Ɗabi’ar Daudanci (EFFEMINACY)

0
32

Daudanci shi ne namiji ya riƙa yin ɗabi’u irin na mata, maimakon maza ‘yan-uwansa. Daudanci shi ne ake kira “effeminacy” a likitance. Shi kuma ɗan-daudu ana kiransa “effeminate “.

Dalilai na kiwon lafiya (medical reasons) da kuma dalilai na tunanin ƙwaƙwalwa (psychological reasons), waɗanda suke haddasa daudanci suna da rikitarwa matuƙar gaske, sa’annan suna da yawa. Kaɗan daga cikinsu su ne, kamar haka:

  1. Tasirin Rashin Daidaiton Zubar Ruwan Sinadarai (Hormonal Influences): Rashin daidaiton zubar ruwan testosterone da estrogen da progesterone a cikin jikin namiji za su iya yin tasirin canza masa ɗabi’unsa, har ya koma yana yin ɗabi’u irin na mace. Yawan testosterone da estrogen da progesterone waɗanda ake samunsu a jikin maza yana bambanta bisa la’akari da shekaru, ƙoshin lafiya, da sauransu. Amma idan yawan sinadaran ya saɓawa adadin da aka fi sani da yawa, to, hakan zai iya haifar da matsalar daudanci kamar haka:
  • Yawan testosterone da ake buƙata (normal range) shi ne daga 300-1,000 ng/dL (nanograms per deciliter).
  • Yawan estrogen (estradiol) da ake buƙata shi ne daga 10-40 pg/mL (picograms per milliliter). Yawan progesterone da ake buƙata shi ne kada ya wuce 1.0 ng/mL (nanograms per milliliter). Idan namiji yana da ƙarancin testosterone, to, zai iya zamowa ba shi da ƙwanji irin na maza (reduced muscles mass), yawan kitse (increased body fat), da rashin kazar-kazar (reduced energy levels), kuma hakan zai sanya a yi masa kallon ɗan-daudu. Idan namiji yana da estrogen mai yawa, to, hakan zai iya haifar masa da yin manyan nonuwa (gynecomastia), rashin gashin baki da gemu (hypogonadism), da yin manyan ɗuwawu (steatopygia). Idan namiji yana da progesterone da yawa, to, hakan zai iya sanya masa ɗabi’u irin na mata (emotional sensitivity) kamar saurin kuka, raunin zuciya, rashin iya rigima da mutane, da sauransu. Abubuwan da suke haddasa rashin daidaiton waɗannan sinadaran su ne kamuwa da cututtukan hanta, cancer, yawan ƙiba, laulayin magunguna, rashin motsa jiki, rashin ci da shan abubuwa masu gina jiki, da kuma gado. Ana iya magance rashin daidaiton zubar ruwan sinadaran ne ta hanyar  ɗora mutum akan maganin da ya dace, da cin ingantaccen abinci, yin ayyukan motsa jiki.
  1. Gado (Genetics): mutum yana iya yin gadon ɗabi’un daudanci daga iyaye ko kanannisa. Ya zuwa yanzu akwai ƙarancin bayanai a kimiyyance akan yadda hakan yake faruwa. Amma masana ilimin kimiyya suna cigaba da yin binciken domin gano yadda a’lamarin yake. 
  1. Tsari Da Ayyukan Ƙwaƙwalwa (Brain Structure and Functions): sakamakon binciken kimiyya ya tabbatar da cewa akwai bambanci a tsakanin ƙira da ayyukan ƙwaƙwalen mace da namiji. Don haka, idan halittar ta yi kama da ta mace, bisa ga yadda Allah SwT ya yi ta, to, akwai yiwuwar mutum ya riƙa yin ɗabi’un daudanci.
  1. Tunanin Ƙwakwalwa Da Yanayin Zamantakewa (Gender Dysphoria, Psychological, and Social Factors): idan namiji ya kasance yana tunanin cewa shi kamar mace yake, ko yana sha’awar ɗabi’un mata, ko ya tashi a cikin muhallin da ba ya hulɗa da maza ‘yan-uwansa sai dai mata, to, akwai yiwuwar ya riƙa yin ɗabi’un daudanci. Maganin wannan shi ne iyaye mu riƙa yin ƙokarin ganin cewa ‘ya’yanmu maza suna yin hulɗa da maza ‘yan-uwansu.

Yana da muhimmanci iyaye mu kiyaye da ɗabi’un ‘ya’yanmu. Idan suka ga namiji yana nuna alamun ɗabi’un daudanci, ko kuma mace tana nuna alamun ɗabi’un ‘yan-mazanci, to, mu ɗauki matakin gane inda matsalar take, domin ɗaukar matakin da ya dace. Ma’ana, mu je asibiti domin a yi bincike a tabbatar da abinda yake faruwa, domin ɗaukar matakin da ya kamata.

Don karanta Muhimman Abubuwan Da Suke Inganta Lafiya danna nan

Edita; Rumasa’u M. Kallamu

labarin da ya wuceWayewar Farko
Labarin na GabaTsarabar Makon Sahabbai 2025