Ƙa’idoji Goma Sha Ɗaya Na Samun Nasara A Rayuwa

0
13

Babu shakka Ubangiji Maɗaukaki ya halicci mutum ya kuma hore masa iko da zaɓi wajen sarrafa rayuwarsa. Ɗan’Adam na da baiwa mai faɗi, da kuma dama yalwatacciya matuƙar ya san yadda Ubangiji Maɗaukaki ya ba shi. 

Mutum zai iya cimma burinsa na rayuwa, darajarsa kuma ta ɗaga ta fuskar imaninsa da ɗabi’unsa da zamantakewarsa da tattalin arziƙinsa da ƙwarewarsa a sana’a ko ilmi, matuƙar ya bi waɗannan ƙa’idoji guda goma sha ɗaya masu zuwa: 

1.TANTANCE MANUFA KO BURI (TARGET) 

Ma’anar manufa ko buri (target) shi ne, dukkan abin da mutum yake kwaɗayin kaiwa gare shi. Ɗan’Adam ba ya rabuwa da buri, sai dai ba dole ne burin ya zamo mai kyau ba. Manufa ko buri za su iya zama gama-gari ko su zanto keɓantattu masu iyaka waɗanda za a iya aunawa ko waɗanda ba za a iya aunawa ba.Buri zai iya zama mai dogon zango ko mai gajeren zango. 

Domin karanta Neman Aure Bisa Koyarwar Musulunci Danna nan

Cimma buri (target) ya dogara ne ga yadda mutum ya ci ɗamara, ya kuma bi hanyoyin cin nasara don kaiwa gare shi. 

Misalin burace-burace a rayuwarmu sun haɗa da: 

⮚ Samun ɗaukaka. 

⮚ Mallakar muhalli. 

⮚ Sayen mota. 

⮚ Digiri a kan likitanci. 

⮚ Ƙarfafa dangantaka da Ubangiji Maɗaukaki. 

⮚ Haddace AlƘur’ani. 

⮚ Samun digiri na biyu (masters Degree) ko phd. 

⮚ Bunƙasar jari. 

⮚ Kiyaye salloli a kan lokutansu. 

⮚ Azumin Alhamis da Litinin duk sati. 

⮚ Karance wani littafi mai amfani cikin kowane wata. 

⮚ Yin umara a watan Azumi. 

⮚ Zuwa Ƙasashen waje don yawon buɗe ido. 

Shin mai karatu wane buri kake da shi a yanzu? 

Kuma wace hanya kake bi don cim masa? Shin burinka mai amfani ne a duniyarka da lahirarka? Ya zama wajibi musulmi ya tantance burinsa da manufarsa a wannan rayuwa. 

Babbar hanyaar cimma wannan shi ne, dole komai na rayuwarmu ya zamo a dandamalin bauta ga Ubangijinmu maɗaukaki. Domin bauta ita ce sababin halittarmu. 

Ya kamata mai ƙoƙarin cimma kowane buri ya kula da ɓangarori uku na bayar da haƙuƙuwa ga ma’abotansu. Ma’ana haƙƙin mahalicci da haƙƙin ababen halitta da haƙƙin mutum a karan kansa.

Domin Karanta Cikekken Littafin Danna nan

labarin da ya wuceYin Jadawalin Ayyukakn Rana Da Yini A Rubuce
Labarin na GabaKamannin Annabi Muhammad (S.A.W), Kyan Halittarsa Da Siffarsa