Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Birgima - Tana nufin a yi ta juyi a ƙasa.
Misali; Yaron yana ta birgima don an hana shi fita wasa.
ENG; Rolling on the ground (A turance yana nufin birgima)
Biri - Tana nufin dabba mai yanayin siffar mutum.
Misali; Da muka je gidan ajiye namun daji mun ga biri da kura.
ENG; Monkey (A turance tana nufin biri)
Biris - Tana nufin nuna halin ko-in-kula da abu ko yin watsi da shi.
Misali; Duk da yana cikin mawuyacin hali amma matarsa ta yi biris da shi saboda rashin kirkinsa.
ENG; Ignore (A turance tana nufin biris)
Birjik - Tana nufin da yawa ko adadi mai yawa.
Misali; Kaya ne birjik a shagon su Bala, sai wanda ka zaɓa.
ENG; Abundantly (A turance tana nufin birjik)
Birki - Tana nufin abin da ake takawa ko matsawa abin hawa ya tsaya, kamar keke ko mota ko babur da sauransu.
Misali; Direban ya taka birki lokacin da shanu suka zo tsallaka titin.
ENG; Brake (A turance tana nufin birki)
Birkice - Tana nufin a juya abu daga sama zuwa ƙasa.
Misali; Ya birkice ɗakin yana neman maɓallin rigarsa.
ENG; Overturn/upside down (A turance tana nufin birkice)
Birni - Tana nufin maraya ko inda ababben more rayuwa na zamani suke.
Misali; A birni ake samun manyan gidaje da manyan makarantu
Kishiyarta; Ƙauye
ENG; Town (A turance tana nufin birni)
Bisa - Tana nufin a kan wani abu.
Misali; Littattafan na bisa teburi.
Kishiyarta; Ƙarƙashin
ENG; On top/above (A turance tana nufin bisa)
Bisani - Tana nufin daga baya ko kuma bayan.
Misali; An ɗauke min kuɗina amma daga bisani an dawo min da su.
ENG; Later (A turance tana nufin bisani)
Biscuit - A turance yana nufin biskit.
Misali; Biskit ɗin kamfanin NASCO yana da daɗi da inganci.
HAU; Biskit (Tana nufin abin ci na maramari da ake yi da fulawa da sikari da wasu sinadaran)