Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
One Thousand - A turance tana nufin dubu.
Misali; Ya ba ni Naira dubu da ya zo duba ni a asibiti.
HAU: Dubu (Tana nufin lambar da ke bin bayan ɗari tara da casa'in da tara)
Oneness - A turance tana nufin kaɗaita.
Misali; Wajibi ne a kaɗaita Allah a wajen bauta.
HAU; Kaɗaita (Tana nufin ɗayantawa ba tare da abokin tarayya ba musamman ga Allah SWT)
Only - A turance tana nufin kawai.
Misali; Kuɓewa kawai na siyo da na je kasuwa.
HAU; Kawai (Tana nufin kaɗai)
Only - A turance tana nufin kurum.
Misali; Kwano ɗaya kurum ta isa kowa ya ƙoshi.
HAU; Kurum (Tana nufin kawai)
Only - A turance tana nufin kaɗai.
Misali; Ita kaɗai ce take zuwa da wuri kullum.
HAU; Kaɗai (Tana nufin kawai)
Open space in front of compound - A turance tana nufin farfajiya.
Misali; A farfajiyar gidan za a yi taron bikin.
HAU; Farfajiya (Tana nufin filin tsakar gida)
Open Space/Arena - A turance tana nufin fage.
Misali; An ba wa 'yan dambe fage don su fafata.
HAU; Fage (Tana nufin fili ko dandali)
Open-ended variable tone drum which is beaten with fingers - A turance tana nufin kotso.
Misali; Ya daɗe yana kaɗa kotso a ƙauyensu.
HAU; Kotso (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kiɗan Hausawa)
Opportunity - A turance tana nufin faraga.
Misali; Mun samu faraga mun yi abubuwan alkhairi da yawa.
HAU; Faraga (Tana nufin samun dama)
Orange-headed male lizard - A turance tana nufin jan-gwada.
Misali; Jan-gwada ne ya hana sauran ƙadangarun cin abinci.
HAU; Jan-gwada (Tana nufin namijin ƙadangare)