Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ƙaƙale -

Tana nufin mutum ya zama mai tsananin tsantseni ko zaɓi fiye da kima, har yana wahalar da kansa ko wasu wajen yin komai.

Misali; Yana ƙaƙale sosai wajen zaɓen abinci.

ENG; Being over-fastidious (A turance tana nufin ƙaƙale)

Ƙaƙƙautawa -

Tana nufin yin abu ba tare da tsayawa ba.

Misali; Ruwan sama yana zuba ba ƙaƙƙautawa tun safe har yamma.

ENG; Non stop (A turance tana nufin ƙaƙƙautawa)

Ƙa’ida -

Tana nufin dokoki ko tsarin da aka kafa domin tafiyar da al’amura cikin tsari.

Misali: Ma'aikatan suna aikinsu bisa ƙa'ida.

ENG: Regulation (A turance tana nufin ƙa’ida)

Ƙera - Tana nufin aikin sarrafa ƙarfe ko ƙirƙirar kayan aiki ta hanyar amfani da wuta da guduma. Misali: Maƙeri yana ƙera fartanya, wuƙa, da sauran kayayyakin noma. ENG: Forge (A turance tana nufin ƙera)
Ƙerere - Tana nufin tsayuwa ba tare da ladabi ko girmamawa ba. Misali: Yaron ya tsaya ƙerere a gaban manya ba tare da nuna ladabi ba. ENG: Stood disrespectfully (A turance tana nufin ƙerere)
Ƙeta - Tana nufin aikata wani mummunan abu da nufin cutarwa ko yin sharri ga wani. Misali: Ƙeta ce raba makaho da sandarsa. ENG: Malicious Act (A turance tana nufin Ƙeta)
Ƙetara - Tana nufin tsallake  hanya, kogi, ko wani wuri daga gefe ɗaya zuwa wani. Misali: Mutane suna ƙetara titi cikin kulawa don kauce wa haɗari. ENG: Cross (A turance tana nufin ketarewa ko tsallakawa).
Ƙeya - Tana nufin bayan wuya, wato sashen da ke tsakanin kai da kafaɗa. Misali: Mutumin ya ji ciwo a ƙeya bayan ɗaukar kaya masu nauyi. ENG: Nape of the neck (A turance tana nufin ƙeya)
Ƙi - Tana nufin rashin yarda da wani abu ko rashin amincewa da shi. Misali: Yaron ya ƙi cin abinci saboda ba ya jin daɗi. ENG: Refuse (A turance tana nufin ƙi)
Ƙiba - Tana nufin girma ko nauyin jiki. Misali: Ƙiba mai yawa na iya jawo matsaloli ga lafiya. ENG: Fatness (A turance tana nufin ƙiba)
1 330 331 332 333 334 337