ABUBUWAN BUƙATA:-
- shinkafa ½ cup
- Nama kilo 225 a yanka ƙanana
- Tumatir ɗin leda ko gwangwani (220g) T lpaste
- Tafarnuwa guda ɗaya babba
- Rabin kofin man gyaɗa ½ cup
- Nutmeg ½ tsp
- sinadarin ɗanɗano: Tumatir albasa, attaruhu da tattasai a markaɗa
- ¼ tsp chilli pepper
- Ruwa 2 cups
YADDA AKE HAƊAWA
Domibn sanin yadda ake miyar karkashi da kubewa danna nan
- Acikin tukunya mai zurfi a wanke nama a zuba aciki azuba ‘yar albasa, tafarnuwa da sinadarin ɗanɗano sai a barshi ya dahu acikin ruwan nama idan nama ya dahu ruwan ya ɗan ƙafe sai a zuba man- gyaɗa a soya naman ya soyu sai a kwashe
- A zuba markaɗaɗɗen kayan miya a ɗan soya shi sama-sama sai a zuba tumatir ɗin gwangwani da kayan ƙamshi (tafarnuwa, kirfa, black pepper da kuma chilli powder) sai ayita juyawa har kayan miya su soyu.
- Idan kayan miya sun soyu sai a zuba nama da ruwa sannan a bar ruwan ya tafasa
- A wanke shinkafa a zuba sai a saka sinadarin ɗanɗano a juya a rufe
NOTE:- A kula wajen juyawa don kar shinkafa ta caɓe
- A rage wutan shinkafa a bar shinkafar ta dahu har ta tsotse sai a sauke za’a iya cin shinkafar da salad idan ana buƙata ko da coslow.
Domin karanta Yadda Ake Coconut Jollof Rice Danna nan