Yogurt na ɗaya daga cikin abin sha mai lafiya kuma mai matuƙar amfani a jikin ɗan Adam.
Abubuwan da ake buƙata
- Madarar gari
- Ruwa
- Nono
- Filebo
Yadda ake haɗawa
- A ɗora ruwa a kan wuta ya tafasa
- Sai ki zuba madarar gari a kwano daban, ki zuba mata ruwa ki kwaɓata
- Sai ki juye a kan tafashasshen ruwan dake kan wuta
- A bar shi ya yi kamar minti biyar a kan wutar yana tafasa
- Sanna a sauke a bar shi ya dan sha iska, sai a zuba nono cokali biyu a kai, amma kar a juya.
- A bar shi ya yi awa takwas a ajiye.
Domin karanta yadda ake danbun shinkafa ko yadda ake kunun zaki