Barkan mu da sake kasancewa a fannin girke-girkenmu na WikiHausa. A yau za mu koyi yadda ake tuwon masara.
Masara na ɗaya daga cikin abincin Bahaushe, Wanda ake iya sarrafa ta ta hanyoyi da dama. Ta kasance abinci mai gina jiki da kuma ƙara lafiya. Masara na ɗauke da sinadaran daban-daban.
Abubuwan da ake buƙata:
-
Masara
-
Ruwa.
Yadda ake haɗawa:
-
Ki tafasa ruwa, ki kawo garin ki, kamar kimanin kashi ɗaya cikin uku na garin.
-
Sai ki zuba masa ruwan sanyi ki juya, wannan shi ne rude.
-
Sannan kuma ki zuba cikin wannan tafashasshen ruwan ki juya.
-
ki bar shi ya dahu na kimanin mintuna sha biyar, sai ki tuƙa shi da sauran garin nan.