Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ƙidaya - Tana nufin lissafa abubuwa ɗaya bayan ɗaya domin sanin adadinsu. Misali: Malamin ya ce ɗalibai su ƙidaya littattafan da ke kan tebur. ENG: Count (A turance tana nufin ƙidaya)
Ƙididdiga - Ƙidayawa/Ƙirgawa domin  sanin haƘiƘanin yawa ko adadi na wani abu.
Ƙifce - Tana nufin rufe ido da buɗe shi cikin sauri, musamman saboda haske ko motsi. Misali: Jaririyar tana ƙifce ido saboda hasken rana ya yi mata ƙarfi. ENG: Blinking (A turance tana nufin ƙifce)
Ƙifil - Tana nufin wani magani ko haɗi da ake shafawa a ido domin jawo soyayya ko tasiri a kan wani. Misali: Wasu mutane sun yarda da cewa ƙifil na iya sa mutum ya ƙaunaci wani. ENG: Love portion smeared on the eye (A turance tana nufin ƙifil)
Ƙirare - Tana nufin ƙananan rassan itace da ake tattarawa domin amfani da su wajen kunna wuta. Misali: Yara sun je daji don samo tattara ƙirare. ENG: Twigs for firewood (A turance tana nufin ƙirare)
Ƙirga - Tana nufin lissafawa don sanin adadi. Misali: Malami ya ce yara su ƙirga daga ɗaya zuwa ashirin. ENG: Count up (A turance tana nufin ƙirga)
Ƙirgi -

Tana nufin sarrafaffiyar fatar saniya, da ake amfani da ita wajen yin takalma, jaka, ko sauran kayayyaki.

Misali: Akan yi amfani da ƙirgi wajen yin takalma masu ƙwari.

ENG: Tanned cowhide (A turance tana nufin ƙirgi)

Ƙiri - Tana nufin buɗe ido sosai saboda mamaki, tsoro, ko kulawa. Misali: Musa ya yi ƙiri da ido lokacin da ya ga abin mamaki. ENG: Being wide eyed (A turance tana nufin ƙiri)
Ƙirin - Tana nufin ƙarfafa ko bayyana baƙin launi sosai. Misali: Hadari ya haɗo, gari ya yi baƙi ƙirin. ENG: Emphasizes blackness (A turance tana nufin ƙirin).
Ƙiriniya - Tana nufin wasa ko ɗabi’ar yin shirme da rashin ji irin na ƙananan yara. Misali: Ƙiriniyar yara a cikin gida tana sa iyaye yawan yin magana. ENG: Playful mischievousness especially by children (A turance tana nufin ƙiriniya)
1 331 332 333 334 335 337