Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Technology Incubation Centre (TIC) - Cibiyar Rainon Fasahar Ƙere ƙere Ta Ƙasa
Ten - A turance tana nufin goma.
Misali; Littattafai goma ne a cikin jakar.
HAU; Goma (Tana nufin lambar da ke bin bayan tara)
Tending animal at pasture - A turance tana nufin kiwo.
Misali; Sana'ar kiwo ta karɓi Malam Iro, garkensa sai haɓaka yake kullum.
HAU; Kiwo (Tana nufin ciyar da dabbobi kamar awaki da shanu da kaji da sauransu)
Termites - A turance tana nufin gara.
Misali; Gara ta cinye kujerun duk sun lalace.
HAU; Gara (Tana nufin ƙwaron da yake cinye katako)
Tertiary Education Trust Fund (TETFund) - Asusun Bunƙasa llimin Mayan Makarantu
Thanks - A turance tana nufin godiya.
Misali; Mun yi wa babanmu godiya ranar da ya siyo mana kayan salla.
HAU: Godiya (Tana nufin yabawa)
Kishiyarta; Rashin Godiya
The cult of spirit possession - A turance tana nufin bori.
Misali; 'Yan bori na gudanar da biki a duk ranar kasuwar garinmu.
HAU; Bori (Tana nufin addinin maguzanci na bautawa aljanu kafin zuwan addini musulunci)
The Public - A turance tana nufin jama'a.
Misali; Bikin ya tara jama'a daga sassan duniya daban-daban.
HAU; Jama'a (Tana nufin mutane da yawa)
The time just before - A turance tana nufin gabani.
Misali; Abin ya faru gabanin zuwan ta.
HAU; Gabani (Tana nufin lokaci da ya zo kafin wanda ake ciki)
Thick Forest - A turance tana nufin kurmi.
Misali; Jami'an tsaro sun kame ɓarayin da ke kurmi gaba ɗaya.
HAU; Kurmi (Tana nufin ƙungurmin daji)