Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Tanyo - Taimakawa gajiyayye ko rarrauna cikin wani al'amari, tallafawa mara karfi ga biyan wata bukata.
Tarkacen Tarihi - Karikice na abubuwan amfani da suke tabbatar da tarihi da wanzuwar wata al'umma a wani wuri.
Tasarrufi - Samarwa da juyawa ko sarrafa abu yadda ya kamata domin amfana da abin.
Taskance - Adana adadin mutane ko ma'aikatun da aka yi wa rijista karkashin wata hukuma.
Taurari - Jam'in tauraro, fitattun mutane musamman 'yankwalisa da 'yanwasa da 'yanfim da sauran mutanen da suka shahara.
Taureg - A turance tana nufin buzu.
Misali; Mai gadin gidan buzu ne, yana tare da su tsawon shekara arba'in.
HAU; Buzu (Tana nufin mazaunin ƙasashen da ke sahara kamar Niger, Mali, Algeriya da sauransu)
Tawaga - Ayari na mutane da suke nufin zuwa wani wuri domin cimma wata manufa ko aiwatar da wani aiki.
Tax - A turance tana nufin haraji.
Misali; An tsaurara hukunci a kan masu ƙin biyan haraji a lardinmu.
HAU; Haraji (Tana nufin kuɗin da al'umma ke biya ga shugabanni wanda ake amfani da su don aiwatar da ayyukan more rayuwa)
Teachres Registration Council of Nigeria (TRCN) - Hukumar Malaman Makaranta Ta Najeriya
Teburi - Teburi wani kayan aiki ne wanda ake amfani dashi wajen rubutu ko kuma ajiye kaya akai musamman a makaranta ko kuma a gida don yin amfani.
Jam'i ; Tebura