Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Carrying load for payment - A turance tana nufin dako. Misali; Ƙungiyar masu dako sun koka kan ƙarancin biyansu da mutane ke yi. HAU; Dako (Tana nufin ɗaukarwa mutum kaya a kai masa inda yake so, ya biya)
Cartilage - A turance tana nufin guringuntsi. Misali; Guringuntsi na da daɗi musamman a miyar taushe. HAU; Guringuntsi (Tana nufin ƙashi mai laushi da ke jikin ɗan Adam da dabba)
Casa - Tana nufin cire tsaba daga cikin kwansonta, kamar shinkafa da gero da sauransu. Misali; Sai an casa shinkafar sannan za a dafa. ENG; Thresh Grain (A turance tana nufin casa)
Cassava Flour - A turance tana nufin kwaki. Misali; Ɗaliban makarantun kwana suna son kwaki sosai HAU; Kwaki (Tana nufin garin rogo)
Cat - A turance tana nufin mage. Misali; Gidansu Hanan suna da ƙaton kule. HAU; Kule (Tana nufin mage)
Catch - A turance tana nufin kama. Misali; Jami'an tsaro sun kama masu lefi da yawa a wannan makon. HAU; Kama (Tana nufin riƙe abu da hannu)
Catch Something - A turance tana nufin cafe. Misali; Mai tsaron ragar ya cafe ƙwallon da aka bugo masa. HAU; Cafe (Tana nufin kama abu da sauri)
Cattle Tax - A turance tana nufin jangali. Misali; Malam Modibbo ya biya jangali da wuri wannan karon. HAU; Jangali (Tana nufin kuɗin harajin da ake biyawa shanu)
Cause - A turance tana nufin haddasa. Misali; Zuwanta a makare shi ya haddasa ta rasa gurin zama. HAU; Haddasa (Tana nufin sila ko zama dalilin faruwar wani abu)
Caɓa - Tana nufin yin ado da yawa. Misali; Amaryar ta caɓa ado sosai. ENG; Make Slushy (A turance tana nufin caɓa)
1 42 43 44 45 46 300