Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Technology Incubation Centre (TIC) - Cibiyar Rainon Fasahar Ƙere ƙere Ta Ƙasa
Ten - A turance tana nufin goma.
Misali; Littattafai goma ne a cikin jakar.
HAU; Goma (Tana nufin lambar da ke bin bayan tara)
Termites - A turance tana nufin gara.
Misali; Gara ta cinye kujerun duk sun lalace.
HAU; Gara (Tana nufin ƙwaron da yake cinye katako)
Tertiary Education Trust Fund (TETFund) - Asusun Bunƙasa llimin Mayan Makarantu
Thanks - A turance tana nufin godiya.
Misali; Mun yi wa babanmu godiya ranar da ya siyo mana kayan salla.
HAU: Godiya (Tana nufin yabawa)
Kishiyarta; Rashin Godiya
The cult of spirit possession - A turance tana nufin bori.
Misali; 'Yan bori na gudanar da biki a duk ranar kasuwar garinmu.
HAU; Bori (Tana nufin addinin maguzanci na bautawa aljanu kafin zuwan addini musulunci)
The time just before - A turance tana nufin gabani.
Misali; Abin ya faru gabanin zuwan ta.
HAU; Gabani (Tana nufin lokaci da ya zo kafin wanda ake ciki)
Thief - A turance tana nufin ɓarawo.
Misali;An kama ɓarawo a gidan Alhaji Iro jiya da daddare.
HAU; Ɓarawo (Tana nufin mutumin da yake sata)
Thin and Flimsy - A turance tana nufin fale-fale.
Misali; Yadin da aka ba mu fale-fale ne ba shi da kauri.
HAU; Fale-fale (Tana nufin abu mara nauyi ko kauri)
Things done or said intentionally - A turance tana nufin gayya.
Misali; Da gayya ta yi mata magana don su yi faɗa.
HAU: Gayya (Tana nufin da gangan ko ana sane)