Abubuwan da ake buƙata
- Farar shinkafa
- Tuwo/dafaffiyar shinkafa
- Yeast
- Sugar
Yadda ake haɗawa
1. Za ki gyara, ki jiƙa shinkafa kamar na awa ɗaya haka.
2. Sai ki kawo tuwon ko shinkafa daffafiya ki zuba ciki, ki sa yeast ki niƙa (amfi son niƙan gida).
3. Sai ki ƙara yeast rabin cokali.
4. Kar ya yi ruwa kar kuma ya yi kauri sosai.
5. Ki rufe ki ajiye wuri mai ɗumi.
6. Bayan mintuna talatin (30 minutes) zai tashi ya dawo kamar kumfa, sai ki dora nonstick frying pan a wuta ki shafa mai, ki rinƙa zuba ƙullun, ki na rufewa.
7. Da ya dahu za ki ga ya yi holes (ramuka), haka za ki yi har ki gama.
Ku karanta Yadda ake ƙosai mai laushi