙanana da manyan ƙasashe. Idan akwai abinda zai iya girgiza gwamnati cikin ‘yan sakanni a wannan zamanin babu kamar Social Media.
Cikin `yan kwanakin nan shugaban ƙasar Amurka Trump ya yaɗa wani shaguɓe da barkwanci a ɗaya daga cikin dandalin social media inda ya nuna shi ne “Yesu” wanda zai ceto duniya. Kafin ka ce wani abu, duniya ta sako Trump a gaba nan da nan ya goge abinda ya wallafa.
Misali na biyu; bayan hare haren da Isra`ila ta kai wasu garuruwa a ƙasar Labanon, ranar 16 zuwa 17 ga watan Afrilu, 2026 sai wani bidiyo ya yi ta yawo a Social Media inda aka gano wasu sojojin Isra`ila sun karya wani mutun-mutumin “Yesu” suna faffasa shi da guduma.
Wannan abin ya janyo kakkausar sukar ƙasar Isra’ila, duk da an san yadda Israila take da taurin kai ga duk ƙudurorinta ko abin sojojinta suka aikata, amma sai ga shi hukumomi a Isra`ila suna ba da haƙuri game da abinda ya faru, har da hukunta sojojin da suka aikata abin da hukuncin dauri na kwana 30 a gida, da kuma samar da wani mutun-mutumin sabo da mayar da shi inda yake nan take cikin kwanaki da bai wuce biyar ba. Wannan abin ba wanda ya isa ya sa Isar`ila ta yi wannan abin duk duniya in ban da tasirin Social Media ba.
MUTANE A YANZU DA SOCIAL MEDIA:
Ɗan adam, Allah ya halicce shi da son burgewa, neman ɗaukaka da shuhura. A yanzu dandalin Social Media ya zama hanya mafi sauƙi wurin samun waɗannan abububwan, nan da nan mutum zai shahara ko`ina a sanshi a ganshi, sunansa ya yaɗu. Akwai mutanen da ban da tasirin social media ba, da har su mutu ba wanda zai san suntaba rayuwa, sai `yan kaɗan da suke kusa da su, sai kuma a labari da hira in ta kama.
Misali, irin manyan shehunan malaman da aka taɓa yi a ƙasaittacen birnin Kano waɗanda muke jin labari da wasu ma da har yanzu bamu sansu ba – Allah yayi musu rahama, Ya sa suna aljannah- da yanzu ne da sun karaɗe sosial media ko`ina an sansu ana ganinsu kamar yadda a yanzu muke ganinsu Prof. Bashir Aliyu Umar, OON da sauransu. Muna jin labarin Barau ƙwallon- shege da aka taba yi shi ma a Kano. Da yanzu ne da duk duniya sai ta san labarinsa kamar yadda aka san su Umar Bush da sauransu.
Shugannin ƙasashe, manyan jagororin kasuwanci da na manyan shugabannin wuraren hada hada a duniya, yanzu sun fi maida hankali wurin nuna manufofinsu ta waɗannan hanyoyi na social media. Daga cikin shugabanni, kan gaba wurin amfani da social media akwai shugaban Amurka Trump, manyan `yan kasuwa akwai su biloniyan nan Elon Musk da kamfanisa na Tesla.
RIYA DA SOCIAL MEDIA
Wannan tasiri da ake gani na wannan sahar da dandali, ya sa wasu mutane dan neman shuhura da neman ɗaukaka, yin amfani da waɗannan hanyoyi ta yadda ba su tsaya neman duniya kaɗai ba, sai suka zarce har da aikin ibada. Mutane kowa yana neman hanyar da zai yi shuhura, wasu sun rungumi tallace tallace da kasuwanci, wasu bada ilimin addini da tarbiyya, wasu sana`o`i da ilimin zamani, wasu ɓarna da fasadi.
Waɗanda suka ɗauki yaɗa ayukan ibadan da suke yi a social media, dan neman ɗaukaka da shuhura, su sani, wannan ba dai dai ba ne. Abin ya zama ruwan dare, sai ka ga mutum zai taimaka wa wani ko wasu masu buƙata, amma sai ya ɗora a media, ko bayan ya yi ibadar sa, sai kuma ya zo media yana ba da labari.
Kai mai imani da ka yi don Allah, ina ka ga tallatawa a social media? Allah mabuwayi ne, kuma baya taɓar da aikin bawa, idan bawa ya yi ne dan Shi, sai Allah ya bashi ladan aikin cikakke kuma ya sa mutane suyi ta yaba masa ba tare da ya tallata a social media ba.
Hadisin Abi Huraira wanda Imamul Bukhari ya fitar da shi, Manzon Allah SAW ya ce: “ Mutane bakwai suna cikin inuwar Al`arshi ranar da babu wata inuwa sai ita (ranar ƙiyama)- daga cikin waɗannan mutane, akwai wanda yayi sadaka da hanun damansa amma hanun hagunsa ba sani ba” a wannan hadisin yana nuna mana tsantsar ikhlasi da boye aikin ibada dan Allah shi kaɗai.
Mu sani, duk wanda ya yi aikin ibada, idan har ya yi ne don a gani, ko don a yaba masa, ba shi da ladan komai a wurin Allah. Allah zai faɗa wa waɗanda suke aikin ibada dan a gani a yaba ranar tashin ƙiyama, Ya ce musu: “Ku je wurin waɗanda kuka yi aiki dan su, ku duba ko suna da ladan da za su ba ku” wanda ya yi aikin ibada a nan duniya ya ɗora a social media don ya sami comment da likes, to waɗannan comments da likes ɗin su ne ladansa, ba shi da komai a wurin Allah.
Allah SWT ya ce “ Sai mu gabatar da ayukan da suka aikata, sai kawai mu sheƙar da shi kamar ƙura”S25:23, wasu malamai sun fassara wannan ayar ta cikin suratul Furƙan da cewa; waɗanda suka yi aiki ne ba dan Allah ba, sun yi ne dan su sami yabo, shuhura da ɗaukaka (likes, commnets and share), ko dan a san sun yi ko suna yi, to Allah sai ya sheƙar da ladan su kamar ƙura. Duk wanda ya yi aikin ibada dan likes, kuma ya samu, toh an biyashi, haka wanda yayi dan comments, share, view ko followers.
Daga ƙarshe, mu ji tsoron Allah mu kyautata niyar ayukanmu, mu sani, Allah ne ya yi umarni da dukkan aikin ibada, kuma Allah ne zai bada lada. Wanda ya yi imani da Allah akan haka, ya sani Shi Allah duk inda bawa yayi aikin ibada – cikin dare ko rana, a bayyane ko a ɓoye, a birni ko a ƙauye- Allah ya sani kuma zai bashi lada cikakke. Shi tsantsance aiki ga Allah, shine duk lokacin da bawa zai gabatar da aiki kar ya nufi kowa da wannan aikin a zuciyarsa in ba Allah Shi kaɗai ba.
Allah yana fada a wani hadisil ƙudsi wanda Abi Huraira ya raiwato, Imam Muslim ya fitar da shi, Allah ya ce: “Ni mawadaci ne ga duk wani mai haɗa Ni da wani a cikin aiki, duk wanda ya yi aiki ya haɗa Ni da wani, toh Ni bana buƙatar wannan aikin” Ɗan’uwa musulmi, mai imani da Allah bazai so a ce Allah ya ce baya bukatar aikinsa ba, ranar da yake cikin tsananin bukatar ladan aikinsa.
Allah ka datar da mu, ka kaɓi ayukan mu. Amin.
Danna nan don karanta Ga Tsoro Ga Ban Tsoro
Edita@rumasau-kallamu






![Gangliyon Sist [Ƙarin Mahaɗar Ƙashi] Gangliyon Sist [Ƙarin Mahaɗar Ƙashi]](https://wikihausa.com.ng/wp-content/uploads/2024/05/Gangliyon-Sist-Ƙarin-Mahaɗar-Ƙashi-100x70.webp)



