Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Tail - A turance tana nufin jela. Misali; Jakin yana da doguwar jela. HAU; Jela (Tana nufin bindi)
Tail used as fly-switch - A turance tana nufin izga. Misali; Da izga yake amfani don kore ƙuda daga kan kayan sana'arsa. HAU; Izga (Tana nufin jela musamman ta doki da ake amfani da ita wajen korar ƙuda)
Take much of - A turance tana nufin kamfata. Misali; Idan ba ka zuba musu abincin ba kamfata za su yi. HAU; Kamfata (Tana nufin ɗiban abu da yawa)
Take shelter or refuge - A turance tana nufin fake. Misali; Lokacin da ruwan ya sakko a shagon na fake. HAU; Fake (Tana nufin samun mafaka)
Taking good care of something - A turance tana nufin haba-haba. Misali; Ana ta haba-haba da manyan baƙi. HAU; Haba-haba (Tana nufin ba da kulawa ka'in da na'in)
Talata - Rana ce ta biyu a cikin ranakun mako.  Misali; Ana cin kasuwar duk ranar Talata. ENG; Tuesday (A turance tana nufin rana ta biyu a mako)
Talkativeness - A turance tana nufin kauɗi. Misali; Lantana tana da kauɗi, maganar ta duk ta cika gidan. HAU; Kauɗi (Tana nufin yawan magana)
Tall - A turance tana nufin dogo. Misali;Na ga wani mutum dogo a ƙofar gida. HAU; Dogo (Tana nufin mai tsayi) Kishiyarta; Gajere
Tanyo - Taimakawa gajiyayye ko rarrauna cikin wani al'amari, tallafawa mara karfi ga biyan wata bukata.
Tarkacen Tarihi - Karikice na abubuwan amfani da suke tabbatar da tarihi da wanzuwar wata al'umma a wani wuri.
1 276 277 278 279 280 300