A yau za mu koyi yadda ake mashe.
Mashe abinci ne mai kama da masa, amma ya fi masar ƙanƙanta; sannan abubuwan da ake amfani da su wajen sarrafa shi daban yake da na masa, ko waina.
An fi cin wannan irin abincin ne a Ƙasar Hausa, domin karyawa da safe. Sannan mafi yawanci, sun fi son cin sa da yajin ƙuli-ƙuli ko kuma yajin barkono.
Abubuwan Da Ake Buƙata
- Garin gero
- Man gyaɗa
- Magi
- Yis
- Fulawa
- Gishiri
- Ƙuli/yaji
Yadda Ake Haɗawa
- A samu gero sannan a wanke a cire tsakuwa a busar, sannan a niƙa ba tare da an saka kayan ƙamshi ba, ko kayan yaji.
- Bayan haka, sai a tankaɗe wannan garin, sannan a sa a roba, sai a samu garin fulawa a zuba a ciki, a gauraya su garayu sosai.
- A ɗumama ruwa sannan a zuba yis a ciki idan ya ɗan tashi,
- Sai a zuba a cikin haɗin garin gero da fulawa.
- A samu ruwa ana zubawa ana kwaɓa haɗin har sai ya yi kauri kaɗan. Hadin ya kasance ba mai kauri sosai ba sannan a rufe a sanya a rana har sai kullun ya tashi.
- Sannan a ɗora tukunyar tuya a wuta, a zuba man gyaɗa da albasa su soyu. Sai a dauko ƙullun ana yankawa da ludayi ko cokali daidai girman da ake so ana soyawa kamar yadda ake tuyar fanke sannan a kwashe.
- A samu yajin ƙuli mai ɗauke da magi a ci da shi ko kuma yaji mai ɗauke da magi ana ɗangwalawa ana ci.
Domin sanin Yadda Masar Dankali danna nan.