Yadda ake hada Rice Flour

0
71

Farkon tambayar da zaizo zuciyoyin idan akace flour ɗin shinkafa shine “meyasa shinkafa ina flour alkama. Amsoshin da dama na nan. 

  1. shinkafa na saurin narkewa a jikin ɗan adam wannan na iya zama lamba ɗaya wurin zaɓen abincin yara  ko kuma na tsofaffi
  2. shinkafa bata da wani wari.
  3. shinkafa hypoalergic properties:- wato duk mutanen da suke da suke da alergic zasu iya cin shinkafa ba tare da matsala ba .
  4. shinkafa bata da sinadarin “fat” aciki kuma tana zuƙar (shan) mai wanda hakan na nuna ma zatai kyaun abinci gashi kamar su cake, bread da sauransu.
  5. shinkafa nada ƙarancin sinadarin protein wanda hakan nada amfani ga masu cutar celiac disease da sauran cututtukan da basu buƙatar sinadarin protein

Domin karanta yadda ake Yadda ake Jollof Rice Danna nan 

Shinkafa itace babban ingredient wajen yin sababbin nau’ikan abincin flour da suya kamarsu cake, bread, crepes, pancakes, doughnuts, rice milk da sauransu.

Akwai hanyoyi biyu na sarrafa shikafa zuwa gari wannan hanyoyi sune:-

  1. Wet method:- na markaɗe
  2. Dry method :- na niƙa.
  3. Wet method:- wannan itace hanyar sarrafa flour shinkafa da zaiyi laushi sosai . A wannan ana jiƙa shinkafa sai a markaɗa .
YADDA AKE YI
  1. Da farko za’a wanke shinkafa sai a jiƙata ta kwana.
  2. A tsiyaye ruwan sai a zuba sabon ruwa a kai a markaɗa.
  3. Idan an markaɗa sai a tace da rariya mai laushi ko kuma abin tata.
  4. Idan an tace sai a barshi ya kwanta kamar yadda ake gasarar koko sai a tsiyaye ruwa.
  5. sai a sami abun tata a juye wannan gasarar aciki sannan a kawo abu mai nauyi a ɗora akai har sai wannan ruwan gasara ya tsane tas.
  6. A kawo faranti  mai kyau a warwara  gasarar akai a kai wuri mai tsafta da inuwa a ajiye har sai ya bushe .
  7. Idan ya bushe za’a iya sake niƙawa da blender idan kuma bai cuccure ba sai a tankaɗe.
  8. wannan hanyar sarrafa shinkafa na haɗa fulawa mai matuƙar laushi.
  9. Dry method:- wannan hanyace da ake samar da fulawar shinkafa cikin sauri da kuma sauƙi.

Domin karanta Yadda Ake Coconut Jollof Rice Danna nan

YADDA AKE YI
  1. A jiƙa shikafa sai a tace ta a baza ta ta sha iska sannan sai a kai a niƙa tayi laushi.
  2. A sami rariyar laushi a tankaƙe ta.
  3. A ajiye a mazubi mai kyau domin yin nau’ikan abincin flour.

Da wannan fulawar za’a iya yin abincin gargajiya da shi kamar su waina da sinasir.

Domibn sanin yadda ake miyar karkashi da kubewa danna nan
labarin da ya wuceYadda ake Madi Rice
Labarin na GabaYadda Ake Pancake Cikin Sauki
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.