Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Sufuri - Aiki ko sana'ar jigilar mutane daga wani wuri zuwa wani a mota ko jirgi.
Sum/Total - A turance yana nufin adadi.
Misali; Kirkin Malam ba shi da adadi.
HAU; Adadi (Yana nufin yawan abu)
Sunday - A turance tana nufin rana ta ƙarshe a mako.
Misali; A kan ɗaura aure a ranar Lahadi.
HAU; Lahadi (Ranar ƙarshe a mako)
Superabundance - A turance tana nufin ɗimbi.
Misali; Muna miƙa godiya mai ɗimbin yawa ga waɗanda suka samu damar zuwa taron buɗe kamfaninmu.
HAU; Ɗimbi (Tana nufin da yawa)
Superior Person - A turance tana nufin fiyayye.
Misali; Manzon Allah S.A.W shi ne fiyayyen halitta.
HAU; Fiyayye (Tana nufin wanda ya ɗara kowa (Annabi Muhammad S.A.w))
Superstition - A turance tana nufin camfi.
Misali; Mutanen da sun yadda da camfi sosai.
HAU; Camfi (Tana nufin yadda da maganganu marasa tushe)
Surround - A turance tana nufin gewaye.
Misali; Ya gewaye gonarsa da kara saboda gudun dabbobi.
HAU; Gewaye (Tana nufi yi wa abu ƙawanya)
Surveyors Council of Nigeria (SURCON) - Hukumar Safiyo Ta Najeriya
Swallow - A turance tana nufin haɗiye.
Misali; Ya haɗiye alawar da na ba shi.
HAU; Haɗiye (Tana nufin cinyewa, ko shigar abu cikin ciki ta hanyar maƙogwaro)
Kishiyarta; Amayar
Sweat - A turance tana nufin gumi.
Misali; Yau ana zafi kowa ka gani gumi yake.
HAU; Gumi (Tana nufin ruwan da yake tsattsafowa a jikin mutum ta saman fata musamman idan yana jin zafi ko ya yi gudu)