Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Seeking Devine Counsel - A turance tana nufin istihara. Misali; Ya kamata ki yi istihara a tsakanin masu neman auren ki. HAU; Istihara (Tana nufin neman zaɓin Allah)
Senate of Nigeria - Majalisar Dattawan Najeriya
Senior Staff Association of Electrical & Allied Companies (SSAEAC) - Ƙungiyar Manyan Ma'aikatan Kamfanonin Kayan Lantarki
Senior Staff Association of Nigerian Polytechnics (SSANIP) - Ƙungiyar Manyan Ma'aikatan Makarantun Fasaha Ta Najeriya
Senior Staff Association of Nigerian Universities (SSANU) - Ƙungiyar Manyan Ma'aikatan Jami'o'in Najeriya
Senior Staff Union of Colleges of Education in Nigeria (SSUCOEN) - Ƙungiyar Manyan Malaman Kwalejojin llimi Ta Najeriya
Sense - A turance tana nufin hankali. Misali; Idris yana da hankali da sanin ya kamata. HAU; Hankali (Tana nufin sanin ya kamata) Kishiyarta: Rashin Hankali
September - A turance yana nufin wata na tara a shekara.  Misali; Sabon zangon karatuna farawa ne a watan Satumba. HAU; Satumba (Wata ne na tara a shekara)  
Sermon - A turance tana nufin huɗuba. Misali; Muna sauraron huɗuba daga masallaci mai alfarma a rediyo. HAU; Huɗuba (Tana nufin jawabai na hikima da jan hankali don faɗakarwa ko kwaɗaitarwa a kan binn Allah da kuma gujewa saɓa masa)
Servant - A turance tana nufin bara. Misali; Idris bara ne a gidan Alhaji Sani. HAU; Bara (Tana nufin mai yin hidima a cikin gida)
1 263 264 265 266 267 300