Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Often - A turance tana nufin jefi-jefi.
Misali; Yana zuwa gaishe da kakarsa jefi-jefi.
HAU; Jefi-jefi (Tana nufin ba kodayaushe ba)
Kishiyarta; A kai-a kai
Oil Mineral Producing Areas Development Commission (OMPADEC) - Hukumar Raya Yankuna Masu Arzikin Man Fetur
Okra - A turance tana nufin kuɓewa.
Misali; Tuwon Shinkafa da miyar kuɓewa muka ci yau da safe.
HAU; Kuɓewa (Tana nufin ɗaya daga cikin tsirrai da ake shukawa a lambu, ana amfani da ita don yin miya da magani da sauransu)
Oktoba - Wata ne na goma a shekara.
Misali; Najeriya ta samu 'yanci a ranar ɗaya ga watan Oktoba 1960.
ENG; October (A turance yana nufin wata na goma a shekara)
Old Woman - A turance tana nufin gyatuma.
Misali; Na ga gyatumarka a bikin gidanmu.
HAU; Gyatuma (Tana nufin tsohuwar mace)
Kishiyarta; Gyatumi
Olden Times - A turance tana nufin gargajiya.
Misali; Sarakunan gargajiya na da karamci.
HAU; Gargajiya (Tana nufin abubuwan da ake yi tun asali ko tun iyaye da kakanni)
Kishiyarta; Zamani (Yanzu)
On top/above - A turance tana nufin bisa.
Misali; Littattafan na bisa teburi.
Kishiyarta; Ƙarƙashin
HAU; Bisa (Tana nufin a kan wani abu)
One - A turance tana nufin guda.
Misali; Gida guda za mu zauna da ƙani na.
HAU; Guda (Tana nufin ɗaya)
One after the other - A turance tana nufin bi da bi.
Misali; Likitan yana duba marasa lafiyan bi da bi.
HAU; Bi da bi (Tana nufin ɗaya bayan ɗaya)
One of the sixty sections into which the Qur’an is divided - A turance tana nufin izifi.
Misali; Abdallah ya haddace izifi biyu a watan da ya gabata.
HAU; Izifi (Tana nufin ɗaya daga cikin kaso sittin na Ƙur'ani)