Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Thursday - A turance tana nufin rana ta huɗu a mako.
Misali; Aisha tana azumi duk ranar Alhamis.
HAU; Alhamis (Rana ce ta huɗu a cikin ranakun mako).
Tickling - A turance tana nufin cakulkuli.
Misali; Sadiya tana yi wa ƙaninita cakulkuli yana dariya.
HAU: Cakulkuli (Tana nufin taɓa kwuiɓin mutum da zimmar sa shi dariya)
Tidy Up - A turance tana nufin kintsa.
Misali; Kar ki fita sai kin kintsa ɗakin tunda kin bari yara sun hargitsa shi.
HAU; Kintsa (Tana nufin tattara kaya guri ɗaya)
Tightly - A turance tana nufin ƙam-ƙam.
Misali; Ya kamata mu riƙe addini ƙam-ƙam domin inganta rayuwarmu.
HAU; Ƙam-ƙam (Tana nufin riƙe abu da ƙarfi)
Tilapia - A turance tana nufin karfasa.
Misali; Malam Idi yana soya karfasa ne bayan la'asar.
HAU; Karfasa (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'ikan kifi)
Time of the day - A turance tana nufin.
Misali; Da hantsi za mu je gidan adana namun daji.
HAU; Hantsi (Tana nufin lokacin da rana ta fito daga misalin ƙarfe bakwai zuwa sha ɗaya na safe)
Tiniest Amount - A turance tana nufin kan ƙuda.
Misali; In dai akwai ɗigon da ya kai kan ƙuda na shirka a zuciya, to ta ɓaci.
HAU; Kan ƙuda (Tana nufin ɗan ƙanƙani)
Tiredness - A turance tana nufin gajiya.
Misali; Gudu na sa gajiya sosai.
HAU; Gajiya (Tana nufin mutuwar jiki da jin rashin ƙarfi)
Tomorrow - A turance tana nufin gobe.
Misali; Gobe babu karatu saboda hutun ƙarshen mako.
HAU; Gobe (Tana nufin bayan kwana guda ma'ana ranar da za biyo bayan wacce ake ciki)
Kishiyarta; Yau
Tongue - A turance tana nufin harshe.
Misali; Ya tauna harshe yayin da yake cin abinci.
HAU; Harshe (Tana nufin gaɓar da ake magana da ita wadda take cikin baki)