Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Non Academic Staff Union (NASU) - Ƙungiyar Ma'aikatan Manyan Makarantu/Jami'o'i
Non Atlantic Treaty Organization (NATO) - Ƙungiyar Ƙasashe Masu Kishi da Gurguzu
Non-Muslim - A turance tana nufin kafiri.
Misali; Duk wanda ya yi sallah ba tare da alwala ba kafiri ne.
HAU; Kafiri (Tana nufin wanda ba musulmi ba)
Nonrth-East Develoment Commission (NEDC) - Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas
Northern Elders Forum (NEF) - Ƙungiyar Dattawan Arewa
Northern Nigeria Development Company (NNDC) - Ma'aikatar Bunƙasa Arewacen Najeriya
Northern States Governors Forum (NSGF) - Ƙungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya
Nose - A turance tana nufin hanci.
Misali; Ƙurji ya fito mata a saman hanci mai ɗan karen ciwo.
HAU; Hanci (Tana nufin gaɓar da ake numfashi wadda take a saman baki)
Nose-bleed - A turance tana nufin haɓo.
Misali; Tun safe yake haɓo, ko za a kai shi asibiti ne?
HAU; Haɓo (Tana nufin zubar jini daga hanci)
November - A turance yana nufin wata na goma sha ɗaya.
Misali; Watan Nuwamba yana da kwana talatin a kowacce shekara.
HAU; Nuwamba (Wata ne na goma sha ɗaya a shekara)