Tag: Abincin gargajiya

  • Yadda Ake Groundnut Sweet Potato Balls.

    Yadda Ake Groundnut Sweet Potato Balls.

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa wanda muke koyarda ƙayatattun abinci namu na gida Najeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe tare da ni Hafsat Shettimah. A yau za mu koyar da yadda ake yin groundnut sweet potato balls (groundnut cake) ku biyo ni a sannu domin mu koya tare……

    Ko kun san groundnut sweet potato balls na da saurin narkewa a jikin ɗan Adam. Hakan yasa ya zama abinci mai kyau wurin yara da tsofaffi.

    Abubuwan Buƙata

    1. Soyayyar gyada ¼ cup
    2. Dankalin Hausa matsakaita
    3. Albasa a yanka Ƙanana ko a jajjaga
    4. Curry ½ tablespoon
    5. Markaɗaɗɗen nama
    6. Sinadarin ɗanɗano
    7. Attaruhu guda biyar jajjagge
    8. Tafarnuwa
    9. Breadcrumbs 1 cup
    10. Kwai 3 (a fasa a kaɗa shi)
    11. Man gyaɗa na suya

    Yadda ake haɗawa

    1. A cikin kwano mai kyau a zuba dafaffen dankali, sai a farfasa su, su fasu da kyau.
    2. Sannan a zuba albasa, attaruhu, tafarnuwa, sinadarin ɗanɗano, curry, thyme da nama a juya a hankali
    3. A samu dan faranti a ringa ɗiban dankalin ana cura kamar ball ana ajiye
    4. A tsoma wannan ball cikin ƙwai sai a saka shi cikin bread crumbs a juya sai a saka cikin mai me zafi idan ya soyu a kwashe. Bon apetite

    Domin koyon  Yadda Ake Groundnut Sweet potato Pie  danna nan.

  • Yadda Ake Moi-Moi Na Musamman

    Yadda Ake Moi-Moi Na Musamman

    Moi moi wadda muka fi sani da alala a Hausance ana yinta ne daga wake, alala ta kasance ɗaya daga cikin abincin gargajiya na bahaushe.

    Abubuwan da ake buƙata

    1. Wake
    2. Taruhu da tattasai
    3. Albasa
    4. Maggi
    5. Tafarnuwa
    6. Manja
    7. Sausage
    8. Ƙwai
    9. Karas

    Yadda ake haɗawa

    1. Da farko za ki wanke wake a surfa, sai a zuba taruhu da tattasai da albasa a niƙa shi ya yi laushi sosai.
    2. Sannan a zuba wannan haɗin a cikin bowl a sa manja, maggi, tafarnuwa, da curry, za a iya saka cray fish ma, a juya shi sosai komai ya haɗe.
    3. A saka mai kaɗan a kan kaskon, a sa sausage da karas a yi stir frying nasu, sai a sauke. A dafa ƙwai a ɓare shi a yanka slices. Shi ma a aje a gefe.
    4. Za a kunna oven 180° sai a ɗauko parchment paper a shimfiɗa ta a kan faranti na gashi, a zuba ƙullun a saka a oven.
    5. Bayan mintina 10 in ya fara yi, sai a sauko da shi a zuba fillings ko’ina, a mayar ya gama gasuwa.
    6. Idan ya yi, za a ji ƙamshin ya haɗe ko’ina a sa toothpick a duba.
    7. Don a tabbatar ya dahu, a sauke a naɗe kaman naɗin tabarma.

    A ɗan bari ya huce sai ki yanka. A ci lafiya.

    Domin sanin Yadda Ake Zobo Na Cucumba dannan nan.

  • Yadda Ake Dafaffiyar Gyaɗa

    Yadda Ake Dafaffiyar Gyaɗa

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa, wanda muke koyar da ƙayatattun abincinmu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah.

    A yau za mu koyar da yadda ake yin dafaffiyar gyaɗa. Ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.

    Ko kun san dafaffiyar gyaɗa tana da sinadarai masu gina jiki, sannan kuma tana da ƙarancin calories wato kitse fiye da soyayyiyar gyada.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    1. Gyaɗa mai ɓawo
    2. Ruwa

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A tsince gyaɗa, a gyara ta tsaf.
    2. Sai a zuba ruwa da gyaɗa cikin tukunya mai zurfi a rufe.
    3. A dafa shi na kimanin awa uku (3) sai a tace.

    Domin karanta Yadda Ake Gyaɗa Marau-marau ko Yadda Ake Soyayyiyar Gyaɗa Mai Gishiri danna koren rubutun nan.

  • Yadda Ake Gyaɗa Marau-marau

    Yadda Ake Gyaɗa Marau-marau

    Barkan mu da sake kasancewa a cikin shirinmu na GIRKE-GIRKEN WikiHausa, wanda muke koyar da ƙayatattun abinci namu na gida Nijeriya da kuma na ƙetare, tare da bayani a kan lafiyarsu cikin harshen Hausa a sauƙaƙe. Tare da ni Hafsat Shettimah.

    A yau za mu koyar da yadda ake yin gyaɗa marau-marau. Ku biyo ni a sannu domin mu koya tare.

    Ko kun san gyaɗa mai ɓawo ta fi bayar da kariya daga sinadarin (Aflotoxin), mai sanya cutar daji wato (cancer) a jikin ɗan Adam.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    1. Gyaɗa mai ɓawo
    2. Gishiri
    3. Toka
    4. Ruwa
    5. Ƙasar yashi ko toka

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A tsince dattin da gyaɗa ko mara kyau sannan a wanke ta fita.
    2. A zuba gyaɗa da gishiri cikin ruwa a dafa, kamar na munti 5-6. Sai a tace.
    3. A ɗora tukunya mai zurfi, idan toka ta ɗau zafi sai a saka wannan dafaffiyar gyaɗar a yi ta juyawa har sai ta yi.
    4. Idan ta yi, sai a juye domin shan iska.

    Domin koyar Yadda Ake Soyayyiyar Gyaɗa Mai Gishiri danna koren rubutun nan.

  • Yadda Ake Tuwon Shinkafa

    Yadda Ake Tuwon Shinkafa

    A yau za mu koyi yadda ake tuwon shinkafa.

    Tuwon shinkafa abinci ne da ake yin sa da shinkafa, wanda ya kasance abincin gargajiya na Bahaushe, wanda yake daɗi musamman ma idan aka tuƙa shi sosai.

    Abubuwan da ake buƙata:
    1-shinkafa ta tuwo(fara).
    2-ruwa.

    Yadda ake haɗawa

    • A wanke shinka fara, a zuba mata ruwa daidai wanda za ta shanye.
    • Sai a bar ta ta dahu, har sai ta shanye ruwan duka. Ta yi laushi sosai.
    • Sannan a tuƙa da muciya sosai. a mai da shi kan wuta, ya turara na ɗan wani lokaci, a sauke a malmala.
    Karin bayani.
    Idan ruwan ya yi kaɗan, kada a ƙara na sanyi. a sauke a ɗora wani ruwan, in ya tafasa, sai a ƙara a kai, a bar shi ya ɗan ƙara haɗuwa ko sannan a tuƙa.

    domin karanta yadda ake tuwon masara danna nan

  • Yadda ake Danbun Shinkafa

    Yadda ake Danbun Shinkafa

    Abubuwan da ake buƙata a wajen haɗa danbun shinkafa ba su da yawa sosai, kuma abinci ne mai daɗin gaske musamaman a ce an kula wajen tsafta a lokacin da ake yin sa.

    Abubuwan buƙata:

    1. Shinkafa
    2. Zogale
    3. Gyaɗa
    4. Attaruhu
    5. Albasa
    6. Mai
    7. Spices.

    Yadda ake haɗawa:

    Za ki kai shinkafarki(ba ta tuwo ba)a ɓarza miki a inji, sai ki tankaɗe, idan kuma ba gari sai ki turara ta, ki ajiye. zogalen ma ki turara shi ko ki dafa, sai ki daka gyaɗa kar tai laushi, attaruhunki ma haka, ki yanka albasa, sai ki haɗe su cikin shinkafarki, ki juya har su haɗe kisa maggi da spices ɗinki da mai kaɗan, saboda kar ya dunƙule. Sai ki maida, ki sake turarawa, idan ya dahu, za ki ji ƙamshi, sai ki sauke ,shi kenan. A ci daɗi lafiya.

    Domin karanta yadda ake barabusku ko yadda ake tuwon masara danna koren rubutu

  • Yadda Ake Sakwara A Sauƙaƙe

    Yadda Ake Sakwara A Sauƙaƙe

    A yau za mu koyi yadda ake sakwara a sauƙaƙe.

    Sakwara abinci ne da ya samo asali  daga doya, doya na ɗaya daga cikin abincin da ke gina jiki.  Sakwara ta kasance mai daɗi, tana ɗauke da fibre da (starch) a  wanda ke ƙarawa jikin ɗan Adam kuzari.

    Abubuwan da ake buƙata:

    • Doya
    • Ruwan zafi

    Yadda ake haɗawa

    1.  A fere doya a yanka ta ƙanana, ki zuba ruwa kaɗan blending ɗinta,
    2.  Idan ta nuƙu sosai a ɗaura ta a kan wuta, tana dahuwa ana juya ta tare da muciya,
    3.  Har sai ta janye ruwan jikin ta, ta yi kamar tuwo, sai a ƙara ruwan zafi kaɗan a kuma tuƙawa.

    Domin karanta yadda ake Biredin kwakwa ko yadda ake tuwon masara

  • Yadda Ake Tuwon Masara

    Yadda Ake Tuwon Masara

    Barkan mu da sake kasancewa a fannin girke-girkenmu na WikiHausa. A yau za mu koyi yadda ake tuwon masara.

    Masara na ɗaya daga cikin abincin Bahaushe, Wanda ake iya sarrafa ta ta hanyoyi da dama. Ta kasance abinci mai gina jiki da kuma ƙara lafiya. Masara na ɗauke da sinadaran daban-daban.

    Abubuwan da ake buƙata:

    • Masara
    • Ruwa.

    Yadda ake haɗawa:

    • Ki tafasa ruwa, ki kawo garin ki, kamar kimanin kashi ɗaya cikin uku na garin.
    • Sai ki zuba masa ruwan sanyi  ki juya, wannan shi ne rude.
    • Sannan kuma ki zuba cikin wannan tafashasshen ruwan ki juya.
    • ki bar shi ya dahu na kimanin mintuna sha biyar, sai ki tuƙa shi da sauran garin nan.