Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Sarcasm - A turance tana nufin gatse.
Misali; Ta yi musu gatse tace su faɗa wuta.
HAU; Gatse (Tana nufin a faɗi abu saɓanin abinda ake nufi)
Satan - A turance tana nufin sheɗan.
Misali; Allah ya raba mu da sharrin sheɗan.
HAU; Sheɗan (Tana nufin sheɗan)
Satchel - A turance tana nufin gafaka.
Misali; Malamin ya saka Al'ƙur'ani a gafaka.
HAU; Gafaka (Tana nufin jakar fata da ake yi musamman don saka littattafai)
Satumba - Wata ne na tara a shekara.
Misali; Sabon zangon karatuna farawa ne a watan Satumba.
ENG; September (A turance yana nufin wata na tara a shekara)
Saturday - A turance tana nufin rana ta shida a mako.
Misali; Ranar Asabar ne bikin.
HAU; Asabar (Rana ce ta shida a ranakun mako)
Sayings of prophet Muhammad SAW - A turance tana nufin Hadisi.
Misali;Malam Ado yana karanta mana hadisi kullum a makaranta.
HAU: Hadisi (Tana nufin maganganun manzon Allah SAW)
Scalp Disease - A turance tana nufin kora.
Misali; Yana da kora, idan ka sa hularsa za ka iya ɗauka kuma lalura ce mai wuyar sha'ani.
HAU; Kora (Tana nufin nau'in cutar fata da yake fitowa a kai)
Scheme - Shiri, Tsari
Science Teachers Association of Nigeria (STAN) - Ƙungiyar Malaman Kimiyya Ta Najeriya
Scorpion - A turance tana nufin kunama.
Misali; Kunama ce ta harbi Lado a ƙafa.
HAU; Kunama (Tana nufin ƙwaro mai cizo kuma mai dafi)