Bahaushe yana da fasaha qirqirar abubuwan amfani yau da kullum, misali:
Masassaqa na sarrafa itatuwa zuwa turmin da tavarya don daka abinci, akushin (kwano) na cin abinci, ludayi, allon karatu, qotar gatari, gora, turken doki, kujerar zama, muciya, duk su yi masa zane mai kyau da wuta.
Maqera na sarrafa qarfe don samar da wuqa, takobi, mashi, kibiya, matsefi, tukunya, adda, zabira, aska, ruwan gatari da fatanya, garma, manjagara, sungumi, lauje, garkuwa da sauransu.
Majema na sarrafa fatatun dabbobi zuwa gugar xibar ruwa, buzu, fatar ganga, gafaka, laya, kambu, kayan shimfixa, sutura, takalmi, tandun mai, salka, maratayi, kube, linzamin doki, dorina da sauransu.