Ƙurajan Pimples

0
35

Kurajen fuska na pimples matsala ce da ta addabi matasa Mata da maza musamman masu kananan shekaru wadan da suka fara balaga sabida samun canji daga sinadaran hormones. 

Duk da kurajen fuska suna Kama Mata da maza , amma mata sunfi damuwa sabida za kaga har liƙab suke sanyawa a fuskokin su saboda kar aga ta’adin da kurajen suka yi musu a fuska. Domin karanta Bayani Mai Mahimmanci Zuwa Ga Mata Akan {Ovulation} Shiga nan

Kurajen pimples ba a fuska kadai take fita ba suna fita a wadannan wuraren:

  •  Kirji 
  •  gadon baya
  •  Cinya
  •  wuya 
Abubuwan Da Suke Taimakawa Wajen Tunzura Ƙurajen Fuska:
  •  Yawan cin abu mai maiko.
  •  Amfani da mayukan da basu dace da fatar jiki ba
  •  Kwayoyin cuta
  •  Shiga rana sosai
  •  Wasu magunguna
Abinda Ya Kamata Ayi Domin Kariyar Yawaitar Ƙurajen Fuska Da Samun Waraka Sune:
  • A rage amfani da abinci masu maiko dayawa.
  • Idan kuraje suka fito kada a yawaita tabawa.
  • Idan zakai daga waya kada ka daura wayar a fuskar ka kusada kurajen.
  • A samu ruwan dumi a matsa lemon tsami a wanke fuska da shi a kalla so biyu a rana.
  • Idan kurajen a kirji ko baya kada ayi amfani da matsesen kaya sabida samun iska.
  • Za’a iya shafa zuma bayan dan mintuna a wanke da ruwan dumi.

Idan wadannan hanyoyin basuyi amfani ba a tuntubi ma’aikacin lafiya domin akwai magunguna da dama masu kashe kurajen pimples.

Domin karanta Ciwon Ciki (Stomach Pain) Da Yadda Za A Magancesa Danna nan

labarin da ya wuceCiwon Ciki (Stomach Pain) Da Yadda Za A Magancesa 
Labarin na GabaKansar Bakin Mahaifa