1. KWARIN GWIWA
Idan ya kasance bakida ƙarfin zuciya gwiwa akan kanki ƙarfin zuciya hakan zaisa ki zama bakya birge mijinki.Kuma zai hanaki samun jituwa da kyautata mu’amala ki dinga faɗawa kanki cewa ke kyakkyawa ce,kina da kyakkyawan ɗabi’u. Kuma mijinki na sonkine saboda halayyarki masu kyau.
2.KULA DA KANKI
Kulawa bawai ta wanka da kwalliya ba a’a ki ɗauki al’amuran da ya shafi yadda kike ji a zuciyarki da muhimmanci,farin ciki ko bakinciki saboda a duk lokacin da mijinki ya ɓata miki bazai sa alaƙarku ta lalace ba Kuma yana da kyau ki rage ɗaurawa kanki laifi akan komai.Hakan na da wahala amma idan kina samun lokaci da ‘yan uwanki ko kawayenki ko kuma kina iya koyon wasu abubuwan sababbi,da kuma wasu abubuwan da kikesonyi kamar zane,rubutu ko karance-karance.
Domin karanta Waya Kamata In Bayyana Wa Sirrina Idan Na Fara Al’ada Danna nan
3.TARAYYA
karki ɗau mijinki ba abakin komai ba,ki nuna masa muhimmanci da girmansa a rayuwarki.Ki samar masa da lokaci acikin ranakun aiki da zakina tattauna abubuwan da suke faruwa daku. Ko ki dinga tura masa saƙo ko kiran waya sau ɗaya ko sau biyu wanda zai nuna masa cewa kina tare dashi kuma kina tunaninsa a ranki.
4.NEMAN TAIMAKO AKAN AIKIN GIDA
Yana da matuƙar wahala kula da miji da kuma larurar gida musamman idan kina da yara.Hakan zaisa ki gaji Kuma ki kasa samun lokacinkanki. Zaki iya samun sauƙin abubuwan ta hanyoyi kamar haka:
Nuna masa yadda ake aikace-aikacen gida da kula da yara,
samun Mai kula da Yara ko kuma mai gyaran gida.
Domin karanta Yadda ‘Yan Mata Ya Kamata Su Kula Da Jikinsu Daga Lokacin Balaga Danna nan