Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Bureau of Public Procurement (BPP) - Hukumar samar wa ma'aikatu kayayyaki
Bureau of public procurement (BPP) - Hukumar samar wa ma'aikatu kayayyaki
Bureau of Public Service Reforms (BPSR) - Hukumar jarabawar ma'aikatun gwamnti
Bureau of Public Service Reforms (BPSR) - Hukumar Kyautata ma'aikatun gwamnati
Burgami - Tana nufin jakar da aka yi ta fatar akuya, wadda yawanci masu ba da maganin gargajiya ke amfani da ita. Misali; Malam Yahaya ya ratayo burgami a gurin bikin maharba. ENG; Goat skin bag (A turance tana nufin burgami)
Burge - Tana nufin ƙoƙarin janyo ra'ayi ko yardar wani. Misali; Samarin na ƙoƙarin yin komai don burge 'yan matan su. ENG; Impress (A turance tana nufin burge)
Burgu - Tana nufin jibgegen namijin ɓera. Misali; Da zan je makaranta na ga wani burgu ya shige rami da gudu. ENG; Giant Male Rat (A turance tana nufin burgu)
Buri - Tana nufin abinda mutum yake so ya cimma. Misali; Zuwa ƙasa mai tsarki shi ne babban buri na. ENG; Wish (A turance tana nufin buri)
Burn - A turance tana nufin ƙone. Misali: Wutar ta ƙone takardun da ke kan tebur. HAU: Ƙone (Tana nufin ƙuna ko lalacewar abu sakamakon wuta ko zafi mai yawa)
Burn Completely - A turance tana nufin ƙurmus. Misali: Wutar ta ƙona gidan ƙurmus cikin ɗan lokaci kaɗan. HAU: Ƙurmus (Tana nufin ƙonewa gaba ɗaya har abu ya lalace ko ya zama toka)
1 40 41 42 43 44 348