Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Canary - A turance tana nufin kanari. Misali; Tun asuba nake jin kukan kanari a kan bishiyar gidan nan. HAU; Kanari (Tana nufin wani nau'in tsuntsu ma'abocin rera waƙa)
Cancak - Tana nufin ɗungurungum, wato a ɗauke abu gaba ɗayansa. Misali; Ta ɗauke jakar cancak daga kan teburin. ENG; Completely Gone (A turance tana nufin cancak)
Cancanta - Tana nufin dacewa. Misali; Malamin ya cancanta a ba shi lambar yabo, saboda ƙokarinsa. ENG; Deserve (A turance tana nufin cancanta)
Canine Tooth - A turance tana nufin fiƙa. Misali; Yaron ya fara fiƙa. HAU; Fiƙa (Tana nufin haƙoran gaba)
Canja - Tana nufin sake wani abu da wani. Misali; An canja lokacin jarrabawar daga ƙarfe ɗaya zuwa ƙarfe biyu na rana. ENG; Change (A turance tana nufin canja)
Cankacakare - Tana nufin ƙarewar abu ƙarƙaf. Misali; Kayan marmarin sun zama cankacakare. ENG; Running short of something (A turance tana nufin cankacakare)
Canoe - A turance tana nufin kwalekwale. Misali; Ba a zuwa ƙauyen sai an hau kwalekwale. HAU: Kwalekwale (Tana nufin ƙaramin jirgin ruwa)
Cap - A turance tana nufin hula. Misali; Ya sanya hula zanna bukar 'yar Maiduguri. HAU; Hula (Tana nufin nau'in sutura da ake sa wa a kai)
Cara - Tana nufin kukan da zakara yake yi musamman da asuba. Misali; Tun da zakara ya yi cara na farka. ENG; Cock Crow (A turance tana nufin cara)
Carabke - Tana nufin wasa da ake yi da dutse, inda ake wurga dutse sama a cafe shi da hannu. Misali; 'Yan matan suna 'yar carabke a ƙofar gida. ENG; Game of tossing and catching stones on hands (A turance tana nufin carabke)
1 41 42 43 44 45 300