Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Run - A turance tana nufin gudu.
Misali; Idan ka yi gudu zuciyarka na harbawa da sauri.
HAU;Gudu (Tana nufin tafiya da ƙololuwar sauri)
Running short of something - A turance tana nufin cankacakare.
Misali; Kayan marmarin sun zama cankacakare.
HAU; Cankakare (Tana nufin ƙarewar abu ƙarƙaf)
Rural Area - A turance tana nufin karkara.
Misali; Mutanen karkara suna da karamci matuƙa.
HAU; Karkara (Tana nufin ƙauye)
Rural Electrification Agency (REA) - Hukumar Raya Karkara da Wutar Lantarki
safiyo - Awo ne na zubin kasar da za a gina a matsayin gari ko mahalli.
Salary/Wage - A turance yana nufin albashi.
Misali; An biya ma'akata albashi yau da safe.
HAU; Albashi (Yana nufin kuɗi da ake biyan mutum sakamakon aikin da ya yi a wata ko sati)
Sallah - Sallah wata nau'in ibace da mutane musulmai suke gabatar da ita a matsayin bauta ga Allah da yayi halitta.
Jam'i ; Salloli
Salt - A turance tana nufin gishiri.
Misali; Kirarinsa shi ne: Gishiri in ba kai ba miya.
HAU: Gishiri (Tana nufin sinadarin da ke ba wa abinci ɗanɗano)
Saluting a superior - A turance tana nufin jinjina.
Misali; Shugaban sojojin yana shigowa ɗakin taron aka yi masa jinjina.
HAU; Jinjina (Tana nufin gaisuwar ban-girma)
Sand Lice - A turance tana nufin kurkudu.
Misali; Yaran sun kamo kurkudu a lokacin da suke wasa.
HAU; Kurkudu (Tana nufin wani ƙwaro da yake fitowa a cikin rairayi)