Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Blabbing -
A turance tana nufin kwarmato.
Misali: An hana shi shiga taro saboda halinsa na kwarmato.
HAU; Kwarmato (Tana nufin yawan faɗin sirri ko magana ba tare da ɓoye abu ba)
Black - A turance tana nufin baƙi.
Misali; Ina neman baƙin takalmi zan siya.
HAU; Baƙi (Tana nufin launi mai duhu)
Black-hooded Cobra - A trurance tana nufin kumurci.
Misali; Kumurci ya sari kaka a gona.
HAU; Kumurci (Tana nufin baƙin maciji mai dafi)
Black-hooded Cobra - A turance tana nufin gamsheƙa.
Misali; Mun ga gamsheƙa a hanyar gonar Malam Mudi.
HAU: Gamsheƙa (Tana nufin ƙaton baƙin maciji)
Blackboard - A turance yana nufin allon rubutu.
Misali; Malami yana rubutu a kan allo.
HAU; Allo (Abin rubutu ne galibi na katako)
Blanket - A turance tana nufin bargo.
Misali; Indo ta wanke bargon da ta siyo ran Asabar.
HAU; Bargo (Tana nufin abin lulluɓa don jin ɗumi da kuma kariya daga jin sanyi)
Blinking - A turance tana nufin ƙifce.
Misali: Jaririyar tana ƙifce ido saboda hasken rana ya yi mata ƙarfi.
HAU: Ƙifce (Tana nufin rufe ido da buɗe shi cikin sauri, musamman saboda haske ko motsi)
Blood - A turance tana nufin jini.
Misali; Likita ya ce sai an ƙara masa jini leda ɗaya.
HAU; Blood (Tana nufin sinadarin ruwa mai launin ja wanda zuciya take harbawa sassan jiki, yana ƙunshe da abubuwan da jiki ke buƙata domin rayuwa)
Blow - A turance tana nufin hura.
Misali; Tun ɗazu nake hura wutar ta ƙi kamawa.
HAU; Hura (Tana nufin fito da iska ta baki)
Blow One’s Nose - A turance tana nufin fyace.
Misali; Tun ɗazu take fyace hanci saboda mura ta kama ta sosai.
HAU; Fyace (Tana nufin fitar da majina daga hanci da ƙarfi)