A yau za mu koyi YADDA AKE OMO, Omo na ɗaya daga cikin abubuwan amfanin gida na yau da kullum, wanda ke da matuƙar amfani, haɗa omo na da sauƙi da kuma samun sauki a yin sa, musamman ma idan aka bi ka’idojin sa
Abubuwan da ake buƙata
Safar hannu
Flavour
Kala
Taxapon kilo 1
Soda ( Ash light) kwano 1.
Yadda ake haɗawa
- A samu Roba a juye Taxapon kilo 1 da Soda kwano 1.
- Sai ki sa safar hannu, ki haɗe su ki yi ta juyawa.
- Ki ci gaba da murzawa, har sai ya zama gari luƙui.
- Sai ki sa flavour ƙamshin da ki ke so.